■ DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN QAI
■ FASALI NA FARKO : MALHAMOMI NA FARI GAME DA
■ FASALI NA BIYU
KASHE-KASHEN DALILAN SHARI'A
SIRRIN IBADA DA HAJJI
ABUBUWA NA MUSAMMAN WADANDA SUKA KEBANTA GA KA'ABA DA AIKIN HAJJI.
SIRRIKAN HAJJI CIKIN TASFTACE ZUKATA
DAGA CIKIN SIRRAKAN AKWAI SIYASA DA ZAMANTAKEWA
DAGA CIKIN SIRRIKAN HAJJI NA IRFANI
Daga cikin muhimman sirrikan irfani a cikin hajji:
NAU'O'IN HAJJI DA BA'ARIN SIRRI CIKIN MUQADDIMARSA
■ DAGA FALSAFAR HAJJI CIKIN ALQUR'ANI
■ DAGA CIKIN SIRRIN AYAR HAJJI
■ KUFAIFAYIN HAJJI DA UMARA CIKIN DUNIYA DA LAHIRA KAMAR YADDA YA ZO CIKIN HADISAI
■ JIKKANTUWAR HAJJI GA ASALAN ADDINI
■ HAJJIN JAZZURU(RAQUMI) DA HAJJIN USFURI(TSATSTSEWALA
■ FASALI NA HUDU
■ DAGA SIRRIKAN HARAMIN MAKKA
■ Daga cikin sirrikan miqatai
■ DAGA CIKIN SIRRIKAN MAKKA MAI KARAMACI DA MASALLACIN HARAMI
■ DAGA CIKIN SIRRIKAN DAKIN KA'ABA MAI DARAJA
■ DAGA SIRRIKAN DUTSEN HAJARUL ASWAD
■ DAGA CIKIN SIRRIKAN MUQAMU IBRAHIM
■ DAGA CIKIN SIRRIKAN HADIMU DA WANDA AKE LAZIMTA
■ DAGA CIKIN SIRRKAN HAIMA (DAKIN) ISMA'IL(AS)
■ DAGA CIKIN SIRRIKAN MUSTAJAR DA RUKUNUL YAMANI
■ DALILIN SHAFAR RUKUNUL YAMANI
■ FALALAR MUSTAJAR DA LADUBBANSA
■ DAGA CIKIN SIRRIKAN RIJIYAR ZAMZAM
■ DAGA CIKIN SIRRIKAN DUTSEN SAFA DA DUTSEN MARWA
■ SIRRIKAN HAJJI WAJEN IMAMU SADIQ(AS)
■ DAGA CIKIN SIRRIKAN MIQATI
■ FASALI NA BIYAR
■ DAGA CIKIN SIRRIKAN HAJJI
■ DAGA CIKIN SIRRIKAN TALBIYYYA(FAXIN LABBAIKA
■ DAGA SIRRIKAN BARIN ABUBUWAN DA AKA HARAMTA
■ DAGA CIKIN SIRRIKAN XAWAFI
■ DAGA CIKIN FALSAFAR XAWAFI
■ Daga cikin falsafar xawafin nisa'i
■ DAGA CIKIN SIRRIKAN SALLAR XAWAFI
■ DAGA CIKIN SIRRIKAN SA'AYI
■ DAGA CIKIN SIRRIKAN SIRRIKAN SAISAYE DA ASKI
■ DAGA CIKIN SIRRIKAN TARWIYYA
■ DAGA CIKIN SIRRIKAN ARAFAT
■ DAGA CIKIN SIRRIKAN MAHS'ARUL HARAM
■ DAGA CIKIN SIRRIKAN MINA
■ DAGA CIKIN SIRRIKAN JIFAN JAMARAT
■ DAGA CIKIN SIRKAN HADAYA
■ DAGA CIKIN SIRRIKAN IBADUN CIKIN HAJJI
■ FASALI NA SHIDA
■ ku cika hajji da umara
■ XAWAFIN BANKWANA DA LADUBBANSA
■ KARBUWAR HAJJI DA HASKENSA
■ ADADIN HAJJIN DA ANNABI YA YI DA UMARARSA
■ HAJJIN ANNABAWA
■ TSUGUNARWAR DA IBRAHIM (AS) YA YIWA XANSA DA MATARSA A GARIN MAKKA
■ XAGA HARSASHIN GININ XAKIN KA'ABA DA HANNUN IBRAHIM DA ISMA'IL(AS)
■ QISSAR YANKAN IBRAHIM GA XANSA ISMA'IL{AS}
■ KHATMA
■ CIKIN ZIYARAR ANNABI MAFI GIRMA MUHAMMADU DA IYALANSA TSARKAKA.
■ DAGA CIKIN LADUBBAN BIRNIN MADINA HASKAKKA.
■ DAGA CIKIN FALALOLIN ZIYARA DA SIRRIKANTA
■ DANGANTAKAR MANZON ALLAH(S.A.W) DA AL'UMMA
- KIBIYOYIN RADDI KAN WUYAN WAHABIYAWA
- CIKIN HALLARAR ALHERI
- HUJJOJIN HALASCIN YIN TAKIYYA A MUSLUNCI DAGA MAHANGAR MANYAN MALAMAI GUDA BIYU
- FARKAR DA MAI BACCI CIKIN TABBATUWAR GANIN IMAM KA'IM A.S
- ALAMOMIN ANNABI CIIKIN KUR'ANI MAI GIRMA
- HAKURI DA FUSHI
- Bada'u tsakanin hakika da kagen makiya
- FALALAR DAREN LAILATUL KADRI
- WAHABIYANCI A TSAKANIN GUDUMA DA
- HASKEN SASANNI CIKIN SANIN ARZIKI
- AQIDUN MUMINAI
- FATIMA TAGAR HASKAYE
- SIRRIKAN AIKIN HAJJI DA ZIYARA
- TARBIYYAR IYALI A MAHANGAR ALKUR'ANI DA AHLULBAITI
Da sunan Allah mai rahama mai jin qai
Abin da ake nufi da sir da abin da ke abokantakarsa kamar buya da baxini wanda bayyanawa ke kishiyantarsa ma'ana zahiri, sirri kan kasancewa daga babini da abin da tattare da shi daga rashin bayyanarsa ga wani mutum, kaxan dai ba mai fuskanta sai wanda ya ke daga ahalin al'amarin, dukkanin sirrin da ya qetaren tsakankanin mutane biyu ya fita daga sunan sirri ya koma bayyanannen al'amari yaxaxxe, ana kiran hikima da sirri kasantuwarta suturtacciya da take boye daga ilimi da fuskanta da ma'arifa.
Amma ita Kalmar falsafa kalma ce daga aka samo daga yaren qasar girka wadda ta tattaru daga kalmomin (filo) da kuma (saufa) ma'ana masoyin hikima, wanda ada ana kiran dukkanin ililamai da wannan suna na falsafa, sai kuma daga baya aka taqaiata iliman hankali da sunan falsafa, amma a wannan zamani na namu ana kiran dukkanin hikima da ma'arifa cikin komai da wannan suna.
Sannan maganar mu cikin falsafa da sirrika za ta kasance kan sabubbab da dalilai ta fuskanin hukuntawa da illa naqisa tawayayya, sai ya kasance cikin sharaxi na lazim wajabcin samuwar ma'alul.
Amma falsafar hukunce-hukunce da dalilan shari'a, lalle abin da ka nufa da ita shi ne abin da ya ke bayan fiqihu daga boyayyun al'amurra da kebantattu daga sirrika da ma'arifa, lalle yadda al'amarin yake shi ne akwai banbanci tsakanin ilimi da ma'arifa, lalle shi ilimi ya na cikin komai da komai dadai lokacin da ita ma'arifa ta ke cikin juzu'ai.
Lalle shi ilimi na cikin zahiri amma ita ma'arifa ta game zahiri da baxini, hukunce-hukuncen shari'a na rassa mujtahidi ya na ciro su daga dalilai na filla-filla ma'ana qur'ani da sunna mai daraja da ijma'I da hankali a wajen masana usul daga mabiyan makarantar iayaln annabi(as), kaxai dai mujtahidi yana bayyana fatawowinsa daga hukuncin zahiri amma shi arifi ya na shallake wannan mataki ya kai ga abin da ya ke bayan fiqihu da hukuncin zahiri da boyayyun hikimomi, shi fiqihu na zuwa gabanin hikimomi da sirrika, na farko ana kiransa da fiqihul asgar wato abin da ya taqaitu da zahri daga hukunce-hukunce da fatawowi, na biyu kuma fiqhul akbar wanda ya yake bayani kan hikimomi da sirrika, na farko dai na wajabta sauke taklifin shari'a dadai lokacin da shin a biyu ke wajabta xaukaka darajoji
(يَرْفَعِ آللهُ آلَّذِينَ آمَنُوا مِنكُمْ وَآلَّذِينَ أُوتُوا آلْعِلْمَ دَرَجَاتٍ ) [1]
Allah na xaukaka daraja waxanda suka yi imani daga cikinku da waxanda aka baiwa ilimi.
Sannan shi xan adam da xabi'arsa da ginin garizarsa ya na son tsinkaya kan boyayyun al'amura da tsage sirrika ta hanyar makulla kwakwalwarsa mai haskaka sai ka same shi ya haifar da wasu `yan tambayoyi cikin kwakwawarsa, wannan shi ne abin da mu ke lura da shi mu ke gani cikin ayyukan hajji, az ka ga mutum na tambayar kansa maya sa zanyi wannan ayyuka na ibadar addini, duk da kasantuwarsu ayyuka na ibada sai dai cewa daga falsafarsu shi en xa'a da jarrabawa, sai dai cewa al'amarin ya fi haka faxaxa, cikin kowanne aiki guda a hajji akwai xaruruwan hikimomi da sirrika boye cikinsa, da ace mai ibada` zai tsaya kansu da ya riski ruhin ibadarsa daga mafi yawa ya zuwa mafi yawan wanda ya gabata, kamar yadda zuciya za ta samu nutsuwa mai tarin yawa kamar misalign wanda ya hango ya kuma tsinkayi inda ya nufi sauka halin tafiyarsa, kmar yanda ya jurewa wahalhalu hakn zai taimake shi wajen cimma kololuwar burinsa.
Kaxai dai ka na tsayawa ga sirrikan hajji daga mabubbugar wayewar muslunci da tushenta.
na farko daga qur'ani mai girma wanda shi ne mai shiriyawa zuwa ga abin da ya fi daidaito wanda wargi bai zuwa gabansa haka ma bayansa, shi littafi ne na gaskiya da ya sauka daga gaskiya kan gaskiya.
Na biyu: hadisai masu daraja daga makarntar manzon Allah mafi girma da iyalnsa tsarkaka.
Na uku: daga hankali lafiyayye da fixra xayantatta mai tushe wadda cikinta akwai asalai na soyayyar alheri da kyawu da kamala.
Na huxu: daga qirqira da qaga daga malamai da arifai masu girma cikin fahimtar nassoshi, daga ilimin ilhama wanda ya ke daga jinsin iliman sammai daga wahayi da nassi da kalaman addini.
Yaye sirrikn hajji kamar fitar da hukunce-hukuncen addini ne, dukkanin biyun biyun sun fito daga kwazazzabo guda don istinbaxi da yayewa daga dalilai na filla-fila, sai dai cewa shi fiqihu an tanade shi don bayanin hukunce-hukuncen hajji kuma ya na ksancewa gabanin hikimomin shari'a, ya attara kan faxaxar huknci da quntatarsa, ya na kuma rataya da zahirin hukunce-hukunce daidai lokacin da shio kuma yaye sirrika ya na kasancewa bayn gabatar hukunce-hukunce ya na tattara kan yaye hikimomi da qarqashin hukunce-hukunce
Fagen hankali cikin sirrika yafi faxaxa daga istibaxin hukunce-hukunce, duk da kasancewar qiaysi da istihsan ba suda wuri cikin istibaxin hukunce-hukunce kaxai shi istinbaxi ya tsaya kan tsantsar ibada da sallamawa, sai dai cewa shi yaye sirrika bai hana qiyasi waje ba cikinsa sakamakon rashin hukuncin shari'a cikinsa.
Lalle qur'ani mai girma kamar yadda ya ke bayanin huknce-hukuncen shari'a haka bai gushe ba ya na nuni ga falsafa da hikimomin da ke cikinsa, idan yay i umarni da sallah sai ka sami ubangiji matsarkaki na cewa:
: (تَنْهَى عَنِ آلْفَحْشَاءِ وَآلْمُنكَرِ وَلَذِكْرُ آللهَ أَكْبَرُ)[2]
Lalle ita sallah ta na hani ga barin alfasha da munkari lalle shi ambaton Allah shi ne mafi girma.
Idan yin umarni da azumi sai ya ce:
(لَعَلَّكُمْ تَتَّقُونَ [3]
Tsammaninku zaku yi taqawa.
Haka al'amarin ya ke cikin makarnatr iyalan annabi da hadisansu masu daraja, lalle cikin riwayoyi xari huxu na asalai akwai littafai masu tarin yawa da suke bayanin dalilai masu hikima daga cikinsu:
1-littafin ilal na ahmad ibn husaini ibn Hassan ibn dauda alqummi: a duba rijalul najashi sh 90
2- littafin ilal na ahmad iban axxar: a duba rijalul najjashi.
3- littafin ilal na aliyu ibn husaini ibn faddal.
4- littafin ilal na aliyu ibn sahal hatim ibn abi hatim alqazwini.
5-littafin ial na muhammadu ibn kalid ibn abdur rahman.
6-littafin ilal na muhammadu ibn ahmad ibn dauda ibn aliyu shaik qummiyun.
7-littafin ilal na abi hashim dauda ibn qasim jafari.
8- littafin ilalul shara'I na shaik saduq.
Daga cikin misalin ilal da dalilai cikin hadisai:
عن أبي عبدالله 7 انّه سأل عن شيء من الحلال والحرام فقال : انّه لم يحصل شيء إلّا لشيء[4]
Daga baban Abdullah(as) lalle shi ya tambayi wani abu daga halal da haram sai ya ce: lalle yadda al'amarin ya ke wani abu ba samuwa sai don wani abun.
وفي الحديث : «لِم صار الحاج لا يكتب عليه ذنب أربعة أشهر» «سألته عن التلبية لم جعلت » «لم سمّيت الكعبة كعبة » «لم سمّي البيت العتيق » «لم سمّي بيت الله الحرام » «لم جعل إستلام الحجر» «لم جُعل المقام بمنى ثلاثاً» «لم جعل السعی[5]
Me ya sa mahajjaci ya kasance ba'a rubutawa masa zunubin watanni huxu, na tambaye shi kan faxin Kalmar labbaika me ya sanya aka sanya ta, me ya sanya aka sanyawa xakin ka'aba suna ka'aba, me yasa ake kiranta da suna baitul atiq, me yas ake kiranta da sunan xakin Allah me alfarma, me ya aka sunnanta sumbatar dutsen hajarul aswad, me yasa aka sanya muqam a mina uku, me yasa aka sanya sa'ayi.
