mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

WANE NE ALKADI TANNUKI MAWALLAFIN LITTAFIN (ALFARAJ BA’ADAL SHIDDA)

Tarihi:
Salamu Alaikum
Tambaya ta farko: wanene Alkadi Tannuki wanda ya wallafa littafin (Alfaraj ba’adal Shidda) shin yana cikin malaman hadisan shi’a?
Tambaya ta biyu: na duba littafin sai na daga Manshurat din Shariful Radi ne kuma na ga an rubuta cewa an ciro Asalin littafin daga rubutun hannu da aka ajiye shi a dakin nazarin karatu da yake kasar Misra, shin dama littafin ya bace daga dakunan kula da litattafai tsahon shekara dubu?
... Ganin amsa

MENE NE INGANCIN WANNAN RIWAYA

Hadisi da Qur'an:
Salamu Alaikum.
Wannan riwaya da za ta zo ta zo cikin littafin Biharul-Anwar
Mene ne martaninku Allah ya saka muku da alheri
Sannan mene ne ingancin riwayar

Cikin Biharul-Anwar J 47 sh 356, babin tarikul Imam Jafarul Sadik (a.s)
... Ganin amsa

BABU WANI ZUNUBI DA YAKE RABA MUMINI DA IMANINSA

Hadisi da Qur'an:
Salamu Alaikum. Manzon Allah (s.a.w) yace:
: ما من عبد قال : [لا اله الااللّه ] ثم مات على ذلك الا دخل الجنة وان زنى وان سرق , وان زنى وان سرق , وان زنى وان سرق ,وان رغم انف ابي ذر
Babu wani bawa da zai fadi Kalmar shahada babu abin bautawa da gaskiya sai Allah sannan ya mutu a kan haka face ya shiga aljanna ko da kuwa ya aikata zina ko da kuwa yayi sata, ko yayi zina yayi sata, ko yayi zina yayi sata, bisa rashin son ran Abu Zarru Gifari.
... ... Ganin amsa

INA BUKATAR BAYANI KAN (INA ROKON ALLAH UBANGIJNA YA SANYA RABONA DAGA ZIYARARKU YA ZAMA SALATI GA MUHAMMAD DA IYALANSA

Aqa'id:
Salamu Alaikum wa Rahmatullahi wa Barakatuhu ya zo cikin ziyarar Imam Aliyu Hadi da Hassan Askari (a.s) wannan jumlar ( ina rokon Allah ubangijina da ku ya sanya rabona daga ziyararku ya kasance salati ga Muhammad da iyalan Muhammad) ina neman Karin bayani kan wannan jumla daga karshe muna barar addu’a daga gareku.
... Ganin amsa

dama ma’anar fadin imam A.s (lallai zan yi kuka kanka kukan jini maimakon hawaye) hakan na nufin buga karafuna a kai

Hukunce-hukunce: salamu Alaikum

Gaisuwa zuwa ga Samahatu Ayatullahi Assayid Adil-Alawi Allah kare mana shi

Hakika wata damuwa ta mamaye mutanen yankinmu sakamakon abin da wani daga cikin Limaman masallatai yayi lokacin da ya hau kan mimbari ya kama sukan Maraji’ai, inda yake cewa: (wasu daga cikin Maraji’ai sai ya zo ya ce mana ma’ana fadin Imam (a.s) (lallai zanyi maka kukan jini maimakon hawaye) shi ne dukan kai da karfe ma’ana mu bugi kawukanmu da karafuna, wannan wanne irin batan basira ce haka da wauta!

Muna bukatar bayani daga Akaramakallahu kan maganar wannan limami? ... ... Ganin amsa

Tambayoyin da akafi karantawa

Tura tambaya