sababun makaloli
- Tarihi » masu tarbiyya ga al'umma
- Fikhu » Mas’ala ta bakwai: kallon gefan hanci a halin sujjada,
- Fikhu » Bahasul Karijul Fikhi shekara 1442 cikin mas’alar shimfida hannun yatsu hade da juna hatta babban yatsa zuwa kusa da kunne
- Akida » Addu’a sirrin ibada
- Akida » Wasiyoyi uku daga Imam Sadik (A.S)
- Akida » Kibiya ta shida
- Akida » Kibiya ta biyar
- Akida » Kibiya ta hudu
- Akida » Kibiya ta uku
- Akida » Kibiya ta uku
- Akida » Kibiya ta biyu-raddi kan Wahabiyawa daga litaffan bangarori biyu-shi’a da sunna
- Akida » Kibiya ta farko-Wahabiya daga Kawarijawa suka fito
- Akida » Kibban Raddi kan wuyan Wahabiyya
- Fikhu » Bahasul Karijul Fikhi- Usul 8 ga watan Jimada Awwal shekara 1442h
- Fikhu » bahasul Karijul fikhi 7 Jimada Awwal shekara 1442 h wada'au shi ne kebantar da lafazi kan wata ma'ana
makaloli
- » Falalar ilimi da malamai
- » mafhumin addini
- » Juyin juya hali na gaskiya da ma’abotansa
- » Daukakar himma
- » Daga ƙissoshin Annabawa amincin Allah ya kara tabbata gare su: kissar Annabi Sulaimanu (as) da shawarar da jemage ya bayar
- » Kashe-kashen ma'arifa
- » Hankali a mahangar makarantar imam kazim (as)
- » KARIJUL FIKHU 7 GA RABIU AWWAL SHEKARA 1441, KAN MUSTAHABBANCIN BAYYANARWA CIKIN AZUHUR DA LA’ASAR
- » Malamai sune magada Annabawa
- » Hasken haskaye nutsuwar zukata
- Akida » Addu’a sirrin ibada
- » Arziki da ni'ima_tareda Alkalamin Assayid Ali bn Husaini Alawi
- » SHIN MUTUM YANA DA ZABI KO KUMA AN MASA TILAS NE_TAREDA AYATULLAH ASSAYID ALI-ALAWI
- » YAYA ZAN RUBUTAWA YARA KISSA
- » Malamai magada Annabawa_ kashi na 3 tarihin Shaik Abbas Qummi
Mukalolin da akaranta dayawa.
- » Addu’o’I da zikiri kan Karin Soyayya a tsakanin ma'aurata
- » Addu’a makamin mumini-tattaunawa tare da Ayatullah samahatus-sayyid husaini shahrudi
- » SIRRIN SALATI
- » Daga ƙissoshin Annabawa amincin Allah ya kara tabbata gare su: kissar Annabi Sulaimanu (as) da shawarar da jemage ya bayar
- » Bahasul karij: Magana mafi karfi itace hade suratu Filu da suratu li’ilafi
- » Sallar Istigfari {NIman gafara} da tasirinta.
- » Me yasa Imam Ali yayi mubayaa wa Abubakar da Umar
- » KAN HANYAR SHUGABAN SHAHIDAI IMAM HUSAINI (AS)
- » Hankali a mahangar makarantar imam kazim (as)
- Akida » Tambaya a takaice: shin Mala'ikan da yake zuwa da surar mutum shima yana da sha'awa
- » HAJJAJU IBN YUSUF!
- » SHIN kana karanta qur'ani
- » Taskar Adduoi 4
- » Taskar Adduoi 2
- » Falalar ilimi da malamai
Dukkanin godiya ta tabbatata ga Allah mai rainon talikai tsira da aminci su kara tabbata ga fiyayyen halitta da iyalan sa jagororin al’umma tsarkaka.
Cikin suratul Fathu Allah ta’ala yana cewa:
(إِنَّا فَتَحْنَا لَكَ فَتْحًا مُّبِينًا * لِّيَغْفِرَ لَكَ اللَّهُ مَا تَقَدَّمَ مِن ذَنبِكَ وَمَا تَأَخَّرَ وَيُتِمَّ نِعْمَتَهُ عَلَيْكَ وَيَهْدِيَكَ صِرَاطًا مُّسْتَقِيمًا * وَيَنصُرَكَ اللَّهُ نَصْرًا عَزِيزًا)
Hakika mun mun yi budi gareka budi mabayyani * domin Allah ya gafarta maka abin da ya gabata daga zunubinka da wana zai zo nan ga domin kuma ya cika maka n’imarsa ya kuma shiriyar da kai tafarki madaidaici* kuma Allah ya taimake ka taimako mabuwayi.
Hakika malaman Tafsiri sun sassaba cikin wadannan ayoyi, sai dai cewa babu laifi mu yi bayani jumlar maganganu cikin su, Allah shi ne mafi sanin manufa daga Fatahu da ya cikin ayar mai albarka, ko dia ya kasance ya zo ne da ma’anar Sulhu Hudaibiya wanda ya kasance share fage zuwa fatahu Makka ko dai ya kasance Fatahu Kaibar ko wani abu makamancin haka.