Da misalin ire ire waxannan masu yawa cikin riwayoyi, lalle abayyane suna nuni kan muhammancin sanin sirrika da falsdafar hajji da baynin hikimominsa da ma'arifofi da baxinai.
Dukkanin wani aiki na ibada ya na da nasa kebantaccen shakalin na zahiri da baxxini, daga cikin abin ban takaici shi ne kasantuwa da yawa yawan mutane sun taqaitu da riqo gangar jikin shari'ada zahirinta da zirinta a daidai lokacin da suka gafala daga zuciyarta da baxininta da ruhinta, haqiqa sun jahilceta sun kuma gafala daga barinta, sabanin wannan al'amrin na gudana cikin al'amuransu na duniya da rayuwarsu ta yau da gobe, za ka gansu suna kallon kowanne abu kallo na dandaqewa da tankaxe da rairaya za ka same su suna kai kawo wajen gano sirrika da baxini, sakamakon wannan fafutika ta su aka samu dukkanin cigaba ilimin sana'o'I da kimiya da qere-qere na zamani da cigaban rayuwa wanda na daga cikin abubuwan da ke qara sanya kwaxayi da dogon buri da cutukan ruhi da zamantakewa masu tarin yawa, da qaruwa rigingimu da yaqe- yaqe masu rusa al'umma da halakar da ita, inama sun sadaukar xaya bisa goman himmar da suka sadaukar kan gano sirrikan duniya cikin gano sirrika ma'anawiyya da malakutiyya.
Amma haka bai nufin mu gafalar da kawukan mu daga gano sirrikan da suka shafi duniyarmu bari ma dai ai ita duniya anan nan ake shuka lahira, abin da yafi zama farilla shi ne manufa da himma ta asasi su kasance neman darajoji da aljanna da yardarm Allah girmansa ya girmama a lahira, kada ya zamanto mun sadaukar da lahirar mu kan duniya, bari ma dai al'amarin kishiyar hakan ne ma'ana zamu sadaukar da duniyar mu kan lahirar mu don samun yardarm Allah, hakan na daga kasuwancin da bai tozarta, wanda ya yi hasara mabayyaniya shi ne wanda ya sayar da lahirarsa da duniyarsa, mafi hasara daga waxancananka ka kuma shi ne wanda ya sayar da lahirarsa don duniyar waninsa.
Tilas ne a kiyaye zahiri da baxini da cikakken sunan kiyayewa da kulawa da dukkanin qafi, dukkanin wanda yay i watsi da zahiri yafi kusa da shi ya yi wasti da baxini, ita duniya kasuwa ce ta waliyyan Allah sannan kuma gonar da mumunai ke shuka lahirarsu. Dukkanin wanda yay i watsi da zahiri da baxini to haqiqa ya yi watsi da muslunci domin muslunci na da baxini da zahiri.
ba boye ya ke ba ga dukkanin zahiri na tare da baxini sakamakon tsakaninsu akwai baquntaka daga (taqabul) kamar dangantakar illa da ma'alul matuqar xaya ya samu to xayan sai ya samu kamar dangantakar ubantaka ta xiyantaka, ba z aka samu uba ba face ka samu xa` tare da shi, saboda ba z aka samu zahiri ba face ka samu baxini bayansa, haka b aka samun baxini sai bayn samuwar zahiri, sdai dai kuma duk sa'ilin da baxini ya wayi ga zahiri to z aka samu bayan wannan zahiri akwai wani baxinin haka zai tayi har ya kai ga ilimin Allah matsarkaki azali abadi sarmadi, shi Allah zahiri ne kuma baxini ne, shi ne farko shi ne qarshe, sai ya kasancewa ilimin da bai da farko bai da qarshe.
(وَقُل رَبِّ زِدْنِي عِلْما)ً. [6]
Ka ce ya ubangiji ka qara mini ilimi.
Kan wannan fikira ne sarkin muminai (as)ke cewa:
قال أميرالمؤمنين علي 7: «علّمني رسول الله ألف باب من العلم ينفتح لي من كلّ باب ألف باب
Manzon Allah(saw) ya koyar dani qofa dubu kowacce qofa xaya daga ciki na buxe wata qofa dubun daban.
Sai da yawan lokuta z aka samu sirri guda xaya rak sirri dube na yayewa daga gareshi, sau da yawa zahiri bayansa akwai baxini dubu cikin dukkanin ciki z aka samu dubban sirrika da abin da ya buya daga haka, lalle tuqewa nag a ubangijinka, shi ne tsantsar ilimi girmansa ya girmama.
KASHE-KASHEN DALILAI DA SABUBBAN SHARI'A
Sannan su dalilaI sabubban shari'a da falsafar hukunce-hukuncen muslunci sun kasu zuwa kashi huxu:
1-daga cikinsu: akwai waxanda annabin rahama da iyalan gidansa suka bayyana, sai mutane suka kewaya da su kamar haramcin yin qarya da tuhuma da munana zato da gulma da kisan kai
(مَن قَتَلَ نَفْساً بِغَيْرِ نَفْسٍ أَوْ فَسَادٍ فِي آلاَْرْضِ فَكَأَنَّمَا قَتَلَ آلنَّاسَ جَمِيعا)[7]
Duk wanda ya kashe rai ba tare da wani rai ba ko kuma ya yaxa barna ban qasa to kamar ya kashe dukkanin mutane ne.
Haka ma kamar gaskiya da kyautatawa da adalci da kiyaye haqqoqin iyaye da sadar zumunci da dai makamantansu…
2-daga cikinsu: waxancn hukunce-hukunce da falsafarsu da hikimominsu dalilinsu ba su bayyana a fili ba ga yawancin mutane kai hatta ga ba'arin manya-manyan malamai, sakamakon rashin bayyanan haka qarara kamar yadda ake buqata, kaxai dai anyi ishara kamar yadda ya zo cikin ayar azumi cikin faxinsa maxaukaki:
(كُتِبَ عَلَيْكُمُ آلصِّيَامُ كَمَا كُتِبَ عَلَى آلَّذِينَ مِن قَبْلِكُمْ لَعَلَّكُمْ تَتَّقُونَ )[8]
An wajabta azumi gareku kamar yadda aka wajabta shi ga waxanda suka gabace ku tsammaninku kwa samu taqawa.
Kamar yadda ya zo cikin hikimar ayar zakka:
(ليستوي الفقير والغني
Don mawadaci da talaka su daidaita
3-daga cikinsu:hukunce-hukunce waxanda ta yiwu mu tsaya kan falsafar da sirrikan wasu jumla daga cikinsu. Sai cewa da shuxewa zamani tare da cigaban ilimai da fannoni kamar misalign cutarwa da barasa giya keyi ga jikin xan adam da hankalinsa.
4-daga cikinsu: waxancn hukunce-hukunce waxanda basu gushe cikin wahami da buya, sirriknsu basu yaye ba kamar misalign adadin raka'o'in salloli biyar da ake yi kullum, ta yiwu su yaye lokacin da hankula ke cika ranar da imam zaman(af) zai bayyana.
Sannan bai buya ba cewa dukkanin hukunce-hukunce shari'a da dukkanin matakanta da kashe –kashenta na ufuqi da amudi kaxai dai muqaddima ne sakamakon abin da ke cikinta na daga maslahohi da ke lazimci cikin wajibai da barna da ke lazimci cikin ababen da aka haramta. Da abin da ke hawa kai daga bijirar mutum da samun lada da kamalarsa da azurtarsa cikin gida biyu duniya da lahira.
Shi hajji na da hukunce-hukunce da hikimomi,, man fiqihu na xaukar nauyi bayanin na farko ma'ana hukunce-hukunce wanda ake kira da fiqihul asgar kamar yadda bayani ya gabata kai, haqiqa shi ya na daga zahirin shari'a, shi kuma kashe na biyu arifai ke xaukar nauyin bayani kansa wanda ke shiga da'iora irfani, ana kiransa da fiqihul akbar lalle shi ya na daga haqiqa da baxini.
Dukkanin biyun ma'ana asgar da akbar sun gangaro daga mai kwararar da fail aba tare da qaidi ba wanda shi ne Allah matsarkaki maxaukaki ga tarbiyyar mutum da kamalar shi da azurtarsa duniya da lahira, don ya yi mi'iraji ya zuwa ubangijinsa hark a ga kasancewa gwargwadon zira'I biyu ko kuma mafi kusa daga haka,
(فَادْخُلِي فِي عِبَادِي * وَآدْخُلِي جَنَّتِي )
Ki shiga cikin bayina, kuma ki shiga aljannata.
Lambu mai duhu biyu lambu malaman fiqihu da lambun masana irfani urafa'u.
Sannan
mgana kan hajji wani lokaci yana kasancewa tare da la'akari da hukunce-hukunce
da ayyukan wajibai da na mustahabbi cikin hajji, wani lokacin kuma kan kasancewa
game dawurare masu tsarki da na tarihi, wani kuma kan kasancewa kan al'amaura
da suka faru a tarihi da kuma tsarkakan al'amurra, wani kuma kan daxaxan
abubuwa da aka ciro daga ayyukan hajji da wurare masu muhimanci da abubuwa da
suka afku, wannan shi muke kira sunan sirrikan hajji da ziyara kuma shi hadafin
wannan littafi da ke gaban mai karatu, wanda muke fatan ya kasance daga ilimi
da ma'arifa da za su amfanar, su kuma qara cikin xaukaka mustawan wayewar
al'ummar musulmi.
وجوه القرآن الأربعة
Fuskoki huxu na alqur'ani:
ورد عن الامام زين العابدين 7: أنّ القرآن نزل على أربعة أوجه
Daga imam zainul abiding(as) lalle shi qur'ani ya sauka kan fuskoki huxu.
1-lafuzza: lalle shi qur'ani ya kasance ga dukkanin mutane, lalle mutane suna tare da qur'ani cikin lafuzzansa ta fuskanin sauke suda kyawunta tilawarsu, da ma'anarsu ta lugga da dai abin da yay i kama da haka….
2-ma'anoni:lalle shi qur'ani ya kasance littafi ga kebantattun masana, lale shi qur'ani na da baxinai da ma'anoni masu tarin yawa, lalle qur'anio igiya ne miqaqqa, gefen guda na igiyar na hannun Allah xayan kuma na hannun mutane, duk wanda kebantattu zai riqo da igiyar Allah ya tsallaka zuwa ga ma'anonin qur'ani har ya kai ga muqamin fana'I narkewa cikin zatin Allah da wanzuwa tare da Allah ace masa karanta ka xaukaka.
3-daxaxan zantuka da isharori: lalle shi wannan matsayi na waliyyai ne, duk wanda ya ke waliyin Allah cikin dukkanin sha'aninsa da iradarsa, shi waliyyi shi ne wanda ke biye da wanda ke gabansa ba tare da ansamu wani abu ya shiga tsakaninsu ba kamar misalign wanda ke kan doki bayan wani sai ya kasance biye da shi, to shi waliyin Allah shi ne wanda ya kasance tare da Allah yardarm Allah it ce yardarsa, fushin Allah fushinsa, misalign irin wannan mutum zai tsinkayi daxaxan zantukan qur'ani da ishararsa, lalle shi tsarkakakke ne mai tsarkakewa.
(لاَ يَمَسُّهُ إِلاَّ آلْمُطَهَّرُونَ )[9]
Babu ma su taba shi sai tsarkakakku.
Tabawa ko shafawa anan na nufin shafawa ta baxini kamar yadda ya zo cikin faxinsa maxaukaki:
وا ذا مَسَّهُمْ طَائِفٌ مِنَ آلشَّيْطَانِ )[10]
Idan wani bala'I daga shaixani ya shafe su.
Misalign sahabi mai daraja irin salmanu wanda shi ya na daga cikin ahlul baiti tabbas zai tsinkayi daxaxan zantukan qur'ani mai girma.
4-haqiqanin al'amurra: lalle haka ya kebantu ga annabwa ga wasiyyai, lalle ita haqiqa siffa da aka tsagota daga haqqu ma'ana tabbataccen abu madawwami, annabawa da wasiayyai na tsinkaya kansu da iliminsu na ladunni na ilhama wanda ya ke daga luxufin Allah maxaukaki, lalle su annabawa da wasiyyai suna tsinkayar sirrikan qur'ani da ma'anarsa da lafuzzaansa, sannan hadisi ya zo daga manzon Allah(saw) cewa
:: «العلماء ورثة الأنبيا.
Malamai su ne magadan annabawa.
Kaxai dai suna gadonsu cikin iliminsu da xabi'unsu da nauyin da ke kansu na shiriyar da al'umma, z aka same su suna gadar annabawa cikin tsayuwarsu kan matakan qur'ani mai girma daga ilimi da ma'arifa ga lafuzzansa da ma'anoni da ishara da sirrikansa kamar yadda hakan ya kasance ga annabawa, saboda ka sanya lura da zurfafawa don sababbin sasannin ma'arifar qur'ani su buxe gareka da taiamko daga Allah da luxufinsa, lalle shi n e m mafi alherin mai kawo xauki da taimako, lalle shi ya na kimsa ilhama sirrikan halittu mayalwata daga sirrikan shari'arsa mai haske ga bawansa, da sirrikan qur'ani mai girma, kowanne abu na da zahiri da baxini, baxininsa shi ne sirrinsa , duk wanda ya tsinkaya kan wani sirrin ko baxini lalle zai zamanto zahiri gare shi babu makawa, lalle babu shakka da sannu zai tsinkayi sirrin wannan sirri da baxinin wannan baxini wanda ya kasance zahiri gareshi. Daga nan ta tsinkayar sirrika da baxianai har sai ya tuqe ilimin Allah matsarkaki azali sarmadi abadi wanda shi ne zahiri da baxini shi ne wanda bai da farko bai da qarshe.
Wannan ya abayyane na nuni da kan cewa sirrika bas u qarshe, lalle ne kan dukkanin wani ilimi akwai masani, babu abin da aka baku daga ilimi face cikin cokali, k ace ubnagiji ka qara mini ilimi ka risker da ni ga salihai.
Lalle ne shi ma hajji na da fuskoki huxu da suke biye ga sanin hajjida riqonsa ga muslunci a ilimane da aikace a aqidance da xabi'ance da suluki, daga cikin mahajjata akwai waxanda suke riqo da zahiaran hajji da ayyukansa suna kiyaye bangaren fiqihu daga inaganci da gurbata waxannan su ake kira da amawan mahajjata, sannan kuma cikin mahajjata kassawa(kebantattu) sune waxanda ke riqo da ma'anonin hajji ma'arifarsa maxaukakiya suna masu neman karbuwar hajjinsu lalle al'amarin yadda ya ke
(إِنَّما يَتَقَبَّلُ اللهُ مِنَ الْمُتَّقينَ )[11]
Kaxai dai Allah na karba daga masu taqawa.
