b TAKAITACCE SAKO KAN ASALAN ADDINI DA RASSANSA
lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

TAKAITACCE SAKO KAN ASALAN ADDINI DA RASSANSA

Da sunan ubangiji tushen Rahama da tautayi da jin kai, dukkanin godiya ta tabbata gareshi mabuwayi tsira da amincinsa su kara tabbata ga fiyayye halittu alal idlak Muhammad da iyalansa tsarkaka.

Bayan haka hakika imani da addini bai samun karfafuwa face sai an fara sanin tushen magangararsa wato Allah mabuwayi cikin zati da siffa, larurar hakata sanya mu rubuta wata yar takaitacciyar Risala da ta kunshi bayani kan Asalan addini da Rassansa ma'ana abubuwa da suke biyo bayan tabbatuwar Asalai.

 

1-Tauhidi: da ma'anar cewa lallai Allah matsarkaki shi ne makagin wannan duniya mahaliccintashi kadai ne bashi da abokin tarayya.

2-Adalci: da ma'anar lallai Allah adali ne baya zaluntar bayi shi mai taushi ne ga bayinsa da ludufi.

3-annabta: da ma'anar lallai Allah ya aiko manzanni ya tura da Annabawa domin shiryar da mutane.

4-Imamanci: da ma'anar Allah ya nassaba wasiyyai ga manzanninsa, domin su kare shari'arsu, su kuma shiryar da mutane zuwa gaskiya.

5-Ma'ad: da ma'anar ranar tashin Kiyama domin Allah ya saka wanda yayi masa biyayya da sakamakonsa hakama wanda ya saba masa.

 

Rassan addini goma:

1-Sallah

2-Azumi

3-Zakka

4-Kumusi

5-Hajji

6-Jihadi

7-Umarni da kyakykyawa

8-Hani da mummuna

9-Wilaya ga Allah da manzansa da Ahlil-baiti

10-Barranta daga makiya Allah da Manzonsa da makiya Ahlil-baiti.

da sannu bayani da bahasi filla-filla dalla-dalla zai zo insha Allah ta'ala.

Takilid bai halasta ba zargi da zato bai isarwa cikin sanin Asalan addini (usulul dini) bari dai dole ne ya kasance daga zage dantse da Ijitihadi da samo dalili da ilimi da yakini, amma rassan addini (furu'ud dini) ma'ana wajiban shari'a da hukunce-hukuncen muslunci da suka ratayu da ayyuka, ba wajibi bane cikinsu yin ijtihadi, bari ya halasta mukallafi ya kasance mujatahidi cikinsu da yake da iko da kudurar mayar da rassa zuwa ga asalai da yalwatawa cikin tsamo hukunce-hukunce shari'a daga dalilansu na filla-filla daga littafin Allah da sunna da ijm'ai da hankali, hakama ya halasta cikin rassa mukallafi ya kasance muhtadi cikin ayyukansa cikin abin da yake da yalwar yin ihtiyadi, hakika shari'ar muslunci ta wajabtawa mukallafi yin taklidi da mujtahidin da yake dakwarewa cikin iliman muslunci cikin rassa daga halal da haram, sannan muslunci ya haramta yin takildi cikin asalan addini (usulud dini) sharia'ar muslunci bata yi sausauci ga kowanne mukallafi ba da yin taklidi cikin Akidun addini, bari dai sanin akida yana lazimta a shari'ance da hankalce gasgata ubangijinsa da annabinsa da imaminsa da ma'ad dinsa makomarsa lahirarsa.

baki dayan malamai sunyi ijma'i kan wajabcin sanain asalan addini (usulud dini) da dogaro da dalili da bawai da taklidanci,

kowanne daga ckin mutane shi ke daukar nauyin sanin akidarsa a wuyansa maimakonin taklidanci da ra'ayinsu wasu da dora masu nauyin bincike da sanin asalan addinininsa.

