■ DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN QAI
■ FASALI NA FARKO : MALHAMOMI NA FARI GAME DA
■ FASALI NA BIYU
KASHE-KASHEN DALILAN SHARI'A
SIRRIN IBADA DA HAJJI
ABUBUWA NA MUSAMMAN WADANDA SUKA KEBANTA GA KA'ABA DA AIKIN HAJJI.
SIRRIKAN HAJJI CIKIN TASFTACE ZUKATA
DAGA CIKIN SIRRAKAN AKWAI SIYASA DA ZAMANTAKEWA
DAGA CIKIN SIRRIKAN HAJJI NA IRFANI
Daga cikin muhimman sirrikan irfani a cikin hajji:
NAU'O'IN HAJJI DA BA'ARIN SIRRI CIKIN MUQADDIMARSA
■ DAGA FALSAFAR HAJJI CIKIN ALQUR'ANI
■ DAGA CIKIN SIRRIN AYAR HAJJI
■ KUFAIFAYIN HAJJI DA UMARA CIKIN DUNIYA DA LAHIRA KAMAR YADDA YA ZO CIKIN HADISAI
■ JIKKANTUWAR HAJJI GA ASALAN ADDINI
■ HAJJIN JAZZURU(RAQUMI) DA HAJJIN USFURI(TSATSTSEWALA
■ FASALI NA HUDU
■ DAGA SIRRIKAN HARAMIN MAKKA
■ Daga cikin sirrikan miqatai
■ DAGA CIKIN SIRRIKAN MAKKA MAI KARAMACI DA MASALLACIN HARAMI
■ DAGA CIKIN SIRRIKAN DAKIN KA'ABA MAI DARAJA
■ DAGA SIRRIKAN DUTSEN HAJARUL ASWAD
■ DAGA CIKIN SIRRIKAN MUQAMU IBRAHIM
■ DAGA CIKIN SIRRIKAN HADIMU DA WANDA AKE LAZIMTA
■ DAGA CIKIN SIRRKAN HAIMA (DAKIN) ISMA'IL(AS)
■ DAGA CIKIN SIRRIKAN MUSTAJAR DA RUKUNUL YAMANI
■ DALILIN SHAFAR RUKUNUL YAMANI
■ FALALAR MUSTAJAR DA LADUBBANSA
■ DAGA CIKIN SIRRIKAN RIJIYAR ZAMZAM
■ DAGA CIKIN SIRRIKAN DUTSEN SAFA DA DUTSEN MARWA
■ SIRRIKAN HAJJI WAJEN IMAMU SADIQ(AS)
■ DAGA CIKIN SIRRIKAN MIQATI
■ FASALI NA BIYAR
■ DAGA CIKIN SIRRIKAN HAJJI
■ DAGA CIKIN SIRRIKAN TALBIYYYA(FAXIN LABBAIKA
■ DAGA SIRRIKAN BARIN ABUBUWAN DA AKA HARAMTA
■ DAGA CIKIN SIRRIKAN XAWAFI
■ DAGA CIKIN FALSAFAR XAWAFI
■ Daga cikin falsafar xawafin nisa'i
■ DAGA CIKIN SIRRIKAN SALLAR XAWAFI
■ DAGA CIKIN SIRRIKAN SA'AYI
■ DAGA CIKIN SIRRIKAN SIRRIKAN SAISAYE DA ASKI
■ DAGA CIKIN SIRRIKAN TARWIYYA
■ DAGA CIKIN SIRRIKAN ARAFAT
■ DAGA CIKIN SIRRIKAN MAHS'ARUL HARAM
■ DAGA CIKIN SIRRIKAN MINA
■ DAGA CIKIN SIRRIKAN JIFAN JAMARAT
■ DAGA CIKIN SIRKAN HADAYA
■ DAGA CIKIN SIRRIKAN IBADUN CIKIN HAJJI
■ FASALI NA SHIDA
■ ku cika hajji da umara
■ XAWAFIN BANKWANA DA LADUBBANSA
■ KARBUWAR HAJJI DA HASKENSA
■ ADADIN HAJJIN DA ANNABI YA YI DA UMARARSA
■ HAJJIN ANNABAWA
■ TSUGUNARWAR DA IBRAHIM (AS) YA YIWA XANSA DA MATARSA A GARIN MAKKA
■ XAGA HARSASHIN GININ XAKIN KA'ABA DA HANNUN IBRAHIM DA ISMA'IL(AS)
■ QISSAR YANKAN IBRAHIM GA XANSA ISMA'IL{AS}
■ KHATMA
■ CIKIN ZIYARAR ANNABI MAFI GIRMA MUHAMMADU DA IYALANSA TSARKAKA.
