mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

MENENE ALAMONIN BAYYANAR IMAMUL HUJJA A.S

Ina son Akaramakallahu yayi mini bayani filla-filla dangane da alamomin bayyanar shugabanmu Alhujja (a.s) sannan wanne abubuwa ne alamomin da suka afku zuwa yanzu atakaice, da alamar bayyanar hannu a bayyane a sararin samaniya shin zai kasance an ganshi karara ba tareda fasahar zamani ba, wannan itce tambaya sakamakon hotunan da ake iya dauka da fasahar telescope wanda cigaban zamani ya zo da su sannan ba zai iya yiwuwa a kalli wannan hannu ba da kwayar idanu.
Ko malam zai iya yi mana Karin bayani shin yana ishara daga abinda ake nufi daga bayanin da ya zo a riwaya cikin bayyanar shugabanmu ko kuma dai ba haka lamarin yake ba?

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Ka sani Allah ya taimake ka su alamomin bayyanar Imamul Hujja (a.s) suna da yawan gaske suna sun daban-daban sai dai cewa zamu yi bayani kan wanda suka fi shahara daga cikinsu daga ciki akwai: husufi a birnin Bagdaza da birnin Basara da alkarya mai suna Jabiyatu da take birnin Sham, da kuma wata wuta da zata bayyana a gabashin sararin samaniya ta wanzu har tsahon kwanaki bakwai a jere da kuma wata wuta da zata bayyana a Azerbaijan, da kuma wata rusa a Sham, da dagawar bakar iska daga farkon rana da girgizar kasa har ta kai ga da mafi yawa daga gareta ya kisfe, da kuma sassabawar sinfi biyu daga ajamawa da zubar da jini tsakaninsu, da kuma galaba bayi kan kasar Sham da kira daga samaniya da mutanen kasa za su ji shi tareda dukkanin banbanci yarukansu sannan za a kira sunansa da sunan mahaifinsa, sannan fuska da kirji zasu bayyana ga mutane cikin idanun rana, sannan za ayi ruwa tsahon kwanaki 24 a jere a cikin watan Jimada Akar da kuma kwanaki goma cikin watan Rajab sai kasa ta zama ta rayu bayan mutuwar ta albarkokinta su bayyana dukkanin wata musiba ta kauce daga cikin musibu akwai kauracewa masallatai, daga alamomin akwai bayyanar tuta a gabas da tuta a yamma. Da wata fitina da zata wanzu, daga ciki akwai bayyanar wani mutum daga `ya`yan Ziadu daga Kasar Yaman, daga ciki akwai daga wawa kan lullubin da rufe Ka’aba da sace shi, da wasu daga alamomi.

Tarihi: [2019/9/15]     Ziyara: [129]

Tura tambaya