Da abin da ke tattare da mahajjaci daga kammiya da kaifiya daga taqawa zai tsinkayi ma'anonin qur'ani kmar zai tsinkaya ma'anar hajji.
Daga cikin mahajjat akjwai wanda suke daga waliyai suna tsinkayar irfanin hajjida sirriaknsa, da suke bayyane cikin gaibu da shaidawar kayawunsa bda girmansa ya xanxana daga zaqin kamalarsa ya na mai nutsewa cikin tekun haskayensa.
Daga cikinsu akwai annabawa da wasiyyai da ke yaye musu sirrikan hajji da girmansa, wanda ya shallake tunanin xan adam da fahimtarsa, na daga luxufinsa kan bayinsa ya sanya malamai magada annabawa suna xauke da ilimin annabawa da ma'arifarsu, sun kasance tsanin kwarar failar tsarkakakka tsakanin annabawa da al'umma, kamar yadda annabawa suka kasance tsanuka faila tsarkakka tsakanin mahalicci da halittunsa.
Saboda haka wajibi kan dukkanin mahajjaci mahajjaciya su yi qoqarin matsar malamai don su tsinka daga bishiyarsu mai kayan marmari nunannu masu zaqi su kasance baqi da suke kan teburin walimar ruhi da haske wanda zukata ke kwaxayi daga abincin ma'anawiyya, idanuwa na daxaxa daga launinsu mai kyawu, da wannan ne zai san menen ma'anar hajji? Wanene mahajjaci?
Lalle Allah ne abin neman taimako kuma shi ne mafi alherin mai taimako da tallafawa.
SIRRIN IBADA DA HAJJI
Lalle Allah matsarkaki maxaukaki bai halicci halittu ba don wasa da wargi
(وما كنّا لاعبين )
Ba mu kasance masu wargi ba.
Kaxai dai yay i halitta kan tsarkakakken hadafi kebantacce, daga mafi bayyana ta fitowa fili cikin haduffan halitta da falsafar rayuwa shi ne cikar kamalar xan adam, wanda hakan na kasancewa da taimakon ubangiji da rahamarsa da ilimi da ibada.[12]
(وَمَا خَلَقْتُ آلْجِنَّ وَآلاِْنسَ إِلاَّ لِيَعْبُدُونِ )[13]
Ban halicci mutum da aljani sai don su bauta mini.
Sai don su sanni haqiqanin sani kamar yadda ya zo cikin hadisai domin ita ibada ba ta tabba da cika face an san wanda za'a bautawa, duk wanda ya san Allah saninsa ga Allah zai shiryar da shi zuwa ga bautarsa.
Bai buya ba kan cerwa shi ubangiji mawadaci daga bautar mai bauta,kaxi ita wannan bauta na komowa ne ga masu bauta bawai ga mahalicci ba wanda ya cancanci bauta, kamar yadda ya ke faxi:
(إِن تَكْفُرُوا أَنتُمْ وَمَن فِي آلاَْرْضِ جَمِيعاً فَإِنَّ آللهَ لَغَنِيٌّ حَمِيدٌ( [14]
Idan ku kafirce ku da dukkanin waxanda ke ban qasa baki xayanku to lalle shi Allah mawadaci godadde.
Sannan ya yin duban ibada cikin shari'o'I tsarkaka za mu ga cewa sun sassaba cikin ayyuka daga wasu guraben, lalle zamu ga cewa sallah cikin juzu'anta ba azumi b ace ta banbanta da shi, haka shi ma azumi ya banbanta da hajji, waxannan iabdu uku sun saba da ragowar ibadu `yan'uwansu.
Ya yin da muke dubanta da wannan fuska zamu ga sabani da banbanci cikin haqiqaninta da sharuxxa da juzu'ai da ladubba da sunnoni, me ya kawo wannan banbanci da sassabawa cikin zahiri ta yadda ba mu iya ganin wata fuska da ta yi kamanceceniya ga wata ibadar.
Kafin mu bada amsa ga bayanin dalilin sabanin, mu na cewa lalle shi Allah matsarkai maxaukaki ya sanya waxannan ibadu ga mutum ya kallafa su, ya yin da idan muka kalli haqiqani da abin da suke haifarwa, zamu ga cewa ba'arin ibadun na komawa ga zatin mutum koma bayn waninsa kamar misalign azumi, wani ba'arin kuma na komawa tsakanin mutum da mahaliccinsa kamar misalign sallah da addu'a, wani ba'arin kuma na kasancewa tsakaninsa da mutane kamar misalign zakka da kumusi da hajji da jihadi da umarni da kyawawa da hani ga munana da wasunsu…..
Daga cikinsu akwai waxanda suka ta'allaqa da xabi'a daga daskararrun abubuwa da tsirrai da dabbobi.
Shi mahalicci matsarkaki ya yin da ya halicci mutum ya nui mutum da yay i wusuli ya kai ga kamala da aka ajiyar cikinsa daga kasantuwarsa halifan Allah cikin siffofinsa da kyawawan sunayensa, Allah ya sanya mutum hanya da shari'a domin cimma wannan kamala.
Kowanne guda daga cikin mu ya na iko gwargwadon halittarsa wajen kaiwa ga kamala sakamakon an kallafa mana yin haka, kuma shi Allah bai kallafawa bawa face abin da ya ke iko kai, kaxai dai abin da zai taimaki mutum ya kai ga kamala ba wani abu bane face ruhinsa, ya zama wajibi tasirinsa ya kasance ta fuskoki masu yawa, wanda zai kawo sassabawa cikin abubuwan da ke tasiri . Lalle mai tasiri guda xaya rak bai iya bada tasirinsa a kowacce fuska, daga nan dalilin sassabawar ayyukan ibada ke bayyana sakamakon kasantuwarsu masu tasiri cikin kasantar da mutumtakar mutum da shaida da hatimin ubangiji don su samu damar shan inuwar al'arshin Allah ya kuma samu damar tsugunawa cikin bigiren gaskiya wajen sarki mai iko da qarfi.
Qari kan haka za a iya cewa akwai wata dangantaka da alaqa qarfaffa da dangantaka ba'arin wasu ibadu ga ba'ari, wannan abu mai dangantawa ta yi ya kasance amudi asasi kasantuwar kowacce ibada ana yenta don neman kusancin Allah matsarkaki.
Sannan shi hajji na daga furu'u dini (reshe) kamar ragowar ibadu wanda sirrinus na komowa ga halittu a kankin kansu.
(وَمَن كَفَرَ فَإِنَّ آللهَ غَنِيٌّ عَنِ آلْعَالَمِينَ )[15]
Duk wanda ya kafirce lalle Allah mawadaci ne ga barin talikai.
Shi mtum akankin kansa akwai bai da tabbacin samuwa da wanzuwa, ya na buqatuwaya na talautuwa ya zuwa ubangijinsa da mahaliccinsa maqaginsa, kaxai dai ya na kammaluwa da ilimi da sanin Allah da rahamarsa da ibada ta gaskiya cikin tafiyarsa ta neman kamala, lalle shi ilimi share fage ne don kaiwa ga shuhudi halarta
: (كَلاَّ لَوْ تَعْلَمُونَ عِلْمَ آلْيَقِينِ لَتَرَوُنَّ آلْجَحِيمَ ثُمَّ لَتَرَوُنَّهَا عَيْنَ آلْيَقِينِ)[16]
Haqiqa da kuna sani na yaqini da kunga wuta qarara, sannan da kun ganta da ido na bayyane.
Da sani na yaqini mutum ke kaiwa ga ainul yaqini ido bayyane, da ido bayyane yake kaiwa ga haqqul yaqini, shi muqami ne na fana'I cikin iradar Allah ta wanzuwa tare da shi.
Shi kuma shuhudi na tabbata ta hanyar tsarkake zukata da haskaka su da ibada, lalllke ita hanya ce ta suluki da bayyanar gaibu.
(وَآعْبُدْ رَبَّکَ حَتَّى يَأْتِيَکَ آلْيَقِينُ )[17]
Ka bautawa ubangijinka har sai yaqini ya riskeka.
Ita ibada it ace share fage zuwa ga yaqini, amma daga cikin mafi cikar abin da ke tabbatar da yaqini da yaye shi it ace mutuwa, ma'ana ka bautawa ubangijinka har mutuwa ta riskeka.
Hajji cikin sirrikansa ya na nuni ga shuhudi da halarta, duk wanda ya bar hajji alhalin ya na da hali to shi ya kasance kafiri, ranar qiyama zai tashi makaho sakamakon duniyarsa ta makanatar da shi, kamar yadda ya zo cikin bayanin faxin Allah maxaukaki:
(وَمَن كَانَ فِي هذِهِ أَعْمَى فَهُوَ فِي آلاْخِرَةِ أَعْمَى)[18]
Duk wanda ya kasance maqaho ana duniya to lahira ma maqaho zai tashi.
Sannan ibada ta kasu zuwa ga wadda ake gabbai na zahiri da gabbai na baxini, abin da ya ta'allaqantu da gabban zahiri to yana daga hukunce-hukunce da ladubba, amma na baxini shi ne abin da ya buya daga haka daga ma'arifa da shuhudi kamar halartar hallarar Allah wannan shi ne abin da muke nufi da sirrin ibada da sirrin hajji
Bai buya ba cewa sirrikan hajji da sirrikan ibada kaxai dai suna wajen ahlul baiti lalle sune ma'ajiyar sirrin Allah mafakar lamarinsa taskar iliminsa gidan hikimarsa, kogon littafansa, ma'ajiyar addininsa.
Sannan kammalallen mutum na ainahi shi ne sirrin ibadu baki xayansu, kuma shi ne sirri kammalalle rubutacce ma'ana qur'ani mai girma, da wannan mu ke cewa taqawa itace sharaxin karbar ayyuka
(إِنَّمَا يَتَقَبَّلُ آللهُ مِنَ آلْمُتَّقِينَ )[19]
Kaxai dai Allah na karba daga masu taqawa.
Karbar taqawa na tare da karbuwar wilaya mai girma ga Allah da manzonsa da halifofinsa imamai tsarkaka: ma'ana kammalallen mutum na haqiqa shi ne siraxi miqaqqe, hanya madaidaciya, ma'aunin ayyuka.
Kamar yadda littafin allah na da zahiri da baxini qur'ani na da cikkuna bakwai kowanne ciki akwai ciki saba'in cikinsa, to haka ma hajji shi ma na da zahiri sune hukunce-hukuncen gabbai, baxininsa kuma sune hikimomi da ma'arifa da shuhudi
(وَمَا يُلَقَّاهَا إِلاَّ ذُو حَظٍّ عَظِيمٍ )[20]
Babu mai samunta sai ma'abocin rabo mai girma.
Zahiri na ta'allaqa da zirin mutum, baxini shuhudi na ta'allaqa da zuciyarsa, lalle shi misalign waninsa daga ilimai ya zuwa ne daga taskokin ilimin Allah.
Mumini arifi ne cikin barzak xinsa ta sauka gabanin wannan qasqantar duniya, haka cikin barzak xinsa ta hawa wadda ya ke riskarta bayan yam utu ya bar wannan duniya, ta yiwu ya ga sirrikan abubuwa da surorin malakutiyya bayan ya misaltu da aikinsa da surorin malakiyya cikin wannan duniya, misali sallah na zuwar masa da surar jiki ta dinga kwantar masa da hankali da xebe asa haso cikin kabari ta dinga haskaka masa kabarin.
Ya zo cikin hadisi mai daraja:
إذا مات المؤمن دخل معه في قبره ستّة صور فيهنّ صورة أحسنهنّ وجهاً، وأبهاهنّ هيئة ، وأطيبهنّ ريحاً، وأنظفهنّ صورةً ، فيقف صورة عن يمينه واُخرى عن يساره ، واُخرى بين يديه ، واُخرى خلفه ، واُخرى عند رجلين ، وتقف هي أحسنهنّ فوق رأسه ، فان أتى عن يمينه منعته التي عين يمينه ، ثمّ كذلک إلى أن يؤتى من الجهات الستّ فتقول أحسنهنّ صورة : ومن أنتم جزاكم الله عنّي خيراً؟ فتقول التي عن يمين العبد: أنا الصلاة ، وتقول التي عن يساره : أنا الزكاة ، وتقول التي بين يديه : أنا الصيام ، وتقول التي خلفه : أنا الحجّ والعمرة ، وتقول التي عند رجليه : أنا برّ من وصلت من إخوانک ، ثمّ يقلن ومن أنتِ ؟ فأنتِ أحسننا وجهاً، وأطيبنا ريحاً، وأبهانا هيئة ؟ فتقول : أنا الولاية لآل محمّد صلوات الله عليهم أجمعين[21]
Idan mumini yam utu surori shida za su shiga kabari tare da shi cikin akwai sura wadda tafi ragowar surori kyawun fuska tafi dukkaninsu kyawun tsari tafi dukkanin daxin qamshi tafi dukkaninsu tsaftatar sura, sai ya tsaya halin damansa akwai surah aka ma hagunsa wata surar gabansa wata kuma bayansa wata sura ta tsaya wajen qafafuwansa, sai mafi kyawun cikinsu ta tsaya saman kansa, idan ya zo sai ta damansa ta hana shi, ya ta haka har akewaya shida, sai mafi kyawun cikinsu ta ce su wanene ku Allah ya saka muku da alheri daga gareni? Sai wadda ke damansa ta ce nice sallah, ita ta hagu sai ta ce n ice zakka, sai wadda take gabansa ta ce n ice azumi, sai ta bayansa ta ce n ice hajji da umara, wadda ke wajen qafafunsa ta ce ni ce kayutatawar da ka sadar tsakanin `yan'uwanka, sannan su tambaye wannan kayakkyawa ke kuma wacece ke? Lalle ke kin fimu kyawun fuska, kin fimu daddaxan qamshi, kin fimu kyawun tsari? Sai ta ce n ice wilayar ahlul baiati amincin Allah ya tabbata garesu baki xayansu.
Hajji da dukkanin ayyukansa da sirrikansa da zahirinsa da duniyoyinsa da sirrin sirrikansa babu mai riskarsu sai kebantattu da xaixaikun mutane, su tsallaka zuwa ga shuhudin ubangijin magidanta, ubangijin xaki mai alfarma
(فَلْيَعْبُدُوا رَبَّ هذَا آلْبَيْتِ[22].(
Saboda haka su bauta ubangijin wannan xaki.
Daga cikin mafi muhimmancin sirrikan hajji shi ne tafiya zuwa ga Allah matsarkaki kamar yadda ya zo cikin tafsirin faxin Allah maxaukaki.
(ففروا الی الله)[23]
Ko gudu zuwa ga Allah.
Ma'ana kuje hajji zuwa ga Allah.
