b taklidi shine riko da ra’ayin wani domin aiki da shi a far’aiyyat ko kuma lazimtarsa cikin akidu
lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

taklidi shine riko da ra’ayin wani domin aiki da shi a far’aiyyat ko kuma lazimtarsa cikin akidu

Wuri: birnin Qum mai tsarki- Muntada Jabalul Amil Islami tareda Assayid Adil-Alawi.

Lokaci: karfe 9 na safe.

Usul (89) 27 ga watan Shawwal shekara 1442 hijiri

 

Fasali cikin bayanin taklidi:

Muhakkikul Hilli (k.s) yace: shi taklidi shine riko da ra’ayin wani Fakihi domin aiki da shi cikin far’iyyat ko lazimtarsa a akidu a bautance ba tareda bincika dalili kan ra’ayin nasa ba.

Ina cewa: maganar tana kasancewa bayan sanin menene ijtihadi a luggance da isdilahi da abinda ya ta’allaka da shi daga hukunce-hukuncen taklidi, bayani kan ijtihadi ya gabata a matsayin shi hattamawa ga ilimin usul kamar yanda muka sani Muhakkikul Hilli bai gushe daga munasaba ba, sai dai cewa bahasi gameda taklidi da abinda ya ta’allaka da shi bahasi ne da yake gamewa bada ban hakan sai muce muhallinsa yana can cikin ilimin fikhu.

Bayann nan sai Muhakkikul Hilli ya gangara zuwa ga mas’aloli guda uku cikin taklidi: ta farko: dalilan wajabcin yin taklidi kan Ba’amen mutum wand aba Mujtahidi ba, ta biyu: wajabcin yin taklidi da A’alam mafi ilimi, ta uku yin taklidi da Mujtahidin da ya rigaya ya mutu, wannan fasali an tanade shi domin da kuma bayanin dalilan da suka shiryar kan halascin yinsa a sharia’nce.
akwai cigaba.

Tura tambaya