sababun makaloli
- Tarihi » masu tarbiyya ga al'umma
- Fikhu » Mas’ala ta bakwai: kallon gefan hanci a halin sujjada,
- Fikhu » Bahasul Karijul Fikhi shekara 1442 cikin mas’alar shimfida hannun yatsu hade da juna hatta babban yatsa zuwa kusa da kunne
- Akida » Addu’a sirrin ibada
- Akida » Wasiyoyi uku daga Imam Sadik (A.S)
- Akida » Kibiya ta shida
- Akida » Kibiya ta biyar
- Akida » Kibiya ta hudu
- Akida » Kibiya ta uku
- Akida » Kibiya ta uku
- Akida » Kibiya ta biyu-raddi kan Wahabiyawa daga litaffan bangarori biyu-shi’a da sunna
- Akida » Kibiya ta farko-Wahabiya daga Kawarijawa suka fito
- Akida » Kibban Raddi kan wuyan Wahabiyya
- Fikhu » Bahasul Karijul Fikhi- Usul 8 ga watan Jimada Awwal shekara 1442h
- Fikhu » bahasul Karijul fikhi 7 Jimada Awwal shekara 1442 h wada'au shi ne kebantar da lafazi kan wata ma'ana
makaloli
- » IMAM HASSAN ASKARI DA TALAKAWA
- » Daga ƙissoshin Annabawa amincin Allah ya kara tabbata gare su: kissar Annabi Sulaimanu (as) da shawarar da jemage ya bayar
- » Addu’o’i da wuridai masu tarin yawa tareda ba’arin tasirinsu na duniya da lahira
- » SHIN kana karanta qur'ani
- » Sallar Istigfari {NIman gafara} da tasirinta.
- » kunya a musulinci
- » DAGA CIKIN SIRRIKAN HADAYA
- » KARIJUL FIKHU 24 MUHARRAM CIKIN MAS'ALAR HALASCIN UDULI DAGA SURA ZUWA WATA MUDLAKAN CIKIN SALLOLIN NAFILA KO DA KUWA YA KAI GA KARANTA RABI
- Fikhu » KARIJUL FIKHU 5 RABIU SANI 1441 CIKIN TA’ARIFIN IJTIHADI A ISDILAHI DA NAKADI A KAN TA’ARIFOFIN DA AKA AMBATA
- » Muhimman wasiyoyi uku daga Imam Sadik (as)
- » Gudummawar da addu’a take bayarwa a rayuwa
- » Wasu takaitattun bincike da zasu amfanar da mumini da mumina.
- » Hasken haskaye nutsuwar zukata
- » Kudin ruwa na ruwa ne
- Fikhu » Bahasul-Karijul Fikhu, Fadin (Kazalikallahu Rabbi) sau daya ko biyu ko uku bayan karatun suratul Iklasi
Mukalolin da akaranta dayawa.
- » Addu’o’I da zikiri kan Karin Soyayya a tsakanin ma'aurata
- » Addu’a makamin mumini-tattaunawa tare da Ayatullah samahatus-sayyid husaini shahrudi
- » SIRRIN SALATI
- » Daga ƙissoshin Annabawa amincin Allah ya kara tabbata gare su: kissar Annabi Sulaimanu (as) da shawarar da jemage ya bayar
- » Bahasul karij: Magana mafi karfi itace hade suratu Filu da suratu li’ilafi
- » Sallar Istigfari {NIman gafara} da tasirinta.
- » Me yasa Imam Ali yayi mubayaa wa Abubakar da Umar
- » KAN HANYAR SHUGABAN SHAHIDAI IMAM HUSAINI (AS)
- » Hankali a mahangar makarantar imam kazim (as)
- Akida » Tambaya a takaice: shin Mala'ikan da yake zuwa da surar mutum shima yana da sha'awa
- » HAJJAJU IBN YUSUF!
