mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

TA YAYA ZAMU IYA SIFFANTUWA DA KYAWAWAN DABI’UN MUSLUNCI DA NESANTAR MIYAGU

Salamu Alaikum
Yaya zamu iya tsiwirwirar kyawawan Aklak din muslunci mu kuma kauracewa rubabbun dabi’u miyagu

 

Salamu Alaikum

Yaya zamu iya tsiwirwirar kyawawan Aklak din muslunci mu kuma kauracewa rubabbun dabi’u miyagu

Da sunan Allah mai Rahama mai jin kai

Ina muku godiya haka zalika ina godiya ga ubangijina  ina yaba masa cikin kowanne hali, amma dangane da samun kyawawan halaye , to lallai dole ne ka zage dantse ka yaki zuciyarka da da ranka mai yawan umarni da mummuna da watsi da aikata zunubai sannan ka kiyaye sauke wajiban da suke wuyanka da kuma kokarin kamanta mustahabbai, dole ka kiyaye wadannan matakai guda uku kamar yanda suke a ilimi Aklak  sune: Takliyatu: wanke zuciya daga dukkanin sabo, Tahliyatu: cancanda mata ado da ayyukan alheri, Tajliyatu: yaye ta, hakika na ambaci wadannan matakai lokuta da dama cikin wallafe wallafe na da laccoci nam zaku iya samunsu a Adirshinmu na yanar gizo idan kuna da bukata, ku koma can lallai zaku samu abinda kuke nema zan kasance tareda ku cikin ladan ilimi mai amfani da aiki nagari da yardar Allah daga gareshi ake samun taufiki.

Tarihi: [2019/10/21]     Ziyara: [422]

Tura tambaya