b MUKAMI NA BAKWAI CIKIN DANNE FUSHI - HAKURI DA FUSHI
فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها

MUKAMI NA BAKWAI CIKIN DANNE FUSHI

 


falalar danne fushi daga hadisai masu daraja:

1- قال رسول الله:من كف غضبه كف الله عنه عذابه , ومن إعتذر الى ربه قبل عذره , ومن خزن لسانه ستر الله عورته.

Manzon Allah (s.a.w) ya ce: duk wanda ya kame fushinsa Allah zai kame daga azabtar da shi, duk wanda ya nemi uzuri daga ubangijinsa gabanin yi masa uzuri, da wanda ya taskace harshensa Allah zai suturce tsaraicinsa

2- وقال ’:>أشدّكم من ملك نفسه عند الغضب ,وأحلمكم من عفا عند القدرة.

Amincin Allah ya tabbata a greshi ya ce: jarumin cikinku shi ne wanda ya mallaki zuciyarsa yayinda ya fusata, mafi hakurinku shie wanda yayi afuwa lokacin da yake da iko kan daukar mataki.

3- قال: من كظم غيظاً ولو شاء ان يمضيه أمضاه, ملأ الله قلبه رضاً.  وفي رواية اخرى : أمناً وإيماناً

Amincin Allah ya kara tabbata a gare shi ya ce: duk wanda ya danne fushinsa wanda da ya so zartar da shi da ya zartar da shi, Allah zai cika zuciyarsa da yarda, a wata riwayar zai cika ta da imani da aminci.

4- وعنه : ما جرع عبد جرعة أعظم أجراً من جرعة غيظ كظمها ابتغاء وجه الله, وفي خبر : وما كظمها عبد الا ملأ الله جوفه إيماناً.

Amincin Allah ya tabbata a gershi ya ce: bawai bait aba kwankadar wata kwankwada ba mafi girman lada daga kwankwadar danne fushi domin neman yardar Allah, ya zo a wani hadisin: wani bait aba danne fushi ba face Allah ya cika zuciyarsa da imani.

5- قال لقمان لولده: يابني لا تذهب ماء وجهك بالمسألة, ولاتشف غيظك بفضيحتك, واعرف قدرك تنفعك معيشتك.

Lukman ya cewa dansa: ya dana kada ka zubar da ruwan fuskarka da rokon mutane, kada huce haushinka da tonawa kanka asiri, ka san darajar kanka rayuwarka zata amfanar da kai.

6- وقال النبي أيوب×:>حلم ساعة يدفع شراً كثيراً.

Annabi Ayuba (a.s) ya ce: hakuri sa'a guda yana tunkude sharri mai tarin yawa.

Duk wanda ya danne fushinsa ya rike shi ya kame shi, shi ne ya hana shi tasiri, ya bar ukubar zunubi ya kau da kai kau da kai mai kyawu da watsi, dukkanin wadannan yayi su domin neman yardar Allah matsarkaki madaukaki, lallai Allah Azza wa Jalla zai bashi sakamako da gwaggwaban lada mai girman gaske, zai kame shi daga azabtar da shi, sannan zai cika zuciyarsa da imani da yarda, ba zain tona masa asiri, zai tunkude sharri mai tarin yawa daga barinsa, bari dai hakan yana daga dabi'u masu daraja mafi alherin dabi'un duniya da lahira, da danne fushi da yin afuwa yayin samun iko kan daukar mataki.

7- قال رسول الله’ في خطبته: (ألا أخبركم بخير خلائق الدنيا والآخرة؟ قالوا: بلى، قال: العفو عمّن ظلمك، وتصل من قطعك، والإحسان لمن أساء إليك، وإعطاء من حرمك).

Manzon Allah (s.a.w) cikin hudubarsa ya ce: (ashe ba zan baku labarin mafi alherin dabi'un duniya da lahira ba? Sai suka ce ka bamu labari, sai ya ce: yin afuwa ga wanda ya zalunceka, ka sadar da zumunci ga wanda yanke maka zumunci, ka yi ihsani ga wanda ya munana maka, kayi kyauta ga wand aya haramta maka.

