b MUKAMI NA TAKWAS: FALALAR HAKURI CIKIN DAUSAYIN RIWAYOYI - HAKURI DA FUSHI
فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها

MUKAMI NA TAKWAS: FALALAR HAKURI CIKIN DAUSAYIN RIWAYOYI

 

1-  قال رسول الله’: (اللهم أغنني بالعلم وزيني بالحلم، وأكرمني بالتقوى، وجمّلني بالعافية).

Manzon Allah (s.a.w) ya ce: ya Allah ya wadata ni da ilimi kayi mini ado da hakuri ka karrama ni da tsoranka, ka cancada mini ado da lafiya.

2-  وقال ’: (أبتغوا الرفعة عند الله، قالوا: وما هي يا رسول الله؟ قال: تصل من قطعك، وتعطي من حرمك، وتحلم عمّن ظلمك أو حمل عليك).

Amincin Allah ya kara tabbata a gare shi ya ce: ku nemi daukaka wurin Allah, sai suka ce: mecece daukaka ya Manzon Allah? Sai ya ce: ka sadar da zumunci ga wanda yanke maka shi, kayi kyauta ga wanda yayi maka rowa, ka yi dauriya kan wanda ya zalunceka ko ya afka maka.

3-  وعنه’: (خمس من سنن المرسلين : الحياء والحلم، والحجامة، والسواك، والتعطّر).

Daga gare shi (s.a.w): abubuwa biyar suna daga sunnonin Manzanni: kunya da hakuri, yin kaho, yin asiwaki, sanya turare.

4-  وقال’: ( إنّ الله يحب الحليم الحييَّ الغنيّ المتعفف، ويبغض الفاسق، والبذييّ السائل الملحف).

(s.a.w) ya ce: hakika Allah ya na son mai hakuri mai jin kunya wadatacce mai kamewa, kuma yana kin fasiki, da mai furta miyagun kalmomi, da mabaraci mai neman taimako.

5-  وعن ابن عباس، قال رسول الله’: ثلاثة من لم يكن فيه واحدة منهن فلا يعتدن شيء من عمله: تقوى تحجزه عن معاصي الله، وحلم يكف به السفيه، وخلق يعيش به في الناس).

An karbo daga Ibn Abbas, ya ce: Manzon Allah (s.a.w) ya ce abubuwa guda uku duk wanda daya daga cikinsu bata kasance tare da shi ba, ba ya tanadi wani abu daga iliminsa: tsoran Allah da zai katange daga aikata sabo, hakuri da zai kame shi daga wawa, da dabi'a da zia rayu da ita cikin mutane.

Ya ce idna aka tattara halittu ranar kiyama mai kira zai yi kira ina kuke ma'abota falala? Sai mutane su tashi suna gaggawa zuwa aljanna, sai Mala'iku su tare su, suce musu ya muke ganinku kuna cikin halin gaggauta zuwa shiga aljanna, sai suce, mune ma'abota faloli, sau suce musu: menene falalarku? Sai suce: mun kasance idan aka zalunce mu sai mu yi hakuri idan aka munana mana sai mu gafarta, idan akai mana jahilci sai mu daure, sai ace musu: ku hsiga aljanna, madalla da sakamakon masu aiki.

Fadakarwa mai muhimmancin gaske:

Ina cewa bai buy aba cewa shi zalunci a kankin kansa abu ne mai muni a hankalce da shari'an ce, hakika Azzalumi abin kyama ne a hankalce kamar yanda ake msa ukuba a shari'an ce kan zaluncin da ya aikata, lallai Allah yayi Azzalumai tanadin wuta jahannama da azaba mai radadi, kamar yanda ya zo cikin littafi mai girma da sunna mai daraja.

Sannan kamar yanda addini bai laminta mutum ya kasance Azzalumi ba, haka zalika bai laminta ya zauna ya zuba a zalunce shi ba, bari dai wajibi kansa ya tunkude zalunci daga kansa, kada kuma ya taimaki Azzalumi kan zaluncinsa ta hanyar yarda da zaluncin, lallai hakan yana cin karo da mutumtakar mutum da `yancinsa da karamcinsa da izzarsa, musamma ma idan zaluncin Azzalumin ya kasance yana hadawa da jama'a ya game su,  kamar misalin zaluncin `yan kama karya da Dawagitai daga sarakuna da shugabanni kasashen duniya da wadanda suke kasa da su daga wadanda jan ragamar al'amuran jama'a suke hannunsa daga ministoci da jagorori da manajoji da makamantansu, hakika Sarkin muminai Ali (a.s) yayi wasiyya cikin wasiyyioyinsa madawwama ga `ya`yansa Imamai biyu Hassan da Husaini amincin Allah ya kara tabbata a garesu: 

« كونا للظالم خصماً وللمظلوم عوناً»

Ku kasance abokan rigimar Azzalumai, masu taimakon wanda aka zalunta.

Zalunci baya halasta da mudlakan hatta tsakanin miji da mata, ta yiwu a rubuta sunan mutum a matsayin Jabberi mai tsaurin kai kuma a tashe shi tare da Fir'aunoni da Dawagitai sakamakon zaluncin da yake aikata kan iyalansa.

Sannan shi zalunci kashi biyu ne: wani lokacin cikin daidaiku, ma'ana mutum guda, Azzalumi da yake zaluntar waninsa kamar misalin makoci ya zalunci makocinsa, ko dan'uwa kan dan'uwansa, wani karo kuma zaluncin na kasancewa daga jama'a kamar zalunci da Jabberai da Dawagitai suke yi, abin da ya zo daga afuwa da kau da kai kadai dai ya zo ne dangane da zalunci kashi na farko koma bayan na biyu, kamar misalin da za ace zalunci zai afka kanka daga waninka, sannan ka samu damar daukar mataki kansa kuma zaka iya daukar fansa kansa ka kwaci hakkinsa ka tunkude zalunci ka dawo abin da ya kwace maka daga dukiya da karamci ko hakki ko dai makamancin haka, to anan yana daga dabi'u masu daraja a duniya da lahira, da kayi hakuri kan zaluncinsa kanka kai masa afuwa da kau da kai daga daukar fansa daga gare shi, bari dai zaka kau da kai ne don gudun kada ka cuta mas aka zarge shi, kamar yanda Yusuf Assidik (a.s) ya aikata kan yan'uwansa cikin fadinsa:

﴿لا تثريب عليكم اليوم﴾.

Yau babu zargi kansu.

8-daga wannan mafarar ne wani mutum daga musulmai ya ce:

«اللهّم ليس عندي صدقة أتصدّق بها، فإنما رجل أصاب من عرضي شيئاً فهو عليه صدقة، فأوحى الله إلى النبي: أن قد غفرت له بذلك»([1]).

Ya Allah ni bani da sadaka da zan bayar d aita, kadai dai wani mutumi yaci muni mutunci sai na yi sadaka da hakan kansa, sai Allah yayi wahayi ga Annabi, lallai na gafarta masa sakamakon wannan abin da da yayi.

9ـ وروي أن رجلاً قال: «يا رسول الله إن لي قرابة أصلهم ويقطعوني، وأحسن إليهم ويسيئون إليّ، ويجهلون عليّ وأحلم عنهم.

An rawaito cewa wani mutum ya ce: ya Manzon Allah ina wasu makusanta ni ina sadar musu da zumunci amma su kuma suna yanke mini, ina kyautatawa zuwa garesu amma suna munana mini, suna aikata jahilci kaina amma ina hakuri da su.

10ـ قال رجل للامام الصادق × : «إنه وقع بيني وبين قوم منازعة في أمر، وإني أُريد أن أتركه فيقال لي: إن تركك له ذُلّ ـ وهذا أكثر ما يتصّوره الإنسان بفعل الشيطان ووسوسته, أو يسمعه من الآخرين عندما يريد ان يعفو عمّن ظلمه ـ فقال الامام الناطق جعفر بن محمد الصادق× : إنما الذليل هو الظالم ـ أي لست انت الذي تكون ذليلاً بعفوك و صفحك، بل من ظلمك هو الذليل حقّاً، والواقع كل واحد ينفق ما عنده، فمن كان عنده الظلم يظلمك، ومن كان عنده العفو فإنّه يعفو عنك، والعفو رحمة وخير ومن الصفات الحميدة ومن جنود العقل، والظلم نقمة وشر ومن الصفات الذميمة ومن جنود الجهل والنار.

Wani ya cewa Imam Sadik (a.s) rigima ta kaure tsakani na da wasu mutane cikin wani al'amari, ni ina son barinsa sai ace mini: barinsa zai jawo maka kaskanci_wani shi ne mafi yawan abin da mutum yake tunani sakamakon wasiwasin Shaidani, ko kuma yake jinsa daga mutane yayinda yake yunkuri da niyar yin afuwa kan wanda ya zalunce shi_sai Imam Sadik (a.s) ya ce: a Azzalumi shi ne kaskantacce_ma'ana ba kaine kaskantacce ba ta hanyar yin afuwarka da kau da kai daga wanda ya zalunce k, bari wanda ya zalunceka shi ne kaskantacce a hakikani, gaskiyar al'amari shi ne kowa yana ciyar da abin da yake wurinsa, wanda bai da komai sai zalunci sai ya zalunceka, wanda yake da afuwa lallai zai maka afuwa, ita kuma afuwa rahama ce kuma alheri ce daga godaddun siffofi daga rundunar hankali, shi ko zalunci ukubace  da sharri daga miyagun siffofi daga rundunar jahilci da wuta.

11ـ مرّ المسيح بن مريم × بقوم من اليهود ـ خذلهم الله ـ فقالوا له شرّاً، فقال لهم خيراً، فقيل له، إنهم يقولون شرّاً وانت تقول خيراً؟ فقال: كل واحد ينفق ممّا عنده ـ أي كل إناء بما فيه ينضح، فمن إناء الخلّ ينضح الخلّ، ومن العسل عسلاً.

Almasihu Isa Ibn Maryamu (a.s) ya wuce ta gefan wasu Yahudawa_Allah ya tozarta su amin_ sau suka fada masa sharri, shi kuma ya gaya musu alheri, sai aka ce masa: su suna fadin sharri kai kuma kana fadin alheri? Sai ya ce kowanne mutum yana fadin abin da yake da shi ne ai_ma'ana kowacce kwarya tana yayyafin abin da yake cikinta ne, kwaryar tsimi na yayyafin tsimi, ta zuma na yayyafin zuma.

Sannan daga natijojin hakuri da afuwa shi ne akwai izza babu kaskanci.