- » SHIN kana karanta qur'ani
- » Taskar Adduoi 4
- » Taskar Adduoi 2
- » Falalar ilimi da malamai
SAUTIN KIRAN HANKALI-TARE DA AYATULLAH ASSAYID ALI-ALAWI
Na kasance cikin wani dare zaune cikin dakin nazarin karatu (libarary) mallakata bayan `yar wata karamar mudala’a da nayi sai na fara duba wannan dakin nazarin karatu tare da karancin abin da ke cikinta daga litattafai ina ta yin tunani, ina tunani cikin kasantuwar wadannan marubuta wadanda ake kirga su dubbai me yasa suka wallafa dukkanin wadannan litattafai? Litattafan da suka cika dakunan nazarin karatu makil. Wadannan zaurukan nazari da ake kirga su matsayin miliyoyi kowanne zauran nazari cikinta akwai dubban litattafai, me yasa duk sa’ilin da wani sabon littafi ya fito sai jamhur suyi gaggawa su fara karatunsa suyi darasinsa suyi nazarinsa?
daidai lokacin da nake cikin wannan hali sai naji wani karaji daga hankali na ya girgiza ni yana kira na: shin baka san wannan ba zuwa yanzu cewa litattafai da marubatansu bari dai annabawa da manzanni dukkaninsu sun fada kuma sunyi rubuce-rubuce don sun bayyana hanyar rayuwa ga mutum.
A wannan lokaci sai na kasance ina duba ya zuwa rayuwa ina zurfafa tunani kanta, mecece rayuwa ne? mecece hanyarta? Me yasa muke neman sanin hanyarta? Menene manufa daga dukkanin hakan?saboda halittu suna da yawa. kuma mafi karancin adadinsu shi ne farkon wanda Allah ya fara halitta admu har zuwa wannan ranar ta mu da muke ciki, dukkaninsu suna karaji da sauti guda daya, mu muna son sanin hanya har mu samu damar isuwa zuwa ga farin ciki wannan rayuwa da ni’imomi, farin ciki cikin gidan duniya, da ni’imtuwa a gidan lahira, tabbas wannan jumla ma’abociya hadaya daddada ta fado kan kunne na a yarda na zamanto ina ta maimaita ta.
Me kuke so ne?
Me mutum yake so ne cikin wannan rayuwa? Shin yana son rayuwa ta kasance masa wata loma mai saukin hadiya gareshi?
Ina aha: shin yana son wanzuwa tsawon rayuwa yana raye kamar misalin iblis? Wannan fa kuma ina ba zata sabu ba.
Na’am babu kwadayi da buri gareshi cikin wanzuwa saboda fana’I (karewa) na daga badihiyat wanda kowa ke iya fahimta, babu buri gareshi da dukkanin arzikin rayuwa, saboda yana daga cikin abubuwa gudu hudu ta ba zasu taba sabuwa ba. Idan haka ne to menene yake so ne? wannan mutum mai yawan jahilci, shin yana son farin ciki lallai shi farin cikin shi ne kayansa da yake cigiya. Babu abin da ke garemu face mu tambayi kawukanmu daga gareshi shin isuwa ga farin ciki yana daga cikin hanyarta ko kuma ba hanyarta ba ne? idan yana nufi isuwa ta hanyar da ba tata ba ce babu abin da ya rage gareshi face komawa a tabe a asarance, idan kuma ya nufi isuwa ta hanyarta sai mu yi tambaya shin wai ma ko ya san hanyar ta ko kuma kwata-kwata ma bai san hanyar ba? Idan amsa ta kasance na’am sai muce tana ina? don muma ya shiryar da mu zuwa gareta.
Guguzu:Tarayya da juna?
A nan wajen ya zama tilas mu san cewa dukkanin mutum, aha ya zama tilas ya zamanto yana da marunguma mafara cikin rayuwa wacce ke sanya mashi wata mahaskaka yana haskaka da ita da kuma wata hanya da zai dinga tafiya kanta idan ya kasance daga masu rungumar tsarin gurguzu na tarayya da juna a bisa misali wanda shi tsarin gurguzu ya ginu kan tushen tattalin arziki masu yada wannan akida ta gurguzu suna cewa shi tsarin gurguzu na tarraya da juna shi ne tsari mai lamintar da farin ciki da kwanciyar hankali ga rayuwar mutum, bara mu dan tsaya mu duba mu gani muga iya zurfafa da za iya karkata ga wannan magana, shin ta inganta ko kuma wannan magana dai ba ingantacciya ba ce? Bara mu dan nemi bijiro da wasu abubuwa yanzu daga akidar gurguzu domin daga karshe muyi hukunci a kai.
Muna cewa a tsarin gurguzu:
1- wajibi ne hukumar `yan kasa ta kasance hannun `yan kwadago daga masu shan matukar wahala daga ma’aikata da manoma.
2- dole kawo karshen tsarin jari hujja a gama da shi.