Kasantuwarsa matsarkaki ya na kowanne bigire saboda haka cikin tafiya zuwa gareshi ba'a dogaro da bigire ko zamani, kaxai dai tafiya gareshi ba wani abu bane face guje duk wani abu wand aba shi da narkewa cikinsa da yin haka ne hajjinsa zai kasance hajji da a kayi shi don Allah cikin Allah tare da Allah, kamar yaddaya zo cikin addu'ar safara(tafiya):
بسم الله وبالله، وفي سبيل الله، وعلى ملّة رسول الله
Ina faraway da sunan Allah don Allahtafarkin Allah, kan addini manzon Allah.
Sannan mafi alherin guziri cikin tafiya zuwaga Allah it ace taqawa, kamar yadda hakan ya zo cikin aya mai daraja wadda ta xayantu da ambaton haqiqanin guziri cikin tafiya zuwa ga Allah matsarkaki, it ace ta ratayu da hajji da hukunce-hukuncensa.
(وَتَزَوَّدُوا فَإِنَّ خَيْرَ آلزَّادِ آلتَّقْوَى )[24]
Kuyi guzuri lalle mafi alherin guzuri shi ne guzurin taqawa.
(وَأَذِّن فِي آلنَّاسِ بِالْحَجِّ يَأْتُوکَ رِجَالاً وَعَلَى كُلِّ ضَامِرٍ يَأْتِينَ مِن كُلِّ فَجٍّ عَمِيقٍ.( [25]
Kayi yekuwa cikin mutane da wajabcin hajji za su zo maka suna masu takawa da qafafunsu, a kan dukkanin xankawararren doki za su zo daga rango mai nisa.
Shi hajji wata tafiya ta imani zuwa ga Allah da manzonsa da waliyyansa, abubuwa masu tsarki da ganinsu ke sa a tuna da Allah da girmamasu cikin zukata ba komai ya ke face taqawa, sannan ita taqawa ba wani abu bace face tanadar guziri cikin tafiya da suluki zuwa ga Allah.
Faxin Allah maxaukaki: (kuyi guzuri) na nuni kan cewa kowa da kowa ya yi tanadin guzuri cikin tafiya sannan shi tanadar guzuri alama ce ta yin tafiya, bai yiwuwa ga mai tafiya ma'abocin hankali mai fahimta ya shirya yintafiya ba tare da tanadar guzuri ba, lalle ita taqawa da taka tsantsan ga barin haramun sune guzuri cikin tafiya zuwa ga Allah matsarkaki.
Shi hajji na daga cikakkun alamu da ke gasgata taqawa bkuma ya na daga mafi falalar nau'o'inta shi ne jin tsoron Allah:
(وَآتَّقُونِ يَا أُولِي آلالْبَابِ )[26]
Kuji tsorona yak u ma'abota hankula.
Bawai don kwaxayin aljanna ko don tsoron wuta, bari dai sai don kasantuwarsa ahalin taqawa da gafara, sai a bauta masa a ziyarce shi hajji ana mai tsarkake niyya don soyayya da shauki da nuna godiya da sanin haqqinsa.
Qarshen misalin wannan taqawa na kasancewa da zuciya ma'abociyar nutsuwa yardaddiya shi ne za ta haxu da Allah ta shiga hallararsa ta shiga aljannar kyawawan sunaye.
(فَادْخُلِي فِي عِبَادِي * وَآدْخُلِي جَنَّتِي( [27]
Ki shiga cikin bayina, kuma ki shiga aljannata.
Kaxai dai ya na tsinkayar sirrika wanda ke neman ilimi don samun tsira, ko kuma babban malami masanin Allah wanda iliminsa ya cakuxa da tsarkake zuciya.
(وَيُزَكِّيهِمْ وَيُعَلِّمَهُمُ آلْكِتَابَ وَآلْحِكْمَةَ( [28]
Ya na tsarkake su ya na koyar da littafi da hikima.
Ba boye yake ba cewa kowanne aiki na da zahiri da baxini, ba komai baxini ba face sirri boyayye wanda bayyane da zahiri ke kishiyantarsa, sannan dukkanin sirri akwai sirri boye bayansa da ya fishi buya, lalle Allah na sane da sirri da abin da ya buya.
Duk wanda ya nufi sirrin aiki ruhinsa za ta tsarkaka zuciyarsa ta tsaftata, don ya gaji wani sabon sirrin(dukkanin wanda yay i aiki da abin da ya sani Allah zai sanar da shi abin da bai sani ba) sai ka samu sirrika suna yayewa gareshi ya tsinkayi haqiqanin abubuwa kamar yadda suke, waxancananka sune rabauta mai girma wadda babu mai samunta sai ma'abocin babban rabo.
Bai yi wasti da aikata ayyukan haramun da kuma yin taka tsantsan daga dukkanin abin da abin da Allah ya haramta cikin hajji face don tsarkake zuciya da tsira daga son kai.
(فَلاَ رَفَثَ وَلاَ فُسُوقَ وَلاَ جِدَالَ فِي آلْحَجِّ.( [29]
Babu jima'I babu fasiqanci babu jidali a cikin aiki hajji.
Lalle qur'ani mai daraja ya na ishara ya zuwa abubuwa uku daga manya-manyan ayyukan haramun cikin hajji, don ya yi nuni ya zuwa ga tsarkake ukun, babu jima'I don tsarkake gabar sha'awa, babu fasiqanci don gabar fusata, babu jidali don tsarkake gabar wahami. A wannan lokaci za ka samu bangaren hankali ke shugabantar rayuwar mutum. Idan waxannan bangarori uku suka tsarkaka to mutum zai samu tsarkaka cikin dukkanin sasannin rayuwarsa da samuwarsa da zamantakewarsa
Duk wanda ya tsinkayi sirrikan hajjinsa aikinsa zai tsarkaka, duk wanda aikinsa ya tsarkaka ya rabauta da arziqin duniya da lahira, duk wanda ya yi aikin hajji gabanin sanin sirrika ta yiwu hajjinsa ya zamanto ya inganta idan aka kalli zahirin shari, sai dai cewa kuma bai ka ga samun kamalar hajjinsa ba daga liyafa da hadayar ubangiji, bai kai ga cimma tsolulwar kamala ba da zai samu damar kallon kyawun Allah da kwarjininsa da girmansa da zai nutsu da xebe haso da kwarjini.
kaxai dai mahajjaci yana kaiwa ga sirrikan hajjinsa idan ya tsarkake niyya ya yi hajjinsa don Allah, ya zamanto ya quduri niyyar ziyartar xakin Allah da dukkanin samuwarsa don a kankare masa zunubansa yay i xawafi tare da mala'iku da dukkanin zuciyarsa, wanda ya je hajjin don kasuwanci ko yawon buxe ido ko neman suna da xauka da girma kai da jiji da kai da riya da dai ire irensu bdag cikin abubuwa masu lalata aikin hajji.
to irin mai wannan niyya ba zai taba samun wannan garabasa ba, mai tsarkake niyya zai kasance daga mutanen da Allah ya xaukar musu alqawari cikin kiransa ga masoyinsa Ibrahim da fansarsa isma'il ga tsarkake xaki mai alfarma.
(وَعَهِدْنَا إِلَى إِبْرَاهِيمَ وَإِسْمَعِيلَ أَن طَهِّرَا بَيْتِيَ لِلطَّائِفِينَ وَآلْعَاكِفِينَ وَآلرُّكَّعِ آلسُّجُودِ)[30]
Kuma muka riqi alkawari gay a tsarkake xaki ga masu xawafi da masu ittikafi da masu ruku'u da sujjada.
Lalle su daga cikin al'ummar cika
makin annabawa shugaban manzanni muhammadu(saw)
(مُحَمَّدٌ رَّسُول آللهَ وَآلَّذِينَ مَعَهُ أَشِدَّاءُ عَلَى آلْكُفَّارِ رُحَمَاءُ بَيْنَهُمْ تَرَاهُمْ رُكَّعاً سُجَّداً يَبْتَغُونَ فَضْلاً مِنَ آللهَ وَرِضْوَاناً( [31]
Muhammadu manzon Allah ne, waxanada ke tare da shi sun da tsanantawa kan kafirai suna tausasawa tsakankaninsu z aka gansu suna ruku'u suna sujjada suna halin neman falala daga Allah da yardarsa.
Na'am dukkanin wanda ya kasance niyya ta gangan da ayyuka nagari ta qaqa zai kasance baqon Allah cikin ziyartar xakinsa mai alfarma, da wanda ya kasance ya na xauke da gumaka cikin kwakwalwarsa da zuciyarsa ko kuma ya riqi son rai abin bautarsa ta qaqa zai shiga xakin tauhidi? da dukkanin waxanda suka kasance suna russunawa gaban dukkanin girman kai da bautar `yan mulkin mallaka, ta qaqa zai hidima ga masu ruku'u da sujjada cikin xakin Allah? Da wanda ya kasance ya xawafi gefen shaixanu ta qaqa zai hidima ga masu xawain xakin Allah kuma ya dinga amsa sunan hadimin harami biyu?
Ba dukkanin wanda ya je hajji ya yi xawafi ke kasancewa hadimin harami biyu ban a haqiqa, da zamantowa an karbi hajjinsa ba, ma'arifarsa ta cika, ya kuma tsinkayi sirrikan hajji da hikimominsa da irfanin da ke tare da shi, da yawa yawan mutane kamar dabbobi suke wasu ma sunfi dabbobi batan hanya, zukatansu kamar dutse kai tafi dutse ma qeqashewa, sun kasance basu san gaskiya zaka ga surarsu ta zahiri surar mutane amma zukatansu na dabbobi. Me yafi tarin yawa daga masu iface iface mai yafi qaranci daga masu hajji?
Lalle hajji cikin tattararsa ya na tattaro ibadu da ayyukan addini kamar sallah tsarki ciyarwa da hijira da juriya da daurewa wahalhalu cikin tafarkin Allah, da kamewa ga barin aikata haramun, da sanya ihrami da sanya harami da tafiya zuwa ga Allah tare da jama'a muminai da yanka hadaya da ciyar da muminai da wilaya da bara'a.
Mai littafin jawahir shaik Hassan najafi ya na cewa: shi hajji misalin motsine na ibadar ruhi da xa'a ta sadaukar da dukiya da ibadar gangar jiki da ta furuci da aiki da samuwa da rashi.
Wannan adadi na daga kebantattun ibadu waxanda wata ibada ba tattaro misalinsu ba daga fannonin xa'a da biyayya[32]
ABUBUWA NA MUSAMMAN WAXANDA SUKA KEBANTA GA KA'ABA DA AIKIN HAJJI.
Lalle shi hajji na daga abubuwan da qur'ani ya ambace waxanda kebantacciyar ma'ana da xayantacciyar alamu sakamakon abin da ke cikinsa na daga tsare-tsare na asali da n agama gari, kamar yadda ya kasance ya kasance cikinsa akwai kebantattun abubuwa da suka banbanta shi da waninsa daga abubuwa da ma'noni da ke cikin muslunci.
Iadan muka nufi tsinkaya da tsayawa kan wani ba'ari daga cikinsu na farko-farko ga hajji bisa doron hasken qur'ani da fahimtarsa to zamu iya yin ishara ga waxannan abubuwa kamar haka:
Na farko: ka'aba mai daraja tushen dukkanin wani batu da ayyukan hajji:
Lalle ita ka'aba it ace xaki na farko da ka sanaya ga mutane an shimfixa qasa daga qarqashinta ta riqe fili mayalwaci tun lokacin da aka sauko da mumini ban qasa har zuwa ranar tashin qiyama, ka'aba ta kasance wajen xawafi da alqibala ga `ya`yan adamu, wanda ya tsara gininta shi ne jibra'il, aikin hajji da umara ba komai bane face wani tarsashin haske da ke farawa da rufeb da ka'aba.
Saboda ya zama dole mu kalli ka'aba daga abin da ya zo daga tsarata da gindayata da bayaninta daga qur'ani, lalle ita ka'aba ta fifita da abubuwa da za mu yi bayani kamar haka:
1 ita ce xaki na farko da aka
sanya a ban qasa don ibada
إِنَّ أَوَّلَ بَيْتٍ وُضِعَ لِلنَّاسِ[33]
Gida na farko da aka sanyawa mutane.
Babu wani wurin bauta daga wuraren bauta a ban qasa da ya rigayeta, lalle wannan tsohon xaki mai daraja ya ratayu da dukkanin ga mutane baki xaya tun daga adamu har zuwa tashin qiyama, babu wani fifiko cikinta ga wani bangare ko wata qungiya daga qungiyoyi ko ga wani sarki daga sarakuna.
2- lalle ita ka'aba xaki ne mai albarka:
(لَلَّذِي بِبَكَّةَ مُبَارَكاً)[34]
Ga wanda yake a bibakka mai albarka.
Albarka na daga cikin sunayen Allah mai albarka da ma'anar alheri matabbaci madawwami.
3- ana danganta ta ga Allah don darajantawa da girmamawa:
(طَهِّرْ بَيْتِيَ لِلطَّائِفِينَ وَآلْقَائِمِينَ وَآلرُّكَّعِ آلسُّجُودِ) [35]
Ka tsarkake xakina ga masu xawafi da masu tsayuwa da masu ruku'I da sujjada.
Lalle duk da cewa dukkanin abubuwan da ke duniyar nan mallakin
(للهِِ مُلْکُ آلسَّمواتِ وَآلاَْرْضِ )[36]
Allah mamallakin sammai da qasa.
Sai da cewa wannan xaki ya kebantu ya darajantu da mallakarsa da malakutiyyarsa ga Allah matsarkaki maxaukaki.
4- lalle ita ka'aba `yantaccen xaki ce:
)وَلْيَطَّوَّفُوا بِالْبَيْتِ آلْعَتِيق)ِ
Su kewaya `yantaccen xaki:
Kalmar atiq: na nufin abu mai daraja mai wahalar samu, ko kuma wanda aka cetar daga xufanan nuhu sai ruwa ya kewaya daura da shi, ko kuma `yantaccen xaki wand aba mallakar kowa ba ne, lalle ita ka'aba `yantacciya ce daga kowanne qaidi.
5- xakin tsayuwa da daidaito:
(جَعَلَ آللهُ آلْكَعْبَةَ آلْبَيْتَ آلْحَرَامَ قِيَاماً لِلنَّاسِ)[37]
Allah ya sanya ka'aba xaki tsararre ma'aunin addini ga mutane.
Ka'aba ta kasance daga abubuwa da ke tsara mutane da daidaita su.
6- lalle ita xaki ce matattara tushen shiriyar da mutane baki xayansu:
(إِنَّ أَوَّلَ بَيْتٍ وُضِعَ لِلنَّاسِ لَلَّذِي بِبَكَّةَ مُبَارَكاً وَهُدىً لِلْعَالَمِينَ )[38]
Lalle xaki na farko da aka sanyawa mutane shi ne wanda ke bibabbaka mai albarka kuma shiriya ga dukkanin talikai.