 

12ـ قال الإمام الصادق × : «قال رسول الله’ : ما أعز الله بجهل قطّ، ولا أذلّ بحلم قط».

Imam Sadik (a.s) ya ce: Manzon Allah (s.a.w) ya ce: Allah bai taba daukakar wani da jahilci, haka bai taba kaskantar da wani da hakuri ba.

13ـ وعن أبي جعفر × قال: «كان علي بن الحسين عليهما السلام يقول: إنه ليعجبني الرجل أن يدركه حلمه عند غضبه».

An karbo daga Abu Jafar (a.s) ya ce: Aliyu bn Husaini amincin Allah ya kara tabbata a gare shi yana cewa: lallai mutumin da hakurinsa yake riskarsa lokacin da yake cikin fushi yana birgeni.

14ـ وعن أبي عبد الله × قال: «كفى بالحلم ناصراً، وقال: إذا لم تكن حليماً فتحلّم».

An karbo daga Abu Abdullah (a.s) ya ce: hakuri ya wadatar kasantuwarsa mai taimako, idan baka da hakuri to ka kallafawa kanka yinsa.

15ـ وعند × قال: «إذا وقع بين رجلين منازعة نزل ملكان فيقولان للسفيه منهما: قلت وقلت وأنت هل لما قلت ستجزي بما قلت، ويقولان للحليم منهما: صبرت وحلمت سيغفر الله إن أتممت ذلك، قال: فإن ردّ الحليم عليه ارتفع الملكان».

An karbo daga gare shi (a.s): (idan rigima ta kaure tsakanin mutane biyu sai Mala'iku biyu su sauko sai suce wawan cikinsu: kace kace shin yanzu kai za a baka sakamako ne kan abin da ka fada, sai su ce wa mai hakuri daga cikinsu: kayi hakuri ka yi dauriya da sannu Allah zai gafarta maka idan ka cika haka, ya ce: idan idan mai hakuri ya mayar da magana kan wawan sai Mala'iku su tashi sama su koma.

16ـ وعن أبي الحسن الرضا × قال: لا يكون الرّجل عابداً حتى يكون حليماً، وإن الرّجل كان إذا تعبّد في بني إسرائيل لم يعدّ عابداً حتى يصمت قبل ذلك عشر سنين».

An karbo daga Abu Hassan Rida (a.s) ya ce: mutum bai kasancewa mai bauta har sai ya fara kasantuwa mai hakuri, hakika mutum ya kasance idan yayi bauta cikin Banu Isra'ila basu kirga shi mai bauta har sai ya kame bakinsa shekaru goma gabanin bautar.

Allama Majalisi cikin Tabyinul Kabar yana cewa; Ragib ya ce: shi Alhulmu hakuri shi ne danne rai daga motsa fushi, wasu sun ce hakuri shi ne jinkiri da dandakewa cikin al'amura, shi yana faruwa daga daidaito cikin karfin fushi, yana hana rai tasirantuwa daga abubuwa da suke shigo masa marasa dadi da baya so, daga cikin kufaifayinsa shi ne rashin gigitar zuciya da rai lokacin afkuwar abubuwa masu ban tsoro, da kuma rashin gangarowar motsi mara tsari da rashin bayyanar da fifiko kan waninka, da rashin sakaci cikin kiyaye abin da ya wajaba a kiyaye a shari'an ce da hankalce, maganarsa ta zo karshe.

Hadisi na shiryarwa ya zuwa shardanta karbuwar ibada da kamalarta da tabbatuwa hankali, saboda wawa yana gaggauta miyagun al'amura daga alfasha daga miyagun kalamai da duka da cutarwa, kai wani lokacin har da rauni dakisa, dukkanin wadannan abubuwa suna bata ibada, lallai Allah yana karbar ibada kadai daga masu takawa, an ce alhulmu anan wajen na nufin ma'abocin hankali, hakika ya gabata cewa ibadar wanda ba ma'abocin hankali b aba kammalalliyar ibada bace, yayin da kame baki daga barin abin da bai shafeka ba yana daga cikin abubuwa da suke biye da hankali sai ya ambace shi a bayansa, saboda haka Annabi (s.a.w) ya ce: idan dayanku ya fusata to ya kame bakinsa yayi shiru, hatta azumi ya kasance kame baki a wurin Banu Isra'ila, duk da cewa an shafe shi kan wannan al'umma, sai dai cewa kamalar shiru ba shafe ta ba_ma'ana an shafe azumin kame baki daga magana amma ba a shafe kalamarsa ba, kamar yanda karbar aiki ya kasu kashi biyu: karba da yake wajabta kasantuwar ingantacce ne ma'ana faduwar aiki lokaci da aka zo da shi, da karbuwar kamalar da yake wajabta daukakar mai aiki lokacin da ya zo da shi_ shi aiki nagari tsarkakakke daga mai takawa Allah yana daukaka shi, d daukakar aikin mai aikin yake samun daukaka, domin shi aiki daga mai aiki ya samu kasantuwa sai a lura, ka kafa dalili kan kyawunsa da kasantuwarsa tabbatacce a sharioa'ce cikin shari'ar Banu Isra'ila, da bai kasance aiki mai kyawu ba da Allah bai shar'anta shi cikin wata al'umma daga cikin al'ummu, hakika Allah baya shar'anta wani abu face abin da yakemai kyawu a zatinsa, sun kasance basa fara kirga mutum cikin ma'abota ibada sai bayan sun ga jikkantu ya saba da yin azumi rashin yin magana, a asalinsa shekaru goma ake yi, magana ta kare ta zo karshe.  

17ـ وعن حفص بن أبي عائشة قال: بعث أبو عبد الله غلاماً له في حاجة، فأبطأ فخرج أبو عبد الله × في أثره فوجده نائماً، فجلس عند رأسه يروّحه حتى انتبه، فلمّا انتبه قال له أبو عبد الله × : يا فلان والله ما ذلك, لك، تنام الليل والنهار، لك الليل ولنا منك النّهار».

An karbo daga Hafsu bn A'isha: ya ce : Abu Ubaida ya aikawa Abu Abdullah wani bawa nasa cikin wata bukata, sai yayi jinkiri nsai Abu Abdullah (a.s) ya fito ya bi bayansa sai ya same shi yana bacci, sai ya zauna kusa da kansa yana yi masa fiffita har sai da ya farka daga bacci, yayin da ya farka sai Abu Abdullah (a.s) ya ce masa yakai wane meye haka kake bacci dare da rana, kana da hakkin kwanciya ka huta da daddare, mu kuma muna da hakki kanka da rana.

Wani abokin wani masanin hikima ya je wajen abokinsa, sai ya kawo masa abinci sai ga matar masanin hikimar ta fito ta kasance mai munin hali da dabi'a sia ta zo ta dauke wannan abinci ta kama zagin masanin hikimar, sai wannan aboki ya fita daga gidan cikin fushi, sai masanin hikima ya bi bayansa ya ce: in iya tuna cewa wata rana mun kasance a gidanka mun cin abinci sai kwatsam kaza ta fado kan abincin ta lalalata abincin amma cikinmu babu wanda yayi fushi kan haka, sai ya ce tabbas an yi haka, sai ya ce: ka kaddara cewa wannan mata ta wa misalin waccan kaza, sai ya yewa abokinsa damuwar da fushin da yake ciki, ya tafi abinsa, yana cewa: masanin hkima yayi gaskiya, lallai hakuri waraka ne daga dukkanin radadi.

Wani mutum ya bugi kafar masanin hikima sai ya ji masa ciwo amma tare da hakan bai sanya shi ya fusata ba, sai aka yi masa tamabaya kan haka, sai ya ce na ajiye shi ma'ajiyar wani rami da na ci karo da shin a fada cikin sa, sai na yanka fushi da wukar hakuri na halakar da shi na kashe shi bai iya motsi ballantana ya ma sadada cikin jikina ya rura wutar fusata mai kuna mai ruguzawa da rusawa cikin zuciyata.

18-daga cikin gajerun kalmomin Sarkin muminai Ali (a.s) wadanda suka kasance sun tattaro ma'anonin hakuri da ma'abocinsa (shi hakuri kyakyawa dabi'a ce), (hakuri labule ne mai suturcewa, hankali takobu ce gayawa jini na wuce mai yankewa, babu wani abu da ya lullube aibobin hankalinka kamar misalin hakuri, ka yaki son zuciyarka da hankalinka), (hakuri jagaban shugabanci) (hakuri abokin zama) duk wanda yake da hakuri zai samu mataimaka kamar danginsa, lallai shi ma'abocin hakuri a kowanne lokaci zaka samu shi ake zalunta, su kuma mutane a dabi'an ce suna tare da wanda aka zalunta suna taimaka masa sai su zama kamar danginsa su taimake shi su tallafa masa su bashi kariya kan mai zaluntarsa, (shi hakuri haske ne hankali shi ne masaukinsa) (hakuri cikar hankali) (babu wata daukaka mafi amfanarwa daga hankali) (babu wata izza mafi daukaka daga hakuri) shi hakuri shike baiwa mutum nasara ya daukaka shi, (ku koyi hakuri lallai hakuri badadin mumini ne kuma wazirinsa) (hakuri ya wadatar matsayinsa mai taimako) (na samu hakuri da juriya mafi bani taimako daga jaruman mazaje) (lallai ana auna ka da ladabin ka ne saboda haka ka kayata shi da hakuri) (duk wanda ya fusata ka da mummunar wautarsa kanka to kai ka fusata shi da kyawuntar hakuri daga gareka).[1]

(mai hakuri shi ne wanda ya jurewa `yan'uwansa) (ma'abocin hakuri shi ne wanda hakuri bai tsananta kansa) (mai hakuri himmarsa tana daukaka cikin abin da aka cuta masa cikin neman miyagun sakamako) (an tambayi Sarkin Muminai Ali (a.s) dangane wanda yafi karfaffar dabi'a? sai ya ce: ma'abocin hakuri.

(ilimi ba zai taba amfanarwa har sai cudanya da hakuri)(ilimi shi ne asalin hakuri shi hakuri adon ilimi ne) (ba a jingina wani abu jikin wani abu ba mafi falala daga jingina hakuri ya zuwa ga ilimi) (shi hakuri yana kashe wutar fushi, kaifafa fusata tana rura kunarsa) (mafi hakurin cikin mutane shi ne wanda baya fushi) (mafi rayuwarku shi ne mafi yawan hakuri)

Hakika bayani ya gabata cewa shi hakuri siffa ce ta Allah tsarkakke, lallai Allah shi ne ma'abocin hakuri mai karamci, yana dauriya kan masu saba masa da masu aikata zunubai yana kuma gafarta musu da kau da kai.

