sababun labare Labarun da ba tsammani Labarai wanda akafi karantawa

Mu,assatul Irshad wattablig ta sami halarta taran duniya da akayi a garin Qum akan ta,addanci

Da suna Allah mai rahama mai jinkai

A ranar lahadi ne da safe a Qum taran duniya akan ta,addaci yafara aiyokasa domin tattauna hadarin ta,addanci a duniya taran da mutane daban-daban daga kimanin kasa tamanin suka halarta daga cikin su akwai malamai da mutane masu mihimmaci a duniya sanna mahalar tataron sun tattauna hadarin ta,addanci a duniya dakuma yaya za,ayi wajan kawo karshan sa gabaki daya a duniya.

Kuma taran yasami halartar malaman addini na kasar Iran kamar su Ayatullahi Makarim SHirazi da Ayatullahi jafar Subahani da shek Muhammad gulfaigani wanda yake shi shugabane na ofishin jagoran musulinci na Iran wato Ayatullahi Al-uzma sayyid Ali Kamna,I da Ayatullahi Ahamad Jannati wannada yake shi amini ne na majalisar kare kundin tsarin mulki da Ayatullahi Husaini  bushahari wanda yake shi mudiri ne Hauza al-ilmiya a Qum dakum limamin juma,a na sunna na garin Zahidan malam Abdulhamid maulawi.

Wanda ya shugabanci taran shi ne Ayatulahi Makarim SHirazi  wanda kuma yajagoranci taran ta bangaran ilimi shi ne Ayatulahi Ja,afar Subahani. Daga cikin wadanda suka halarci taran akwai shugaban harkokin waje na kasar Iraqi wato Ibrahim Al-ja,afari dakuma manyan mutane daban-daban.

Wanda ya bude taran shi ne Ayatullahi Makarim Al-shirazi wanda yayin budewar yayiwa mahalarta taran fatan alheri yakuma baiyana musu manifar taran yace shiwanna taro anshiryashi ne domin shawokan ta,addanci a duniya bakidaya wanda shi ta,addanci wana abune da yake kalubalantar duniya baki daya masammama musulinci da musulmi.

Kuma shi wanna taro yana da mutikar mihimmaci,saidai ana jiran wanna taro dayawarware hadarin da duniyar musulinci take fuskanta kuma shi wanna hadari ba takaita da wata mazahaba ba a,a ya shafi kowa ne ,kuma kazalika daga cikin makasudun shi samar da wani zaure na fatawa wanda zai gunshi dukan cibiyoyi na addini kamar hauza ta Najaf da ta Al-azahar dakuma ta Qum,

Mahalarta wanna taro nacewa shi wanna taro na duniya amfara shi ne shekara uku baya da tawoce sakamakon tinani mai kyau da malaman Qum suke dauke da shi ga al,umar musulmi ta duniya wanna kuma yafaru ne sakamakon kalobalan da duniyar musulmi take ciki kuma take fuskanta wato na ta,addaci akan musulmi da musulinci ba tare da bambancin wanna Sunna ne ko Shi,a,sukuma nanata cewa abun dayake da muhimmanci a taran shine halartar malamai daga kasashan duniya daban-daban kimanin kasa tamanin da shida. Sunkuma karadacewa makasudun wanna taro na duniya shine wayar da kan mahalarta taran dakuma mutanan duniya cewa shi ta,addanci wana abune daya da alaka da musulinci yana farowa ne a cikin musulmi sakamakon mummunar fahimta da wasu suka yiwa musulinci.

Amma shi wanna taro yana da ajandodi guda hudu sune kamar haka:

-Tattauna asali ko mabubbuga ta,addanci dakuma ‘yan ta,adda

-Ganu shikashika ko asasi na aqida a gun ‘yan ta,adda.

-fahimtar alqa tsakanin siyasa da ‘yan ta,adda.

-Tattauna hanyoyi wadanda za,abi domin magance ta,addanci a duniya dakuma abubuwan da za.a iya fuskantar ‘yan ta,adda da shi.

