mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Ta wace hanya zan bi na isah ga malaman tarbiyya?

Aqa'id: Assalamu alai kum
Ina rayuwa a kasar turai, sannan kamar yadda kuke da masaniya akwai hanyoyin shaidan da yawa awurin, ni kuma ina da alaqa da tsarkake zuciyata gashi bani da wani malami da zai taimakamin , sai dai nakan yawaita karanta littattafai daga internet amma hakan baya isa na, ina neman shawarar ku, wacce hanya ce zan bi na sami malami da zai taimakamin a wurin da nake rayuwa?
... Ganin amsa

Ina rokon ku, ku kasance min malami na tarbiyya.

Hanyar tsarkake zuciya: Assalamu alaikum
Ina rokon ku da kukasance min malamin tarbiyya, sannan ina rokon ku kumin addua ni da iyalaina, musamman wa kanwata tana da matsalar Aljannu.
Allah saka da alheri.
... Ganin amsa

Shin akwai wani aikin da ke hana mutum samun galba kan sirrin badini?

Hanyar tsarkake zuciya: Assalamu alaikum
Shin akwai wata hanya da zan iya galba kan sirrin badini na, ko wata tasbihi da zai taimaka wurin samun galba din.?
... Ganin amsa

Shin Limami zai iya Sallar idi sau biyu, ko kuma sallar da yayi a ranar da marja’in sa ya tabbatar masa cewa Idi ne ya wadatar?

Aqa'id: Assalamu alaikum
Na kasance ina limanci a wani husainiya, sannan ina taqlidi da sayyid khu’I amma yawancin wanda nake musu limanci suna taqlidi da sayyid Sistani ne.
Sai ya kasance aka sami ban bancin fatawa akan yaushe ne ranar Idi. Sayyid Khu’I yace ranar Talata ne, shi kuma sayyid Sistani yace laraba, sannan mutane da suke taqlidi da sayyid Sistani sun bukace ni da na jagorance su sallar idi ranar Laraba.
Tambayata anan itace shin zan iya yin sallar Idi a rana biyu? Wato ranar Talata da kuma ranar Laraba?
... Ganin amsa

Neman gafara

Aqa'id: Ina neman taikon kan wata matsala da nake da shi, ina yawan istigfari da kuma neman gafara a ko da yaushe amma ina komawa gidan jiya. ... Ganin amsa

Wasu daga cikin tambayoyi

Tura tambaya