-3 dole ne ya zamanto tushen samar da dukiya da sana’o’i su game kowa da kowa su kasance mallaka kowa da kowa, da abin da ke tukewa ga wani wannan daga rassa suna da’awar cewa farin ciki da arziki na boye karkashin wadannan tsare-tsare da dokoki, sai dai kuma cewa hakikanin markisawa ya sabawa wannan da’awa ta su dari bisa dari ta yadda muke iya ganin `dan kwadago da manomi ana korasu a wajensu kamar yadda ake kora dabbobi cikin gonaki. Mun iya ganin `dan kwadago wajensu kamar daurarren bawa yake, yana aiki sai dai cewa ba bisa son ransa ba, kadai saboda karfin hukuma da ta ke da iko kansa da tafi karfinsa. Sannan abu ne a fili cewa dukkanin mutum yana da baiwowi idan yanayi ya bashi dama zai bayyanar da baiwowinsa ya fa’idantu ya fa’idantar da wasunsa. Idan kuma yanayi bai bashi dama ba bisa halin da yake rayuwa ciki ko kuma bisa tasirin muhallin da yake rayuwa cikin sai ya zoma baiwar da Allah yayi masa ta kwanta kais au da yawan lokuta ma tana mutuwa muris cikin zuciyarsa, ya zamanto babu wani kufai da ya rage mata a aikace, wannan na daga cikin abin da mutane basa shakka ko kokwanto cikinsa. Zamu mu ga `dan kwadago yana abin tilastuwa kan aikinsa tsawon rayuwarsa bai da wani zabi ga kansa, idan wata baiwa ta kasance gareshi alal misali ya kuma nufi fito da ita zuwa duniyar samuwa zai tunanin cikin ransa ya tattaunata maganar cikin rada da ransa me yasa nake wahalshe da kaina nake wahalar da ita ga wani abu da amfaninsa ba zai dawo gareni ba, ko kuma wani lokacin ya cudanyo ciki kwakwalwarsa, wannan yana daga mafi girman dalilai da suke haramta farin ciki da arziki da jawo tsiyata madawwamiya.
Jari hujja?
Yanzu mu `dan koma baya mu kaddara wata kaddarawa a wannan mutum ma’abocin wani tushe kai kace shi yana daga cikin masu imani da kudurce tsarin jari hujja yana fadin cewa tushen tsarin jari hujja kadai ke ceton daga wannan abin halitta tsiyatacce ma’ana mutum, ga mu zamu `dan tsayu tare da shi kan doron hanya domin muga wadanda suka tafi kan wannan mazhaba ta jari hujja ina ta tuke da su? Ina suka kai? Shin sun azurtu a hakika suna cikin farin ciki ko kuma suna cikin tsiyata suna gigice da fagarniya kan hanya zalunci da bata da danniya da bakin zalunci, da fasikanci da fajirci, alhalin sune jagororin arziki da farin ciki? Jagororin rayuwa mafififciya daga ina arziki dafarin cikin mafifici yake zuwa?
Alhalin jari hujja na cewa: (ga kowanne mutum yana da tsantsar `yanci cikin zabin hanya da kowanne suluki da uslubi don neman dukiya da habbakata da ninnikata kan hasken bukatunsa da alfanunsa na kankin kansa) da zamu zurfafa kallo cikin wannan jumla, cikin wannan reshe daga rassan jari hujja abar kyama da zamu ga mafi muni da kyama mabayyanar tsiyata, domin shi mutum yana garizozi da karkata na kankin kansa da suke boye cikin ransa, suna yawo tare da tunane-tunanensa, ya karanta ka ga ya barsu face kadan matuka, daga ciki garizarsa ta kwadayi, da ace mutum zai wurga igiyarsa kan kashekararsa shi yana kwadayi a dabi’ance kuma babu wani mai tsawatar msa daga sama ko daga kasa ko na hankali ko na nafsu, me kake tsammni wannan mutum da aka sakar masa ragama zai aikata? Shin ashe baka sameshi ya totse baki dayan abin da yake mallakar wasunsa ba? Shi ahse baka ganshi yana yana caccakar naman `yan `uwansa ba daga mutane? Ashe baka ganshi ba yana shan jinin `yan’uwansa ba daga kasan jinsinsa ba? Dukkanin wannan ya faru ne sakamakonsa ya kaucewa hanyar daidai cikin tsiwirwirarsa cikin neman dukiya, lallai idan ya tsiwirwireta