b Kudin ruwa na ruwa ne
lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Kudin ruwa na ruwa ne



Ya zo a wata hikaya cewa akwai wani mutumi da yazo Madina daga wani gari mai nisa ya wanzu yana aiki cikin Madina ayyuka daban-daban har ya samu damar tara yan wasu kudade ya sayi Saniya yana tatsar nonanta ya sayar, Allah ya Albarkanci wannan Saniya da ya siya ya kara samun wasu kudaden ya sayo wata Saniyar ya kara sayo wata har sai da takai an wayi gari yanada da gona cike da shanu, sai dai cewa wannan mutumi ya jarrabtu da masifar kwadayi da buri har wannan hali ya kai shi ga ya fara yin algus ya na cudanya nono da ruwa ya wayi gari ya tara dukiya mai yawan gaske daga haramun ya kuma zama daga masu kudi, wata rana wata wasika ta zo gareshi da cikinta aka bashi labari cewa yayi gaggawa ya shirya ya taho yanzu haka mahaifiyarsa bata da lafiya  ya taho tun kafin ta mutu, sai wannan mutumi yaji tsoran barin dukiyarsa yayi tafiya ya barsu haka nan, sai kawai ya siyar da gonar da shanunsa, sai ya tafi yaje yah au jirgin ruwa ya nufi garinsu, bayan kwanaki kadan yana cikin tafiya cikin jirgin ruwa sai kawai kakkarfar iska ta taso da fara girgija jirgin dama da hagu sama da kasa tana juya shi, ya zama dukkanin wadanda suke cikin jirgin maza da mata yara a manya sun sami kansu a saman ruwa, wasu cikinsu suna rike da wani abu kamar barin katako ko allako da zai taimaka musu kada su nutse wasu kuma sun nutse kasan ruwa sun mutu.

Amma wannan mutumi sai ya zama shima ya samu wani alloy a rike gam-gam yana iyo har ya samu ya kai ga gabar tafkin cikin aminci, sai ya godewa Allah kan tseratar da shi da yayi, bayan ya dan huta sai ya fito da jakar kudinsa ya bincika ta sai ya ga ya samu kasan da rabin kudin da ya zuba ciki, sai ya fadi shahararriyar maganar nan tasa yace: (dukiyar ruwa ta ruwa ce) ma’ana kudin ruwan da ya kasance yana algus da shi cikin nono ta koma cikin ruwa iya kudin nono tsantsa sun wanzu.  

Tura tambaya