mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Wasu daga cikin tambayoyi

Shin jazabar ubangiji tana kasancewa maimaici ta hanyar barin aikata sabo

Salamu Alaikum
Shin jazaba na kasancewa maimaici sakamakon barin aikata sabo da zunubi, kuma ba wajibi bane ga majzubi ya zama sai ya bar aikata zunubi da sabo zai samu jazaba?

Shin jazabar ubangiji tana kasancewa maimaici ta hanyar barin aikata sabo

Salamu Alaikum

Shin jazaba na kasancewa maimaici sakamakon barin aikata sabo da zunubi, kuma ba wajibi bane ga majzubi ya zama sai ya bar aikata zunubi da sabo zai samu jazaba?

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Ka sani ita jazabar ubangiji kashi biyu ce, wani lokaci tana iya kasancewa daga jazabar majzubi da jazabar suluki Allah yana fizgarsa zuwa gareshi wannan na biye da hikimar ubangiji da mashi’arsa da take daga rahamarsa da jinkansa da suke kusa-kusa ga Muminai masu kyautatawa, wani karon kuma jazaba ce ta mamallakin majzubi da yake fisgarsa zuwa ga ubangiji wannan ya dogara ne da aikinsa da sairinsa da suluki da dayyin manazilul Arifin wacce farkawa ta horar da ita sannan tuba da gudu daga zunubai dss

Kana iya duba littafin (Manazilul Arifin) Allah ya bamu dacewa da damdagatar, soyayya ce asalin jazaba, wani lokacin suna son Allah shima yana sonsu a wani karon kuma Allah yake fara sonsu sai suma su so shi, da farko soyayya tana kasancewa cikin Kausul su’udi na biyu cikin Kausul nuzuli, cikar dukkanin kamala na cikin hade kausin guda biyu bawa ya kasance cikin da’irar ubudiya bautar Allah da soyayya da kauna, ya zo cikin hadisul Kudusi daga Allah matsarkaki kamar yanda aka ce

 (مَن طلبني وجدني ومن وجدني عرفني ومن عرفني عشقني ومن عشقني عشقته ومن عشقته قتلته ومن قتلته ناديته).

Duk wanda ya nemeni zai sameni duk wanda ya sameni zai san ni ko waye duk wanda ya san ni zai kaunace ni duk wanda ya kaunace ni zai zan kaunace shi duk wanda ya na kaunace shi zan kasheshi duk wanda na kasha shi zan kiraye shi.

Ya daga bakin shugaban shahidai a ranar Ashura a filin Karbala:

تركت الخلق طرّاً في هواكا            وأيتمت العيال لكن أراكا

فلو قطعتني في الحبّ ارباً             لما حنّ (مَالَ) الفؤاد إلى سواكا

na watsi da kowa da kowa cikin soyayyarka* na maraitar da iyali domin na ganka

da zasu yankani gunduwa gunduwa cikin soyayyarsa* da har abada zuciyata ba zata karkata zuwa ga waninka ba,

اللّهم ارزقنا حبك وحب من يحبك وحبّ كل عمل يوصلنا إلى قربك إلهي هب لنا كمال الإنقطاع إليك وأنر أبصارنا بضياء نظرها إليك حتى تخرق أبصار القلوب حجب النور فتصل إلى معدن العظمة وتصير أرواحنا معلقة بعز قدسك وجلال مجدك آمين يا رب العالمين وصلى الله على محمد وآله الطاهرين.

Ya Allah ka auzrtani da soyayyarka da soyayyar wanda yake sonka da son duk wani aiki da zai kusantani gareka, ya ubangiji ka bani kamalar yankewa gareka ka haskaka idanunmu da hasken kallo zuwa gareka har idanunwan zukata su samu damar keta hijaban haske su sauka zuwa ga ma’adanan girma rayukanmu su zama rataye da izzar tsarkakarka da girmanka.

Amin tsira da aminci su tabbata ga Muhammad da iyalansa tsarkaka

 

Tarihi: [2020/11/16]     Ziyara: [61]

Tura tambaya