Yana suturce mummuna yana bayyanar da kyakkyawa, rahamarsa ta gabace fushinsa, shi mai afuwa ne.

{Allah mai gafara da hakuri ne) suratu Ma'ida:101, (Allah madawadaci ne mai hakuri) Bakara:263, (Allah mai yawan godiya ne da hakuri ne) Attagabun:17, (Allah masani mai hikima ne) Annisa:12.

Lallai shi yana gafara da hakurinsa da ikonsa sakamakon wadatuwarsa ta zati, kamar yanda yake godiya da yawa daga bawansa da yake bauta masa yake masa da`a, lallai shi mai yawan godiya ne, kamar yand ako da yaushe yake hakuri tare da iliminsa kan abin da ya kasance da wanda zai kasance da wanda yake kasancewa, lallai shi mai hakuri ne masani.

Shi ma'abocin hakuri: sifface da ake siffantuwa da ita da take zama jiki mutum bai gafala daga ita, ya zo cikin addu'a: 

«الحمد لله الذي يحلم عنّي كأنني لا ذنب لي ) (خيره اليّ نازل وشّري إليه صاعد).

Godiya ta tabbata ga Allah wanda yake hakuri dani kai kace banda wani zunubi, alherinsa yana ta sauka kaina amma kuma ni sharrina sai hawa yake zuwa gare shi.

19-ina hadaku da Allah ina hadaku da Allah cikin hakuri da juriya(mafi falalar hakuri danne fushi, da mallakar zuciya tare da iko kai).

Kowanne abu yana da nasa adon amma adon hakuri shi ne sakin fuska. Kowanne abu yana da nasa aibobin, aibin hakuru kaskanci, baka sani mutum mai hakuri sai lokacin fushi.

Ba ma'abocin hakuri bane wanda idan ya gaza sai yayi hujumi, idan ya samu iko sai ya dauki fansa, kadai ma'abocin hakuri shi ne wanda idan ya samu dama da iko sai yayi afuwa, shi hakuri ya kasance mai galaba kan al'amarinsa.

Babu hakuri kamar kau da kai da shiru, kowanne abu yana da tasa kamalar, kamalar ilimi hakuri, kamalar hakuri yawan juriya da danne fushi ma'ana kayi hakuri kan wanda yake cutar da kai yake saba maka hakuri mai yawa, ka danne fushinka, ka kallafa kanka yin hakuri har sai ka zama ma'abocin hakuri, cikin sauki zaka dinga kau da kai da danne zuciya.

20ـ البحار بسنده قال: وفد العلاء بن الحضرمي على النبي’ فقال: يا رسول الله إن لي أهل بيت أحسن إليهم فيسيئون، وأصلهم فيقطعون، فقال رسول الله‘: (إدفع بالتي هي أحسن فإذا الذي بينك وبينه عداوة كأنه ولي حميم. وما يلقّاها إلا الذين صبروا وما يلقاها إلا ذو حظ عظيم) فقال العلاء بن الحضرمي: إني قلت شعراً هو أحسن من هذا، قال: وما قلت ؟

Daga Biharun-Anwar da isnadinsa ya ce: Ula'u Ibn Hadrami ya je wajen Annabi (s.a.w) sai ya ce: ya Manzon Allah lallai ina da iyali ina kyautata musu amma suna munana mini, ina sadar da zumunci garesu suna yanke mini, sai Manzon Allah (s.a.w) ya ce: ka tunkude da wacce tafi kyawu sai kaga wanda tsakaninku akwai kiyayya ya wayi gari kai kace shi masoyi ne mai tace soyayya, babu masu samun haka sai wadanda suka yi hakuri babu masu samun haka sai masu babban rabo, sai Ula'u Ibn Hadrami ya ce: lallai ni na yi wata waka tafi wannan aya kyawu, sai ya ce masa: me ka fada ciki?

Sai sabi rera waka kamar haka:

 

ka gaishe da ma'abota kiyayya zukatansu na zagi lallai gaisuwarka ma'abociar girma tana iya kawar da gaba da kiyayyar da ke tsakaninku.

Idan suka bayyanar da alheri to kai musu sakayya da misalinsa

Idan suka boye maka magana to kada ka tambaya.

Lallai wanda dai zai cuta maka wani dan kankanin lokaci ne.

Lallai abin da zasu fada bayan idonka bai baya fadarsa.

 




Sai Annabi (s.a.w) ya ce: lallai cikin waka akwai hikima, lallai daga cikin bayani akwai sihiri, lallai wakarka tana da kyawu, lallai zancan Allah yafi kyawunta.[2]

21ـ عن أبي الحسن الرضا ×: أنّ المأمون قال له: هل رويت من الشعر شيئاً فقال: قد رويت منه الكثير.

فقال: أنشدني أحسن ما رويته في الحلم.

فقال ×:

 

An karbo daga Abu Hassan Rida (a.s) hakika Mamun ya ce masa: shin ka ra waici wani abu daga waka, sai ya ce masa: hakika na rawaito da yawan gaske daga garerta.

To rera mini mafi kyawun abin da ka rawaito ciki hakuri.

Sai ya ce:

إذا كان دوني من بليت بجهله
وإن كان مثلي في محلّى من النّهي
وإن كنت أدنى منه في الفضل والحجي


 

أبيت لنفسي أن تقابل بالجهل
أخذت بحلمي كي أجلّ عن المثل
عرفت له حق التقدّم والفضل


Idan ya kasance na jarrabtu da jahilcin wanda yake kasa dani* sai in hana kaina aikata jahilci.

Idan ya kasance irina cikin mahallina daga hani* sai in rike da hakurina don in girmama daga irina.

Idan na kasance kasa da shi cikin falala* sai in bashi hakkin gabata da falala da hankali.

Sai Mamun ya ce masa: kai me yafi kyawu daga wannan? Wanene ya yayi wannan waka?

Sai ya ce wasu daga ba'arin samarin cikinmu.[3]

Ina cewa: abin da Imam (a.s) ya ambata yana daidaita da halittar mutumtaka da lafiyayyen hankali, lallai mutanen da suke kiyayya da kai da kowanne irin sababi ta kasance lallai su sun kasu zuwa sinfi uku:

1-ko dai mai kiyayya da kai ya kasance jahili sai ya zama ka jarrabtu da jahilcinsa, abin da ya kamata shi ne kada ka kishiyan ce shi da jahilcinsa, idan jahili yayi zagi sai na nufi in masa raddi in saka masa da irin abin da yayi mini to meye banbanci na da shi kenan? Daga nan zaka san cewa duk wanda aka zaga sannan yayi niyyar ramawa da zagi, lallai duka su biyu sun zama jahilai babu hankali da ilimi tattare da su.

Lallai shi jahilci wnai lokacin ana kalubalantarsa da hankali_kamar yanda ya zo cikin hadisi mai daraja, a wani lokacin kuma da ilimi.

2-ko kuma dai ya kasance misalinka sai ya fusata, kamar abokin karatunka ko abokinka sai ya kasance misalinka cikin matsayi da mukami cikin jama'a da ilimi da hankali, abind aya kamata shi ne kayi hakuri domin ka girmama daga sakayya da misali, sai ya zame maka falala a kansa, ka sani cewa da sanne zai nemi uzuri daga gereka ya kuma yi nadama kan abin da ya aikata kanka, sai kai ka wanzu ma'abocin falala.

3-ko kuma dai ya kasance yafi girma da daukakar matsayi cikin falala da ilimi da aiki, abin da ya kama a wannan lokaci shi ne ka kiyaye ladabi tare da shi ka bashi hakkin gabata da falala a kanka.

Lallai ma'abocin daraja da girma sakamakon falalar ilimi da hankali, lallai yana da hakkin gabata, idan ka amsa mas aka saka masa da misali, lallai babu makawa zaka kasance ka munana ladabi, wanda hakan yana cin karo hankali da mutumtaka da halitta lafiyayya da shari'a tsarkakka, sai a lura.

Daga hakurin Manzon Allah (s.a.w) da afuwarsa:

: عن أبي جعفر × قال : إن رسول الله‘ أُتي باليهودية التي سمّت الشاة للنبي’ فقال لها: ما حملك على ما صنعتِ؟ قالت : قلت : إن كان نبيّاً لم يضره، وإن كان ملكاً أرحت الناس منه، قال: فعفا رسول الله عنها([6]).

An karbo daga Abu Jafar (a.s) ya ce lallai Manzon Allah (s.a.w) an kawo wata bayahudiya wajensa wacce ta sanya masa guba cikin naman akuya, sai ya ce mata: me sanya ki aikata haka? sai tace: idan Annabin gaskiyar ne ba zata cutar da shi ba, idan kuma basarake ne kaga na hutar da mutane daga gare shi, sai ya ce: sai Manzon Allah (s.a.w) yayi mata afuwa.[4]

23ـ قال رسول الله’: ينادي منادٍ يوم القيامة من بطنان العرش، ألا فليقم كلّ من أجره عليّ، فلا يقوم إلا من عفى عن أخيه.

Manzon Allah (s.a.w) ya ce: mai kira zai yi kira a ranar lahira daga cikin Al'arshi, duk wanda yake da lada kaina ya tashi tsaye, babu mai tashi face wanda ya yiwa `dan'uwansa afuwa.

24ـ قال الإمام السجاد زين العباد على بن الحسين ×: ما تجرعت جرعة أحبّ اليّ من جرعة غيظ لا أكافي بها صاحبها.

Imam Sajjad Zainul Abidin Aliyu Ibn Husaini (a.s) ban kwankwadi wata jur'a ba mafi soyuwa gareni daga jur'ar fusata kuma bana sakawa ma'abocin ta da ita ba.

Bayani: ita jur'a daga ruwa take kamar misalin lomar tuwo, shi ne abin da mutum ke hadiye shi kai tsaye karo guda, asalinta shi ne sha cikin gaggawa, wasu kuma sunce kankanin abin da sha.

Wasu mutane masu daraja sun ce: ba a kiran fusata halitta da dabi'a gad an Adam ko kuma zabi gare shi, to ta yaya za a kallafa masa magan ce ta saboda muna cewa an kallafa mana tsarkake zuciya ta fuskar da sabubban fusata ba zasu motsa ta ba cikin sauki.

