b FUSHI MABUDIN DUKKANIN SHARRI - HAKURI DA FUSHI
فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها

FUSHI MABUDIN DUKKANIN SHARRI

 

2-hakika wani mutumi ya nemi Manzon Allah (s.a.w) yayi masa wasiyya sai ya ce masa: kada kayi fushi, ya ce sai na yi tunani lokacin da Manzon Allah (s.a.w) ya fadi abind aya fada: fushi na tattaro dukkanin sharri.

3- an tambaye shi menene zai nesanta mutum daga fushin Allah, sai ya ce; kada ka yi fushi.

4- Ibn Mas’ud ya ce: Annabi (s.a.w) ya ce: wanene ku ke kirga shi jarumi cikin ku sai suka ce wanda mazaje basa kayar da shi, sai ya ce: a’ a jarumi shi ne wanda yake mallakar kan sa lokacin da yake cikin halin fushi.

5- Annabi (s.a.w) ya ce: dukkanin wanda ya iya kame fsuhinsa Allah zai suturta tsaraicinsa.

6-sarkin muminai (a.s) ya ce: fushi yana motsa kiyayya, shi rurarriyar wuta ce dukkanin wanda ya iya danne shi ya kashe wannan wuta, duk wanda ya sakar masa ragama shi ne na farko wanda zai fara konewa cikin sa.

7- an karbo daga gare shi (a.s) shi fushi sharri ne wanda idan ka biye masa zai dammaraka, na haneka da biyewa fushi lallai shi shu’umanci ne daga Shaidan.

8-daga gare shi (a.s) fushi abin hawan Shaidan ne, shi fushi wutar cikin zuciya ne, ku gujewa fushi lallai shi fushi babbar rundunar Iblis ne.

9- daga gare shi (a.s): fushi yana halakar da ma’abocinsa yana kuma bayyanar da aibobinsa, shi fushi wani nau’ine daga hauka, na haneka da yin fushi domin shi fushi farkonsa hauka karshensa nadama, shi rurur fushi nau’I ne na hauka; saboda mai yinsa yana nadama, dain bai yi nadama ba to lallai haukansa zai kankama.

Shi fushi yana gurbata ma’abota hankula yana nesanta daidai, mafi samun ikon cikin mutane kan daidai shi ne wanda baya yin fushi da wanda fushinsa bai yi galaba kan hankalinsa ba.

10-an karbo daga gare shi (a.s) tirr da abokin tarayya fushi, yana bayyanar da aibobi, yana kusanto da sharri, yana nesanta alheri.

11-daga gare shi (a.s) ku guji saurar fushi, ku tanadar masa abin da zaku yake shi daga danne fushi da hakuri.

12- daga gare shi (a.s) ukubar masu yawan fushi da hassada da gaba tana fara da kawukansu.

13- daga gare shi (a.s) daga cikin dabi’ar jahili mai yawan jahilci gaggawar fushi cikin kowannce hali.

14-daga gare shi (a.s) izzar fushi bata mikuwa da bada hakuri, ba’arinsu sunce: kun kauracewa fushi lallai shi fushi yana mayar da kai zuwa ga kaskancin neman uzuriu da bada hakuri.

15- an karbo daga Imam Sadik (a.s) fushi mabudin kowanne sharri ne.

Wannan kadan daga tarin riwayoyi da suka yi bayani kan hatsarin fushi da kuma zarginsa kan rayuar mutum cikin dukkanikn sasanninta daga daidaiku da jama’a da ilimi da aiki, da rayuwa da makoma da waninsu.

