mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

SHIN YA HALASTA A KARBI RIWAYA DAGA WANDA YAKE KAN GURBATACCIYAR MAZHABA


Salamu Alaikum. Shin yana halasta aka karbi riwaya daga wanda yake kan mazhabar bata

 

Salamu Alaikum. Shin yana halasta aka karbi riwaya daga wanda yake kan mazhabar bata
 

Da sunan Allah mai Rahama mai jin aki

Akwai shubuha mai yawan gaske da Dajjalai da masu mummunar niyya wahabiya suke yawo da ita, da shubuha ek kai kawo kan maganar Allama Hurrul Amili Allah ya kara masa yarda.

Gabani kawo muku maganarsa, ina son fadin: lallai ya inganta cewa Allama Hurrul Amili yana daga Akbariyun, kuma kasance magangarar bayani mai zuwa:

 

1-tabbatar da ingancin hadisan ingantattun litattafai.

20 watsi da sabon taksimin hadisi wato (Assahihu, Alhassanu, muwassak, da’if)

Kan haka ne muke cewa babu laifi ayi munakashar abubuwa da ya bijiro da su  cikin wadancan maudu’ai, sai dai cewa kuma ya fadi wata kalma da ake la’akari da ita cikin ba’arin lamurra, abinda yace cikin littafinsa Wasa’ilul Shi’a juz 39 sh 260 : da’awar wasu daga malamai da suka daga bayan na farko cewa Sikatu da ma’anar Adali Dabidi wannan da’awa hananniya ce, ana bukatar dalili kan haka.

Ta yaya alhalin sun yi furuci bayyane sabanin wannan da’awa inda suke wassaka wanda suka yi Imani da fasikancinsa da kafircinsa da gurbatar mazhabarsa?!

Wannan shine abinda ya fada.

 

Ina cewa: maganar Allama akwai ishara zuwa ga wadannan abubuwa masu zuwa a kasa:

1-hakika akwi wadanda suke wassaka kafiri da ma’abocin gurbatacciyar mazhaba.

2-idan ya kasance akwai bayani karara daga wannan nau’I, hakan yana nuni kan tausiki ya tabbatu da aiki da riwaya da ta zo daga hannun kafirai da ma’abota gurbatacciyar mazhaba.

Zahiri kamar yanda yake sanannen al’amari ana kirga Shaik Hurrul Amili daga mabiya mazhabar Akbariyu Ahlil hadis, sakamakon tarayya da juna tsakanin Akbariyun da Ahlil hadis sai aka kirga shi daga cikinsu, Allah ne mafi sani.

Abin nufi daga kafiri a wannan muhalli ba kafirin akida ba wanda ya sabawa matafiyar Ahlil-baiti ai kafiri cikin aiki cikin biye gaskiya da kafircewa wilayarsu amincin Allah ya kara tabbata a garesu, ta yiwu muradi daga kafiri da ma’abocin gurbatacciyar mazhaba shine wannan ma’ana.

Sannan wajen malamai magabata ana kasa hadisi zuwa kashi uku: Assahihu, Hasanu Da’if, malaman da sukai zamani da Allama Hurrul Amili sun kasa hadisai zuwa kashi hudu: daga akwai Karin Muwassak wanda ake nakalto shi daga wurin Sikatu ko da kuwa yana kan gurbatacciyar mazhaba kamar misali Rawi Assakuni da Naufali, daga manyan malamanmu akwai wanda baya karba riwayarsa sakamakon gurbatar mazhabarsa duk da kasancewarsa Sikatu, a wurinsa ta yaya zai zama Sikatu tareda gurbatar  mazhabarsa da akida?! Sai dai cewa daga malamai akwai na baya da na wannan zamani baki dayansu suna karbar hadisin Sikatu wannan shine ra’ayin da muma muke kai, ko da kuwa yana kan gurbatacciyar akida da kafirci na aiki da boye hakkin Sarkin muminai Ali (a.s)

Sabani ne tsakani manyan malamai wanda kowa akwai maginar da ya dogara d aita da yake komawa ga dalilai wacce daga cikinsu akwai:

 ( ان جاءكم فاسق بنبأ فتبيّنوا )

Idan fasiki ya zo muku da labari ku bincika.

Mafhumin ayar idan wanda ba fasiki ba ya zo muku ka da ku bincika ku karbi hadisinsa kamar yanda siratul ukla’u ta tafi kan haka, sai dai muradi daga Adali shine wanda ya kasance Sikatu kuma ba ya karya ko da kuwa yana kan gurbatacciyar mazhaba, sai dai cewa a wurin wasu malamai gurbatar mazhaba yana daga manyan alamomin rashin sikkanci, mas’ala ce da ake da sabani cikinta, abind aya kamata ka koma wurin wanda kake taklidi da shi cikin ayyukan taklifi wadanda cikinsu Fakihi yana tsamo hukunci shin yana aiki da hadisin Sikatu daga masu gurbatattun mazhaba ko kuma baya yi, wannan wani abu da yake komawa garemu mu mukaddi’atu da muka yadda istinbadi zai iya dacewa da waki’u kuma zai iya sabawa mu bamu tafki ka taswibu ba da cewa duk istinbadinmu shine daidai a waki’u kamar yanda Ahlis-sunna suka tafi kai, mu wurinmu mujtahid zai iya dacewa kuma zai iya kuskurewa, idan ya dace yana da lada biyu idan kuma ya kuskure yana da lada daya.

Allah ne masani..
Tarihi: [2019/11/12]     Ziyara: [91]

Tura tambaya