Bayani: dabi'u jam'I ne daga dabi'a abin da ake nufi da ita shi ne wani abu da zuciya da raiu basu iya rabuwa da shi, ma'ana siffofi masu amfanarwa duniya da lahira, abin da ya kawo daga afuwa da sadar da zumunci da ihsani wanda shi kari ne kan afuwa da kyauta, kadai yana daga uawayen da Asalan dabi'u masu daraja.

8- ya zo cikin wani hadisi: dabi'u masu daraja na duniya da lahira: shi ne kayi afuwa ga wanda ya zalunceka, ka sadar da zumunci idan ya yanke shi kanka.

9- قال أمير المؤمنين× في الكلمات القصار (أفضل الملك ملك الغضب) (أقدر الناس على الجواب من لم يغضب) (أشرف المروءة ملك الغضب وإماتة الشهوة) (أعظم الناس سلطاناً على نفسه من قمع الغضب وأمات شهوته) ( رأس الفضائل ملك الغضب وإماتة الشهوة)  (ضبط النفس عند حادث الغضب يؤمن مواقع الغضب) (ظفر الشيطان من غلبه الغضب، وظفر الشيطان بمن ملكه غضبه) (أعدى عدوّ للمرء غضبه وشهوته، فمن ملكهما علت درجته، وبلغ غايته) (الغضب عدوّ فلا تملّكه نفسك) (ليس منا من لم يملك غضبه) (من غلب عليه غضبه وشهوته فهو في حيز البهائم ) (من كتاب أمير المؤمنين× لمالك الأشتر لما ولاه على مصر/ إملك حميّة أنفك، وسورة حدّك، وسطوة يدك، وغَرب لسانك، واحترس من كل ذلك بكف البادرة وتأخير السطوة، وأرفع بصرك إلى السماء عندما يحضرك منه، حتى يسكن غضبك فتملك الاختيار، ولن تحكم ذلك في نفسك حتى تكثر همومك بذكر المعاد) (أقوى الناس من قوي على غضبه بحلمه) (من خاف الله لم يشق غيظه) (من كتاب أمير المؤمنين× إلى الحارث الهمداني: أكظم الغيظ، وتجاوز عند المقدرة، وأحلم عند الغضب، وأصفح مع الدولة، تكن لك العاقبة).

Sarkin muminai (a.s) cikin gajerun kalmomi yana cewa: (mafi falalar mulki mallakar fushi) (mafi samun ikon yin jawabi shi ne wanda baya fusata) (mafi darajar mutumtaka mallakar fushi da kashe sha'awa) (mafi girmamar mutane a sarauta kan kansa shi ne wanda ya yi wa fushinsa takunkumi ya kuma kashe sha'awarsa) (jagaban falaloli mallakar fushi da kashe sha'awa) (danne zuciya yayin fushi yana amintar da mutum daga afkawa cikin fusata) (Shaidan yayi nasara kan wanda fushi yayi galaba kansa, Shaidan yayi nasara kan wanda fushin sa ya mallake shi) (mafi kiyayyar makiyi ga mutum shi ne fushinsa da sha'awarsa, duk wanda ya mallake su darajarsa zata daukaka zai cimma burin sa) (fushi makiyi ne kada ka mika masa kanka) (daga cikin wasikar Sarki muminai Ali (a.s) zuwa ga Malikul Ashtar lokacin da ya nada shi gwamnan Misra: ka mallaki hananar hancinka, da tsananta fushinka, da damkar hannunka da kaifin harshenka, da ka tsare baki dayansu da sanyayayyen hanu da jinkirta tumbe, ka daga kallonka zuwa sama lokacin da fushi ke hallara gareka har sai ya tausasa gareka sai ka mallaki zabi, kadag ka huknta haka cikin ranka  har sai ka yawaita damuwarka da tunawa da lahira) (mafi karfin cikin mutane shi ne wanda ya gi karfin fushinsa ta hanyar hakurinsa) (duk wanda ya ji tsoran ba zai taba tsaga fusatarsa ba) (daga cikin wasikar Sarkin muminai  Ali (a.s) zuwa ga Harisul Hamdani: ka danne fusata, kayi afuwa lokacin da kake ikon ramuwa, kayi hakuri sa'ilin fushi, ka kau da kai tare da daula, kyakkyawan karshe zai kasance gareka.