shi yana farin ciki bisa yadda yake kudurcewa, mudan sanya lura dan kadan cikin abin da wannan `yantacce mai sakkakiyar ragama yake yi da `yan’uwansa `yantattu, shin su ko suna cikin arziki da farin ciki ko kuma suna cikin tsiyata? Idan sun kasance cikin azurta to wannan abin da muke karantawa cikin jaridu na da suke fitowa kullum ko kuma mujalloli ko kuma abubuwa da muke ji kullum daga radiyo da cewa wane miloniya ya kashe kansa, ko kuma wani ma’abocin aiki kaza ya kashe kansa, cikin kowacce shekara muna ganin daruruwan mutane suna ta kashe kansu a kasashen yammacin turai (tabbas azabar lahira ta fi kunyata) fussilat:16. Nan wajen ina son in buga wani misali na gaskiya da dukkanin muke ganinsa muke jinsa kowacce rana, wannan babban `dan jari hujjar wanda ya kasance za iya buga misali da shi wanda yake da gidaje da fadoji da manya-manyan gine-gine ga motoci da dukiya cikin bankuna zuwa masha Allah, abin da zamu fio kaddarwa shine ya kamata mu sameshi cikin farin ciki da kwanciyar hankali bisa imanin `yan’uwansa `yan jari hujja sai dai cewa sai muka same shi bai da kwanciya hankali da farin ciki cikin rayuwarsa, yana waiwayawa dama da hagu don tsoron kada wani talaka ya nemi ya bashi wani abu daga kudinsa, bai nutsuwa cikin zamansa saboda tunaninsa ma motsa shi daga kowanne janibi da kowanne bigire ta yanda take ba shi damuwa daga mafi nisan iyakoki, bai kwanciyar hankali cikin barcinsa mafdu yawa-yawan lokuta yana jarrabtuwa da cutar rashin iya barci saboda tsoron kada barawo ya shigo yayi masa sata, ya rike bindiga har ya fada kan wata akwatu da zamu iya kaddara ta da dinare dubu biyar, bai da kwanciyar hankali cikin cinsa da shansa saboda shi an jarrabce shi da cutuka masu naci kamar misalin ciwon sukari da asma dake hana numfashi da dai makamatansu Allah ya karemu,
Ina kwanciyar hankalin ya ku `yan jari hujja, ya ku `yan gurguzu ??
Tsakaninku da Allah shi cikin wannan akwai kwanciyar ko sai cikin waccan? Ko kuma dai a hakika duka su biyun suna kan hanyar kishiyantar kwanciyar hankali bama su bi hanyar samunsa ba? Hukuncin wannan na hannunku-kamar yadda muka gabatar zuwa ga ma’abucin hankali da basira da tunani, babu abin da ya rage kanmu sai dai mu bincika tushen karfaffa ma’abocin azama da karefin gwiwa mai karfin gaske mai ban kwarjini ba karama ba babba cikin sha’anin rayuwa face sai ka samu yana da wani hukunci cikinta kanta, mu cikin wannan bahasin namu mun nesantu daga kaidantuwa daga komai, babu so babu kiyayya babu sako-sako babu tsanantawa da dai abin da yayi kama da haka, kadai dai muna kiransu da mafi kyawuntar harshe, muna bayanin gaskiya a fili, muna jayayya da su da abin da ya fi kyawunta kamar yadda Allah ya umarce mu. Yanzu zamu nemi bijiro da tushen da muke bahasi kansa.
Muslunci:
Asasin muslunci shi ne kur’anin muhammad (s.a.w) shi ne addinin Allah wanda ya kagi mutane kansa:
(فطر الناس عليها لا تبديل لخلق الله) (الأنعام: 79)
Ya kagi mutane kanta babu canji ga halittar Allah.
Allah ne mahaliccin mutane, mahaliccin abu shine mafi sani da shi babu makawa, Allah shi ne ya samar da mutum wanda ya samar shine mafi sanin bukatun abin da ya samar yanke babu jayayya.
Muna fadi kumafadinmu gaskiya ce: lallai farin ciki kwanciyar hankali da nutsuwa na cikin muslunci, muslunci wanda da bai bukatar karin bayani kansa, muslunci wanda zamu iya fassara shi da:
(لا جبر ولا تفويض ولكن أمر بين أمرين) (الكافي ـ باب الجبر)
Babu jabar babu tafwidi sai lamari cikin al’amura guda biyu, littafin kafi babin jabar.