■ DAGA CIKIN LADUBBAN BIRNIN MADINA HASKAKKA.
■ DAGA CIKIN FALALOLIN ZIYARA DA SIRRIKANTA
■ DANGANTAKAR MANZON ALLAH(S.A.W) DA AL'UMMA
- KIBIYOYIN RADDI KAN WUYAN WAHABIYAWA
- CIKIN HALLARAR ALHERI
- HUJJOJIN HALASCIN YIN TAKIYYA A MUSLUNCI DAGA MAHANGAR MANYAN MALAMAI GUDA BIYU
- FARKAR DA MAI BACCI CIKIN TABBATUWAR GANIN IMAM KA'IM A.S
- ALAMOMIN ANNABI CIIKIN KUR'ANI MAI GIRMA
- HAKURI DA FUSHI
- Bada'u tsakanin hakika da kagen makiya
- FALALAR DAREN LAILATUL KADRI
- WAHABIYANCI A TSAKANIN GUDUMA DA
- HASKEN SASANNI CIKIN SANIN ARZIKI
- AQIDUN MUMINAI
- FATIMA TAGAR HASKAYE
- SIRRIKAN AIKIN HAJJI DA ZIYARA
- TARBIYYAR IYALI A MAHANGAR ALKUR'ANI DA AHLULBAITI
Dukkanin godiya ta tabbata ga Allah wanda ya sanya kalmar la'ilaha illa lahu matsayin qarfafaffen shinge dukkanin wanda ya shige shi zai kasance cikin aminci ya kuma sanya `yantaccen xakinsa mai albarka shiriya wajen samun lada ga mutane dukkanin wanda ya shiga cikinsa zai kasance cikin aminci, ya sanya ziyartarsa da kewaya shi tuba da da hijabi tsakanin bawa da azaba mai qasqantarwa.
tsira da aminci su tabbata ga annabin rahama zababbe amintacce muhammadu shugaban annabawa cika makin manzanni, da iyalansa ma'asumai tsarkaka jagororin gaskiya shuwagabanni halittu baki xaya.
godiya da yabo sun tabbata ga Allah.
Godiya da tabbata ga ubangijin talikai, sunansa na rububiya yana yin tajalli cikin tarbiyar halittunsa, haqiqa ubangiji matsarkaki tun daga halittar adamu (as) ya zuwa tashin qiyama ya ayyana wata salsala ta ibadar gangar jiki da ta ruhi ga bayinsa, haka ya ayyana ayyuka addini da na kyautata xabi'u, da ke da hadafin tarbiyantar da mutum da kuma sanya shi bawan Allah nagari da zai kasance halifan Allah wanda Allah zai halifantar da shi cikin zababbun sunayensa da maxaukakan siffofinsa don ya cimmma kamalarsa da ta fi cancanta da shi bisa abin da aka ajiye cikinsa daga sirrika na xabi'a da wanda suka buya daga xabi'a, lalle mutum qarqashin inuwar waxannan ibadoji da kyawawan xabi'u da aikata su a kankin kansa tare da ubangijinsa da kuma tare da jama'a da xabi'a zai kai ga kamalar da aka ajiye cikinsa da kaiwa ga hadafin halittarsa ya cimma nasibinsa mafi cika da rabonsa mai girma daga daxaxan baxini da na ruhi cikin duniyoyin biyu wato duniyar malak da malakutiyya, ko kuma ace duniya da lahira da gaibu da bayyane.