Hakika Allah ya zargi wadannan da suke dora nauyin sanin asalan addininsu kan wuyan iyayensu don gujema nauyinsa, ko kuma sakamakon ta'assubanci ko kasala da jumudi da daskarewar kwakwalwa da hankali, kamar yadda ya zo cikin fadinsa madaukaki:          

(إنَّا وَجَدْنَا آبَاءَنَا عَلَى اُمَّةٍ وَإنَّا عَلَى آثَارِهِمْ مُـقْـتَدُونَ ) .

Lallai mu mun samu iyayenmu kan wata al'ada lallai kuma mu kan gurabensu masu shiriya ne.[1]

 

Kadai an kallafawa kowanne mutum guda daga cikinmu da yin bahasi da bincike da zurfafa tunani cikin addininsa gwargwadon yadda ya dace da mustawansa da tanadinsa, lallai Allah bai kallafawa rai face abin da ya yalwaceta.

Hakika Allah matsarkaki ya kwadaitar kan yin bincike da Kafa dalili cikin fadinsa madaukaki:

 (آئْـتُونِي بِكِتَابٍ مِنْ قَبْلِ هَذَا أوْ أثَارَةٍ مِنْ عِلْمٍ إنْ كُـنْتُمْ صَادِقِينَ ) .

Ku zo mini da littafi gabanin wannan ko kuma wani gurbi alama daga ilimi idan kun kasance masu gaskiya.[2]

 

Cikin furu'a rassa idan mutum bai kasance daga masu ikon yin ijtihadi ba bai kuma kasance daga masu ihtiyadi ba to wajibi kansa yayi taKlidi da malaman fikihu Maraji'ai lallai su amintattun manzanni cikin al'umma matukar basu kasance daga masu biyewa duniya ba, lallai malamai sune magada annabawa, hakika ya zo cikin hadisi mai daraja daga maulana shugabanmu Sahibuz-zaman amincin Allah ya kara tabbata gare shi Allah ya gaggauta bayyanarsa madaukakiya:

«فأمّا من كان من الفقهاء صائنآ لنفسه ، حافظآ لدينه ، مخالفآ لهواه ، مطيعآ لأمر مولاه ، فعلى العوام أن يقلّدوه ».

Amma wanda daga cikinku ya kasance mai katantge kansa, mai kiyaye addininsa, mai sabawa bin son ransa, mai da'a ga umarnin ubangijinsa, to wajibi mutane game gari suyi taklidi da shi.

 

Shi muslunci Akida ce da aiki, ya tattaro Asalai da rassa.

Asalai sune aKidoji wadanda muslunci ya wajabta imani da su, dukkanin wanda bai yi imani da su to shi ba mumne bane, ilimin da ke daukar nauyi bayanin wadannan asalai da karfafarsu da hujjoji da dalilain hankali da dalilan nakali shi ne ilimin (kalam) amma rassa sune hukunce-hukunce da suka ratayu kan wadanda aka kallafawa yin ibada daga ciki abin da ke gangarowa daga su mukallafan da ya shafi rayuwarsu ta yau da gobe wanda ake kira da mu'amalat, sannan ilimi da yake daukar nauyin bayanin wadannan ibadoji da mu'amaloli na hukunce-hukuncen rassa shi ne(ilimin fikihu) samun sanin hukunce-hukuncen shari'a na rassa hyena kasance ta hanya guda biyu: ijtihadi ga wanda ya nemi iliminsa da zama fakihi masanin fikihu, taklidi ga wanda bazai iya tsamo hukunci daga dalilansa na filla-filla ba.

Muslunci yana farlanta aiki da hukunce-hukuncen addini, sannan dukkanin wanda bai aiki da su ba lallai bai daga cikin masu yiwa Allah girmansa ya girmama da manzon Allah mafi karamci (s.a.w) da shugabannin Al'umma wadanda Allah da Manzonsa suka nasabta ta su ga al'umma da'a da biyayya.