Ina cewa sannan abin da zan fada magana ce ta Allama Majalisi: bisa kaddara samuwar fusata ba tare da zabi ba, shi ba a rataya masa kau da shi ba, sai dai cewa an kallafa masa rashin yin aiki da abin da fusata take hukuntawa, lallai shi wannan galibi yana kasancewa cikin zabinsa, idan an cire masa zabinsa to ba zai kasance kallafaffe ba, maganarsa ta zo karshe.[5]

Ina cewa kamar yanda manyan masana suka fada: abin da bai kasance cikin zabi ba baya kore abind ayake cikin zabi, kamar misalin wanda ya wurgo kansa daga saman dutse yana mai niyyar kashe kansa, lallai shi lallai hakan baya kore hukunci kan fadowarsa kan cewa ta kasance bisa zabinsa ne, daga nan kuma ya aikata haramun ko za ai masa ukuba kansa, to haka al'amarin yake cikin fusata, ta yiwu mutum ta yiwu ya kai ga haddin hauka mutum ya fice daga nutsuwarsa da daidaituwarsa kamar yanda hakan yake yawan faruwa, ta yiwu a wancan lokaci ya kasance daga haukansa na jifa-jifa, shi kuma mahaukaci babu hukuncin shari'a a kansa, sai dia kuma hakan bai ya kore zabinsa na farko, abin da yake wajabta fitar faitarsa daga zabi, sannan bisa la'akari da zabinsa na farko zai kasance an kallafa masa hukuncin shar'ia, da haka ne ya zama wajibi ya danne fushinsa.

Na'am ayyukan haram zasu gangaro daga gare shi a halin da yake cikin fusata kamar misalin zagi da duka da kisa, lallai za ai masa ukuba kan haka a duniya kamar misalin ladabtarwa da kisasi a lahira kuma ai masa azaba da kuma shiga wuta, idan a halin fusatar babu abin da ya gangaro daga gare shi kawai dai ya takaitu ruruwar da fushi cikin zuciyarsa, to sai ya kasance kamar misalin hassada wacce take daga siffofi ababen zargi a dabi'an ce, wacce suke tasiri kan rashin kamalarsa, ko kuma ta kasance daga sabubban hana kammalarsa da daukakar darajojinsa, da yawa daga cikinmu yana da abubuwa da suke hukunta daukakar darajarsa, kamar misalin ilimi mai amfani da aiki nagari cikin kansa, sai dai cewa kuma tare da haka shinge da hanau suna hana tasirinsu cikin samar da ma'aluli da natija kamar misalin kammaluwa da kuma samun kusanci zuwa ga Allah matsarkaki, sai su abubuwa masu hukunta daukaka su kasance daga illa da sababi tauyayye, a wannan lokaci sai ya zama dole a fara da kawar da shinge da hanau domin illa sababi ya su kasance cikakku maa'bota tasiri cikin samar da natija da ma'aluli.

Daga nan ne muhimmanci ilimin Aklak yake bayyanuwa cikin daidaiku da jama'a, kamar yanda da sannu girmamar marhalar farko da marhalolinta guda uku yake kara bayyanuwa, ma'ana 1 wanke zuciya da tsaftace ta daga miyagun siffofi da dabi'u ababen zargi 2 cancada mata ado da kyawawan siffofi, har ya kai ga kammaluwa ya zuwa kololuwar kamalarsa da karshen da kyawunsa daga tsaftatar zati da tsarkaka ta Allah, sai ta zama madubi mahallin tajalli sunayen Allah da siffofinsa girmansa ya girmama, ya kubuta daga dukkanin migayun siffofi, hakika mutum wannan halitta wacce ba ta gushe abar jahilta ba cikin hakikaninsa shi rayayye ne mai imani da ubangiji, wanda yake fana'i cikin iradar Allah, wanzazze da har abadantakarsa, babu mai samun haka face mutum mai babban rabo, babu tsimi babu dabara sai da Allah madaukaki ma'abocin girma.

25ـ عن الامام الصادق × قال: نعم الجرعة الغيظ لمن صبر عليها، فإنّ عظيم الأجر لمن عظيم البلاء، وما أحبّ الله قوماً إلاّ ابتلاهم.

An karbo daga Imam Sadik (a.s) ya ce: madalla da kwankwade fushi ga wanda yayi hakuri kanta, lallai lada mai girma yana ga bala'i mai girma, Allah baita ba son wata al'umma ba face ya jarrabe su da bala'i.

Bayani: (daga bala'I mai girma) ma'ana jarrabawa da ibtila'i, lallai Allah ta'ala ya jarrabar muminai da zama da makiya Ahlil-baiti da da Azzalumai da ma'abota miyagun dabi'u, tare da haka ya umarci muminai da yin hakuri da danne fushi, lallai wannan yana daga cikin mafi tsananin bala'i.[6]

26ـ عن الصادق ×: كظم الغيظ من العدوّ في دولاتهم تقية حزم لمن أخذ به، وتحرّز عن التعّرض للبلاء في الدنيا، ومعاندة الأعداء في دولاتهم ومماظتّهم في غير تقية ترك أمر الله، فجاملوا الناس يسمن ذلك لكم عندهم، ولا تعادوهم فتحملوهم على رقابكم فتذلّوا.

An karbo daga Imam Sadik (a.s): danne fushi daga makiyi cikin daularsu sabida takiyya kariya ce ga wanda yayi riko da hakan, garkuwa daga afkawa bala'i cikin duniya, tsaurin kai ga makiya cikin daularsu da jayayya da su cikin rashin takiyya lallai hakan barin umarnin Allah, ku bi mutane sannu-sannu hakan zai fa'idantar daku a wurinsu, kada kuyi kiyayya da su sai ku dora su kan wuyayenku kuma ku kaskanta.

Ina cewa lallai ita takiyya a makarantar Ahil-baiti (a.s) tana nufin bayyanar da gaskiya da bayyanar da abin da yake dacewa daular makiya, idan larura ta hukunta hakan domin kiyaye rai da yana ma halasta kayi sallar da sallarsu, kamar yanda ya zo cikin fikhun Imamiya 9 Imam Sadik (a.s) yana cewa takiyya addini n ace kuma addini iyayena na ce.

Sannan danne fushi shi ne kwankwadarsa da juriya kansa da hakuri kai, shi ne kallafa kai yin hakuri kamar yanda bayani ya gabata, daga cikin wannan ma'ana hadisi ya zo:

(إذا تثاءب أحدكم فليكظم ما استطاع، فإن الله يحب العطاس، ويبغض التثاءب

Idan dayanku yayi hamma ya wangare bakinsa to ya damke ta gwargwadon iyawarsa.

Ma'ana ya rike ta gwargwadon ikonsa ka da ya bari bakinsa ya bude ya wangare, lallai Allah yana kaunar atishawa, yana kin hamma.

Dole a daular makiya ka danne fushinka daga makiya da wadanda kake da sabanin addini da akida da su, lallai hakan yana daga takiya, yana daga taka tsantsan da tabbatar da lamura suna tafiya daidai, al'amarin da yake wajabta taka tsantsan da kare kai da kiyayewa daga fatawa bala'i cikin duniya, lallai wanda ya kasance cikin wadanda suka fishi yawa sannan ya so bayyanar da sabaninsa da shelanta yakinsa ba tare da cikakken tanadi da karfi ba da tara mataimaka a boye cikin takiyya, to lallai fa yana kai kansa cikin afkawa hatsari da bala'I cikin duniya da lahira ba tare da samun wata riba da sakamako mai kyawu ba, tsaurin kai ga makiya cikin mulkinsu da daularsu lalatacce  da hukumarsu ta zalunci da kwace, da bayyanar da jayayya da sub a tare da yin takiya ba yana jawo barin umarnin Allah, lallai Allah matsarkaki madaukaki yayi umarni da yin takiyya cikin kur'ani da sunnar Annabinsa da minhajin tsarkakakken tsatso masu shiriyarwa (a.s).

Abin da ya fi kamata cikin misalin wadannan matsayu da matakai masu tsanani da hatsari shi ne abi a sannu-sannu tare da mutane har su samu su yawaita akai ga kiransu jama'a cikin wannan taron Azzalumai, lallai rigima da mutane ba tare da aunawa da sanya hankali da lissafi ba daidai yake da dora makiyi kan wuyayun muminai, a bayyane yake cewa su makiyan su mulki da makaman yami ke hannunsu da dukiya da iko, hakan zai taimaka musu kan mamaye su samu iko kan wuyayun muminai cikin zalunci da kiyayya, sai su dinga wulakanta muminai tsiraru ta hanyar wurga gidan yari (prison) da azabtar da su da korar su da kisa da kwace dukiyoyinsu da cutar da su cikin iyalansu da mutuncinsu da makamancin haka daga kaskanci, (Allah ya tsaremu da kaskanci nesa-nesa da shi) ana kubuta daga haka ta hanyar amfani da takiyya har sai karfi ya karfafa kamar yanda Imam Hassan Almujtaba (a.s) yayi, wani karon kuma ta hanyar jihadi da rungumar shahada cikin tafarkin Allah idan maslaha ta hukunta yin hakan kamar yanda Imam Husaini (a.s) yayi, Hassan da Husaini dukkaninsu Imamai sun tashi tsaye ko kuma suna zaune, ya zama dole cikin misalin wadannan kaziyoyi da batutuwa na makoma wadanda suka ginu kan mutuwa da rayuwa a koma wajen Maraji'ai cikin kowanne zamani da cikin kowaccce kasa da gari, hakan na daga abin da zai kawo izza, kamar yanda A'immatu Ahlul-baiti (a.s) suka yi umarni da yin hakan, wurin Allah ake neman taimako, ana iya fa'idantuwa daga daga hadisi mai daraja da cewa danne fushi kala biyu ne: wani lokacin cikin daidaiku, wani karon kuma tare da jama'a kamar daula da hukuma da abin da yayi kama da haka, sai a lura sosai.

25- قال الصادق× : (ما من عبد كظم غيظاً إلا زاده الله عز وجل عزّاً في الدنيا والآخرة، وقد قال الله عزّ وجل {وَالْكَاظِمِينَ الْغَيْظَ وَالْعَافِينَ عَنِ النَّاسِ وَاللَّهُ يُحِبُّ الْمُحْسِنِينَ}(سورة آل عمران: من الآية 134)، وأثابه الله مكان غيظه ذلك.