Bai buya ba cewa shi mumini da farko yana dabi’amtuwa da dabi’un Manzon Allah da waliyansa, kuma daga cikin dabi'un Allah kyawawa baki dayansu da girma da kamala, kuma shi muminai yana da jinkirin fushi yana kuma da saurin yarda,

 Na biyu: daga jahilci akwai fushi, kuma daga cikin dabi’ar jahili akwai saurin yin fushi cikin kowanne hali, shi ko mumini yana cikin hanyar ilimi kuma duk wanda iliminsa da sanin Allah da ranar lahira su ka karu ya kuma yi Imani da falaloli da kyawawan dabi’u da dayantacciyar halitta da kasantuwa da lafiyayyan hankali, da neman sanin abin da ya zo daga wahayi saukakke da bayyanannen batu daga sunna mai daraja da hanyar A’imma tsarkaka lallai ba za ka same shi yana yin fushi ba sai don Allah matsarkaki, ya karanta matuka ka same shi yana yin fushi domin kansa, idan ma yayi fushin domin kansa to cikin gaggawa zai dawo cikin hayyacinsa ya canja fushin zuwa hakuri da juriya, su muminai idan wani shafa ya shafesu daga shaidani sai su ambaci Allah suyi wuridi, sai ka samu sun Ankara daga kuren da suka tsinci kansu ciki daga fushi da jahilci da nadama da nesantar Allah da mutane da aljanna, kamar yanda shi mai hakuri yana kusa-kusa daga Allah da mutane da aljanna, kamar yanda yake cikin kyauta da sauran kyawawan faloli da kyawawan dabi’u.

Domin Karin bayani kan munin fushi da kari kan bayanin da ya gabata zamu kawo jumla daga riwayoyi masu daraja cikin wannan babi.

قال رجل للنبي’ علّمني، قال: إذهب ولا تغضب، فقال الرجل : قد اكتفيت بذلك، فمضى إلى أهله، فإذا بين قومه حرب، قد قاموا صفوفاً ولبسوا السلاح، فما رأى ذلك لبس سلاحه، ثم قام معهم, ثم تذكر قول رسول الله’، (لا تغضب) فرمى السلاح، ثم جاء يمشي إلى القوم الذين هم عدو قومه، فقال: يا هؤلاء ما كانت لكم من جراحة وقتل، أو ضرب ليس فيه أثر فعليّ في مالي أنا أوفيكموه، فقال القوم: فما كان لكم فهو لكم، نحن أولى بذلك منكم، قال: فاصطلح القوم وذهب الغضب.

16-wani mutum ya cewa Annabi (s.a.w) ka sanar dani, sai ya ce:  kad aka yi fushi, sai mutumin ya ce: na wadatuwa da wannan, sai mutumin ya tafi wurin iyalinsa, sai ya samu yaki ya kaure tsakankanin mutanensa, sun yi sahu-sahu sun sanya kayan yaki, yayinda ya ga haka shima sai ya rataya makaminsa ya mike tare da su, sai kwatsan ya tuna maganar da Manzon Allah (s.a.w) ya gaya masa (kada kayi fushi) sai yayi wurgi da wannan makami, sannan ya tafi zuwa wurin abokan fadan mutanensa ya ce musu: yaku wadannan bai kamata ku yiwa kanku rauni da kisa ba ko sara ba da bai da wani tasiri cikin dukiyata ko cikinku, sai suka ceduk abin da ya kasance gareku na ku ne, mune mafi cancantuwa da shi daga gareku, ya ce sai sukayi sulhu fushi ya tafi.

17- cikin Al’asar: daga Zul Karnaini wata rana ya hadu da Mala’ika daga Mala’iku sai ya ce: ka sanar da ni wani ilimi da zan karu da Imani da yakini da shi, sai ya ce: kada kayi fushi lallai Shaidan yafi samun ikon kan mutum lokacin da yake cikin fushi, ka yi raddin fushi da danne shi  da lausasa shi, na haneka da yin gaggawa lallai kai idan kayi gaggawa zaka kuskurewa rabonka, ka kasance mai sauki kai mai taushi ga naku sa da na nesa, kada ka kasance Jabberi mai taurin kai

18- Kusaimatu ya ce: Shaidan yana cewa: ta yaya `dan Adam zai galaba kaina alhalin idan ya yard azan zo wurinsa har sai na kasance cikin zuciyarsa, idna yayi fushi zan tashi sama har sai na kasance a cikin kansa.

