mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Ta yaya dukkanin aikina da motsina zai kasance domin neman yardar Allah

Salamu Alaikum
Ta kaka ayyukana da motsina zasu kasance don Allah, alal misali ina da wata bukata da nake neman biyanta, ance wanda yake neman soyayyar Allah sannan yayi dukkanin ayyukansa don Allah bai zama wajibi ya zama burinsa shine wata bukata ko wani nema ko shauki zuw aga Aljanna ko tsoron wuta ba, ya kamata shi ya kubuta daga dukkanin bukatun gidan duniya da kwadayinsa na lahira ya zama tsantsar hadafinsa shine Allah da yardarsa da soyayyar Allah da Manzonsa da iyalansa tsarkaka, ta kaka zan iya zama kamar haka tareda burika da fata da suke cikina, ta kaka zan sanya Allah ya zama shine hadafina da burina,
Shin akwai wasu bukatu da muke bukatuwa zuwa garesu?
Allah mai taimako.

Da sunan Allah Mai rahama Mai jin kai

Ka roki Allah soyayya da shauki  ka nemi bukatunka daga gareshi  lallai Allah yana cikin ranka sabid ashi Allah yana son a roke shi ka nemi bukatu daga gareshi hatta gishirin da yake cikin abinci kamar yanda Allah ya cewa masoyinsa abokin maganarsa Musa (A.S) ka nema daga gareshi zaka same shi cikin mai nema da abinda ake nema ba zakata ba ganin kanka har abada, lallai kanka wani hijabi ne tsakaninka da ubangijinka, sabida haka ka yaye wannan hijabi da rukuni ga Allah cikin komai babu wani abu face ayace ta ubangijinka, ita aya da ma’anar madubi da cikinta zaka ga ma’abocin ayoyin sai kaga Allah cikin komai gabaninsa bayansa tareda shi, kamar yanda shugabanmu Sarkin Muminai  Ali amincin Allah ya tabbata a gareshi ya kasance, wannan shine kololuwar buri da hadafion Arifai da makusanta babu mai samunsa sai mai babban rabo, ya Allah ka sanya mu daga cikinsu tareda su amin ya ubangijin Talikai.

Sannan ka lazimci karanta Munajatul Arifin da Zahidin.

Allah ne mai taimako.

Tarihi: [2021/1/16]     Ziyara: [28]

Tura tambaya