Imam Sadik (a.s) ya ce: babu wani bawa da zai danne fushi face Allah Azza wa Jalla ya kara masa izza a duniya da lahira, hakika Allah Azza wa Jalla ya ce: {da masu danne fushi da masu afuw aga mutane lallai Allah yana son masu kyautatawa} Alu Imrana:134, Allah zai saka masa kan haka

Allama Majalisi cikin bayanin wannan hadisi yana cewa: (hakika Allah ya ce) bayani ne ga izza lahira sabida cikin suratu Alu Imrana yana cewa

Ku yi gaggawa zuwa ga neman gafara daga ubangijinku da neman aljanna fadinda kamar fadin sama da kasa an tanade ta ga masu takawa wadanda suke ciyarwa cikin kunci da yalwa da masu danne fushi.

Malam Baidawi cikin Anwarul Tanzil sh 81 ya ce (masu danne fushi) ai masu rike shi su hana shi gudana tare da cewa suna da iko kai, daga ciki akwai fadin larabawa:

 (كظمت القربة، إذا ملأتها وشددت رأسها).

Na danne salka, idan na cika ta ruwa na daure bakinta kada ya zuba.

وعن النبي’: (من كظم غيظاً وهو يقدر على أنفاذه، ملأ الله قلبه أمناً وإيماناً).

An karbo daga Annabi (s.a.w) duk wanda ya danne fushi alhalin yana da iko kan zartar da shi, Allah zai cika zuciyarsa da imani da aminci.

(da masu afuwa ga mutane) masu watsi da yin ukuba daga wadanda suka cancanci haka.

(Allah yana son masu kyautatawa) wannan zai iya daukar ismul jinsi sakamakon zuwan Alifun da lamun, sannan iya kasancewa Ahadul zihni kamar yanda yake a ilimn lugga, sai ya kasance ishara zuwa garesu ai masu danne fushi da masu afuwa, maganarsa ta zo karshe.

Ya isar musu izza da daukaka a lahira Allah yayi musu bushara da aljanna, ya yi hukunci da cewa an yi tanadin ta domin su, lallai kuma Allah yana son su.

Zai iya kasancewa illa ga izza duniya, da cewa su zasu shiga karkashin wannan aya, wannan daukaka ce ita ma, ko kuma dia ta shiryar kan cewa su suna daga masu kyautatawa da kasancewarsu wanda Allah yake son su, shi duk wanda Allah yake son sa madaukaki ne shi duniya da lahira.

Zata iya kasancewa cigaba ne na bayani ko badali mayi daga fushinsa, sai sakayya ta kasance cigaba kan (zadahu) ya kara masa, ma'ana Allah ya bashi lada tare da izzar duniya daga asalin fushi, sani da yana daga ibtila'I da yake samun mutum ba tare da zabinsa ba, Allah ya sauya masa da wani mayi kamar yanda malaman tauhidi suke fadi_abin nufi da Kalmar (sawab) shi ne mayi, sabida shi sawab lada wani mayi ne d ayke kasance kan al'amuran zabi bisa rayawarsu, shi kuma fushi bai kasance ba cikin zabinsa yake ba, duk da cewa danne fushi yana cikin zabinsa, aljanna tana kan danne fushi, shi kuma sawab lada mayi ne na asalin fushi, wasu kuma sun ce abin da ake nufi da wani bigire saukakke da ya kebantu ga yan aljanna, idafarsa ya kasance ta fuskanin idafar ma'aluli ya zuwa ga illarsa.

26- قال الإمام الصادق×: (من كظم غيظاً ولو شاء أن يمضيه أمضاه، ملأ الله قلبه يوم القيامة رضاه).

An karbo daga Imam Sadik (a.s) ya ce: (duk wanda ya danne fushi wanda ya zo zartar da shi zai iya zartar dashi, ranar lahira Allah zai cika zcuiyarsa da yarda.

Bayani: (da ya so zartar da shi) ma'ana yayi aiki da abin da fushin yake hukunci da shi daga yiwa wanda yayi masa wauta da ketare haddi sakamakon ikon da yake da shi kan yin hakan, sai dai kuma ya danne fushinsa yayi masa afuwa, lallai Allah zai bashi lada kan aikata haka ta hanyar cika zuciyarsa da yardarsa, ma'ana zai bashi lada da sakamako da karamci, da ceto da darajoji har sai yarda cikakkiyar yarda mai gimra da zarce tunani mai tunani, bari ba a tunanin wata yarda sama da ita.

27- قال الإمام الباقر×: (من كظم غيظاً وهو يقدر على إمضائه حشى الله قلبه أمناً وإيماناً يوم القيامة).

Imam Bakir (a.s) ya ce: (duk wanda ya danne fushi alhalin yana da iko kan zartar da shi ranar lahira Allah zai cike zuciyarsa da aminci da imani.

Bayani: aminci da imani suna daga mafi girmamar ni'imomin Allah matsarkaki madaukaki kan bayinsa babu banbanci cikin kasancewasu ckin duniya ko lahira, lallai cikin duniya akwai ni'imomi guda biyu da aka jahilce su, sune koshin lafiya da aminci, amma a lahira shi ne amintuwa daga tsoran yininta da ukubarsa ranar da mai shayar taki man cewa da jinjirin da take shayarwa, duk wanda ya danne fushinsaa duniya ba don gazawarsa ba, bari dai yana da iko kan zartar da shi da sakinsa, sai dia cewa yayi zabi yin hakuri da dauriya, lallai Allah matsarkaki zai bashi sakamao kan haka zai cika zuciyarsa da aminci da imani a ranar lahira, wannan natija tana biye da mukaddimomi, duk wanda ya kasance cikin aminci ranar lahira, babu makawa zai kasance cikin aminci da imani a duniyarsa da lokacin kakakin fitar rai da barin duniya, da cikin kwanciyar kabari, sai kushewarsa da kabarinsa su kasance dausayi daga dausayoyin aljanna, kai kace abin da ake nufi da imani shi ne kammalallen gasgatawa da karamcinsa da ludufinsa jalaluhu, mabayyani boyayye da rahamarsa mayalwaciya mai tattaro komai, sakamakon yawan abin da yake bayarwa daga lada da sakamako, a wannan lokaci sai ma'anar ta komawa zuwa abin da aka amabata cikin hadisi da ya gabata.

Zai kuma iya kasancewa: mafi gamewa daga(Al'imla'u) cikawa, shi cikawa yana rataya da abin da yake waje, shi kuma (Al'isha'u) tumbayewa yana rataya da abin da yake ciki, sai ya tumbaye zuciyarsa da aminci da imani, ta hanyar kara masa yakini da imaninsa daga haskensa cikin haraminsa, iata zuciyar mumini haramin Allah, sai ya cancanci kari daga lada mai kyawu, da gwaggwaban sakamako da karamar ubangiji daga rahama jin kai kebantattu ga muminai da makusanta, tsakanin baka biyu ko kuma mafi kusa, domin babu dalili kan rashin halascin karuwar imani cikin wannan rana, musammam ma Allah yana sanya idon mutum ya zama mai kaifin gani sai ka same shi yana gani tabbatattun abubuwa kamar yanda suke a hakikarsu, daga cikin abin da yake karawa cikin sani da daukakar darajoji, lallai kauwar ilimi baya yankewa bayan mutuwa, kamar yanda idlaki saki babu kaidi daga fadinsa madaukaki yake shiryarwa a kai

{وقل ربي زدني علماً}

Kace ya ubangiji ka kara mini ilimi.

Lallai Muhammad da iyalansa iliminsu yana dada karuwa a wasu lokuta a duniya da lahira daga wurin masani matsarkaki, kamar yanda ya zo daga cikin mutawatiran hadisai ingantattu, sai a lura sosai.

28- قال الامام السجاد علي بن الحسين×: (قال رسول الله : من أحب السبيل إلى الله عزّ وجل جرعتان، جرعة غيظ يردّها بالحلم، وجرعة مصيبة يردّها بصبر).

Imam Sajjad Aliyu Ibn Husaini (a.s) ya ce: (Manzon Allah (s.a.w) ya ce: daga cikin mafi soyuwar tafarkin Allah akwai kwankwada guda biyu: kwankwadar fushi da yake mata martani da danne shi da yin hakuri, da kuma kwankwadar musiba da yake hakuri kanta.

Bayani: (yake martani) anyi amfani da wannan kalma na jeka na yika bisa misali, kai kace fusatacce wanda yake nufin bayyanar da fusatarsa da daukar fansa da huce haushi, lallai abin da yake bayan haka daga maslahohinsa na duniya da lahira na tunkuda kan kada ya bayyanar da shi, da abin da yake biyo bayansa daga ribar dauriya da hakur_ kamar yanda bayanin haka zai zo daga baya- sai ya kasance kamar wanda ya sha magani mai daci mara dadi da ransa bai son s, sai ya nufi tunkude shi da tofar da shi daga bakinsa, sai dia cewa yana tunanin akwai alfani da fa'ida cikin wannan magani sai ya dawo da shi ya hadiye shi kamar yanda yake kwankwade da shan kwankwadar ruwa, haka hakuri yayin bala'i da barin raki da razana, lallai yana kama da wancan hali, cikinta akwai aro da misaltawa.

Banbanci tsakanin danne fushi da hakuri cikin abin da ake da ikon daukar fansa kansa, shi hakuri yana kasancewa ne cikin abin da baka da iko kansa, sannan akwai wani banbanci tsakanin na daban zamu kawo shi cikin hadisin da zai zo nan gaba kadan.

29- قال الأمام الصادق×: (ما من جرعةٍ يتجرّعها العبد أحب إلى الله من جرعة غيظ يتجرّعها عند ترددها في قلبه، إما بصبر أو بحلم).

Imam Sadik (a.s) ya ce: babu wata kwankwada da bawa zai kwankwadeta mafi soyuwa ga Allah daga kwankwade fushi lokacin da yake kai kawo a zuciyarsa, ko dai da juriya ko da hakuri.

Bayani: abin da ake nufi da kai kawo cikin zuciyarsa shi ne gabatar zuciya a wani lokaci cikin kwankwade shi sakamakon abin da yake tattare da shi daga lada mai yawa da sakamako mai kyawu, da gyara nafsu da tsarkake ruhi, a wani karon kuma ya zuwa watsi da kwankwade shi sakamakon abin da yake cikin sa daga muni da daci, ko dai da hakuri ko da dauriya.

Banbanci tsakaninsu: ko dai na farko cikin idan mutum bai kasance ma'abocin dauriya ba sai ya daure da kyar ya kuma yi hakuri, na biyu idna ya kasance mai dauriya hakan kuma ya kasance daga dabi'arsa da bai rabuwa da ita, kuma hakan ya kasance gare shi abu saukakka.