Daga cikin fuskar da gafartar zunubin da ya gabata da wanda ya jinkirta za ta iya dauka , shi ne zai iya kasancewa zunubin `yan shi’a daga al’ummar Manzon Allah (s.a.w) ko kuma daga al’ummomin da suka gabata, nassoshin ba’arin wasu riwayoyi da suka zo daga Ahlil-baiti (as) yana karfafar wannan fuska, kadai dai Allah ya bayyana shi da sunan zunubin Manzon Allah domin hakan yana bayyana karfafar dangantaka da alaka da take tsakanin Manzon Rahama da al’ummarsa, hakika Annabi (s.a.w) yana cewa Ali (as)
1-يَا عَلِيُّ،إِنَّ اللَّهَ تَبَارَكَ وَ تَعَالَى حَمَّلَنِي ذُنُوبَ شِيعَتِكَ ثُمَّ غَفَرَهَا لِي،وَ ذَلِكَ قَوْلُهُ عَزَّ وَ جَلَّ: لِيَغْفِرَ لَكَ اللّٰهُ مٰا تَقَدَّمَ مِنْ ذَنْبِكَ وَ مٰا تَأَخَّرَ
Ya Ali hakika Allah tabaraka wa ta’ala ya dora mini zunuban shi’ar ka sannan ya gafarta mini su , hakan ya kasance cikin fadinsa domin Allah ya gafarta maka abin da ya gabata daga zunubinka da wanda ya jinkirta.
2-عَلِيُّ بْنُ إِبْرَاهِيمَ:حَدَّثَنَا مُحَمَّدُ بْنُ جَعْفَرٍ،قَالَ:حَدَّثَنَا مُحَمَّدُ بْنُ أَحْمَدَ،عَنْ مُحَمَّدِ بْنِ الْحُسَيْنِ، عَنْ عَلِيِّ بْنِ النُّعْمَانِ،عَنْ عَلِيِّ بْنِ أَيُّوبَ،عَنْ عُمَرَ بْنِ يَزِيدَ بَيَّاعِ السَّابِرِيِّ،قَالَ: قُلْتُ لِأَبِي عَبْدِ اللَّهِ×:قَوْلُ اللَّهِ فِي كِتَابِهِ: لِيَغْفِرَ لَكَ اللّٰهُ مٰا تَقَدَّمَ مِنْ ذَنْبِكَ وَ مٰا تَأَخَّرَ،قَالَ:«مَا كَانَ لَهُ ذَنْبٌ،وَ لاَ هَمٌّ بِذَنْبٍ،وَ لَكِنَّ اللَّهَ حَمَّلَهُ ذُنُوبَ شِيعَتِهِ ثُمَّ غَفَرَهَا لَهُ
Daga Aliyu Ibn Ibrahim: Muhammad Ibn Jafar ya zantar da mu ya ce: Muhammad Ibn Ahmad daga Muhammad Ibn Husaini daga Aliyu Ibn Nu’umanu daga Aiyu Ibn Ayyub daga Umar Ibn Yazidu Bayya’ul Sabiri ya zantar da mu ya ce: na cewa Abu Abdullah (as) fadin Allah cikin littafin sa: domin ya gafarta maka abin da ya gabata daga zunubinka da wanda ya jinkirta, sai ya ce: (bashi da wani zunubi da ya aikata, kuma bai himmatu kan aikata wani zunubi ba, sai dai cewa Allah ya dora masa zunuban shi’arsa sannan ya gafarta masa shu)
الطَّبْرِسِيُّ:رَوَى الْمُفَضَّلُ بْنُ عُمَرَ،عَنِ الصَّادِقِ×،قَالَ: سَأَلَهُ رَجُلٌ،عَنْ هَذِهِ الْآيَةِ،فَقَال
«وَ اللَّهِ مَا كَانَ لَهُ ذَنْبٌ،وَ لَكِنَّ اللَّهَ سُبْحَانَهُ ضَمِنَ لَهُ أَنْ يَغْفِرَ ذُنُوبَ شِيعَةِ عَلِيٍّ×مَا تَقَدَّمَ مِنْ ذَنْبِهِمْ وَ مَا تَأَخَّرَ».
Daga Dabarasi: Almufaddal Ibn Umar ya Rawaito daga Imam Sadik (as) ya ce: wani mutumi ya tambaye shi dangane da wannan aya, sai ya ce: wallahi Manzon Allah bai da wani zunubi, sai dai cewa Allah matsarkaki ya yi masa lamini da ya gafarta zunuban shi’ar Ali (as) daga abin da ya gabata daga zunubinsu da wanda ya jinkirta.