Idan mutum ya kasance fursunan son zuciyarsa ya kuma kasance qasqantaccen zuciyarsa mai yawan umarni da mummuna, sai dukkanin miyagun ayyukansa da munan halayensa su kewaya da shi, sai ka same shi yana zakkewa munanan ayyuka da muggan zunubai da siffantuwa da dukkanin halaye masu muni, a irin wannan hali ruhiyarsa da ma'anawiyya za su wayi gari jinginannu cikin duniyar tanadi da jinkiri, ba zaka same shi ya kai ga duniyar aiki da rayuwa ba haka zai zauna kasashshe rarrauna wanda bai iya riskar xanxanon hankali da ma'nawiya da ruhiya, sakamakon shi bai da tanadi da zai iya kasancewa tare da duniyar malak da malukitiyya, shi ya fi kama da a siffanta shi da mutumin qauye wanda bai karatu ba da aka sanya shi cikin xakin nazari da ya ke cike da manyan-manyan littafai masu tarin fa'ida, shin irin wannan mutumin zai iya fa'idantuwa da wannan xakin nazari da abin da ya ke cikinsa?
Sannan bugu da qari shi halittar duikkanin halittu bata kasance don wargi da sakarci ba, sakamakon haka na cin karo da kalmar mahalicci da luxufinsa da iliminsa
(وَمَا خَلَقْنَا آلسَّمواتِ وَآلاْرْضَ وَمَا بَيْنَهُمَا لاَعِبِينَ * مَا خَلَقْنَاهُمَا إِلاَّ بِالْحَقِّ وَلكِنَّ أَكْثَرَهُمْ لاَ يَعْلَمُونَ(.[1]
bamu halicci sammai da qasa ba da abin da ke tsakankaninsu don muna wargi ba* bamu halicce su ba face don gaskiya sai dai cewa mafi yawansu basu da ilimi kan haka.
Sannan shi hadafi da manufar halittar halittu da halittar xan adam a kebance bai komawa ga mhalicci matsarkaki sakamakon shi ubangiji mawadaci ne cikin zatinsa bai da buqatuwa da komai, kaxai dai hakan na komawa ga xan adam a kankin kansa don ya kai ga qololuwar kamala da kyawunta da girma.
قال أميرالمؤمنين 7 في مقدمة خطبة همّام : «إنّ الله تعالى خلق الخلق حين خلقهم غنيّاً عن طاعتهم ، آمناً من معصيتهم ، لأنّه لا تنفعه طاعة من أطاعه ، ولا تضرّه معصية من عصاه ».
Sarkin muminai Ali(as) cikin muqaddimar hauxubar hammam ya na cewa: lalle shi Allah ya halicci halittu ya na mawadaci daga xa'arsu ya yin da ya ke halittarsu, ya na mai aminta daga dukkanin sabonsu, sakamakon biyayyarsu ba ta amfana masa komai haka kuma sabon mai sabonsa bai cutar da shi da komai.
haqiqa an assasa mazhabobi da makarantu ba don komai sai don tarbiyyar mutum da kama hannunsa ya zuwa kamalarsa, sai dai cewa waxanda suka yi wannan yunkuri sun wuce gona da iri wani lokacin kuma suna taqaitawa sakamakon jahilcinsu kan haqiqanin mutum cikin gininsa na gangar jiki da ruhi, sai dai cewa ubangiji matsarkaki bai barsu haka ba kara zube ba tare da yi musu bayanin hanyar gaskiya da hanyar bata ba, haqiqa ya aiko musu manzanni da annabawa ya sauko da littafi sakamakon shi ne mafi sanin abin da ya halitta wanda shi ne ya cancanci yabo cikin faxinsa:
: (فَتَبارَکَ آللهُ أحْسَنَ آلخالِقينَ )[2]
Albarku sun tabbatar masa mafi kyawun masu halitta.
haqiqa ya halicci mutum cikin mafi kyawun tsayuwa, ya kuma sanar da shi abin da bai sani ba ya tsarkake shi, ya tarbiyantar da shi da umarninsa da haninsa, sakamakon abin da ke ciki na daga maslahohi da barna.
annabawa da wasiyyai da dukkkanin wanda ke bin sawunsu daga magadansu da malamai nagargaru sun tabbatar da abin da ya zo daga wajen matsarkaki cewa hanyar kamalar mutum shi ne bautawa Allah girma ya tabbatar masa, babu wata hanya zuwa gareshi koma bayanta, sannan ita bautar Allah ita ce tsantasar zurfafar ubangijintaka kamar yadda ya zo cikin hadisil qudusi mai daraja:
: «عبدي أطعني حتّى أجعلَکَ مثلي ، أقول للشيء كُن فيكون ، وتقول للشيء كُن فيكون
bawana ka yi mini biyayya zan sanya ka misalina irina, ina ba da umarni ga abu sai wannan abu take ya kasance, to kai ma za ka ba da umarni ga abu ta ke ya kasance.