Muslunci wanda ya baiwa mai’aikaci `yancinsa da hakkinsa ba tare da iyakoki ba, ga mai rainon aiki ma haka, ga manomi da `dan kasuwa ma haka, kowannensa gwargwadonsa aikin da yake kowannen ggwargwadon ikonsa da iya iyawarsa
(قد جعل الله لكل شيء قدرا) (الطلاق: 3)
Hakika Allah ya sanyawa komai ma’auni. Suratul dalak:3
Ba zai yiwu wani mutum ya ci amfanin wani sai da iyakoki, bai yiwuwa ga `dan kasuwa ya yi kasuwanci ya ci riba face hakkoki,
(واعلموا إنما غنمتم من شيء فلله خمسه وللرسول ولذي القربى) (الأنفال: 41)
Ko sani lallai abin da kuka ci ganima daga wani abu lallai Allah yanada daya bisa biyar dinsa da manzonsa da ma’abota kusanci. Suartu anfal:41
Bai yiwuwa ga manomi ya yi shuka ya girbe face da zakka.
(وأقيموا الصلاة وآتوا الزكوة) (البقرة: 43)
Ku tsayar da sallah ku bada zakka. Bakara 43.
Haka al’amarin yake ga dukkanin ma’abocin kudin shiga da riba.
(خذ من أموالهم صدقة تطهرهم وتزكيهم بها وصل عليهم إنّ صلاتك سكن لهم) (التوبة: 103)
Ka karba daga dukiyoyinsu sadaka ka tsarkake su da ita kayi salati garesu lallai salatinka nutsuwa garesu. Suratu tauba: 103
(وفي أموالهم حق للسائل والمحروم) (الذاريات: 19)
A cikin dukiyoyinsu akwai hakki ga mai tambaya da wanda aka haramta masa.
Wannan itace farin ciki da kwanciyar hankali ya ku masu kaunar farin ciki da kwanciyar hankali babu wani mawadaci d zai cutu babu wani talaka da zai yunwatu. Na’am kwanciyar hankali na wurinmu mu musulmi idan mun san asasin muslunci, farin ciki da kwanciyar hankali na gurinmu karkashin dabbaka hukunce-hukuncen muslunci..muslunci ba wai kadai tsuran suna bane da ake kiran wasu mutane ko wasu al’umma da shi, muslunci akida da aiki, muslunci kundin tsari ne, muslunci hukuma ce da al’umma, musulmi shine wanda ya kyale bukatar kansa don bukatar wasu,
(ويؤثرون على أنفسهم ولو كان بهم خصاصة) (الحشر: 9)
Suna fifita wasusnu kansu ko da kuwa suna da tsananin bukatuwa, suratul hashar:9 musulmi shi ne wanda ya sadaukar da tsatsatsada da saukakka, bai kasancewa cikin wanda fadin baban shahidai (as) ke gasgatuwa kansa ta yadda aka nakalto daga gareshi (as) cikin fadinsa:
(الناس عبيد الدنيا والدين لعق على ألسنتهم إذا مُحصّوا بالبلاء قَلَّ الديّانون)
mutane bayin duniya ne addini kuma yana damfare ne kan fatar harshensu idan aka jarrabce su da bala’i sai ma’abota addini su karanta cikinsu.
Idan dabi’un muslunci mai girma suka tattaru cikinmu da siffofinsa ababen yabawa tabbas zamu kasance musulmi na gaskiya, a wannan zamu rabauta da duniya da farin ciki da kwanciyar hankali ya cikata
(وما عند الله خير وأبقى) (الشورى: 36)
Lallai abin da ke wurin Allah shi yafi alheri da wanzuwa. Surety shura:36
Idan mu muka wanzu a kan abin da muke kai daga nesanta da kiyayya daga muslunci da rarrabuwa da karkasuwa daga musulmi cikin gabashinta da yammaci kudu da arewa toi babu abin da ya rage mana face karbar kaskanci da raunana da tsiyata da wahaltuwa har sai mun farka daga dogon barcin da muke domin kowannenmu ya san
«إنّ الله لا يُغيّر ما بقوم حتى يغيّروا ما بأنفسهم» (الرعد: 11)
Lallai shi Allah fa bai canja abin da ke tare da mutane har sai sun canja abin da ke tare da su.