Ayatullahi Makarim: yace fuskanta ko kalobalantar ‘yan ta,adda a duniya nauyi ne wadda ya haukan kowa yakuma kara dacewa dukan abun da ‘yan ta,adda skeyi baya da alaqa musulinci yakuma kara dacewa abun damuke su muttauna a wanna taro daya ne daga cikin manyan matsaloli da duniya take fuskanta shi ne ta,addancin da ‘yan ta’adda sukeyi a duniya.

Yakuma su ‘yan ta,adda suna mutukar cutar da musulinci da musulmai dakuma dan adam bakidaya amma nauyin daya haukammu shine fahimtar hadafin su dakuma sanin abubuwan dasuke angizasu yin munanan aiyikan su da tumbuke su daga asalin su.

Yace yaushane zamutsaya muna kallo ta’addanci na keta alfarmar musulmi dakuma kashe musulmi ,yakara dacewa shi musulinci addini ne na rahama da tausayi amma ‘yan ta,adda suna nunawa mutanan duniya cewa addinin musulinci addini ne na rashin imani da tausayi sabodahaka mukesu mutabbatarwa mutanan duniya cewa su ‘yan ta,adda basu da alaka da musulinci kuma malamai suna kokari wajan suga sukawar da ta’addanci da ‘yan ta,adda.

Ayatullah Ja’afar Subahani yace: ta’addanci da ‘yan ta,adda sun samu ne sakamakon mummunar fahimata babba malamin na kasar Iran yakuma yi kira ga malaman duniya dasudauki nauyin wayar da kan jama,a dakuma baiyana musu musulinci iggantacce dakuma nuna musu cewa musulinci ‘yan ta’aadda musulinci ne gurbatacce.

Sanna sheik Subahani yayi nuni daggane da alaqar ‘yan ta’adda da wanna haramtacceyar kasa ta Isra,il dukan abun da ‘yan ta’adda sukeyi kokari ne na samawa ita wanna haramtacceyar kasa guri mai amunci malamin yakuma yi kira ga al-umar musulmi da su tashi tsaye domin bada kariya ga masallacin Qudus daga wolakancin da yake fuskanta daga Yahudawa ‘yan kama guri zauna. Yakuma baiyana cewa munanan aiyokan da ‘yan ta’adda sukeyi basu da alaqa da musulinci babu wani addini na ALLAH daya yarda dahakan babu wata aya daga AL-QUR’ANI ko Linjila ko Attaura da take nuni akan munanan aiyokan su.yakuma yi nuni dacewa wasu daga cikin kasashan duniya su suke daukan nauyin su ta ban garan makami da kudi daga cikin kasashan hadda na musulmi.

Yayi nuni da makasudi na masu daukan nauyin ‘yan ta,addar  shine ruguje kasashan musulmi,haifar da yake-yake a tsakanin musulmi, kashakashe,zubar da jinni,bata musulinci a idan duniya wanda tabbatar da hakan zai samar da amuntaccen guri ga Banu Isra’il sukuma kawar da hankulan mutane daga kashe Falatsinawa da sukeyi da korar su daga gida jan su dakuma wasu munu fofin su wanda sai nan gaba zasu baiyana.yakumace shi wanna yaki da ‘yan ta,adda sukeyi akan musulmi yasasu sun manta da makiyin sun a asali wato yahudawa ‘yan kama guri zauna da matsalar su wacce ta shafi kowa da kowa.

Malamin yakuma yi nuni da muhimmancin wayar da kan jama,a dasu yaki ta,addanci dakuma magance shi ta hanya daban-daban bawai kawai ayi amfani da karfin soja ba, wanda shi akan yi amfani da shi ne a wani yanayi na masamma yakuma suki tsarin koyarwa na wasu daga cikin kasashan Larabawa a matsayin sakandiri wanda yake rura wata bangaranci na mazahabanci wanda yakai ga kiran wani bangare daga cikin musulim da kafurai, a garshe yayi kira ga malaman addini da masu ji da fada da suyi kori domin kawo garshan irin wanna tsare na koyarwa.