 Wannan kenan sannan dalilin dawwana wannan `yar karama Risala wacce na sanya mata suna da (Akidun Muminai) shi ne cewa lallai ita ta kasance daga babin shimfida zuwa ga littafin fikihu mai suna (minhajul muminin) wand ana rubuta cikin mas'alolin fikihu don ya kasance risala ilimiyya da ta dace da fatawowin Samahatus Ustaz Ayatollah Uzma Assayyid Mar'ashi Najafi (rd) hakika an buga wannan risala cikin godiyar Allah cikin mujalladai biyu na farko ya kunshi abin da a shafi ibadoji mujalladi na biyu kuma abubuwan da suka danganci mu'amalat. Allah matsarakaki ya so wannan mukaddima ta fito bayan an buga galibin abin da ke cikinta cikin jaridar larabci mai suna Kihan Banagaren sakafa da wannan tsari mai cin gashin kansa, sai nayi bakin kokarina daga abin da na samu dama daga lokaci daga abin da ya shafi asalan addini da rassansa, ina mai kafa dalili da dalilan hankali dana nakali daga littafin Allah da sunna tare da bin tsarin kauracewa tsawaitawa da kuma tare da ishara.

Hakika na gangara bahasosin asalan addini ina mai bayaninsu filla-filla dalla-dalla cikin darasussuka da gidan rediyon jamhuriyar muslunci ta iran suka nada a watan ramaan shekara ta 1408, hakika aya daga mutane masu daraja daga cikin wadanda nake kansatuwa cikin hidimasu ciikin bada darasussuka a hauza ilimiyya dake cikin birnin Kum mai tsarki ya naKalo cikin kaset kamar yadda cibiyar majma'ul ilimi ta Daliban Kasar Bahrain dake Kum, bugu da Kari harkar hijira da `yan hijira suma sun nakalci darasina ga da na bayar na littafin babul hadi ashara gabanin `ya shekaru da suka gabata, Allah ya sakawa dukkaninsu da alheri, hakama na rubuta sharhin littafi babul hadi ashara cikin juzu'ai da sunan (Bidayatul fikri fi sharhi Babul Hadi Ashara) shi ne mafi cika da bayanin filla-filla.

Hakama an nadi sautin darasina da nayi kan littafin Tajrid juzu'ai na kuma rubuta shi cikin juzu'aida sunan (Kaulul hamid fi sharhi tajrid)

Wannan duka bai kasance komai ba face daga falalar ubangijina mai girma da Daukaka, ina rokon ubangijina mai ikon yi matsarkaki madaukaki da ya bani dacewa da katanguwa bani da wni taufiki face da Allah da shin a dogara gare shizan koma, Allah na bayan manufa, Karshen magarnarmu dukkanin godiya ta tabbata ga Allah mai rainon talikai.

 

«اللهمّ عرّفني نفسک ، فإنّک إن لم تعرّفني نفسک لم أعرف رسولک .

اللهمّ عرّفني رسولک ، فإنّک إن لم تعرّفني رسولک لم أعرف حجّتک .

اللهمّ عرّفني حجّتک ، فإنّک إن لم تعرّفني حجّتک ضللت عن ديني .

اللهمّ لا تمتني ميتة الجاهلية ، ولا تزغ قلبي بعد إذ هديتني ، وهب لي من لدنک رحمة ، إنّک أنت الوهّاب ».

Ya Allah ka sanar da ni kanka* lallai kai idan baka sanar da ni kanka ba ba zan taba sanin manzonka ba.

Ya Allah ka sanar manzonka* lallai kai idan baka sanar da ni manzonka ba bazan taba sanin hujjarka ba.

Ya Allah ka sanar dani hujjarka* lallai kai idan baka sanar da ni hujjarka ba zan bata ga barin addini na.

Ya Allah kada ka kashe ni mutuwar jahiliya, kada ka karkatar da zuciyata bayan ka shiryar dani, ka bani rahamar aga gareka, tabbas kaine mai yawan kyauta.


«يا الله، يا رحمن يا رحيم ، يا مقلّب القلوب ، ثبّت قلبي على دينک ».

Ya Allahu ya Rahmanu ya mai jujjuya zuciya ka tabbatar da zuciya ta kan addininka.

 

[1] Zukruf:23

[2] Ahkaf:4


Tura tambaya