mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Tambayoyin da akafi karantawa

SHIN ISNADIN WANNAN RIWAYA YA INGANTA


Salamu Alaikum
Hadisi ya zo cikin littafin Attauhid na Shaik Saduk cikin babin Sawabul Muwahiddin:

Salamu Alaikum

Hadisi ya zo cikin littafin Attauhid na Shaik Saduk cikin babin Sawabul Muwahiddin:

 ( عن أبي ذر - رحمه الله - قال: خرجت ليلة من الليالي فاذا رسول الله صلى الله عليه واله وسلم يمشي وحده ليس معه إنسان، فظننت أنه يكره أن يمشي معه أحد، قال: فجعلت أمشي في ظل القمر، فالتفت فرآني، فقال: من هذا؟ قلت: أبوذر جعلني الله فداك، قال: يا أبا ذر تعال، فمشيت معه ساعة، فقال: إن المكثرين هم الاقلون يوم القيامة إلا من أعطاه الله خيرا فنفح منه بيمينه وشماله وبين يديه ووراء ه وعمل فيه خيرا، قال: فمشيت معه ساعة، فقال: اجلس ههنا، وأجلسني في قاع حوله حجارة، فقال لي: إجلس حتى أرجع إليك، قال: وانطلق في الحرة حتى لم أره وتوارى عني، فأطال اللبث، ثم إني سمعته صلى الله عليه واله وسلم وهو مقبل وهو يقول: وإن زنى أن سرق، قال: فلما جاء لم أصبر حتى قلت: يانبي الله جعلني الله فداك من تكلمه في جانب الحرة؟ فإني ما سمعت أحدا يرد عليك من الجواب شيئا، قال: ذاك جبريئل عرض لي في جانب الحرة، فقال: بشر أمتك أنه من مات لا يشرك بالله عزوجل شيئا دخل الجنة، قال: قلت: ياجبرئيل وإن زنى وإن سرق؟ قال: نعم وإن شرب الخمر .)

An karbo daga wurin Abu Zarri Allah yayi masa rahama- ya ce: na fito a cikin wani dare daga darare kwatsam sai na ga Manzon Allah tsira da amincin Allah su kara tabbata a gareshi da iyalansa yana tafiya shi kadai babu kowa tareda shi, sai na yi zaton baya son tafiya ne tareda kowa, sai na dinga sadadawa cikin inuwar wata sai ya waiwayo sai ya ganni, sai ya ce: waye wannan? Sai nace: Abu Zarri Allah ya sanya fansarka, ya ce: ya Abu Zarri taho mana zo mana, sai na tattaka na tafi tareda shi zuwa dan wani kankanin lokaci, sai ya ce: hakika masu yawaitawa suna yan kadan ranar kiyama face wanda Allah ya bashi wani alheri sai yayi kyauta daga gareshi da damansa da hangunsa da gabansa da bayansa ya aikata alheri cikinsa, ya ce: sai na kara tattakawa kadan tareda shi, sai ya ce zauna a nan sai ya zaunar dani cikin wnai fili da yake kewaye da duwatsu ya ce mini: zauna ka jira har sai na dawo, ya ce: sai ya tafi har ya bacewa idanuna, sai ya zama ya jima bai dawo ba, sannan sai na ji Manzon Allah (s.a.w) a halin fuskantowarsa yana cewa: ko da kuwa ya aikata zina da sata, ya ce: yayin da ya zo gareni sai na kasa hakuri n ace: ya Annabin Allah Allah ya sanya ni fansarka   da wanene kake Magana a gefan wannan wuri mai duwatsu ? ni banji sautin wani mutum da yake Magana da kai ba, ya ce: tareda Jibrilu na kasance ya zo mini a gafen wannan wuri mai duwatsu ya ce: kayi bushara zuwa ga al’ummarka cewa duk wanda ya mutu baya shirka da Allah Azza wa Jalla zai shiga Aljanna, ya ce: nace ya Jibrilu ko da ya aikata zina da sata? Ya ce na’am ko da ma ya sha giya.

 

Yayin da na karanta wannan hadisi sai wasu yan tambayoyi suka fado cikin kwakwalwata da farko dai wannan hadisi ingantacce mana kuwa? Idan isnadinsa bai inganta ba shin cikin mataninsa akwai bakunta ma’ana Nakaratu? Tambaya ta biyu menene ma’anar mutum ya kasance musulmi mai dayanta Allah ko da kuwa ya aikata zina da sata tareda haka zai shiga aljanna?

Muna fatan zaku bamu amsa kan wadannan tambayoyi da suke kaikawo cikin kwakwalwata suka gigita ni.

Muna barar addu’a daga gare ku.


da sunan Allah mai Rahama mai jin kai

ma’ana dai shi ne Allah matsarkaki madaukaki zai datar da shi da tuba daga aikata wannan miyagun laifuka gabanin mutuwarsa, babu shakka cewa duk wanda ya fadi Kalmar tauhidi yana mai tsarkake niyya an yafe masa zunubansa kuma zai shiga aljanna, sannan alamar tsarkakar niyyarsa shi ne a same shi yana taka tsantsan daga aikata haramun, jigo shi ne ya mutu mumini yana mai tsarkake Allah da daynata shi idan ko ba haka ba lallai daga cikin mutane akwai wanda imaninsa na ajiya ne an ajiye shi wurinsa za a karbe shi lokacin kakin mutuwa da barin duniya Allah ka tsaremu, sannan da ace ya kasance mai tsarkin Imani to lallai kyawawan ayyuka suna goge munana sai Allah ya gafarta masa ko da kuwa yayi sata  hakan ya zo cikin misalin kaddarawa da bada misali ma’ana Allah zai datar da shi zuwa ga tuba sai ya bar duniya yana mai tuba kuma hakika Allah yana gafarta zunubai baki daya in banda shirka.

Tarihi: [2019/12/4]     Ziyara: [71]

Tura tambaya