Ko kuma na farko cikin abin da idan bai kasance yana da iko kan daukar fansa ba sai yayi hakuri, bai yi raki ba, na biyu cikin lamarin bashi da iko kuma bai aikata shi ba saboda dauriya da kau da kai da kuma karamci, bisa gina cewa danne fushi ana amfani da Kalmar cikin idna bai samu iko kan daukar fansa ba kenan.

Wasu sun ce hakuri shi ne kada ya ce komai kada ya dauki kowanne mataki, shi kuma dauriya da kau da kai shi ne yayi magana ya kuma aikata wani abu da zai janyo kau da fitina da warware matsalar, da tausasa zuciya, sai juriya ta kasance da ma'anar hankali da aiki da shi.

30- البحار عن آمالي الصدوق بسنده عن الربيع صاحب المنصور، قال: قال المنصور للصادق× حدّثني عن نفسك بحديث اتعظ به، ويكون لي زاجر صدقٍ عن الموبقات.

فقال الإمام الصادق×: عليك بالحلم، فإنّه ركن العلم، وأملك نفسك عند أسباب القدرة، فإنك إن تفعل ما تقدر عليه كنت كمن شفي غيظاً، وتداوى حقداً، أو يحب أن يذكر بالصولة، وأعلم أنك إن عاقبت مستحقاً لم تكن غاية ما توصف به ألا العدل [لا أعرف حالاَ أفضل من حال العدل] والحال توجب الشكر أفضل من الحال التي توجب الصبر.

فقال المنصور ـ من خلفاء بني العباس ـ: وعظت فأحسنت, وقلت فأوجزت.

Daga littafin Biharul-Anwar daga Amali da isnadinsa daga Rabi'u abokin Mansur,ya ce: Mansur ya cewa da Imam Sadik (a.s) ka zantar da ni dangane da kanka da wani zan ce da zan wa'aztu da shi, ya kuma kasance mini mai tsawatarwa da gaskiya daga abubuwa masu halakarwa.

Sai Imam Sadik (a.s) ya ce:kayi riko da juriya, lallai shi rukunin ilimi ne, ka mallaki zuciyar lokacin samuwar sabubban iko, lallai kai idan ka aikata abin da kake da iko kansa to ka kasance kamar wanda ya huce haushi, ya magan ce kiyayya, ko kuma yake son a ambace da tumbe, ka sani lallai kai idan ka yiwa wanda ya cancanci ukuba ukuba kololuwar abin da za a siffantaka da shi shi ne adalci, ban sani wani hali mafi falala daga adalcin ba, da halin da yake wajabta godiya mafi falala daga halin da yake wajabta hakuri ba.

Sai Mansur wanda ya kasance daga halifofin Abbasiyawa ya ce: hakika kayi wa'azi ka kyawunta, ka magantu ka takaice maganarka.

31- وعن الإمام الصادق×، عن آبائه^، قال: قال رسول الله’: قال عيسى بن مريم ليحيى بن زكريا×، إذا قيل فيك ما فيك، فأعلم أنه ذنب ذكرته، فاستغفر الله منه، وإن قيل فيك ما ليس فيك، فأعلم أنّه حسنة كتبت لك لم تتعب فيها.

An karbo daga Imam Sadik (a.s) daga babanninsa (a.s) ya ce: Manzon Allah (s.a.w) ya ce: Isa Ibn Maryam (a.s) ya cewa Yahaya Ibn Zakariya (a.s) idan aka ambaci abin da yake cikinka, to ka sani lallai hakan zunubi da aka tuna da shi sai ka nemi gafarar Allah daga gare shi, idan kuma aka ambaci abin da babu tare da kai, ka sani lallai shi kyakkyawan aiki ne aka rubuta maka ka da ka yi bibiya cikinta.

32- قال أمير المؤمنين×: ثلاثة لا ينتصفون من ثلاثة، شريف من وضيع، وحليم من سفيه، وبرّ من فاجر.

Sarkin Muminai Ali (a.s) ya ce: abubuwa uku basa daidaituwa daga abubuwa uku, mutum mai daraja daga wulakantacce, mai hakuri daga Wawa, mutumin kirki daga Fajiri.

Ina cewa: zai iya yiwuwa abind aake nufi da wadannan mai daraja da mai hakuri da mutumin kirki, ba a nemansu da karamcinsu da hakkokinsu cikin mukamin daidaita, da daidaituwa daga wadannan mutane uku: wulakantacce da Wawa da Fajiri, ta kaka mutum mai daraja wand aya kasance daga manya-manyan mutanen gari zai so ya daidaita da daga mutumin da yake wulakantacce talautacce kaskantacce babu dangantaka tsakaninsu, ina tauraruwar Surayya ina turbaya, wutsiyar Rakumi tayi nesa da kasa, kamar yanda Sarkin muminai Ali (a.s) yake fadi cikin bayanin irin zaluncin da aka yi masa:

إنّه نزل بي الدهر حتى قالوا: علي ومعاوية ذلك المنافق شارب الخمر! الذي دعى عليه رسول الله،

Lallai yanda al'amarin yake shi ne yau wai zamanin ya sauke ni ta kai ga wasu suna daidaita ni da Mu'awiya wannan munafuki mashayin giya! Wanda Manzon Allah (s.a.w) ya la'an ce shi.

Hakika masadir din dukkanin bangarori biyu shi'a da sunna sun kawo wannan maganar zaluncin Mu'awiya da danniyarsa, sai wai ta kai ga har wasu suna kamanta shi da Sarkin masu tauhidi jagoran masu takawa Sarkin muminai Zakin Allah da Manzon Allah Aliyu Ibn Abu Dalib (a.s) wai yau wasu na ambatonsa su kiyasta shida Mu'awiya, ina shugaban masu daraja ina shi ina wulakantacce `dan wulakantacce! Haka zalika batun yake ga wanda ya kasance mai hakuri ace za a daidaita shi da wawa, da wanda ya kasance mutum nagari da yaya zai daidaita da Fajiri Azzalumi?

Abin da yafi dacewa daga mutum mai daraja yak au da kallonsa daga wulakantacce kamar yanda mai karamci yake kau da kansa daga mutumin banza, idan ya wuce ta gefansa yana zaginsa ya cin mutuncinsa, baya waiwayarsa ballantana ma ya kula da shi, bari dai cikin ransa sai ya ce: lallai wannan zage-zagensa da yake yi bai shafeni ba, haka batun yake dangane da mai hakuri da Wawa, mutumin kirki tare da Fajiri.

33- قال الإمام الصادق× : ثلاث من كنَّ فيه استكمل خصال الإيمان، من صبر على الظلم، وكظم غيظه، واحتسب، وعفاء وغفر، كان كمن يدخله الله عز وجل الجنة بغير حساب، ويشفعه في مثل ربيعة ومضر.

Imam Sadik (a.s) ya ce: abubuwa uku duk wanda yake da su hakika dabi'un imani sun cika cikin sa, duk wanda yayi hakuri kan zalunci, ya danne fushinsa, ya daure, yayi afuwa da gafara, ya kasance kamar wanda ya Allah yake shigar da shi aljanna ba tare da hisabi ba, ya bashi ceto cikin Banu Rabi'a da Madar.

Ina cewa: lallai imani kebantacce mafhumi da misdak ne daga muslunci, da kebantacciyar ma'anarsa, shi muslunci a wani lokaci da gamammiyar ma'ana shi ne sallamawa da imani da dayantar Allah wanda dukkanin Annabawa da Manzanni suka zo da shi tun daga Adam (a.s) har zuwa cikamakin Annabawa da Manzanni, kamar yanda ya zo cikin fadinsa madaukaki:

{إِنَّ الدِّينَ عِنْدَ اللَّهِ الْإِسْلامُ } آل عمران: 19.

Hakika addini wurin Allah shi ne muslunci.

A wani karon kuma da kebantacciyar ma'ana shi ne musluncin da cikamakin Annabawa shugaban Manzanni Muhammad (s.a.w) ya zo da shi

 {وَمَنْ يَبْتَغِ غَيْرَ الْإِسْلامِ دِيناً فَلَنْ يُقْبَلَ مِنْهُ وَهُوَ فِي الْآخِرَةِ مِنَ الْخَاسِرِينَ}سورة آل عمران: 85.

Duk wanda yake nema wani addini koma bayan muslunci ba za a taba karba daga gare shi ba kuma shi ranar lahira yana cikin hasararru.

 Kebantaccen muslunci yana tabbatuwa da zahirin mai da’awarsa ana kuma yi masa hukunci da kasantuwarsa cikin musulmai, idan yayi ikirari da Kalmar shahada (na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah na shaida Muhammad Manzon Allah ne) jininsa da dukiyarsa da mutuncinsa suna cikin kariya, amma Imani shi ne abin da lada ya doru kansa a ranar lahira, shi ne ikirari da fatar harshe da kudurcewa a zuciya da aiki da gabbai_ ta hanyar sauke wajibai da kauracewa abubuwan da aka haramta da abin da yake riskuwa da- wannan Imani na zuciya yana karbar karfafa da raunana, da karuwa da tawaya, lallai shi yana daga kulli tashkiki ma’abocin martabobi mikakku da masu bijira, yana karbar kammala da kuma shi ne mutum yake samun kammaluwa, kansa yake samun kammalar imanins, wannan shi ne abin da ake kira da kammaluwar Imani, kamar yanda Imani yake tattaro kyawawa da darajoji-ya zo cikin riwayoyi cewa darajoji 400, ko kuma dai goma, ko kuma sun tattaru cikin gomomin darajoji, Slamanul muhammadi Allah ya kara masa yarda ya kasance yana da guda goma, sai ya zama imaninsa ya kammala, ya kasance daga kammalallu rabautattu makusanta-Salmanu daga garemu yake mu Ahlil-baiti-domin ya kasance daga malamai.

Sannan abubuwa uku wanda duk suka kasance tare da shi Imaninsa ya kammalu ya kuma kasance cikin madaukakan darajoji cikin matsugunin gaskiya wurin Sarki mai iko.

