b MAGAN CE MATSALAR FUSHI A ILIMAN CE DA - HAKURI DA FUSHI
فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها

MAGAN CE MATSALAR FUSHI A ILIMAN CE DA

 

Amma magani ga wanda ya jarrabtu da matsalar fushi mai tashi ya kuma fada cikin tarkon Shaidan da nafsu ammara, kuma yake son kubuta da magani lokacin da ya fusata, hakika malaman Aklak da rhi sun ambaci cewa magan ce shi ya kan kasancewa da maganin da aka saba da shin a batu da ilimi mai amfani da aiki na kwarai.

Bayani dangane da haka a takaice:

Amma a iliman ce to shi yana kasancewa da abubuwa guda shida: tunani, tsoratuwa, zantuwa, tunatuwa, jinkirtawa, magani, fahimtuwa.

Amma a aikace: akwai wasu ayyuka kebantattu kamar misalin shan ruwan sanyi, yin alwala, zama zaune idan ka kasance a tsaye, da dai makamantan haka, kamar yanda zai zo nan gaba.

Amma bayani filla-filla cikin haka:

Lamari na farko wato:tunani: shi ne cewa mutum yayi tunani cikin abin da ya zo cikin nassoshin addini daga ubangijinsa da manzonsa da wasiyyansa (a.s), daga ayoyi masu daraja da hadisai madaukaka, sannan abin da ya zo daga kissoshin Annabawa da wasiyyansu da masana hikima da malamai sailahai da manyan shugabanni da mutane masu daraja daga batun abind aya zo cikin danne fushinsu kan waninsu, haka daga afuwa da dauriya da daurewa cutarwa da kuma kau dakai da yafiya, da barin daukar fansa da huce haushi da yin hakuri kyau, mutum yayi kwadayi cikin neman wannan falala mai girma, ba wani abu bace face hakuri me ka sani dangane da hakuri, shi ne danne fushi da yin afuwa, lallai hakuri shi yafi daukakar matsayi daga danne fushi, hakuri ke hana mutum yunkurin daukar fansa da huce haush, sakamakon abind aya zo cikin sa daga lada mai girma da sakamako mai kyawu ga wanda yayi hakuri ya yafe ya danne fushinsa.

Me yafi kyawu daga abin da ya zo daga rayuwar Imam Zainul Abidin shugaban masu sujjada Aliyu bn Husaini (a.s) yayin da ya sanya baiwarsa ta zubo masa ruwa domin yayi shirin sallah sai butar ruwan ta fado daga hannunta ta ji masa ciwo sai ya daga kansa ya kalleta, sai tace: Allah yana cewa (da masu danne fushi) sai ya ce mata, na danne fushinam sai tace: Allah yana cewa: (masu afuwa ga mutane) ya ce: nayi miki afuwa, tace: (Allah yana son masu kyautatawa) ya ce je ki kin `yantu domin neman yardar Allah.

Ka sani lallai ya zo cikin hadisi mai daraja daga Imam Sadik (a.s) fadinsa: ku dabi’antu da dabi’un Allah- ma’ana siffofinsa madaukaka da kyawawan sunayensa, shi wani bayani ne daga tajallin sunaye da madaukakan siffofi cikin kamilin mutum mai kammaluwa, da ya kasance madubi mabayyanar sunayensa kyawawa da siffofinsa madaukaka, wannan shi ne mihwarin cikin talifina da darasussukana na ilimin Aklak da Irfan, lallai ni nayi Imani cewa manufar halittar mutum da hikima cikin rayuwarsa shi ne kammaluwa da kaiwa ga tsololuwar kamala, shi ne halifantuwa cikin sunayen Allah da tajallin Allah cikin sa, lallai rayayyen mutum da yayi Imani sa samuwar Allah ba dabbace mai Magana ba-kamar yanda yake a ilimin Mandik-aiko da manzanno da litattafai da bayanin ilimu da ma’arifa da fannoni, da ayyuka nagari baya bakin komai face don mutum ya tafi kan wannan matafiya ta ubangiji mara karshe ta har abadam babu tsimi babu dabara sai da Allah madaukaki mai girma.

Daga cikin kyawawan sunaye Allah akwai (Alhalimu) mai yawan hakuri, Allah yana son yaga siffofinsa suna tajalli cikin halittunsa, Allah tsaftatacce ne yana son mai tsafta da tsafta, shi mai hakuri ne yana son hakuri, lallai shi mai hakuri ne yana hakuri da ma’abocinsa.

Wannan shi ne mafara, hakika Allah ya yabi hakuri da danne fushi da afuwa da yafiya da kau da kai da gafara cikin littafinsa da sunnoni da shari’ar Annbawa da minhajin wasliyyansa, musammam ma cikin makarantar Ahlil-baiti amincin Allah ya kara tabbata a garesu.