mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

MECECE NASIHARKU DOMIN KUBUTA DAGA HASSADA DA TAKE BOYE A CIKIN ZUCIYA

Salamu Alaikum Assayid ina fama da matsalar jin hassada a cikin zuciyata duk yand ana kai da tsawatarwa da kaina daga wadannan sawwale-sawwale na Shaidan bana iya samun nasara, hatta lokacin da na ke yin addu’ar alheri ga wasu mutane sai na dinga jin cewa ina kallafa ma kaina wahala ne kadai, da Allah ka nusantar da ni zuwa ga gaskiya

Da sunan Allah mai Rahama mai jin kai

Tunani cikin tauhidi da dayantar da Allah da kuma cewa Allah yana rarraba arziki tsakankanin bayinsa kowa yana cin iya arzikin da Allah ya kaddara masa na daga cikin hanyar waraka daga matsalarka, ka karanta litattafan Aklak kamar misalin Jami’ul Sa’adat kan babin Hassada, lallai zai amfanar da kai da yardarm Allah ta’ala.

Kayi wurgi da watsi da wahamin da damuwa ka mai da hankali cikin yin rayuwarka ta yau da gobe ta dabi’a, lallai matsalolin rayuwa na da matukar yawa da zaka tsaya kaba batawa kanka lokaci da wannan sawwale-sawwale, ka dinga yawaita karanta wannan addu’a

(اللهم أخرجني من ظلمات الوهم واكرمني بنور الفهم..)

Ya Allah ka fitar dani daga duhun wahami ka karrama mini hasken fahima.

Wurin Allah muke neman taimako.

Tarihi: [2019/10/20]     Ziyara: [84]

Tura tambaya