10- أوحي الله إلى داود× : ( إذا ذكرني عبدي حين الغضب ذكرته يوم القيامة في جميع خلقي ولا أمحقه فيمن أمحق).

Allah yayi wahayi zuwa ga Dauda (a.s): idan bawana ya tuna dani lokacin fushi nima zan tuna da shi ranar lahira cikin baki dayan halittuna bazan rusa shi cikin abin da ya ruguza.

11- في التوراة: يا موسى إمسك غضبك عمّن ملكتك عليه، أكفّ عنك غضبي).

Ya zo cikin Attaura: ya Musa rike fushinka daga wanda kaek da iko kansa, nima zan kame fushina daga barinka.

12- سُئل عيسى×: أي الأشياء أشدّ؟ فقال: أشدّ الاشياء غضب الله عز وجل، قالوا: فبم يتقي غضب الله؟ قال: بأن لا تغضبوا.

An tambayi Isa (a.s) wadanne abubuwa ne suka fi tsanani: ai ya ce: mafi tsananin abubuwa shi ne fushin Allah Azza wa Jalla, sau suka ce: dame mutum zai kare kansa daga fushin Allah: sai ya ce: kada ku yi fushi.

13- سأل رجل رسول الله’، فقال: أحب أن أكون آمناً من غضب الله وسخطه، قال لا تغضب على أحد تامن غضب الله وسخطه).

Wani mutum ya tambayi Manzon Allah (s.a.w) sai ya ce: ina son in kasance cikin aminci daga fushin Allah, sai ya ce masa: kada kayi fushi kan kowa zaka kubuta daga fushin Allah.

14- قال رسول الله’: من كفّ غضبه كفّ الله عنه عذابه).

Manzon Allah (s.a.w) ya ce: duk wanda ya kame fushinsa Allah zai kame azabarsa daga barinsa.

15- عن الإمام زين العابدين، قال: من أحب السبيل إلى الله جرعتان، جرعة غيظ تردّها بحلم، وجرعة مصيبة تردّها بصبر.

An karbo daga Imam Zainul Abidin (a.s) ya ce: daga cikin mafi soyuwar tafarki zuwa ga Allah kwankwada biyu, kwankwadar fusata da kake danne shi da yin hakuri, dan kwankwadar musiba da kake magan ce ta da hakuri.

16- وعن أبي جعفر ×، قال: (من كظم غيظاً وهو يقدر على إمضائه حشا الله قلبه أمناً وإيماناً يوم القيامة).

An karbo daga Abu Jafar (a.s) ya ce: duk wanda ya danne fushi alhalin yana da iko kan zartar da shi Allah zai cika zuciyarsa da aminci da imani ranar lahira.

17- قال الإمام الصادق×: (ما من عبد كظم غيظاً, إلا زاده الله تعالى عزّاً في الدنيا والآخرة، وقد قال الله تعالى:{وَالْكَاظِمِينَ الْغَيْظَ وَالْعَافِينَ عَنِ النَّاسِ وَاللَّهُ يُحِبُّ الْمُحْسِنِينَ} (آل عمران: 134) وأثابه الله مكان غيظه ذلك).

Imam Sadik (a.s) ya ce: babu wani bawa da zai danne fushinsa face Allah  ya kara masa daukaka cikin duniya da lahira.

18- وعنه ×: (من كظم غيظاً ولو شاء أن يمضيه أمضاه, ملأ الله قلبه يوم القيامة رضاه).

An karbo daga gare shi (a.s) duk wanda ya danne fushinsa wanda da ya so zai iya zartar da shi, ranar lahira Allah zai cika zuciyarsa da yardarsa.

Wadannan jumlar riwayoyi masu daraja daga Annbawa da Ahlil-baiti (a.s) da suka zo cikin bayanin falalar danne fushi da abin da ya doru kansa daga kufaifayi cikin gidan duniya da lahira, farin ciki dubu ga wanda baya fusata, idan kuma yama fusata sai ya danne fushinsa sai ya rabauta da farin cikin gida biyu, babu mai samun haka sai mai babban rabo