Shin imami yana jin muryan mala’ika amma baya ganin sa?

Salamu alaikum
A wannan yan kwanakin a gidan talabijn (walayat) kun fadi cewa imami yana jin muryan mala’ika amma baya ganin sa,shin ba zai iya ganin sa bane ko kuma shi ne bayaq so ya gani,dukkanin shia dai sun yarda cewa matsayin imami yafi na mala’ikata ko wani fanni,idan ya kasan ce baya iya ganin sa meye bambancin sa da nana marya?

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Manufa shi ne;rashin ganin abu baya nufin baza a iya ganin sa bah,tabbas imami zai iya ganin mala’ika sabo da dan shi imamin sa ne mala’ika hadimin imam ne kuma daga babin wilaya na takwini imam yana da cikakken iko akan mala’ika amma abun da muke magan a nan gani ne musamman ganin mala’ika a yayin saukar daba irin  wahayi irin wahayin dake sauka ma annabawa ba ,dan yazo a hadisin ahaqlil baiti cewa bambanci tsakanin imamai da annabawa shi ne annabawa yayin wahayi suna iya jin muryan sa da kuma ganin sa su kuma imamai sukan iya jin muryan sa ne kawai,

Zamu iya duba littafin alkafi don Karin bayani akan wannan bahasin.

Tarihi: [2016/4/11]     Ziyara: [774]

Tura tambaya