Ita ka'aba ta na sanya shiriya ga mutane baki xayansu ga wanda ya nufi ya kasance daga shiryayyu, saqon ka'aba bai taqaitu ga wanda ya tsayu cikinta ba ko kuma musulmai kaxai ita ka'aba ta dukkanin talikai ce.
7- aminci ga ka'aba da makka mai karamci:
(وَإِذْ جَعَلْنَا آلْبَيْتَ مَثَابَةً لِلنَّاسِ وَأَمْناً وَآتَّخِذُوا مِنْ مَقَامِ إِبْرَاهِيمَ مُصَلًّى وَعَهِدْنَا إِلَى إِبْرَاهِيمَ وَإِسْمَعِيلَ أَن طَهِّرَا بَيْتِيَ لِلطَّائِفِينَ وَآلْعَاكِفِينَ وَآلرُّكَّعِ آلسُّجُود)[39]
Ya yin da muka sanya xaki ya zama makoma ga mutane da aminci, kuma ku riqi wurin sallah daga muqamu Ibrahim kuma muka yi alqawali ga Ibrahim da isma'il da su tsarkake xaki ga masu xawafi da masu lazimta da masu ruku'I da sujjada.
Wannan amsa kiran Ibrahim badaxin Allah ne
:(وَإِذْ قَالَ إِبْرَاهِيمُ رَبِّ آجْعَلْ هَذَا بَلَداً آمِناً)[40]
Ya yin da Ibrahim ya ce ya ubangiji ka sanya wannan gari ya zma mai aminci.
Sai Allah ya sanya wannan bigire daga ban qasa cikin aminci da wurin aminta
(وَمَن دَخَلَهُ كَانَ آمِناً)[41]
Duk wanda ya shige shi zai kasance cikin aminci
(أَوَلَمْ نُمَكِّن لَهُمْ حَرَماً آمِناً يُجْبَى إِلَيْهِ ثَمَرَاتُ كُلِّ شَيْءٍ)[42]
Ashe ba mu mallaka musu harami amintacce ana karkato da `ya`yan itace gareshi kowanne iri.
(وَهذَا آلْبَلَدِ آلامِين)[43]
Da wannan gari amintacce.
Misalin ire iren wannan ayoyi da suke bayanin kasantuwar xakin Allah mai alfarma tushen aminci suna da tarin yawa cikin qur'ani mai daraja suna nuni kan girman batun da tasirinsa cikin rayuwar xaixaiku da jama'a
8-girma da alfarmar xakin ka'aba da masallacin harami da gari mai alfarma ma'ana makka da alfarmar wanda ya shiga ciknsa:
Alfarmar ka'aba:
(عِندَ بَيْتِکَ آلْمحَرَّمِ )[44]
A xakinka mai alfarma.
Haka masallacin harami na da tasa alfarma
(وَآلْمَسْجِدِ آلْحَرَامِ آلَّذِي جَعَلْنَاهُ لِلنَّاسِ )[45]
Da masallacin harami da muka sanya shi saboda mutane.
Haka wajibi ne a dinga girmama garin makka baki xayansa.
(حَرَماً آمِناً يُجْبَى إِلَيْهِ ثمرَاتُ كُلِّ شَيْءٍ)
Harami amintacce ana karkato da `ya`yan itace kowanne iri.
Kai bari madai dukkanin wanda ya shoiga cikin wannan gari zai kasance cikin aminci da amincin garin
(يَا أَيُّهَا آلَّذِينَ آمَنُوا لاَ تُحِلُّوا شَعَائِرَ آللهِ وَلاَ آلشَّهْرَ آلْحَرَامَ وَلاَ آلْهَدْىَ وَلاَ آلْقَلاَئِدَ وَلاَ آمِّينَ آلْبَيْتَ آلْحَرَامَ([46]
Ya ku waxanda suka yi imani ka da ku halasta ayyukan ibada da wata mai alfarma da hadaya da ratayar raquman hadaya da waxanda suka nufi xaki mai alfarma.
9-makoma ga mutane:
)وَإِذْ جَعَلْنَا آلْبَيْتَ مَثَابَةً لِلنَّاسِ وَأَمْناً.( [47]
Sa'ilin da muka sanya xaki makoma ga mutane da aminci.
Makoma ma'ana yankin da suke kai kawo su zo su koma lokacin mai tsayi. Ga misalign rin wanna aiki na ibadar I akwai alfanu mai tarin yawa cikin kowanne fage na rayuwa.
10- daidaito cikin haqqoqi tsakankanin mazauna garin maka da baqi.
)سَوَاءً آلْعَاكِفُ فِيهِ وَآلْبَادِ)[48]
Daidai cikin shi tsakanin mazauni da xan kauye.
Shi ne gari xaya rak da fifita da
kasantuwa garin kowa da kowa babu banbanci tsakanin baqo da xan gari, babu wani
mai daraja ta biyu cikinsa dukkanin mutane na da hukunci xaya duk da cewa
wannan doka ba ta aiki a wajen masarautar alu sa'ud saudiya, sai dai duk da haka
wannan doka tana nan cikin asalai maxaukaka cikin muslunci da ke nunu kan
girman wannan gari maia tsarki.
11- tsarki da tsafta:
Allah tasaftatacce ne ya son tsafta, lalle ita tsafta na daga imani lalle ubangiji na son masu tsarkaka, ya umarci masoyinsa badaxinsa Ibrahim da xansa fansa isma'il bayan gama ginin ka'aba da sabuntata
(أَن طَهِّرَا بَيْتِيَ لِلطَّائِفِينَ وَآلْعَاكِفِينَ وَآلرُّكَّعِ آلسُّجُودِ)
Ku tsarkake xakina ga masu xawafi da masu zama da masu ruku'I da sujjada.
Kalmar tasarkakewa ba tare da sanya mata qaidi ta tattro ma'anar tsaftacewa ta zahiri da tsaftacewar baxini, bai halasta mushriki ya kusanci xakin Allah ba sakamakon shi najasa ne wanda shirkasa na iya qazanta xakin Allah na tauhidi mai alfarma, wannan na yayewa da tajalli cikin da yawa yawan ayyukan hajji, kamar misalign mustahabbancin wankan wuraren tsayuwa waxanda daga cikinsu wurin gangara ga harami mai alfarma da wurin gangara ga masallacin harami da dai makamantansu…..
12- 1 daga ibadun Allah:
Lalle qur'ani mai girma bayan ya Ambato wasu adadi daga ayyukan hajji ya yi nuni kan cewa suna daga ibadun Allah:
(يَا أَيُّهَا آلَّذِينَ آمَنُوا لاَ تُحِلُّوا شَعَائِرَ آللهِ وَلاَ آلشَّهْرَ آلْحَرَامَ )
Ya ku waxanda suka yi imani ka da ku halasta ibadun Allah da wata mai alfarma.
Sha'a'ir jam'I ne Kalmar sha'ira a harshen larabci wanda ma'anarsa shi ne alama ga wuraren ibadar Allah matsarkaki maxaukaki.
13- 2 halartar mawadata masu iko da qoshin lafiya da amincin hanyar da zasu bi suje makka:
(وَللهِ عَلَى آلنَّاسِ حِجُّ آلْبَيْتِ مَنِ آسْتَطَاعَ إِلَيْهِ سَبِيلاً( [49]
Kuma Allah na da haqqin ziyartar xakinsa kan mutane ga wanda ya samo iko ya zuwa garsehi.
Cikin kowacce shekara wajibi kan wanda ke da iko cikin dukiyarsa da lafiyarsa da amincin hanya da ya je aikin hajji sau xaya a cikin tsawon rayuwarsa amma idan ya qara kan wajibi to hakan na daga taxawwa'I da nafila(musatahabbi).
14- 3 halartar faqirai da mabuqata:
Duk da cewa ubangiji ya wajabta hajji kaxai kan mawadata masu iko sai dai cewa duk inda dukiya ta ke baza a rasa talakawa ba da mabuqata sakamakon samuwar talakawa da mabuqata cikin makka ma karamci, lalle Allah ya kebance su da faxinsa:
(وَأَطْعِمُوا آلْبَائِسَ آلْفَقِيرَ )[50]
Ku ciyar da matsatstse da talaka
(فَكُلُوا مِنْهَا وَأَطْعِمُوا آلْقَانِع وَآلْمُعْتَرّ)[51]
Ku ci daga gareta ku ciyar da talaka mai wadatar zuci da mai roqo.
15- 4 ambaton Allah:
Daga cikin muhimmai da mafi tsarkakar manufofin aikin hajji shi ne ambaton Allah matsarkaki a aikace da furuci:
(وَيَذْكُرُوا آسْمَ آللهَ فِي أَيَّامٍ مَعْلُومَاتٍ )[52]
Su ambaci sunan Allah cikin qididdigaggun kwanaki.
(لِتُكَبِّرُوا آللهَ عَلَى مَا هَدَاكُمْ وَبَشِّرِ آلْمحْسِنِينَ( [53]
Don ku girmama Allah sakamakon abin da ya shiryar da ku kayi bushara ga masu kyautatawa.
16- 5 riska tsakanin annbata da imamanci da rawar da suka taka cikin rayuwar mutum.
Lalle bayn xawafi wajibi yin sallah xawafin bayan muqamu Ibrahim, don mai sallah ya tuna da shehun annbawa ma'abocin addinan sama uku wato Ibrahim mai sallah ya kasance kan aqidarsa da hanyarsa madaidaiciya.
Lalle cikin masallacin harami akwai wasu bayyanannun ayoyi, lalle Allah ya kenace ba'arisnu da muqamiu Ibrahim hakan nanuni da girman wannan al'amari, lalle Ibrahim ya kasance limamin masallata da masu xawafi.
(فِيهِ آيَاتٌ بَيِّنَاتٌ مَقَامُإِبْرَاهِيم)[54]
Cikinsa akwai ayoyi mabayyana muqamu Ibrahim.
17- 6 motsin da kai kawo da hijira daga wani waje zuwa wani waje:
Haqiqa aikin hajja ya fifita da kai kawo ba tare da hutawa ba, motsawa daga miqati sannan harami sannan xawafi da ihrami ga hajja da tsayuwar Arafat da mash'arul haram da mina da ayyukan da ke cikinta da wasusnsu….
Daga cikin abin da ke wajabta miotsawa mahajjata da kai warsu ga hadafai maxaukaka tsarkaka, da motsa al'ummar musulmai ya zuwa gaba shi ne wannan xan qaramin taro na hajji wanda ya ke sabunta a kowacce shekara don cigaba da wannan tafiya da dawwama kanta ba tareda sanyi jiki da jumudi da kasala ko qosawa, bari ma dai taron na gudana da dukkanin nishaxi da ninka himma daga musulmi mazajensu da mata.
Me yafi kyawu da qayatarwa daga wannan motsi da kai kawo na miliyotyin mutne daga kowanne bangare na wannan duniya tare da dukkanin banbancin mazhabobinsu na fiqihu da launin fatarsu da banbancin harshensu da garuruwansu da daulolinsu da hukumominsu, wasunsu sun fito daga gabashin duniya zuwa yammaci wasu daga arewa zuwa kudanci, kowannensu ya na keawaya daura da ka'aba da dukkanin girmamawa da kyawu da kamala.
18- 7 nesantar daga munanan xabi'u da halaye daga xaiku da jama'a
)آلْحَجُّ أَشْهُرٌ مَعْلُومَاتٌ فَمَن فَرَضَ فِيهِنَّ آلْحَجِّ فَلاَ رَفَثَ وَلاَ فُسُوقَ وَلاَ جِدَالَ فِي آلْحَجِّ وَمَا تَفْعَلُوا مِنْ خَيْرٍ يَعْلَمْهُ آللهُ وَتَزَوَّدُوا فَإِنَّ خَيْرَ آلزَّادِ آلتَّقْوَى وَآتَّقُونِ يَا أُولِي آلاْلْبَابِ[55].(
Hajji wasu qididdigaggun watanni ne duk wanda ya farlanta hajji cikinsu to babu jima'I babu fasiqanci babu jayayya a hajji dukkanin abin da kuku aikata daga alheri Allah na sane da shi kuyi guzuri haqiqa mafi alherin guzuri shi ne guzurin taqawa, ku ji tsorona yak u ma'abota hankula.
Lalle hajji da batutuwansa da wuraren ibadunsa tsarkaka masauki ne ga ma'abota hankula sune waxannan da suka mallaki kawukansu daga rai mai umarni da munanan ayyuka, sai suka kubuiuta daga fursun xin biyewa sha'awe –sha'awe.
19- 8 wuraren alheri:
(إِنَّ آلصَّفَا وَآلْمَرْوَةَ مِن شَعَائِرِ آللهِ فَمَنْ حَجَّ آلْبَيْتَ أَوِ آعْتَمَرَ فَلاَ جُنَاحَ عَلَيْهِ أَن يَطَّوَّفَ بِهِمَا وَمَن تَطَوَّعَ خَيْراً فَإِنَّ آللهَ شَاكِرٌ عَلِيمٌ( [56]
Lalle safa da marwa na daga wuraren ibada da ke sanyawa a tuna da Allahdukkanin wanda ya ziyarci xakin don hajji ko kuma umara babu laifi gareshi ya yi xawafi garesu, duk wanda ya qara yi aikin alheri lalle mai godiya ne masani.
Haqiqa Allah matsarkaki ya yi wasiyya da aikata alheri cikin hajji da umara da wuraren ibadarsu da na hadaya
(وَمَا تَفْعَلُوا مِنْ خَيْرٍ يَعْلَمْهُ آللهُ وَتَزَوَّدُوا فَإِنَّ خَيْرَ آلزَّادِ آلتَّقْوَی)[57]
Abin da kuka aikata daga alheri Allah na sane da shi ku yi guzuri lalle mafi alherin guzuri shi ne guzurin taqawa.
Hajji na rugurguza zunubai kuma hajji mahalli ne na guzuri da taqawa da aikata alheri da kyautatawa. Ibada ne ta fuska game gari. ba'arin wasu daga cikin ayyukan hajji da kabantaccen yanayi suna da tasiri cikin nisantar munanan halaye da aikata zunubai wasu ba'arin kuma suna da tasiri cikin yin ado da sallamawa ubangiji da yi masa biyayya da faloli da kyawawan halaye, wani ba'arin kuma ya tattaro dukanin bangarorin biyu, shi hajji na daga kason qarshe sakamakon shi hajji ya cxanya daga juzu'ai da suke ingije dukkanin cututtuka zuciya da ke hana mutum gangara da kaiwa ga duniyara haske da hallara cikin masaukin gaskiya wajen sarki mai iko.