Na farko: hakuri kan zalunci_ sai dai cewa kamar yanda ya gabata abin da ake nufi daga zalunci zaluncin daidaiku na mutum, mutum kasance yana fuskantar zalunci daga dan’uwansa da danginsa ko makotansa, lallai shi a farkon al’amari wajibi kansa ya yaki wannan zalunci ya kawar da shi daga kansa, idan bai samu iko ba sai yayi hakuri, idan ya samu nasara kansa da iko kai a nan yayi hakuri daga abin da ya gaggauta gangarowa daga zalunci, yayi masa afuwa ya kau da kai kau da kai mai kyawu, kada yayi masa ukuba bayan afuwar farko da yayi, ka da ya gurbata aikinsa da gori da cutarwa, kada ya yiwa wanda ya zalunce shi martani da misalin abin da yayi a kans, bari dai yayi kokari ganin cewa bai zama kasa da misalin bishiyar dabino ba, lallai kananan yara suna jifan ta da duwatsu amma ita kuma sai ta yi musu martani da zakakan `yayan dabino to zubo musu su kyauta, duk wanda ya kasance karamin yaro cikin dabi’unsa tare da kai yayi maka tsageranci da rashin kunya, to kai abin da ya kamace ka yi kada kayi masa misalin abin da yayi maka, kai dai ka kyautata masa kayi masa afuwa, ka saka masa da mafi falala ka tunkude daga kanka da wacce tafi kyawu, har ya zama ka mayar da shi aboki mai tace soyayya, lallai muatne bayin wadanda suke kyautata musu ne, sannan yana daga dabi’u masu daraja a duniya da lahira kayi afuwa kan wand aya zalunce ka.

Na biyu: danne fushi da yin dauriya daga wanda ya fusata, ya kona maka zuciya, ka tsammaci ladan hakan a wurin Allah ta’ala.

Na uku: afuwa da gafara daga wand aya munana maka Magana da aiki, ya zama bai mutuntaka ba, bai girmama matsayinka da mutuntakarka ba cikin jama’a.

Sannan kufaifayi da riba duniya da lahira suna biyu wadannan dabi’u uku zababbu sune hakuri da danne fushi da afuwa, daga ciki zai kasance daga wanda Allah zai shigar da shi aljanna ba tare da hisabi ba, haka yana bashi hakkin ceto kamar yanda yake baiwa Annbawa da wasiyyai da shahidai da malamai, sai ya zama ya yi ceto cikin misalin manyan Kabilu guda biyu Rabi’atu da Madar.

34 - عن الإمام جعفر بن محمد، عن آبائه^، عن النبي’، قال: (ثلاثة من لم تكن فيه فليس مني ولا من الله عز وجل، قيل: يا رسول الله ما هي؟ قال: حلم يرد فيه جهل الجاهل، وحسن الخلق يعيش به في الناس، وروع يحجزه عن معاصي الله عز وجل)

An karbo daga Imam Jafar Ibn Muhammad Sadik (a.s) daga babanninsa (a.s) daga Annabi (s.a.w) ya ce: (abubuwa uku duk wanda baya tare da su baya daga gareni ba ya kuma daga Allah Azza wa Jalla, sai aka ce wadanne abubuwa ne ya Manzon Allah? Sai ya ce: hakuri da yake raddin jahilcin jahili da shi, da kyawuntar dabi’a da yake rayuwa da shi tsakankanin mutane, da tsantseni da yake katange shi daga aikata sabon Allah Azza wa Jalla.

35- عن الإمام الرضا×، عن آبائه^، عن أمير المؤمنين×، قال: (قال رسول الله’: عليكم بمكارم الأخلاق، فإنّ الله عزّ وجل بعثني بها، وإنّ من مكارم الأخلاق: أن يعفو الرجل عمن ظلمه، ويعطي من حرمه، ويصل من قطعه، وأن يعود من لا يعوده).

Daga Imam Rida (a.s) daga babanninsa (a.s) daga Sarkin muminai Ali (a.s) ya ce: Manzon Allah (s.a.w) ya ce: kuyi riko da dabi’u masu daraja, lallai Allah Azza wa Jalla ya turo ni da su, lallai yana daga cikin dabi’un daraja mutum yayi afuwa kanb wanda ya zalunce shi, yayi kyauta daga wanda ya haramta masa, ya sadar da zumunci daga wanda ya yanke masa, ya ziyarci mara kafiyan da shi idan bai da lafiya baya zuwa duba shi.

Ina cewa: daga cikin falsafar aiko da Annabawa (a.s) da cigaba kan kaddinsu daga Wasiyyai da gadar su da malamai suke shi ne tsayar da adalci cikin jama’a da karfafar asasin kyawawan dabi’u cikin jama’a mutane, da mutane su dabi’untu da dabi’un Allah Azza wa Jalla.

Daga wannan asasi cikamakin Annabawa shugaban Manzanni macecinmu likitan zukatanmu malamin mutumtaka shugaban kyawawan halaye Muhammad (s.a.w) yana cewa: (an aiko ni domin in cika kyawawan dabi’u)

Sannan ya zo cikin riwayoyi masu tarin yawa kai sun kai haddin tawatiri cikin ma’ana da takaicewa, amincin Allah ya kara tabbata a gare shi yayi ishara ya zuwa kyawawan dabi’u duniya da lahira- kamar yanda ya gabata-cikin wannan hadisi mai daraja yayi ishara ya zuwa ga jumlar dabi’un daraja kamar yanda yake a wasu hadisan daban, sune: (afuwa) me ya sanar da kai dangane da afuwa! Lallai cikinta akwai izza domin Allah a duniya da lahira lallai tana daga siffofin Allah madaukaka da kyawawan sunayensa, lallai shi Allah girmansa ya girmama shi ne afuwa yana afuwa yana gafara ga wanda yake so yanda ya so, yana son afuwa da gafara, kamar yanda yake son wanda ya siffanta da siffarsa, yana son mutum mai yawan afuwa da yawan gafara, daga cikin dabi’un daraja da falala shi ne mutum yayi afuwa kan wanda ya zalunce shi cikin zaluncin daidaiku a iya kansa- kamar yanda ya gabata koma bayan jama’a da zamantakewa, lallai wannan yana daga hakkin kowa da kowa, wanda babu damar afuwa ciknsa bari dai a nan (ka kasance abokin rigimar azzalumi mai taimakon wand aka zalunta).

Hadisi mai daraja duk da cewa cikin sa Kalmar (Rajlu) namji, sai dai cewa hukunci mudlak ne ya tattaro maza da matam kai hatta kananan yara, ita afuwa tana daga dabi’un daraja kowa da kowa yana tarayya a cikinta, ba ta daga cikin hukuncin taklifi daga wajibai da haramun da suka kebantu da wadanda suka balaga, ya zama dole mu tarbiyantar da `ya`yanmu da koyar da su kan yin afuwa da kau da kai, idan aboki ya aikata kuskuer kan abokinsa a makaranta ya kuma zalunce shi sannan ya samu iko kan ramuwa da daukar fansa ya huce haushi kansa, ta yanda zai ikya kai karar sa wurin shugaban makaranta. Sannan malaminsu yayi niyyar daukar mataki kansa kan zaluncin da ya aikata sai dai cewa mun tarbiayntar da dalibin da cewa yana daga dabi’un daraja yin afuwa kan wand aya zalunce shi, da kuma cewa cikin yin afuwa jin dadi data zarce daukar fansa, kuma tana daga cikin kyawawan dabi’u, asalinta daga kyawawan halaye  

36- عن الإمام الرضا× في قول الله عز وجل: {( فَاصْفَحِ الصَّفْحَ الْجَمِيلَ) (سورة الحِجْر: من الآية 85)} قال: العفو من غير عتاب، ومن الأمثال العربية (حرّ التعذر حرّ الذي قبل العذر) أي: من حرية الإنسان إنّه إذا أخطأ سرعان ما يعتذر، كما من حرية الطرف الآخر الذي ورد عليه الخطأ أن يقبل عذره، وأن يجعل ما وقع من الخطأ نسياً منسياً، وكأنّه لم يقع.

An karbo daga Imam Rida (a.s) cikin fadin Allah Azza wa Jalla: (ka kau da kai kau dakai mai kyawu) ya ce afuwa ba tare da zargi ba, daga Karin maganar larabawa (`yantacce da ya nemi uzuri daga `yantacce gabanin uzuri) ma’ana yana daga yancin mutum idna ya aikata kuskure take ya nemi uzuri, kamar yanda yana daga cikin yancin daya bangaren wanda aka aika kuskure kansa ya karbi uzurin, ya mantar da abin da aka yi masa kai kace kwata-kwata ma bai faru ba. 

37- روي أن الإمام موسى بن جعفر× أحضر ولده ـ أولاده ـ يوماً فقال لهم: يا بني إني موصيك بوصية فمن حفظها لم يضع معها،  إن أتاكم آت فأسمعكم فالإذن اليمنى مكروه، ثم تحول إلى الأذن اليسرى فاعتذر وقال: لم أقل شيئاً، فاقبلوا عذره.

An rawaito daga Imam Musa Ibn Jafar (a.s) wata ya tattaro `yayansa sai ya ce musu: ya ku `dana hakika ina maka wasicci da wata wasiyya duk wanda ya kiyaye ta ba zai taba bat aba tare da ita, idan wani ami zuwa ya zo ya jiyar da ku kunnen dama makaruhi, sannan ya juya ya zuwa kunnen hagu ya nemi uzuri ya ce: ni ban ce komai bako karbi uzurinsa.

Ina cewa: wannan yana daga masadik din afuwa, ta yiwu ya kasance mukaddimar hakanm idan kana son ka san mukami da girman afuwa da abin da yayi kama da haka daga godaddun siffofi, ka dubi abin da ya zo daga hadisai masu daraja daga lada mai girma da sakamako gwaggwaba da ya doru kan haka, sannan daga sanin ma’aluli kake iya sanin illa, kamar yanda yake a burhanul Inni

38- ففي الحديث الشريف: إذا كان يوم القيامة، نادى منادٍ: من كان أجره على الله فليدخل الجنّة، فيقال: من هم؟ فقال: العافون عن الناس يدخلون الجنّة بلا حساب.

Daga hadisi mai daraja: idan ranar lahira ta kasance, mai kira zai yi kira: duk wanda ladansa ya kasance kan Allah to ya zo ya shiha aljanna, sai ace: su wane ne? sai ya ce masu yiwa mutane afuwa zasu shiga aljanna ba tare da hisabi ba.

Bai buya ba cewa afuwa tana gasgatuwa cikin abin da ya kasance gareka sauki da zabi cikin ukuba daga wand aya zalunceka, musammam ma idan ka samu iko kansa.

39- عن أمير المؤمنين×، قال: (وأمّا الرخصة التي صاحبها فيها بالخيار، فإنّ الله تبارك وتعالى: رخّص أن يعقاب العبد على ظلمه، فقال الله تعالى: {وَجَزَاءُ سَيِّئَةٍ سَيِّئَةٌ مِثْلُهَا فَمَنْ عَفَا وَأَصْلَحَ فَأَجْرُهُ عَلَى اللَّهِ إِنَّهُ لا يُحِبُّ الظَّالِمِينَ} (سورة الشورى: 40)  وهذا هو فيه بالخيار إن شاء عفى وإن شاء عاقب.