haka cikin inagantaccen hadisi da bangare biyu suka naqalto ma'ana shi'a da sunna:
ـ عن رسول الله 6 في حديث قدسي عنّ الله عزّوجلّ : «ما تقرّب إليّ عبد بشيء أحبّ إليّ
ممّا إفترضت عليه ، وانّه يتقرّب إليّ بالنافلة حتّى اُحبّه ، فاذا أحببته كنت سمعه
الذي يسمع به ، وبصره الذي يبصر به ، ولسانه الذي ينطق به ، ويده التي يبطش به».[3]
ankarbo
daga manzon Allah(saw) ya ce: bawana bai kusance ni da wani abu mafi soyuwa
gareni ba fiye da abin da na farlanta kansa, lalle shi ya na kusanta ta da
nafiloli har in so shi, idan na so shi sai in kasance jinsa da ya ke ji da shi,
in kasance ganinsa da ya ke gani da shi, da harshensa da ya ke furuci da shi,
in kasance hannunsa da ya ke damqa da shi ya ke azaba da shi.
maqasudi kan mutum shi ne tarbiyya da gamsar da garizar son kamala da kyawu da alheri boyayye wanda ya ke da tushe da jijiya cikin halittarsa xayantatta lafiyayya, daga nan ne zai kai ga zirai biyu ko kuma mafi kusa daga mafi xaukaka, cikin matsugunin gaskiya wajen sarki mai iko, sai Allah matsarkai ya kasance jinsa da ganinsa da harshensa da hannunsa, kamar yadda ba zai gushe ba ya na kusantar Allah da farillai har sai Allah ya kasance jinsa ganinsa harshensa hannunsa, banbanci nawa ne tsakanin kusancin biyu kusanci da farillai da kusanci da nafiloli kamar yadda hakan yake sanannen al'amari wajen ahalinsa.
Sannan don bawa ya samu tsayuwa cikin ibadarsa kan ruhinta lalle shi ya na qoqarin gano sirrikanta da luxufinta da falsafarta da ladubbanta na zuciya da na ma'nawiya.
daga wannan tunani ne ka ke ganin jama'a daga manya-manyan malamai a kowacce mazhaba daga mazhabbin muslunci musammam makarantar iyalan manzon rahama cikin ziri daga rubuce –rubucensu suka zage dantse don bayanin wani ba'ari daga sirrikan ibada daga cikin waxannan ibadoji akwai ibadar (hajji da ziyara) saboda abin da ke tattare da su daga ayyukan ibada mabanbanta da xayantattu, waxanda a kansu akwai tattarowa, akwai sigar xayanta da jama'a daga abin da ke sanya ban mamaki daga dukkanin matakan al'ummu
kowanne
mutum guda cikin hajjinsa da umararsa yakan tambayi kansa me yasa aka sanya
wannan ayyuka na hajji da umara da wannan shakali mai ban mamaki?
! lalle dukkanin
alfanun ibadoji na komo garemu ne, lalle shi Allah wadatacce ne a zatinsa,
saboda haka menene alfanu da zamu iya gani a ayyukan hajji?
اللّهمّ إنّ أقدامنا قاصرة عن الوصول إلى جناب قدسک ، وإنّ أيدينا قاصرة عن النيل إلى ذيل اُنسک ، وإنّ حجب الشهوات والغفلات قد حجبت بصائرنا عن جمالک الجميل ، وإنّ الأستار الكثيفة الناشئة من حبّ الدنيا ومن أعمالنا الشيطانيّة قد صيّرت قلوبنا مهجورة عن التوجّه إلى عزّ جلالک ، إن صراط الآخرة لدقيق ، وان طريق الانسانيّة لحديد، ونحن المضطرون في فكرتنا كالعنكبوت قديد، ونحن الحائرون كدود القزّ قد نسجنا لأنفسنا سلاسل الشهوات والآمال ، فها نحن فيها مقيّدون ، وعن عالم الغيب ومحفل الاُنس بالمرّة آيسون ، اللّهمّ إلّا أن تبرق لأبصارنا وقلوبنا ببارقة إلهية ، فتنورنا وتجذبنا بجذبة غيبيّة يذهلنا بها عن أنفسنا.