Lalle shi hajji na da sasanni mabanbanta wanda suka tattaru kan tushen tauhidi da annabta ta gaskiya da iamamnci cikin aminci da aminta da lafanun duniya da lahira cikin shiryar da mutane da korasu zuwa ga rabautar duniya da lahira da `yantar da su daga iyakoki da qaidojin `yan mulkin mallaka da na qabila da mazhaba, dukkanin mutane bayi ne ga Allah cikin xawafin ka'abarsa mai daraja da xakinsa `yantacce da masallacinsa mai alfarma, da halartar mawadata da motsa tattalin arziqi tare da siyasa ta hikima wadda ruhin ibada da ambaton Allah matsarkaki cikin jama'a ke jagorantar hakan ba tare da kubucewa ko yankewa, wannan na daga cikin hikimar ubangiji ma'abocin nasara, lalle shi masani ne mai hikima.
Lalle hajji na da wasu alamomi daga aljanna lalle ya zo cikin hadisi mai daraja cewa dutsen hajarul aswad daga aljanna yake, lalle ita ka'aba bayan akwai wata hema wacce take daga aljanna, lalle harami shi ne amudi da hasken wannan hema, ziyartar xakin ka'aba komawa ne ga aljanna.
(جِئْتُمُونَا فُرَادَى كَمَا خَلَقْنَاكُمْ أَوَّلَ مَرَّةٍ )[58]
Haqiqa kun zo mana xaixaiku kamar yadda muka halicce tun farko.
(وُجُوهٌ يَوْمَئِذٍ نَّاضِرَةٌ * إِلَى رَبِّهَا نَاظِرَةٌ )[59]
Fuskoki suna cikin annashuwa da annuri, suna saurare zuwa ga ubangijinsu
(آدْخُلُوهَا بِسَلاَمٍ آمِنِينَ ) [60]
Ku shiga da aminci kuna amintattu
(وَمَن دَخَلَهُ كَانَ آمِناً)[61]
Duk wanda ya shiga cikinsa ya kasance cikin aminci.
Halartar mahajjaci mahajjaciya da mai umara namiji da mace ga xakin Allah mai alfarma kamar wani misali daga shigar mumini da mumina masu xayanta Allah cikin gidan aminci cikin aljanna.
Hassan najafi mai littafin jawahirul kalam na cewa: lalle hajji na daga mafi girman alammomin ibadar Allah cikin muslunci mafi falalar ibadar da mutane za su kusanci ubangiji masani, sakamakon abin da ke cikinsa daga qasqantar da kai da gajiyar da jiki da qauracewa iyali da baqunta cikin garin da ban aka ba da barin al'adu da barin jin daxi da sha'awe- sha'awe da makaruhi, da sadaukar da kuxi da ciyar da su da xaura xamara da jurewa wahala da kai kawoda cuxanya da ibtila'o'I cikin mu'amala da mutanen banza.
Lalle hajji na taimakon mutum kan sanin kansa(duk wanda ya san kansa haqiqa ya san ubangijinsa) duk kuma wanda ya san ubangijinsa haqiqa ya san komai, lalle shi tun daga xaura haraminsa har zuwa saisaye, tun daga tsayuwar Arafat har zuwa jifan shaixan ya na rugurguza gumakan da ke cikin zukata yay i galaba kan biyewa son zuciya da rai, idan hajinsa ya kasance cikin ma'arifa da gaskiya
da tsarkin niyya to sai ya kubuta daga bautar ubanijai
(مَنِ آتَّخَذَ إِلهَهُ هَوَاهُ)[62]
Wanda ya riqi son zuciyarsa abin bautarsa.
(وَلِكُلِّ أُمَّةٍ جَعَلْنا مَنسَكاً لِيَذْكُرُوا آسْمَ آللهَ عَلَى مَا رَزَقَهُمْ مِن بَهِيمَةِ آلاَْنْعَامِ فَإِلهُكُمْ إِلهٌ وَاحِدٌ فَلَهُ أَسْلِمُوا وَبَشِّرِ آلْمخْبِتِينَ )[63]
Kowacce al'umma mun sanya ibadar yanka domin su ambaci sunan Allah bisa abin da ya azurta su da shi daga dabbobin ni'ima lalle abin bautarku abin bauta ne guda xaya rak ku sallma gareshi ka yi bushara ga masu qasqantar da kai
(وَمَنْ أَحْسَنُ دِيناً مِمَّنْ أَسْلَمَ وَجْهَهُ للهِ وَهُوَ مُحْسِنٌ وَآتَّبَعَ ملَّةَ إِبْرَاهِيمَ حَنِيفاً وَآتَّخَذَ آللهُ إِبْرَاهِيمَ خَلِيلاً)[64]
Waya fi kyawunta addini daga wanda ya sallama fuskarsa ga Allah ya na halin kyautatawa ya bi aqiadar Ibrahim madaidaiciya Allah ya riqi Ibrahim badaxi.
(مَا كَانَ إِبْرَاهِيمُ يَهُودِيّاً وَلاَ نَصْرَانِيّاً وَلكِن كَانَ حَنِيفاً مُسْلِماً وَمَا كَانَ مِنَ آلْمُشْرِكِينَ )[65]
Ibrahim bai kasance bayahude ba ko banasare sai dai cewa ya kasance mai karkata zuwa ga tafarkin gaskiya ya na musulmi bai kasance daga mushrikai ba.
(وَوَصَّى بِهَا إِبْرَاهِيمُ بَنِيهِ وَيَعْقُوبُ يَا بَنِيَّ إِنَّ آللهَ آصْطَفَى لَكُمُ آلدِّينَ فَلاَ تَمُوتُنَّ إِلاِّ وَأَنْتُم مُسْلِمُونَ( [66]
Ibrahim ya yi wa xiyansa wasicci da ita da yaqub ak u xiyana lalle Allah ya zaba muku addini ka da ku sake ku mutu face kuna musulmi.
Mahajjaci bawa musulmi da ya sallama ya fawwala al'amarinsa ga Allah mai girma da xaukaka, misalign tsantsar wannan sallamawa ya na tajalli cikin ibadun hajji cikin wajibai da haramu da mustahabbi da makaruhi, musammam ga wanda ya kasance daga arifai ma'abota shuhudi da kashefi.
SIRRIKAN HAJJI CIKIN TASFTACE ZUKATA
Lalle daga cikin mafi tsarkaka da girma cikin saqonnin annabawa baki xaya da shari'ar shugaban mu zababbe muhammadu(saw) shi9 ne tsarkake zuciya da koyar da mutane littafi da hikima don su tsayar da ma'auni da adalci da kyautatawa.
Daga cikin asasin muslunci da ruhinsa da gundarinsa shi ne kyawawan xabi'u
«إنّما بعثت لاُتمّم مكارم الأخلاق »
Kaxai dai an aiko ni ne don in cika kyawawn xabi'u.
Kai hatta ana cewa: shi muslunci addini kyawan xabi'u ne, wannan shi ne hadafin ubangiji da annabi cikin tarbiyar mutum da tsarkake xabi'unsa zai ta yin tajalli da qaruwa cikin hajji da ibadun da ke cikinsa da ladubbansa da ma'anawiyarsa, lalle shi hajji makaranta ce ta tarbiyya da tashar kankare zunubai da imani da taqawa wadda kyawawan xabi'u daga ubangiji da annabi da waliyinsa ke jagorantar ta, da darussa cikin kyawawan xabi'u na nazari da na aiki.
Daga cikin mafi balagar wasiyyoyin imam sadiq(as) ga mahajjaci shi ne faxinsa:
«اذا أردت الحجّ فجرّد قلبک لله تعالى من كلّ شاغل وحجاب كلّ حاجب »[67]
Idan ka nufi zuwa aikin hajji to ka cire dukkanin wani hijabi da duk wani abu mai shagaltarwa da dukkanin wani shinge daga cikin zuciyarka.
Duk son ya isa ga zuwa ubangijinsa gwargwadon zira'I biyu ko mafi kusa daga haka, to zai samu haka cikin sulukinsa hanyoyin falaloli da kyawawan xabi'u cikin ayyuka da siffofi, Allah ya sanya ibadu kan shakalai mabanbanta, ta yiwu cikin hikimar say a sanya kowanne shakali kae korar muguwar xabi'a daga muggan xabi'u, ya wajabta yin ado da xaya daga cikin falaloli, lalle shi hajji ya tattara cikin samun dukkanin falaloli halaye nagargaru.
Lalle shi hajji na koyar da mahajjaci da mahajjaciya qaqa za su kasance tare da kawukansu haka qaqa za su kasance da ubangijinsu haka ma da qarama al'umma ma'ana iyali, da babbar al'umma ma'ana ragowar jama'a daga maqota da makusanta da abokai da dai sauransu…. Lalle hajji na koyar da ruhin sadaukarwa da fansa da hidima ga mutane da tausayi da soyayya da nuna qauna da girmama juna da kyauta da kyawunta murmushi da kyawawan xabi'u da ciyarwa
(لِيَشْهَدُوا مَنَافِعَ لَهُمْ وَيَذْكُرُوا آسْمَ آللهَ) [68]
Don su halarci alfanu garesu su ambaci sunan Allah.
Su ambaci sunansa a kan harshe da cikin zuciya da ruhi.
Imam rida(as) bayan yay i bayani wasu adadi daga hikimomi da falsafar hajji:
«وما في ذلک لجميع الخلق من المنافع والرغبة والرهبة إلى الله سبحانه وتعالی)[69]
Da dukkanin abin da ke ciki haka ga dukkanin halittu daga alfanu da kwaxayi da tsoro zuwa ga Allah matsarkaki maxaukaki.
Albarkataccen hajji shi ne wanda ya kasance cuxanye da kyawawan xabi'u da kyawun abokantaka ga wanda ya abokantaka.
Imam ya cigaba da cewa:
«إنّ علّة الحجّ الوفادة إلى الله... وما فيه من الخضوع والإستكانة والذلّ » «والخروج من كلّ ما إقترف » «وحظرها عن الشهوات واللذّات » «ومنه ترک قساوة القلب وخساسة الأنفس ونسيان الذكر وانقطاع الرجاء والأمل ... وحظر الأنفس عن الفساد» «وعند ما حلقت انک نويت انک تطهّرت من الأدناس وخرجت من الذنوب كما ولدتک اُمُّک [70]»
Lalle dalilin sanya aikin hajji shi ne ziyartar Allah.. da abin da ke cikin ziyara daga qasqantar da kai da talautuwa da qasqanta, da fita daga dukkanin zunubion da ya aikata, da hanawa kai jin daxi da sha'awe-sha'awe, daga cikin hakan akwai wasti da bushewar zuciya da wulaqantarta da mantuawa da ambaton Allah da yanke fata da buri da tsawatarwa da rai daga barna, ya yin da kayi aski to lalle kai ka xau xamarar cewa ka tsarkaka daga dattin zunubi ka fita daga greshi kamar ranar da mahaifiyarka ta kawo ka duniya.
(علة الحجّ الوفادة إلى الله... وليكون تائباً ممّا مضى مستأنفاً لما يستقبل )
Dalilin sunnanta aikin hajji shi ne ziyara zuwa ga Allah don mahajjaci ya kasance mai tuba daga abin da ya gabata daga kurakurensa ya xau himmar sake aiki nan gaba.
Daga cikin sirrikan hajji shi ne kawuntar xabi'un tuba da komawa ga Allah matsarkaki da yin istigfari da tuba daga zunibai adag abin da ya bayyana daga garesu da wanda ya buya.
Taqawa it ace shugaban dukkanin kyawawan xabi'u, lalle ubangiji ya umarci bayinsa da suyi guzuri da taqawa.
(وَتَزَوَّدُوا فَإِنَّ خَيْرَ آلزَّادِ آلتَّقْوَى ) [71]
Kuyi guzuri lalle mafi alheri guzuri taqawa.
Lalle taqawa da tsantseni sune ruhin hajji kai sune ruhin dukkanin ibada.
(لَن يَنَالَ آللهَ لُحُومُهَا وَلاَ دِمَاؤُهَا وَلكِن يَنَالُهُ آلتَّقْوَى).[72]
Lalle namanta bai samun Allah haka jininta sai dai cewa zai sameshi.
قال الامام الصادق 7: «إذا أحرمت فعليک بتقوى الله وذكر الله كثيراً»
Imam sadiq(as) ya ce: idan ka xaura harami to ka lazimci taqawa da yawaita ambaton Allah.
(فَإِذَا قَضَيْتُمْ مَنَاسِكَكُمْ فَاذْكُرُوا آللهَ كَذِكْرِكُمْ آبَاءَكُمْ أَوْ أَشَدَّ ذِكْراً)[73]
Idan ku gama ayyukan hajjinku ku ambaci Allah kamar yadda kuke ambaton iyayenku ko kuma mafi tsanani daga ambaton.
(وَآذْكُرُوا آللهَ فِی ايَّامٍ مَعْدُودَاتٍ )[74]
Ku ambaci Allah cikin qididdigaggun kwanaki.
«إنّما جعل الطواف بالبيت وبين الصفا والمروة ورمی الجمار لإقامة ذكر الله» «إنّما فرضت الصلاة وأمر بالحج والطواف واشعرت المناسک لاقامة ذكر الله».
Kaxai dai an sanya xawafi tsakanin dutsen safa da marwa da jifan shexan don tsayar ambaton Allah, kaxai an farlanta sallah anyi umarni da hajji da xawafi da raya alamomin ibadu don tunawa da Allah.
Abin da ake nufi daga ayyukan hajji shi e ambaton Allah matsarkaki cikin kowanne hali
(أَن تَقُومُوا للهِ مَثْنَى وَفُرَادَى( [75]
Ku btsayu domin Allah bibiyu da xai xai.
Sa'ilin da kake gifta mash'arul haram sai ka quduri niyyar cewa kai ka jiyar da zuciyarka alamomin ma'abota taqawa da tsoron Allah mai girma da xaukaka.
DAGA CIKIN SIRRAKAN AKWAI SIYASA DA ZAMANTAKEWA
1-samar wahada da haxa kan zukata da sahun muslmai
2- kammalar tunani da cikakkiyar wayewa tsakanin musulmi
3-sulhu da abokantaka da kyawunta zamantakewa cikin soyayya da fuskantar juna tsakanin dukkanin kungiyoyi da mazhabobi.
4-samar da yanayi da ya dace don gina al'ummar musulmi kwaya xaya
5- kammalar kyawawan xabi'u da zamanatakewa da kiyaye iyakoki da dokoki.
6- himmatuwa da kiyaye tsaftar muhalli da lafiyar al'umma.
7- qarfafa zamantakewar al'ummar musulmi.
8-koyarwa da shirya bajokolin aiki ga birni abin buga misali
9- shiri da tanadi don fuskantar maqiya muslunci.
10 shirya wasan kwaikwayo don girman muslunci da musulmi.