19-Mujahid yana cewa: Iblis ya ce: `dan Adam bai gajiyar dani, kuma har abada ba zai taba gajiyar dani ba cikin abubuwa uku: idan yayi maye ya bugu ya fita daga hayyacinsa sai mu kama akalar sa, mu juya shi yanda muka ga dama yayi aikin da muke so, idan ya fusata sai ya dinga fadin abind aba sani bay a dinga aikata abin da zai yi nadama kansa, mu sanya shi yana yin rowa da abin da yake hannunsa, mu snaya masa burin da abin da bai da iko kai.

20-an cewa Abdullah ibn Mubarak ka takaice mana kyawuntar dabi’u cikin kalma day arak, sai ya ce yin watsi da yin fushi.

21- wani Annabi daga Annabawa (a.s) ya fadawa wadanda suke tare da shi wane ne zai yi mini alkawarin cewa ba zai yi fushi ba sai ya kasance tare da ni cikin darajata, bayana ya kasance halifa na, sai wani saurayi daga cikinsu ya ce ni ne sai Annabi ya maimaita masa abin da ya fada da fari sai saurayin ya ce: ni ne zan cika wannan alkawari, yayin da ya mutu sai ya kasance cikin gidansa bayansa, shi ne Zul Kiflu an kira ye da wannan suna saboda ya dau alkawarin danne fushi ya kuma cika alkawari.

22- Manzon Allah (s.a.w) ya ce: fushi yana bata Imani kamar yanda kunu ke bata zuma.

23- shi fushi yana daga dattin Shaidan, Imam Bakir (a.s) yana cewa:

إنّ الرجل ليغضب قما يرضى أبداً حتى يدخل النار، فأيّما رجل غضب على قوم وهو قائم فيجلس من فوره ذلك، فإنّه سيذهب عنه رجز الشيطان، وأيّما رجل غضب على ذي رحم فليدن منه، فليمسّه فإن الرحم إذا مُسكتْ سكنت.

Mutum yana fusata ba zai taba yard aba har abada har sai ya shiga wuta, duk sanda wani mutum ya fusata kan mutane alhalin yana tsaye to take nanya zauna, lallai zai dattin Shaidan zai tafi ga barinsa, duk sanda wani mutum ya fusata kan danginsa to ya kusan ce shi ya shafe shi, dan’uwa idan aka rike shi yana tausasa.

24- وقال×: إنّ هذا الغضب جمرة من الشيطان توقد في جوف ابن آدم، وإن أحدكم إذا غضب أحمّرت عيناه وانتفخت أوداجه، ودخل الشيطان فيه، فإذا خاف أحدكم ذلك من نفسه، فليلزم الأرض، فإن رجز الشيطان يذهب عنه عند ذلك، ومن كفّ غضبه ستر الله عورته، ومن لم يملك غضبه لم يملك عقله. إنّ الرجل ليغضب فيقتل النفس التي حرّم الله، ويقذف المحصنة

24- Amincin Allah ya kara tabbata a gaershi ya ce: lallai wannan fushi wani garwashi ne daga Shaidan da yake ruruwa cikin cikin `dan Adam, lallai dayanku idna ya fusata idanunsa suna yin jajawur jijiyoyinsa su kumbura, Shaidan ya shige shi, idan dayanku ya jima kansa tsoran hakato ya lazimci kasa ya zauna, lallai dattin Shaidan yana tafiya daga gare shi yayin yin hakan, duk wanda ya damke fushinsa Allah zai suturta tsaraicinsam duk wanda bai mallaki fushinsa ba bai mallaki hankalinsa ba, lallai mutum yana fushi sai ya kashe rai wacce Allah ya hana kasheta, yayi kazafi ga mace katangaggiya.