ya Allah haqiqa qafafuwanmu sun gaza zuwa farfajiyar tsarkinka, hannuwanmu sun gaza samun xebe hasonka, lalle hijaban sha'awe- sha'awe da gafala sun hijabance ganinmu daga kyawunka, lalle kauraran labulaye waxanda suka bubbugo daga son duniya da ayyukan shaixananci sun mai da zukatan mu gudaddu daga fuskantar ya zuwa xaukakar girmanka, lalle siraxin lahira dandaqaqqe ne, lalle hanyar mutumtaka ta yi tsauri, mu mun rikirkice mun gigice cikin tunanin mu kamar gizo-gizo, lalle mu gigice kai kace tsutsar da ke cikin alhariri mun saqawa kawukan mu sasarin sha'awe-sha'awe da burace-burace, ga mu a xaxxaure cikinsa muna masu xebe tsammani daga duniyar gaibu da xebe haso,ya Allah sai dai idan ka haskaka ganin mu da zukatan mu da walqiyar bautarka sai ya zamanto ta haskaka mu ta fisge mu da fisgar gaibu da zai gigita mu da ita daga kawukan mu.
«الهي هب لنا كمال الانقطاع إليک ، وأنر أبصار قلوبنا بضياء نظرها إليک ، حتّى تخرق أبصار القلوب حجب النور، فتصل إلى معدن العظمة ، وتصير أرواحنا معلّقة بعزّ قدسک » .
ya Allah ka ba mu kamalar yankewa ya zuwa gareka ka haskaka idanuwan zukatan mu da hasken kallo ya zuwa gareka, har idaniyar zukatan mu su keta hijabai su kai ga ma'adanin girmanka, ruhin mu su kasance rataye da izzar tsarkinka.
lalle shi aikin hajji kamar ragowar ayyukan ibada ne ya na da zahiri da baxini da surarsa da ma'ana, kamar yadda zahiri ya na da ladubba da hukunce-hukunce waxanda rashin kiyaye su ke kaiwa ga lalacewa da gurbatar hajji cikin surarsa da zahirinsa, to haka zalika baxininsa ma na da na sa ladubban hikimomi na zuciya da ruhi waxanda su ma rashin kiyaye su da aikata su da rashin maida hankali kansu ke kaiwa ga gurbata da tawaya cikin hajji cikin ma'anarsa da baxininsa. Amma idan ya kula da kiyaye su cikakkiya kulawa ga waxancan ladubba na ma'anawiyya da na zuciya, babu makawa mahajjaci zai kasance cikin ruhin malakutiyya, mahajjaci da umara bayan ya kiyaye ladubban baxini ya ba su kulawa da himma, to akwai fatan cewa zai samu nasibi daga sirrin Allah wanda ya ajiye shi cikin hajjin ma'abota ma'arifa da ma'abota zukata wadda itace sanyin idaniyar ga ma'abota suluki, sannan shi haqiqanin mi'raji shi ne samun kusantar masoyi, wannan shi ne abin da dalili da irfani da qur'ani ke shaidawa.
daga cikin abin da ke nuni kan cewa mutum na ganin baxinin ayyukansa shi ne faxin Allah maxaukaki:
: (يَوْمَ تَجِدُ كُلُّ نَفْسٍ مَا عَمِلَتْ مِنْ خَيْرٍ مُحْضَراً وَمَا عَمِلَتْ مِن سُوءٍ تَوَدُّ لَوْ أَنَّ بَيْنَهَا وَبَيْنَهُ أَمَداً بَعِيداً) [4]
Ranar da kowanne rai za ta samu abin da ta aikata daga alheri da abin da ta aikata na sharri an halarto mata da shi, za ta fatan ace akwai fage mai nisa tsakaninta da shi.
na baxini da gaibu, ayyukan su da surar jiki kamar yadda wanda suka zabi tafiya kan kasantuwar jikkantuwar ayyuka wanda hakan shi ne zababben ra'ayi nima a gurina.
وَوَجَدُوا مَا عَمِلُوا حَاضِراً)[5]
suka samu abin da suka aikata a halarce.