11- barranta daga mushrikai.[76]
DAGA CIKIN SIRRIKAN HAJJI NA IRFANI
Lalle daga mauhimman sasannin hajji shi ne zurfafar irfani abin da ake nufi daga irfani shi ne sanin ayyuka da ibadun hajji da ladubbansa na ma'anawiyya wanda suka ginu kan haqiqanin abubuwa da ayoyin shuhudi da ishraqi da wusuli da haxewa tare da haqiqa da tsafatace ruhi da haskaka zukata, har ta kai ga kaiwa ga misalin mudubi wanda haqiqanin abubuwa kebayyana cikinsa ba tare da kallafawa kai dogon bayani da kafa hujja ba kai da dalilan hankali da riwaya. Duk wanda ke kallon hajji daga wannan zawiya to lalle shi zai tsinkayi sirrikan abubuwa da haqiqaninsu waxanda suke kan daidai ya kuma riski luxufai masu girma da za su yi tasiri cikin sululkinsa cikin gaba xayan hajjinsa na ibada da irfani da aiki.
Daga cikin muhimman sirrikan irfani a cikin hajji:
1-Xayanta Allah da saninsa da tafiyar aqida tsakankanin mafara da makomawa da suka misaltu cikin tauhidin zati da na siffa da na aiki, har ya ka ga qarawa mutum imani da yaqini da shiriya, lalle hajji ya na bayyana mana tauhidi ya na kuma kore dukkanin shirka shirka. Lalle hajji wata tafiya ce daga Allah zuwa ga Allah da kore dukkanin waninsa da narkewa cikinsa da wanzuwa tare da shi.
قال الامام الصادق 7: «وزر البيت متحقّقاً لتعظيم صاحبه ومعرفة جلاله وسلطانه .[77]
Imam sadiq(as) ya ce: ka ziyarci xakin Allah ka na mai tabbatar da girmama ma'abocnisa da sanin girmansa da mulkinsa.
2- neman kusancin Allah matsarkaki cikin hajji bayan mahajjaci ya riski ma'arifar ubangijinsa ka da ya tsaya iya nan cikin tafiyarsa gareshi, bari dai ya yi kai kawo wajen tsaftace ruhi da mutunta zuciya, ya kewaya daura da ka'abar soyayyar abin bauta don ya sha daga tsarkakakken zamzam xinsa , ya tsaya cikin Arafat da masha'arul haram don ya bayyana burinsa ga ubangijinsa.
Wannan kusanci bai taqaitu da lokaci ba ko wani bigire ba, bari da ana nufin kusanci na zuciya da ma'anawiyya, sai ya ga ubangijinsa halarce yay i munajati da shi cikin sirrikansa, ya gudu zuwa gareshi a hajji da umara, ya kubuta daga dukkanin munanan halaye don ya samu ya yi ado da falaloli ya xebe haso da ubangijinsa don ya samu keta hijaban haske cikin duniyar ruhi da hankula, kuma ya keta duhu cikin duniyar misalai da inuwa har ya samu ya kai ga zuwa ga ubangijinsa gwargwadon zira'I biyu ko kuma mafi kusa daga haka cikin bigire masauki na gaskiya wajen mai ikon yi mai ikon zartarwa
قال الامام الرضا 7 :«انّ علّة الحجّ ... التقرّب في العبادة إلى الله عزّوجلّ».
Imam rida(as) ya ce: dalili sanya hajji… shi ne don neman kusanci cikin ibada ya zuwa ga Allah mai girma da xaukaka.
Duk wanda ya nufi makka don aikin hajji kaxai dai ya na ziyartar ubangijinsa ne ya nufinsa cikin al'arshina cikin addu'ar tafiyarsa ya na mai cewa:
«يسم الله دخلت ، وبسم الله خرجت ، وفي سبيل الله... أنا عبدک وبک ولک » [78]
Da sunan Allah na shiga da suanasa zan fita cikin tafarkin Allah, ni bawanka ne naka don kai.
Lalle ya kamata mahajjaci yay a yi iya qoqarinsa wajen ganin hajjinsa bai baci da jima'I ko fasiqanci da cece kuce da jayayya ba.
3- liyafa ta har abada don Allah matsarkaki, lalle dukkanin halittu suna cikin liyafar Allah kan teburin darbar mai rahama.
(وَإِن مِن شَيْءٍ إِلاَّ يُسَبِّحُ بِحَمْدِهِ ) [79]
Babu wani abu face ya na tasbihi da godiyarsa.
Kamar yadda musulmi cikin watan Ramadan suke cikin liyafar Allah baki xanysu da ma'ana mai gamewa. amma cikin makka mai karamci cikin qididdigaggun kwanaki suna cikin liyafar Allah da kebantacciyar ma'ana.
Duukanin wanda ya ziyarci kammalallen mutum cikin hajjinsa ma'ana manzon Allah(saw) da imami ma'asumi(as) shi ya na cikin sanin haqqinsu to lalle zai kasance cikin maffi karamcin waxanda suka ziyarci xakin Allah maxauakaki zai kuma kasance cikin liyafar Allah da keabantacciyar ma'ana.
Lalle shi hajji liyafar Allah da walima da darba da sunan mai rahama mai jin qai.
(إنّ علّة الحجّ الوفادة إلى الله تعالى )
Lalle aikin hajji ziyara ce zuwa ga liyafar Allah maxakaki
(وَأَذِّن فِي آلنَّاسِ بِالْحَجِّ يَأْتُوکَ رِجَالاً وَعَلَى كُلِّ ضَامِرٍ يَأْتِينَ مِن كُلِّ فَجٍّ عَمِيقٍ( [80]
Kayi yekuwa cikin mutane don ibadar hajji za su zo mka suna masu tafiya kan qafafuwansu a kan dukkanin xankwararen doko zsu daga dukkanin rango mai nisa.
قال الصادق 7: «إنّ ضيف الله عزّوجلّ رجل حج وإعتمر، فهو ضيف الله حتّى يرجع إلى منزله » . [81]
Imam sadiq(as) ya ce: baqon da halarci liyafar Allah mai girma da xaukaka shi ne mutumin da ya je umara da hajji, lalle yana cikin liyafar Allah har lokacin da zai dawo gida.
قال أميرالمؤمنين علي 7: «الحاج والمعتمر وفد الله، وحق الله أن يكرم وفده ويحبوه بالمغفرة[82]
Sarkin muminai ali(as) ya ce: mahajjaci da mai aikin umara baqin Allah ne, kuma na daga cikin haqqin allah ya girmama baqonsa ya kuma nuna masa soyayya da gafara.
4- daga cikin sirrikan irfani cikin hajji shi ne qarfafar janinbin ma'anawiya da ruhiya, lalle zamani da bigire da ayyukan hajji na da tasiri na ma'anawiyya da ruhiya da suke bayyana a ruhin mutum, lalle sun a daga abin da ke wajabta tsarkakar baxini da lafiya, da qarfafa imani da addini da yaqini
قال أميرالمؤمنين علي 7: «والحجّ تقوية الدين[83]
Sarkin muminai ali(as) ya ce: shi hajji qarfafa addini ne.
وقال الامام الرضا 7 في فلسفة الحجّ : «وحظر النفس عن الفساد» .[84]
Imam rida(as) ya ce: cikin falsafar hajji: katange kai daga barna.
Shi hajji waraka daga dukkanin cutuka da ciwon ruhi da cututtukan zuciya.
5- tajallin bauta da ma'auni cikin biyayya kammiya da kaifiya:
Ya zo cikin hadisi qudusi:
«خلقت الأشياء من أجلک وخلقتک من أجلي »
Na halicci dukkanin halittu domin kai, na halicce ka don kaina.
«عبدي أطعني حتّى أجعلک مثلي أقول للشيء كن فيكون وتقول للشيء كن فيكون » «العبوديّة جوهرة كنهها الربوبيّة »
Ya kai bawana ka yi mini biyayya har in sanya ka misalina ina cewa abu kasance sai take ya kasance, kai z aka cewa abu kasance take ya kasance, lalle ita bauta gundarin zurfafarta shi ne ubangijintaka.
Abin da ake nufi da halitta da sirrin halifa da falsafar rayuwa shi ne ibada da ma'arifa ma'ana sanin Allah. Wannan shi ne abin dake tajalli da bayyana cikin hajji da mfi haskakar sura da girma, lalle shi hajji sallamawa ga Allah, mahajjaci ya yinda ya xaura harami sai ya haramtawa kansa dukkanin ayyukan haramu, sannan ya keawaya xakin Allah tare da masu xawafi yay i ruku'I da masu ruku'I da sujjada yay i sa'ayi yay i jifan shaixan ya yanka hadaya ya aske gashin kai ya yi saisaye.
(لبّيک بحجّة حقّاً تعبّداً ورقّاً)
Ina amsa kiran hajji haqiqa don bauta da kasantuwa bawa.
Shi hajji na kammalawa bawa muqamin bautar Allah matsarkaki maxaukaki.
6- shi hajji mosti ne na shari'a ga al'ummar musulmi:
Hajji daura ce cikakka cikin motsa jiki na shari'a wadda ke taimakawa mutum matafiyi da mai suluki zuwa ga Allah cikin sulukinsa na irfani, lalle shi hajji xan qaramin jihadi ne, mahallin imani don risker failoli Allah abin bauta da kamaloli mutumtaka. Kai madalla da wannan jihadi na hajji.
7- tunawa da mutuwa da tashin qiyama:
Hajji wata ce da aka sanya tsakanin duniya da lahira, lalle cikin ibadunsa ya na sanyawa a tuna da Allah da ranar tashin qiyama, me yafi kyawu daga mahallin miqati da wajen xaura tufafin harami kai kace mahajjaci na ganin kansa cikin taron qiyama yana jiran lokacin xawafi ya qarato, kai kace lokcin tsayuwar hisabi ne.
قال الامام الصادق 7: «ولا شرع نبيّه في حلال وحرام ومناسک على ترتيب ما شرعه ، إلّا الاستعداد والإشارة إلى الموت والقبر والبعث والقيامة ، وفصل بيان السبق في الدخول الجنّة أهلها، ودخول النار أهلها، بمشاهدة مناسک الحجّ من أوّلها إلى آخرها لاُولى الألباب واُولى النهى.[85]
Imam sadiq(as) ya ce:bai shar'antawa annabinsa ba cikin hala da haram da ayyukan hajji a bisa tsarin da ya shar'anta shi ba face don tanadi da ishara ya zuwa mutuwa da qabari da tashin qiyama, da faifaice bayanin rige cikin shiga aljanna ga ahlinta, da shigar ahlin wuta cikinta da shaida ayyukan hajji tun daga farko zuwa qarshe ga ma'abota hankula.
Tafiya zuwa aikin hajji yay i kamanceceniya da tafiya zuwa lahira daga halartowar mala'ikan mutuwa da qabari da tashin kiyama amma fag a wanda ya ke daga cikin ma'abota hankula haskaka tsarkakakku daga dattin duniya da sabo da munana halaye.
8- yankewa da komwa ga Allah:
Daga cikin himmar arifai cikin tafiyarsu da sulukinsu shi ne yankewa daga dukkanin abin da ba Allah ba. kamar yadda ya zo cikin addu'a:
(وهب لي كمال الانقطاع إليک )[86] .
Ya
ubangiji ka azurta ni da kamalar yankewa zuwa gareka.
قال الامام الصادق 7: «إذا أردت الحجّ فجرّد قلبک لله عزّوجلّ من قبل عزمک ، من كلّ شاغل وحجاب كلّ حاجب » . [87]
Imam sadiq(as) ya na cewa: idan ka nufi hajii ka kwabe zuciyarka daga don Allah mai girma da xauka ta fuskanin azamaraka da dukkanin wani mai shagaltarwa haka ma da dukkanin hijabi da shinge.
Daga mafi muhimmancin falsafar hajji da sirrikansa shi ne yankewa zuwa ga Allah matsarkaki da haxuwa da shi ma kyawu da kamala da girma sai dai kuma hakan ba tabbata sai bayan an tsarkake zuciya daga munana abubuwa da yi mta ado da falaloli daga kyawawan xabi'u da ayyuka nagargaru, shi mhajjaci da xaura ihrami ya na nufin ya haramtawa kansa duk wani abu koma bayan ubangijinsa, da dukkanin abin da babu sunan Allah cikin, sannan kuma ya kasance bawa mai tsarkake niyya ga Allah matsarkaki
فعلّة الحجّ الوفادة إلى الله وطلب الزيادة »
Saboda haka dalilin sanya hajji shi ne baquntar liyafar Allah da neman qari.
وسئلالامامالباقر عن وجه تسمية الحجّ فقال 7: «حج فلان أي أفلح فلان
An tambayi imam baqir(as) game dasanya sunan hajji? Sai ya ce: wane ya je hajji ma'ana wane ya rabauta.
وقال الامام الصادق 7: «هو شعبة من رضوانه ، وطريق يؤدّي إلى غفرانه منصوب على إستواء الكمال ومجتمع العظمة والجلال [88]
Imam
sadiq(as) ya ce: hajji wani yankin daga yardarm Allah, kuma hanya ce da za ta kai
ka ga gafararsa da aka kafa ta kan daidaitar kamala da matattarar girma.
Idan ya wajaba kan alhaji da hajiya da su yanka abin hadaya a mina ranar idi, to lalle bayansu akwai wani babban yanka da ake buqatar su yi shi ne yanka rai mai yawan umarni da mummuna, cikin dukkanin ayyuka daga ayyukan hajji wannan ishara da luxufi da ladubban ma'anawiya na yin tajalli, lalle shi hajji tsanin ne da ake hawa da mi'iraji zuwa ga duniyar malakut da jabarut da lahutu.
( وَأَتِمُّواْ الْحَجَّ وَالْعُمْرَةَ لِلّهِ فَإِنْ أُحْصِرْتُمْ فَمَا اسْتَيْسَرَ مِنَ الْهَدْيِ وَلاَ تَحْلِقُواْ رُؤُوسَكُمْ حَتَّى يَبْلُغَ الْهَدْيُ مَحِلَّهُ فَمَن كَانَ مِنكُم مَّرِيضآ أَوْ بِهِ أَذًى مِّن رَّأْسِهِ فَفِدْيَةٌ مِّن صِيَامٍ أَوْ صَدَقَةٍ أَوْ نُسُکٍ فَإِذَا أَمِنتُمْ فَمَن تَمَتَّعَ بِالْعُمْرَةِ إِلَى الْحَجِّ فَمَا اسْتَيْسَرَ مِنَ الْهَدْيِ فَمَن لَّمْ يَجِدْ فَصِيَامُ ثَلاثَةِ أَيَّامٍ فِي الْحَجِّ وَسَبْعَةٍ إِذَا رَجَعْتُمْ تِلْکَ عَشَرَةٌ كَامِلَةٌ ذَلِکَ لِمَن لَّمْ يَكُنْ أَهْلُهُ حَاضِرِي الْمَسْجِدِ الْحَرَامِ وَاتَّقُواْ اللّهَ وَاعْلَمُواْ أَنَّ اللّهَ شَدِيدُ الْعِقَابِ[89]
Ku cika hajji da umara don Allah, kuma idfan a ka kange to kuyi hadaya da abin da ya samu, ka da ku aske gashin kawukanku har sai hadaya ta isa mahalinta, duk wanda ya kasance mara lafiya cikinku ko kuma ma'aboci wani ciwo a kansa to ya bada fidiya daga azumi ko sadaka ko kuma yanka, idan ku ka samu aminci to dukkanin wanda ya ji daxi da umara zuwa ga hajji sai ya bada hadaya daga abin da ya sauqaqa, duk wanda bai samu daman hakan ba to yay i azumin kwanaki uku a hajji, ko kuma kwanaki bakwai idan kuka dawo gida daga hajji, waxancan goma ne cikakku, wancan ya nag a wanda iyalinsa bas u kasance mazauna masallacin harami ba, kuji tsoron Allah ku kwana da sani cewa Allah ya na tsananin uquba.
