b HAKURI DA DANNE FUSHI DA YIN AFUWA DAGA CIKIN KUR’ANI MAI GIRMA - HAKURI DA FUSHI
فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها

HAKURI DA DANNE FUSHI DA YIN AFUWA DAGA CIKIN KUR’ANI MAI GIRMA

 

 

Allah madaukakin sarki cikin littafinsa mai girma ya ce:

{اعْفُوا وَاصْفَحُوا حَتَّى يَأْتِيَ اللَّهُ بِأَمْرِهِ}

Ku yi afuwa ku kau da kai har sai Allah ya zo da umarninsa.[1]

{وَالْكَاظِمِينَ الْغَيْظَ وَالْعَافِينَ عَنِ النَّاسِ وَاللَّهُ يُحِبُّ الْمُحْسِنِينَ}

Da masu danne fushi da masu afuwa ga mutane Allah yana son masu kyautatawa.[2]

{فَاعْفُ عَنْهُمْ وَاصْفَحْ إِنَّ اللَّهَ يُحِبُّ الْمُحْسِنِينَ}

Kayi afuwa daga garesu ka kau da kai lallai Allah yana son masu kyautatawa.[3]

{خُذِ الْعَفْوَ وَأْمُرْ بِالْعُرْفِ وَأَعْرِضْ عَنِ الْجَاهِلِينَ}.

Kayi riki afuwa kayi umarni da kyakkyawa ka kauracewa jahilai.[4]

{فَاصْفَحِ الصَّفْحَ الْجَمِيلَ}

Ka kau da kai kau da kai mai kyawu.[5]

6- {ادْفَعْ بِالَّتِي هِيَ أَحْسَنُ السَّيِّئَةَ نَحْنُ أَعْلَمُ بِمَا يَصِفُونَ}

Ka tunkude da wacce tafi kyawunta mugunya mu ne mafi sani daga abin da suke siffantawa.[6]

Wacce tafi kyawu itace hakuri da afuwa.

 

{لْيَعْفُوا وَلْيَصْفَحُوا أَلا تُحِبُّونَ أَنْ يَغْفِرَ اللَّهُ لَكُمْ وَاللَّهُ غَفُورٌ رَحِيمٌ}

Su yi afuwa su kau da kai ashe bakwa son ace Allah ya gafarta muku Allah mai gafara da jin kai ne.[7]

{وَإِذَا خَاطَبَهُمُ الْجَاهِلُونَ قَالُوا سَلاماً}

Idan jahilai suka yi musu magana sai suce salamu Alaikum.[8]

{وَلا تَسْتَوِي الْحَسَنَةُ وَلا السَّيِّئَةُ ادْفَعْ بِالَّتِي هِيَ أَحْسَنُ فَإِذَا الَّذِي بَيْنَكَ وَبَيْنَهُ عَدَاوَةٌ كَأَنَّهُ وَلِيٌّ حَمِيمٌ*وَمَا يُلَقَّاهَا إِلَّا الَّذِينَ صَبَرُوا وَمَا يُلَقَّاهَا إِلَّا ذُو حَظٍّ عَظِيمٍ}

Mummuna da kyakkyawa ba zasu taba daidaita ba ka tunkude da wacce tafi kyawu sai ka ga wanda kuke gaba da kiyayya ya zama kamar misalin masoyi mai tace soyayya* babu mai samun haka face wadanda suka yi hakuri babu mai samun haka face mai babban rabo.[9]

{وَإِذَا مَا غَضِبُوا هُمْ يَغْفِرُونَ}.

Idan suka fusata sai ka gansu suna fagartawa.[10]

{فَاصْفَحْ عَنْهُمْ وَقُلْ سَلامٌ فَسَوْفَ يَعْلَمُونَ}.

Ka kau da kai daga barinsu kace salamu alaikum da sannu za su sani.[11]

{وَاصْبِرْ عَلَى مَا يَقُولُونَ وَاهْجُرْهُمْ هَجْراً جَمِيلاً}.