(وَمَا تُقَدِّمُوا لاِنفُسِكُم مِنْ خَيْرٍ تَجِدُوهُ عِندَ آلله.[6]
abin da kuka aikatawa kawukanku daga alheri za ku same shi wajen Allah.
(فَمَن يَعْمَلْ مِثْقَالَ ذَرَّةٍ خَيْراً يَرَهُ )[7]
duk wanda ya yi wani aiki gwargwadon kwayar zarra zai ganshi.
(يَوْمَ يَنظُرُ آلْمَرْءُ مَا قَدَّمَتْ يَدَاهُ. [8]
ranar da mutum zai kalli abin da hannuwansa suka gabatar.
misalin waxannan ayoyi da tarin hadisai daga abin da ke nuni kan cewa mutum ya na kallo ya na ganin ayyukansa qarara a malakutiya xinta da gaibu da bayyane.
daga cikin martabobin hasara da cutuwa shi ne gamsuwar mutum da surar ibadarsa da bawonta ya zamanto ya haramtu daga albarkatunta da kamalarta na baxini wadda ke kawo azurta madawwamiya
(يَرْفَعِ آللهُ آلَّذِينَ آمَنُوا مِنكُمْ وَآلَّذِينَ أُوتُوا آلْعِلْمَ دَرَجَاتٍ [9])
Allah na xaukaka darajar waxanda suka yi imani cikinku da waxanda aka baiwa ilimi.
Ibadoji su ne tsanin da ruhi ke takawa ya tsallaka zuwa ga makotaka ga ubangijin izza da fana'i cikin iradarsa da wanzuwa da shi.
wanda shi ne tsololuwar fatan waliyyai kuma tuqewar burin masana ubangiji da masu tarbiyyar zukata……
mamakin wannan hasara da hankulan mu suka gaza riskarta face bayan fita da bayan barin gidan duniya, matukar mu na cikin hijabin duniyar mulk da gurbatar xabi'a lalle mu ba za mu taba samun ikon riskar komai ba daga waccan duniyar, kaxai mun miqar da hannuwan mu ne ya zuwa wuta daga wani bigire mai nisa, wacce hasara da nadama da cutuwa da tabewa ta fi girma daga ace abin da ya ke tsani zuwa ga kamala da azurta ga mutum waraka daga dukkanin raxaxi da tawayar zuciya amma kuma shi mutum xin bai amfana da kowacce irin fa'idar ruhi daga gareshi..
ya kai aboki ka xaura xamara ka zage dantse ka shimfixa hannu don nema, ka gyara halin da kake ciki daga xaukar wahala da gajiya, ka yi qoqarin cika sharuxxan ruhi domin yin kwatakwacin hajjin masana ubangiji, ka sani cewa abin da ya ke rataye da zirin gangar jiki ya ke bayyana kansa galibin lokuta ana kiransa da suna fiqihul asgar, sannan abin da ya ratayu da zuciya da ruhi ya ke bayyana kansa galibin lokuta ana kiransa da fiqihul akbar, kamar yadda bayanin hakan zai zo daga baya da izinin ubangiji.
Dukkanin godiya ta tabbata ga Allah kamar yadda ya kasance ahalin hakan ya kuma cancanci hakan.
haqiqa Allah ya so ya hukunta daga abin da ya gabata a rayuwata da in bigi qirji da xaukar nauyin koyar da wasu adadi daga `yan'uwa mata masu daraja da suke shirin tafiya aikin hajji, sai na koyar da su darasin sirrikan aikin hajji da ziyara da harshen farisanci, na rubuta darasin cikin wasu `yan qananan takardu da harshen larabci wanda na sanya xan abin da ya sawwaqa gareni daga sirrikan hajji, sai tashar talabijin ta tauraron zamani mai suna {alfurat} suka nemi da inje in gudanar da shirin bayanin sirrikan hajji cikin halqa takwas sai na amsa buqatarsu a shekara 1427 hijra qamariya, a xabi'ance sai wannan shiri ya haifar da faxaxar bahasin da qaruwarsa sai ga shi ya wayi gari cikakken littafi, sai na qaunaci in gabatar da shi ga dukkanin al'umma musammam ma'abota ilimi da ma'abota ayyukan tablig cikin matafiya aikin hajji, ta yiwu wannan xan littafi ya kasance wata `yar kyauta guzuri ga `yan'uwa masu karatu masu daraja, ni kuma ya kasance ilimi mai amfanarwa gareni wanda mutum ya ke tafiya ya barshi bayan mutuwarsa ya amfanu da shi ranar qiyama in kuma rabauta da addu'ar muminai mazansu da matansu.
