mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Yana halasta mutum ya tafi jihadi ba tare da izinin Mahaifansa ba

Salamu Alaikum

Ina son zuwa jihadi cikin tafarkin Allah amma ba tareda izinin mahaifiyata ba shin hakan ya halastam gaskiya ni bana son zama cikin wannan duniya tareda rudunta da halakarta ni na zabi jihadi domin kare kaina da tabbatar da wilayata, sai dia kuma tambaya anan shin ya halasta in tafi babu izini babata

Salamu Alaikum

Ina son zuwa jihadi cikin tafarkin Allah amma ba tareda izinin mahaifiyata ba shin hakan ya halastam gaskiya ni bana son zama cikin wannan duniya tareda rudunta da halakarta ni na zabi jihadi domin kare kaina da tabbatar da wilayata, sai dia kuma tambaya anan shin ya halasta in tafi babu izini babata.

 Da sunan Allah Mai rahama Mai jin kai

Ba ayiwa Allah `da’a da saba masa, lallai shi jihadi tsarkakiyar ibada ce abune mai kyau a kankin kansa kuma `da’a ne ga Allah sai dai cewa da sharuddansa da sharadinsa, alal misali idan ya kasance wajibul aini to a wannan lokaci babu sharadin neman izini daga iyaye, amma idan ya kasance wajibul kifa’i ko kuma mustahabbi to abinda yafi dacewa ka kiyaye kada ka batawa mahaifiyarka rai tayi fushi kamar yanda ya zo cikin hadisai daga Annabi da A’imma amincin Allah ya tabbata a garesu baki daya.

Allah ne mai taimako.

Tarihi: [2021/2/7]     Ziyara: [18]

Tura tambaya