Ka yi hakuri kan abin da suke fad aka kauracewa musu kaurace mai kyawu.[12]

Wannan sune wani adadi daga ayoyin kur'ani mai girma da suke nassanta girmamar hakuri, lallai yana daga wasiccin Allah da Annabawa da manzanni, da shiriyarsu ne ake shiriya, lallai kuna abin da kwaikwayo mai kyawu cikin Manzon Allah (s.a.w), wannan nasiha ce ga muminai mazansu da matans, musammam ma ma'abota ilimi da daliban Hauzozi da mazajen gobe jagororin al'umma da ya zuwa gabobi muslunci da bakin kogin azurta da alheri, ya zuwa ga aljannar Firdausi, cikin matsugunin gaskiya wurin Sarki mai ikon yi, lallai su malamai sune magada Annabawa, suna fara tarbiyantar da kawukansu da farko da tsarkake zukatansu da dabi'antuwa da dabi'un Allah da Manzansa, sannan tarbiyantar da mutane da koyar da su littafi da hikima.

Me yafi kyawu daga hakuri su wanene suka fi kyawunta daga masu hakuri, lallai shi hakuri abokin ilimi ne, babu alheri cikin wanda bashi da hakuri, kada ko dinga fusata da zababbaka, idan kuka fusata ku danne fushinku, ku yi afuwa ku kau da kai daga barin mutane, lallai hakan yana daga ayoyi da alamomin ihsani da yin alheri zuwa garesu, mafi alherin muatne shi ne wand aya amfanar da su, lallai Allah yana son masu kyautatawa, Yusuf Siddik (a.s) ya kasance daga cikinsu, (lallai mu muna ganinka daga cikin masu kyautatawa, ka riki afuwa kayi umarni da kyakkyawa, idan jahili ya tare ka da cutarwa su dama mutane makiyan abin da basu sani ba ne to ka kau da kai daga gare shi da kau da kai mai kyawu, ba tare da kai ka kona masa rai ka bakanta masa, ka tunkude da wacce tafi kyawu, ma'ana da hakuri da danne fushi, , ashe baka son Allah yayi maka gafara, ka kubuta daga fushinsa, lallai yanda al'amarin yake shi ne duk wanda bai fushi da mutane ba shima Allah ba zai fushi kansa, idan jahili yayi maka magana kace masa salamu alaikum, ma'ana ni daga gareni ba zakat aba jin abin da zai cuta maka ba, lallai ni aminci ne gareka domin ni nasan cewa kai jahili ne kuma shi jahilci ciwo ne, kuma wajibi a lallaba mara lafiya, kamar yanda na san cewa kyakkyawa ba zata taba daidaita da mummuna ba, saboda haka zan yi mu'amala da kai da dukkanin tausasawa da ihsani da hakuri da danne fushi, Allah ne ya so ya canja kiyayyarka wacce ta kasance sakamakon jahilci ya zuwa ka kasance aboki na  mai tace soyayya mai gasgatawa da cikawa cikin abokantakarsa, sai ka canja jahilci zuwa ga ilimi, ka sauya yanke zumunci da cikawa, duhu da haske, karya da gaskiya, cutawa da aminci, misalin wannan babu mai samun sa face wanda ya kasance mai hakuri da dauriya, babu mai samun sa face mai babban rab, zai rabauta da azurta cikin duniya da lahira, wannan ya faru sakamakon gafara da afuwa da hakuri daga wanda ya fusata shi, shin yanzu bayan wadannan madaukakan mukamai mai fusata bai danne fusatarsa, kok kuma mahakurci baya yin hakuri kan jahilcinsa ko kuma kan wanda yayi masa wauta da ta'addanci?!  

Yaku abokai masu daraja, `ya`yana masu karamci, ku taho tare da ni mu shiga dausayi hadisai masu daraja, lallai su litattafai lambunan malamai ne_ da kalaman Imaman mu (a.s) mu ya kiwo mu yi farin ciki mu dibi zakakan kayan marmari, mu karanta mu sauraro ya zuwa jumlar hadisai  da suka daga Manzon Allah shugaban kyawawan dabi'u (s.a.w) da iyalan gidansa tsarkaka (a.s) cikin falalar danne fushi da kuma yin hakuri, domin mu karu cikin shauki ya zuwa mu siffanta da wadannan siffofi godaddu maus albarka cikin duniya da lahira, gabanin shiga cikin bahasi da maudu'i, ina son yin ishara zuwa ga wata gaba mai muhimmanci, da ta ke gangarawa cikin baki dayan siffofin kyawawa, daga nan ne zaka san banbanci tsakanin danne fushi da yin hakuri. 



[1]-Bakara:109

[2]-Alu Imrana:134

[3]-Ma'ida:13

[4]-A'raf:199

[5]-Hijri:86

[6] Muminun:96

[7]-Nur:22

[8]-Furkan:65

[9] Fussilat:34-35.

[10]-Shura:37.

[11]-Zukruf:89.

[12]-Almuzammil:12.