(يَوْمَ لاَ يَنفَعُ مَالٌ وَلاَ بَنُونَ * إِلاَّ مَنْ أَتَى آللهَ بِقَلْبٍ سَلِيمٍ )
ranar da dukiya ko `ya`ya ba su amfanarwa face wanda ya je wa Allah da zuciya lafiyayya.
qarshen zancen mu shi ne mu na godiya ga Allah ubangijin talikai.
sannan ina rufewa da maganar imam komaini{ks} cikin muhimmancin zurfin ma'anawiyyar hajji:
lalle matakan ma'anawiyya ga hajji su ne jari ga rayuwa madawwamiyya, wadda ita ce ke kusanta mutum cikin sasanni tauhidin tsarkaka, sannan ba zamu samu komai ba matuqar bamu zartar da hukunce hukunce da dokokin aikin hajji ba da ingantacce yanayi xaya bayan xaya, saboda haka ya zama wajibi kan mahajjata masu alfarma da malamai masu girma da masu lura da mahajjata da su sadaukar da lokutansu, sannan dukkanin himmarsu ta kasance cikin koyarwa da faxakar da mahajjata kan ayyukan hajji, sannan wajibi kan masana ubangiji su lura da waxanda ke rakiyarsu ta yadda za a kiyaye ka da wani ya sabawa umarni, Allah ya tsare faruwan hakan.
lalle shi zurfin siyasa da na zamantakewa ga mahajjaci bai tabbata face bayan tabbatar zurfafa ma'anawiyya da na bauta, sannan kalmar labbaika wadda ake furta ta a matsayin amsa kiran Allah maxaukaki.
lalle ku kuna cikin harami don ku isa ga fadar tsarki kuna masu jiyar da kawukanku cewa lalle shi amsa kiran Allah shi ne kore masu dukkanin siifar tarayya da shirka da dukkanin matakanta, ku na hijra da kawukanku wadda ita ce tushen shirka mai girma ga maqagi ya girmama da xaukaka, mu na fatan masu bincike su samu ladansu kan haka wanda shi ladan na kan Allah wanda da ace mutuwa za ta riske su suna kan hanyarsu ta hijira.
lalle shi mahajjaci cikin dukkanin dunyoyinsa da alamominsa cikin ayyukansa na ibadar hajji ladubba da ma'anawiyya na zuciya da gangar jiki to ya kamata ya yi don neman yardar Allah, hakan na buqatar cikakken sani ga fiqihul asgar da akbar cikin ayyukan hajji da ziyara, ma'ana mahajjata su san ayyukansu na hajji daga fiqihu daga hukunce hukuncen wajibai da mustahabbi da haramun da makaruhi, haka ya kamata su san ladubba ma'anawiyya da sirrikan hajji da hikimarsa da falsafarsa.
bai buya ba kan cewa bangaren irfani da ladubba da mahajjaci suna da yawan gaske amma xan abin da ya zo cikin wannan littafi da ke gaban mai karatu xan xigo ne daga tafkin wancan haske mai huda.
taku xaya ne rak cikin tafiyar mai tsawon mil dubu, sai dai cewa muhimmi shi ne mahajjaci ya san inda zai tafi? ya kuma san kiran wanene ya ke amsawa? ya san wacce liyafa zai je? ya kuma san cewa shi baqon waye?
menene sharuxxan ladubban wannan liyafa ta ban qasa cikin zahiri da ziri, wadda kuma take ta sammai a baxini da zuciya, lalle ita hijirar mahajjaci ce daga duniya zuwa malakutiyya, daga turbaya ya zuwa ubangijin magidanta, daga shimfixa zuwa al'arshi, lalle hakan na daga mafi bayyanar alamun guduwa da hijira zuwa ga Allah matsarkaki da inuwantuwa da bishiyoyin soyayyarsa da luxufinsa, mamaki daga wannan muqami mai karamci babu samunsa sai ma'abocin rabo mai girma