mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Wasu daga cikin tambayoyi

Mene ne banbanci tsakanin Hisabi da ukuba

Salam Alaikum
Wanne banbanci ne yake tsakanin Hisabi da ukuba?

Da sunan Allah Mai rahama Mai jin kai

Banbanci a bayyane yake, lallai shi hisabi mukaddima ne da share ga ukuba, saboda mutum yayin da ake masa hisabi ko dai ya kasance mai `da’a da ayyukansa na kwarai suka yi galaba kan munanan ayyukansa sai a saka masa da lada da tak’warsa ya samu damar shiga aljanna, ko kuma dai ya kasance mai sabo wanda miyagun ayyukansa suka rinjayi kyawawan ayyukansa, lallai za ai masa ukuba ya kasance daga `yan wuta, Allah ya halicci mutum cikin bashi cikakken zabi ya kuma shiryar da shi hanyoyi guda biyu, hanyar ma’bota gaskiya da hanyar batattu , kana da cikakken zabi cikin zabar daya daga hanyoyin, ina rokon Allah ya sanya ni da ku da dukkanin Muminai mazansu da matansu gabas da yamma daga rayayyunsu da matattu cikin `yan Aljanna, amin ya Rabbal Alamin.

 

Tarihi: [2020/6/11]     Ziyara: [139]

Tura tambaya