Fuska ta biyu: ya gafarta ya kuma canja akidun mutanen Makka da Kafirai, wadanda suka kasance suna Imani da kudurci kan rashin ingancin maganar Annabi cikin sakon sa wadannan maganganu da suka kasance suna gangarowa daga Annabi a wurinsa suna matsayin zunubi suna la’akari da su matsayi wake da bokanci da hauka amma bayan Fatahu Makka da kuma rungumar muslunci da suka yi da sannu matsayin Manzon Allah (s.a.w) zai bayyana a garesu da kuma kuskuren da suka kasance suna Imani da shi wannan duka ya faru albarkacin Fatahu Makka
Fuska ta uku: gafarta zunubai yana da ma’anar shafe dokoko da yarjeniyoyi da suka gangaro daga kafirai dangane da Annabi (s.a.w) a Makka da kuma tsakanin Kabilu daban-daban, wannan shi ne ra’ayin da Assayid Murtada (r) ya tafi kansa cikin littafin sa Tanzihul Anbiya wal A’imma, ga maganar da yayi ciki: shi ne ya kasance abin da yake nufi daga fadinsa (abin da ya gabata daga zunubin ka) zunubai zuwa gareka domin shi zanbu masdari ne shi kuma masdar ya halasta a jingina shi ya zuwa Fa’ili da Maf’uli duka, ashe baka ga cewa suna fadin:
أعجبني ضرب زيد عمرا
Dukan da Zaidu ya yi wa Amru ya burgeni
Sai suka jingina duka masdari zuwa ga Fa’ili, da kuma fadinsu: (dukan Zaidu daga Amru) anan sai suka jingina shi ga Maf’uli, ma’anar gafara a kan wannan tawili tana kasancewa kawar da hukunce-hukuncen makiyan sa daga mushrikai da lalata su da shafe su, sannan zunbansu zuwa gareshi na nufin hana shi shiga Makka da suka da katange shi daga Masallacin Harami, wannan tawaili yana dacewa da zahirin Magana domin gafara ta kasance manufar Fatahu Makka fuska ga hakan, idan ya kasance ya nufi gafartawa zunubansa to fadinsa: (lallai mun yi maka budi budi mabayyani domin Allah ya gafarta maka abin da ya gabata daga zunubinka da wanda ya jinkirta) ba zai kasance ya bada ma’ana da za ta dace da hankali ba, saboda gafarta zunubi bai ta’allaka da Fatahu ba, saboda bai kasance manufa ba cikinsa, amma fadinsa ta’ala: (abin da ya gabata daga zunubinka da wanda ya jinkirta) baya hana ya zama ya nufi abin da ya gabata daga zamani daga aikinsu mummuna kansa da mutanen sa da abin da ya jinkirta daga tsarkake Annabawa.
Fuska ta hudu: ina fadi sannan Allah ne masani, Magana da aiki cikin ayar farko yana kasancewa da sigar Mutakallim mazi (hakika mun yi budi) sai dia cewa cikin aya ta biyu ya zo da sigar ga’ibi da mustakbal, a ranar lahira, saboda hisabi zai kasance a wannan rana, hakama gafara mafi cika da girma duk a wannan rana za su kasance, a ranar ne za a tashi kowacce al’umma tare da jagoranta sai dai cewa ba komai wannan jagoran ba face lissafi da awon ayyuka da adalcin ubangiji za a yiwa kowacce al’umma hisabi da hisabin jagoranta da sannu Imami zai gabatar da ayyukan al’ummarsa ga hallarar ubangiji, saboda haka ayyukan al’umma za su kasance a hannun Imami sannan Allah zai gafarta zunuban al’ummar Manzon Allah wacce suke hannu da gaban Manzon Allah (s.a.w) a ranar lahira da ceton Annabi ga al’ummar saa hallarar Allah sabida girmansa da matsayinsa a wurin Allah, sabida haka cikin ayar ya kira wannan zunubai na su da zunubin Annabi, wannan fuska tana daga fuskar da zahirin ma’anar wasu daga riwayoyi suke karfafa ta
Fuska ta biyar: ina fadi Allah ne masani, kyawawan rabautattu munanan ayyukan makusanta ne, kan wannan nazariya ne a bisa misali bari aiki mustahabbi ko aikata makaruhi ake daga mutum misalin Manzon Allah (s.a.w) ake kirga shi zunubi sakamakon girman ma’arifarsa kebantacciya kuma madaukakiya da daukakar Allah, duk da bai kasancewa zunubi kan sauran gama garin mutane
Daga cikin tambayoyin wanna sashin ()
- Falalar ilimi da malamai
- Rigima da dauki ba dadi tsakanin hankali da wahami
- MALAMAI MAGADA ANNABAWA_TARIHIN SHAIK JAFAR TUSTARI.
- bayanin annabta
- HAJJAJU IBN YUSUF!
- gudummawar imam sadik (as) cikin gina al'umma ta gari
- Ma'aikaci tsoho
- Bahasul karakul fikhu: fatawa halascin karanta surori biyu
- Ili yasin cikin kur’ani_tareda Assayid Muhammad Alawi
- Imamu Ali shine hanya madaidaiciya