b MUKADDIMA GABATARWA - HAKURI DA FUSHI
فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها

MUKADDIMA GABATARWA

 

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Dukkanin godiya ta tabbata ga Allah mai yawan hakuri da juriya da karamci, tsira da aminci su kara ta tabbata kan mafi daukakar halittun Allah wanda aka aiko domin cika kyawawan dabi’u shi ne Muhammad amintacce da iyalan sa jagorori halittu baki daya.

Ya ubangiji ka buda bakina da fadin shiriya ka kimsa mini tsoran ka, bayan haka: hakika Allah madaukaki cikin littafin sa mai daraka yana cewa:

{وَالْكَاظِمِينَ الْغَيْظَ وَالْعَافِينَ عَنِ النَّاسِ وَاللَّهُ يُحِبُّ الْمُحْسِنِينَ}[1].

Kuma da masu danne fushi da masu afuwa ga mutane Allah yana son masu kyautatawa.[1]

A wani wurin yana cewa:

{وَإِذَا مَا غَضِبُوا هُمْ يَغْفِرُونَ}[2] .

Idan suka fusata sai su dinga yin gafara.[2]

Ka sani Allah ya karfafeka cikin gidan duniya da lahira shi fa fushi yana daga rundunar jahilci wanda aka halicce shi daga duhu, wadanda asalinsu karshen sa wuta, sannan kishiyar fushi shi ne hakuri d adanne fushi, lallai shi hakuri yana daga rundunar hankali wanda Allah ya halicce shi daga haskensa_ kamar yanda ya zo cikin hadisai masu daraja da suka yi bayani yanda aka halicce hankali da jahilci kamar yanda ya zo cikin littafin Alkafi cikin babin ilimi da jahilci kana iya komawa can_ shi asalin fushi bakin wuta mai ruruwa da aka tsono su daga wutar Allah rurarra wacce take huda kan zukata, tana ruruwa cikin zuciya domin ta kone ta ta rusa musu nutsuwa da kwanciyar hankali, idan zuciya ta samu nutsuwa da ambaton Allah, lallai shi yana girgiza ya rasa nutsuwarsa da lafiyarsa da fushi, lallai shi fushi yana rurarren garwashinsa yana likimo  karkashin toka, girman kai da jiji da kai da hassada na fito da shi daga zuciyar dukkanin Jabberi mai tsaurin kai, shi fushi yana komawa asalin sa ya zuwa wutar Shaidan  

{ خَلَقْتَنِي مِنْ نَارٍ وَخَلَقْتَهُ مِنْ طِينٍ }[3] .

ka halicce ni daga wuta shi kuma ka halicce shi da yunbu tabo.[3]

daga sha’anin tabo shi ne nutsuwa da saukaka, daga cikin sha’anin wuta ruruwa da babbakuwa da motsi da yake rugu-rugu da rusawa da girgizawa da babbaka, sannan natijar fushi shi ne kai mutum zuwa ga halaka da rushewa da ragargaza duniya da aikata abin kunya da abin kyama.

Sannan Magana kan fushi tana da rassa sai dai cewa cikin wannan takaitacciayr Risala ta cikin gaggawa zamu kawo wasu ba’arin bahasosi da suka ta’allaka da fushi domin mu kasance kan basira cikin al’amarin mu, zamu magan ce kawukanmu daga saurar fushi mai halakarwa mai rusau, mai yafi yawa daga mutanen da suka kamu da wannan mummunan ciwo na fushi a wannan zamani.

Magana ta farko cikin zargin fushi a hankalce da nakalce daga cikin littafin Allah mai girma da hadisai masu daraja da aka rawaito su daga Manzon Allah (s.a.w) da iyalansa tsarkaka da abin da masana hikima da malamai cikin zargin jahilci.

Magana ta biyu: zamu kawo wasu abubuwa mu yi bayanin hakikar fushi da mahiyarsu bayan babbakar sa da habbakar sa.

Na uku: zamu kawo sabubba da dalilai da suke motsa fushi.

Na hudu: zamu kawo bayani kan abin da yake magnace matsarl fushi, shin za a iya kawar da asalinsa ta hanyar tiraina zuciya, ka kuwa ba zai yiwu ba?

Na biyar: zamu kawo bayanin falalar danne fushi da hakuri da makamancin haka daga abubuwan da suka ta’allaka da fushi da danne shi, da jerantawa ta mandiki cikin zuba maudu’ai da tsara su, zamu kawo su cikin mukamai, daga wurin Allah muke neman taufiki da dacewa shi ne masanin manufa da niyya.

Dukkanin godiya ta tabbata ga Allah ubangijin talikai tsira da aminci su kara tabbata ga shugabanmu cikamakin Annabawa da manzanni Muhammad da iyalansa zababbu tsarkakakku.

[1] Alu Imran:134

[2] Shura:37

[3] A’araf:12