mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

ta yaya zan magance matsalolin istimna'i a > tattare dani?

Assalamu Alaikum mallam tayaya zan magance matsalolin istimna'i a
tattare dani?

 

 

da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Salamu Alaikum.

ka ji tsoran Allah ka ji tsoran shiga wutar jahannama, duk mutumin da ya yi yakini da cewa istimna'i yana jawo shiga wuta sannan kuma ita wuat gaskiya ce ta yaya zai yi gangancin aikata istimna'i?!.

haka kuma duk wanda ya kasance yana ganin Allah yana ganinsa yana kuma yakini da sani cewa doin yana ganinsa ta yaya zai saba masa, saboda haka kaji tsoran Allah cikin dukkanin lokacin kadaituwarka lallai ubangiji shine na biyunka da yake tareda kai, yanzu ka kaddara cewa da ace akwai wani yaro karami a gabanka shin don Allah zaka aikata istimna'i a gaban wannan yaron? ko kuma da zaka ji tsoran tonuwar asirinka da tsoran kada ya yada labarionb abinda ka aikata, shin yanzu kafi tsoran ganin yaro fiye da ganin ubangijinka, ina kiranka ina kiranka ina yi maka nasiha da kaji tsoran Allah ka so Allah da manzonsa da iyalan manzonsa, kayi fatan Allah ya tashi ku tare a ranar kiyama, ka sani duk wanda yake aikata istimna'i ba za a tashe shi tareda su ba.

ka tuba dga wannan mummunar dabi'a ka koma ga Allah da manzonsa da kur'ani da Ahlil baiti (as)

gurin Allah muke neman taimako.

Tarihi: [2019/7/28]     Ziyara: [156]

Tura tambaya