NAU'O'IN HAJJI DA BA'ARIN SIRRI CIKIN
MUQADDIMARSA
A fili ya ke kamar yadda fiqihun muslunci ya karakasa hajji zuwa kashi uku:
1-Hajjin ifradi: ya na wajaba kan mazauna garin makka da gefenta da daura da ita har ya zuwa mil 48 haka ga wanda bai samu dacewa da uamarar tamattu'I cikin lokacinta ko kuma wani abu hana shi kammala hajjin tamattu'I, a irin wannan hali sai ya canja daga hajjin tamattu'I zuwa hajjin ifradi.
2- hajjin qirani: shi ma ya na wajaba kan mutanen makka za su riqi abin hadaya daga miqatinsu.
3- hajiin tamattu'i: ya nag a waxanda suka nesanci makka da mil 48 shi ne mafi falala daga nau'o'in hajji tarihinsa na komawa ga hajjin manzon Allah(saw) wanda aka fi sani da hajjin bankwana wanda ya yi shi qasrhen rayuwarsa mai daraja bayan saukar faxin Allah maxaukaki:
(وَأَذِّن فِي آلنَّاسِ بِالْحَجِّ يَأْتُوکَ رِجَالاً وَعَلَى كُلِّ ضَامِرٍ يَأْتِينَ مِن كُلِّ فَجٍّ عَمِيقٍ )[90]
Ka yi yekuwa cikin mutane don ibadar hajji za su zo maka suna masu tafiya da qafafunsu kan dukkanin xankwararren doki za su daga dukkanin rango mai nisa.
Sai annabi ya fito cikin taron musulmi ya yi huxuba cikin marwa sai yah axe yatsunsa biyu ya ce: na shigar da umara cikin hajji kamar misalin yatsun hannuna sashensu ikin sashe
فخرج النبيّ في معشر المسلمين ... فخطب النبيّ
الأعظم 6 في المروة ، وأشبک بين أصابعه وقال : «دخلت العمرة في الحجّ كأصابع يدي بعضها في بعض[91]
Sai wani mutum daga cikin mutanen ya ce: yanzu zamu fito aikin hajji alhalin gashin kawukanmu na xigar daruwa? Sai manzon Allah ya ce masa kai ba zaka taba imani da ita bayanta har abada. Shi wannan mai faxin haka shi ne wanda ya haramta mutu'atul hajji bayan wafatin manzon Allah lokacin da ya samu halifanci bayan abubakar.
الكافي بسنده عن معاوية بن عمّار قال : سمعت أبا عبدالله 7 يقول : «الحجّ ثلاثة أصناف : حجّ مفرد وقران وتمتّع بالعمرة إلى الحجّ ، وبها أمر رسول الله6 والفضل فيها، ولا نأمر الناس إلّا بها».
Daga littafin alkafi mai daraja da isnadinsa daga mu'awiyatu xan ammar ya ce: na ji baban Abdullah(as) ya na cewa: lalle hajji sinfi uku ne: hajjin ifradi da hajjin qirani da hajjin da ake umara cikinsa gabanin tsayuwar Arafat da shi ne manzon Allah(saw) ya yi umarni sannan dukkanin falala na cikin shi, ba ma umratar mutane face shi.
وقال 7: «التمتّع أفضل الحجّ وبه نزل القرآن وجرت السنّة ».
Wani wajen kuma ya ce: hajjin tamattu'I shi ne mafi falalar shi qur'ani ya saukar sunna ta tafi kai.
وعن صفوان قال : قلت لأبي عبدالله 7 ان بعض الناس يقول جرد الحجّ وبعض الناس يقول أقرن وسُق ، وبعض الناس يقول تمتّع بالعمرة إلى الحجّ ، فقال : «لو حججت ألف عام لم أقرنها إلّا متمتّعاً».[92]
An karbo daga safwanu ya ce: na cewa baban Abdullah lalle ba'arin mutane suna cewa a kwabe hajji ayi ta zalla, wasu kuma na cewa ayi hajjin qirani a kora hadaya, wasu kuma nacewa ayi tamattu'I da umara ya zuwa hajji(hajjin tamattu'i), sai imam ya ce: da zanyi hajji sau dubu da bazan yi qirani ba, hajjin tamattu'I kaxai zanyi.
وقال الامام الرضا 7 في سرّ حجّ التمتّع : «إنّما اُمروا بالتمتّع إلى الحجّ لأنّه تخفيف من ربّكم ورحمة ، لا يسلم الناس في إحرامهم ولا يطول ذلک عليهم ، فيدخل عليهم الفساد، وأن يكون الحجّ والعمرة واجبين جميعاً، فلا تعطّل العمرة ، وتبطل ولا يكون الحجّ مفرداً من العمرة ، ويكون بينهما فصل وتميز، وأن لا يكون الطواف بالبيت محظوراً، لأن المحرم إذا طاف بالبيت أحلّ إلّا لعلّة ، فلو لا التمتّع لم يكن للحاج أن يطوف ، لأنّه إن طاف أحلّ وأفسد إحرامه[93]
Imam rida(as) cikin sirrin hajjin tamattu'I yana cewa: kaxai dai an umarce su da hajjin tamattu'I saboda shi sauqi ne da rahama daga ubangijinku, bai sallama mutane cikin ihraminsu bai tsawaitawa kansu ta yadda barna za ta shiga kansu, da kuma kasantuwar hajji da umara wajiabai baki xayansu, ka da ka bata umararka ya gurbata, ka da hajji ya kasance hajji ba tare da umara ba sai ya kasance tsakanin umara da hajji akwai wata fasila da banbanta, don gudun ka da xawafi ya kasance abin hani, saboda wanda ya xaura harami idan ya yi xawafi zai warware haraminsa ne sai dai idan wata larura ta bijiro, ba da bon tamattu'I ba da mai hajji ba zai yi xawafi ba, saboda idan yay i xawafi y agama sannan kuma harami ya baci.
Sannan dole ayi cikkaken shiri da tanadi don hajji da guzuri da abin hawa da makamantansu daga share fage da shimfixa zuwa ga hajji daga cikin akwai passport(katin izinin shiga da fice)
ثمّ لابدّ من التهيّأ الكامل
للحج بالزاد والراحلة وغيرهما من مقدّمات الحجّ
قال الامام الصادق 7 لعيسى بن منصور: «يا عيسى اني اُحبُّ أن يراک الله عزّوجلّ فيما بين الحجّ إلى الحجّ وأن تتهيّأ للحجّ » . [94]
Imam sadiq(as) ya cewa isa xan Mansur: ya isa lalle ni ina qaunar ace Allah ya ganka cikin tsakankanin hajji zuwa hajji da kuma ace kayi don hajji.
Daga wannan mafara ma daraja hadisi ya zo :
عن الامام الصادق 7: «لو أنّ أحدكم اذا ربح الربح أخذ منه شيء فعزله فقال : هذا للحجّ ، وإذا ربح أخذ منه وقال هذا للحجّ ، جاء أبّان الحجّ وقد إجتمعت له نفقة ، عزم الله فخرج ، ولكن أحدكم يربح الربح فينفقه فاذا جاء ابّان الحجّ ـ أي وقت الحجّ ـ أراد أن يخرج ذلک من رأس ماله فيشق عليه » . [95]
An karbo daga iama sadiq(as) da ace xayanku zai samu wata rida sai ya xibi wani kaso daga cikin ribar ya ce wannan kasaon na aikin hajji ne, haka ya qara samun wata ribar ya qara xiban wani kaso ya aje don zuwa hajji, lalle lokacin aikin hajji zai zo masa yana da halin abin da zai je, zai shirya ya xaura niyyar zuwa hajji domin Allah ya fita, sai dai cewa xayanku a cin riba sai ya ciayar da ribar baki xaya ba tare da ya aje wani abu daga ciki ba, ya yin da lokacin zuwa hajji ya gabato sai ya yi yunqurin cire abin da zai je hajji daga jarinsa uwar kuxin da ya ke juyawa sai hakan tsananata gareshi ya gaza fitarwa.
Duk wanda ya ke da tunanin zuwa hajji zai tanadi guzuri da abin da zai kaishi hajjin tsawon shekara lalle babu shakka da kokwanto zaka sajmme shi yana rayuwa cikin ma'anawiyya da mahajjaci ke rayuwa cikinta lokacin aikin hajji, Allah zai sanya albarka cikin rayuwarsa da dukiyarsa.
Daga cikin mabayyanin al'amari lalle shi karbabben hajji na kasancewa daga kuxaxxen halal.
Idan wani mutum ya tsiwirwiri kuxaxen haramun ya tara su ya je hajji, idan ya ce: labbaika sai mala'iku su amsa masa da la labbaika wala sa'adaika ba a amsa kiranka ba, amma idan ya kasance daga kuxaxen halal idan ya ce labbaika sai a amsa masa da labbaika wa sa'adaika.
(إذا اكتسب الرجل مالاً من غير حلّه ثمّ حجّ ولبّى نودي لا لبّيک ولا سعديک ، وإن كان من حلّه فلبّى نودي لبّيک وسعديک( [96]
Lalle Allah matsarkaki ya na karbar aiki daga masu taqawa, lalle shi kyakkyawan aiki na daga kyakkayawan mutum, duk wanda kuxaxensa su kasance daga halal lalle hajjinsa ya ksance tsaftatacce karbabbe idan kuma sabanin haka ne to hajjinsa zai kasance wurgagge ya kuma wayi gari ukuba ga ma'abocinsa.
Sannan abin da yake farilla tun farko shi ne mutum ya tanadi guzuri daga mafi kyawun abin da ke gareshi daga guzuri.
كان الامام علي بن الحسين 7 اذا سافر إلى مكّة للحجّ أو العمرة تزوّد من أطيب الزاد من اللوز والسكّر والسويق والحمّص والُمحلّى[97]
Imam aliyu ibn husaini(as) ya kasance idan zai tafiya zuwa makka domino hajji da umara sai ya tanadi guzuri daga mafi kyawun guzuri daga gyaxar luz da sukari da sawiqu da himsi(chickpeas) da …….
Kai hatta mutumin da yi yi guzuri cikin guzuri ba a qidaya shi daga matafiyi
قال رسول الله 6: «ما من نفقة أحبّ إلى الله عزّوجلّ من نفقة قصدٍ ـأي الانفاق باقتصادـ، ويبغض الإسراف إلّا في الحجّ والعمرة.[98]
Manzon Allah(saw) ya ce: babu wata ciyarwa da tafi soyuwa ga Allah daga da matsakaiciyar ciyarwa, lalle Allah a qin wuce gona da iri face ckin hajji da umara.
Abin da ya fi zama farilla shi ne ciyarwar ta kasance mafi kyawunta da falala da tsaftata cikin tafarkin Allah kamar misalign hajji da umara da jihadi da makamantansu…..
[1] Mujadala:11
[2] Ankabut:45
[3] Bakara:183
[4] Littafin farisanci mai suna fish amadi bar farhangi asrar wa ma'arifi hajji:17
[5] Ilalul shara'I:ju 1 sh 8
[6] Daha:114
[7] Ma'ida:32
[8] Baqara:183
[9] Waqi'a:79
[10] A'araf:201
[11] Ma'ida:27
[12] Hakika na kawo bayani kan haka fila-filla cikin risala(falsafatu hayat wa sirril kalika) wan an buga cikin mausu'ar littafan mu mai suna(risalatul islamiya) mujalladi 10
[13] Azzariyat:56
[14] Ibrahim:8
[15] ALI IMRANA:97
[16] Altakasur:5-7
[17] Alhijir:99
[18] Isra'i:72
[19] Ma'ida:27
[20] Fussilat:35
[21] Bihar anwar: juz 6 sh 234
[22] Kuraish:3
[23] Azzariyat:50
[24] Bakara:197
[25] Hajji:27
[26] Bakara:197
[27] Fajar:29-30
[28] Jumu'atu:2
[29] Bakara:197
[30] Bakara:127
[31] Fatahu:29
[32] Jawahirul kalam:farkon kitabul hajji
[33] Alu imrana:96
[34] Alu imrana:96
[35] Hajji:26
[36] Hajji:27
[37] Ma'ida:97
[38] Ali imrana:96
[39] Baqara:125
[40] Bakara:126
[41] Bakara:126
[42] Ankabut:67
[43] Tini:3
[44] Ibrahim:37
[45] Hajji:37
[46] Ma'ida:2
[47] Bakara:126
[48] Hajji:25
[49] Alu imrana:97
[50] Hajji:28
[51] Hajji:36
[52] Hajji:28
[53] Hajji:37
[54] Alu imrana:97
[55] Bakara:197
[56] Bakara:158
[57] Bakara:197
[58] An'am:94
[59] Alkiya:22
[60] Hijri:46
[61] Alu imrana:97
[62] Furkan:43
[63] Hajji:34
[64] Nisa'i:125
[65] Alu imrana:67
[66] Bakara:132
[67] Misbahul shar'ia:142
[68] Hajji:28
[69] Ilalul shara'i:404
[70] Mustadrakul wasa'il: juz 10 sh167
[71] Bakara:197
[72]Hajji:37
[73] Bakara:200
[74] Bakara:203
[75] Saba'i:46
[76] Ina kana bukatar bayani dalla-dalla kana iya koma littafin farhang nameh asrar wa ma'arif hajji, wallafar ma'iakatar mu'awanatul ruhaniyun iran
[77] Misbahul shari'a
[78] Wasa'ilul shi'a: juz 8 sh 5
[79] Isra'iu:44
[80] Hajji:27
[81] Bihar anwar:juz 99 sh 8
[82] Tuhuful ukul:133
[83] Nahjul balaga: kuduba 1
[84] Ilalul shara'i:404
[85] Adabul duniya waddini:172
[86] Munajat sha'abaniya-mafatihul jinan
[87] Misbahul shari'a:74
[88] Alkafi:juz 4 sh 197
[89] Bakara:196
[90] Hajji:27
[91] Wasa'ilul shi'a:juz 8 sh 151
[92] Alkafi:juz 4 sh 292
[93] Wasa'ilul shi'a:11 sh 232
[94] Alkafi: juz 4 sh 281
[95] Alkafi: 4 sh 280
[96] Alfakihu: juz 2 sh 317
[97] Alfakihu: juz 3 sh 382
[98] Alfakihu: adireshin da ya gabata.