Cikin muslunci zaku samu rahama.
Nade marhaloli:
ya zama dole ga mutum ya nade wasu marhaloli.
Marhala ta farko: jarintaka, yarinta, tasowa, balaga, mazantaka, dattijantaka, furfura, tsufa, gazawa, zaunuwa.
Cikin dukkani wadannan marhaloli yana karba yana kuma fuskantowa cikar kammaluwa shi ne yana mai nufarsa.
Amman aikinsa: to shi cikin ba’arin wadannan marhaloli yana cikin wata tafiya ne da bai da zabi, yana bin duk inda aka karkata da shi, yana ya fuskantar abin da yake bayarwa, bai sanin daga ina zuwa ina, wannan iatce sunnar tarbiyya mas’uliyar ta ta kuma tana wuyan mai raino, shi ba gareshi ba ga waninsa ba.
Idan ya tsallaka zuwa marhalolin sababbi, zai kallo zuwa ga rayuwa sabanin kallonsa na baya da ya gabata kanta, zai yi ta’ammuli da ita kan hasken alfanunsa na kankin kansa, sai ya zage dantse yayi bakin kokarinsa don ya amfanar da kansa da wahalar kansa, ya kewaya da bukatunsa kamar yadda kwasfo ke kewaye jinjirin wata, ya amafanu kan hasken bukatunsa gwargwadon ikonsa na hankali da jiki, gwargwadon himmarsa, anan wurin kaifin basirar mai basira ke yin tajalli. Daga nan kuma idan mariskansa suka daga imaninsa ya karfafa, hankali ya cika, sai damuwarsa ta dinga motsawa ya daga zuwa ga sabuwar ma’ana da ba kewaya da ita a baya, shine neman yardar Allah matsarkaki ta yadda Allah yake cewa ya daukaka daga mai magana:
(ورضوان من الله أكبر) (التوبة: 72)
Yardar Allah it ace mafi girmama. Suratu tauba:72
A wannan lokaci ne zai manta da bukatun kankin kansa masu kayyadadden lokaci da dade-dade na yanzu-yanzu, ya nufi ya karkata da fuskanta zuwa ga abin da Allah mai girma da daukaka ke yarda da shi, idan ya nemi dandanar zakin yarda zai je masa duk inda ya same shi ya narkar da kansa cikinsa, wannan shi rabauta mai girma.
. (وما يلقاها إلّا ذو حظ عظيم) (فصلت: 35).
Babu mai samunta sai ma’abocin babban rabo. Suratu fussilat:35
Ranar lahadi ishirin da uku ga shawwal karfe sha biyu na azahar.
Daga cikin tambayoyin wanna sashin ()
- Tambaya a takaice: ya zo cikin hadisi hazrat Fatima (as) a wata rana bayan wafatin Manzon Allah (s.a.w) ta yi shaukin ganin Salmanul Farisi sannan Fatima lokacin haduwarta da Salmanu ta sanya gajerun kaya, yaya za ai bayani kan wannan hadisi
- Imam Sadik (as)
- falsafar humanism (mutumtaka) ka'ida ce ta mazhabar Almaniyanci
- Ta yaya za mu iya karbar ko dogaro da masdarin hadisi tareda cewa kwafin asalin masdarin wasu ba’arin malamanmu sun karbe shi ne da kyautata tsammani ba tareda sun san asalin marawaicin hadisin ba ko sun taɓa ganinsa
- Siyasar muslunci zama na Arba’in
- Bahasul karakul fikhu: fatawa halascin karanta surori biyu
- KARIJUL FIKHU RABI’U AWWAL 1441 CIKIN BAYYANAR DA KARATU DA BOYE SHI Qum mai tsarki-Muntada Jabalu Amil Islami tareda Assayid Adil-Alawi
- BEGEN SHUGABAN SHAHIDAI YA ZAUTAR DA NI
- KARIJUL FIKHU 11 GA WATAN RABI'U AWWAL SHEKARA 1441 CIKIN BAHASIN MUSTAHABBANCIN BAYYANAR DA BISMILLA CIKIN AZUHUR DA LA'ASAR 21
- KARIJUL FIKHU 7 GA RABIU AWWAL SHEKARA 1441, KAN MUSTAHABBANCIN BAYYANARWA CIKIN AZUHUR DA LA’ASAR