An karbo daga Sarkin muminai Ali (a.s) ya ce: amma saukakewa wacce ma’abocinta yake da zabi cikin yinsa, lallai Allah tabaraka wa ta’ala: ya saukaka daga yiw abawa ukuba kan zaluncinsa, sai Allah ta’ala: (sakamakon mummuna mummuna misalinta duk wanda yayi afuwa ya gyara tabbas ladansa na gurin Allah lallai Allah baya son Azzalumai) kanada zabi idan kaso ka yafe idan kaso yi ukuba

40- قال إمامنا الناطق جعفر بن محمد ^: (إنّه ليعرض لي صاحب الحاجة، فبادر إلى قضائها مخافة أن يستغنى عنها صاحبها، ألا وإن من مكارم الدنيا والآخرة في ثلاثة أحرف من كتاب الله: {خُذِ الْعَفْوَ وَأْمُرْ بِالْعُرْفِ وَأَعْرِضْ عَنِ الْجَاهِلِينَ} سورة الأعراف: 199)، وتفسيره: أن تصل من قطعك، وتعفو عمّن ظلمك، وأن تعطي من حرمك.

Imamin mu mai Magana Jafar Ibn Muhammad (a.s) ya ce: (hakika mabukaci yak an zuwa wurina sai in yi sauri in bashi bukatarsa don godin kada yayi sauri ya fasa ya wadatu daga tambayata, ku sani lallai yana daga dabi’un daraja na duniya da lahira cikin haruffa uku daga littafin Allah (ka riki afuwa kayi umarni da kyakkyawa ka kauracewa jahilai) bayaninsa wannan aya shi ne ka sadar da zumunci ga wanda ya yanke shi daga gareka, kayi afuwa daga wanda ya zalunceka, kayi kyauta daga wanda yayi maka rowa.

قال أمير المؤمنين×: (أشرف خصال الكرم : غفلتك عما تعلم.

Sarkin muminai Ali (a.s) ya ce: mafi daukakar karamci: ka gafalta daga abind aka sani.

وقال ×: أولى الناس بالعفو أقدرهم على العقوبة. وإذا قدرت على عدوك فاجعل العفو شكراً للقدرة عليه.

Amincin Allah ya tabbata a gare shi ya ce: mafi cancantar mutane da yin afuwa shin mafi samun ikon su kan yin ukuba, idan ka samu dama da iko kan makiyinka to ka sanya afuwa ta kasance godiya kan ikon kansa.

41- وقال×: (عاتب أخاك بالإحسان إليه، وأرد شره بالأنعام عليه).

Amincin Allah ya tabbata a gare shi ya ce: ka zargi dan’uwanka da ihsaninka kans, ka kwararar da sharrinsa da yi masa ni’ima kansa.

42- وكان× يقول: متى أشفي غيظي إذا غضبت أحين أعجز عن الانتقام، فيقال لي: لو صبرت أم حين أقدر عليه، فيقال لي: لو غفرت.

Amincin Allah ya tabbata a gare shi ya kasance yana cewa: yaushe zan huce haushina idan na fusata? Shin lokacin dana gaza daga daukar fansa, sai ace da kayi hakuri, ko kuma dai lokacin da na ke da iko, sai ace mini da dai kayi gafara.

Ayi taka tsantsan ayi taka tsantsan kamar yanda Zaki yake taka tsantsan. Kamar yanda kububuwa mai guba ke taka tsantsan.

43- قال×: شدّة الغضب تغيّر المنطق، وتقطع مادة الحجة، وتفرق الفهم، فمن يغضب بتغير كلامه ومنطقه، ومن الأحسن إلى الحسن، ومن الحسن إلى السيء، ومن السيء إلى الأسوء، وإذا أراد أن يحتجّ مع الآخرين ويقيم الحجة, فإنّه عند الغضب تنقطع مادة الحجة، وأساسها، إذ الحجة في العقل، والغضوب يفقد القوة العاقلة، أو تتغلب عليها قوة الغضب، كما لا يمكنه أن يستجمع فهمه في القضايا، بل يتفرق ويتشتت فهمه، ممّا يسقطه في المجتمع، وتظهر عيوبه، ويكون ذليلاً عند الناس. وفي أعين العقلاء، وأمّا إذا تحلّم وكظم غيظه، ثم حلم وعفى بصفح جميل،  فإنّه ينال العزة في الدنيا والآخرة.

Amincin Allah ya kara tabbata a gare shi ya ce: tsananin fushi yana canja tunani, yana yanke madar hujja, yana daidaita fahimta, duk wanda ya fusata maganarsa da tunaninsa suna canjawa, daga mafi kyawu ya zuwa mai kyau, daga mai kyau ya zuwa mai muni, daga mai muni ya zuwa mafi munana, idan ya so kafa hujja tare da wasu ya tsayar da dalili, lallai yayin fusata sinadarin hujjar da asasinta zai yanke, domin ita hujja da hankali take, shi kuma mai fushi yana rasa hankalinsa, ko kuma fushi yayi galaba kansa, kamar yanda bai iya samun damar tattaro fahimtarsa cikin batutuwa, bari dai duk fahimtarsa zata rikirkice da warwatse, abind azai zubar da kimarsa cikin jama’a, aibobinsa su bayyana, ya zama kaskantaccea idon mutane da idon ma’abota hankali, amma idan ya daure yayi hakuri ya danne fushinsa, yayi afuwa da kau da kai mai kyawu, lallai zai samu izza a duniya da lahira.

44- قال×: (لا عزّ أنفع من الحلم، ولا حسب أنفع من الأدب، ولا نسب أوضع من الغضب، فإن الغضب يجعل الإنسان الشريف صاحب الحسب والنسب وضيعاً في المجتمع ويحتقر ولا يحترم من نسبه وحسبه.

Amincin Allah ya kara tabbata a gare shi ya ce: babu wata izza mafi amfani daga hakuri, babu wani matsayi mafi amfani daga ladabi, babu wata nasaba mafi wulakanta daga fushi, lallai shi fushi yana mayar da mutum mai daraja ma’abocin matsayi da nasaba ya zuwa wulakantacce cikin jama’a ba za a dinga girmama shi tare da nasabarsa da matsayinsa.

45-a karhe wanda bashi ne karshen magana b azan kawo muku wata riwaya daga cikin riwayoyi masu daraja wacce take siffanta fushi da danne shi da wani abu na zahiri da ake iya tabawa, hakan yana zuwa ne daga babin siffantawa d ata dace da hankali ga abu na zahiri na kusa-kusam sakamakon ya fi tasiri cikin zukata, lallai galibin mutane rayuwa tafi imani da abu na zahiri da suke iya gani da ji da tabawa koma bayan fusga ya zuwa abu na badini na ma'anawiya, daga cikin tarbiya da koyarwa da yafi tasiri shi ne wanda ya kasance cikin buga misali da ab abubuwa na zahiri da batutuwan da mutane suke gogayya da su cikin rayuwarsu ta yau da gobe, wadancan misalsalan da muke bbuga su ga mutane tsammaninsu sa hankaltu su kuma karu da su cikin hankali da ilimi da tunani, abin da ya fi dacewa shi ne yayin da muke karanto wadannan hadisai da suke kusantowa da abin da hankali ke iya tsinkaya ya kuma fahimce shi shi ne cewa mu zurfafa tunani mu lura, mu fadaka domin mu ga ne manufa da muradi da yake boye cikin misalsalan da kissoshin.

عيون أخبار الرضا×، والخصال، بسنده عن الهروي قال: (سمعت الرضا× يقول: أوحى الله عز وجل إلى نبي من أنبيائه إذا أصبحت فأوّل شيء يستقبلك فكله، والثاني فإكتمه، والثالث فإقبله، والرابع فلا تؤيسه، والخامس فإهرب منه.

قال: فلما أصبح فاستقبله جبل أسود عظيم فوقف وقال: أمرني ربّي عزّ وجلّ أن آكل هذا، وبقي متحيراً ثم رجع إلى نفسه، فقال: إن ربي جل جلاله لا يأمرني إلا بما أطيق فمشى إليه ليأكله، فلما دنى منه صغر حتى انتهى إليه, فوجده لقمة فأكلها، فوجدها أطيب شيء أكله، ثم مضى فوجد طشتاً من ذهب، فقال: أمرني ربّي عز وجل أن أكتم هذا، فحفر له وجعله فيه، وألقى عليه التراب، ثم مضى فالتفت فإذا الطشت قد ظهر،فقال: قد فعلت ما أمرني رب عز وجل، فمضى فإذا هو بطير وخلفه بازيّ فطاف الطير حوله، فقال: أمرني ربي عز وجل أن أقبل هذا، ففتح كُمّه فدخل الطير فيه، فقال له البازيُّ: أخذت مني صيدي، وأنا خلفه منذ أيام، فقال: أمرني ربي عز وجل أن لا أُيس هذا، فقطع من فخذه قطعة فألقاها إليه، ثم مضى، فلما مضى فإذا هو بلحم ميتة منتن مدوّد ـ أي جعل فيه الدود ـ فقال: أمرني ربي عز وجل أن أهرب من هذا، فهرب منه.

فرجع فرأى في المنام كأنه قيل له: إنك قد فعلت ما أُمرت به، فهل تدري ماذا كان؟

قال: لا، قيل له: أمّا الجبل فهو الغضب، إن العبد إذا غضب لم يرى نفسه، وجهل قدره من عظيم الغضب، فإذا حفظ نفسه وعرف قدره، وسكت غضبه، كانت عاقبته كاللقمة الطيبة التي أكلها.

وأما الطشت فهو العمل الصالح إذا كتمه العبد وأخفاه أبى الله عزّ وجل إلا أن يظهره ليزيّنه به، مع ما يدّخر له من ثواب الآخرة.

وأمّا الطير، فهو الرجل الذي يأتيك بنصيحة فأقبله، وأقبل نصيحته.

وأما البازيّ فهو الرجل الذي يأتيك في حاجة فلا تؤيسه.

وأما اللحم المنتن فهي الغيبة فاهرب منه).

 

Uyunul Akbarul Rida (a.s) da Alkisal, da isnadin sa daga Harawi ya ce: ( na ji Rida (a.s) yana cewa: Allah yayi wahayi ya zuwa ga Annabi daga Annabawansa cewa idan ka wayi gari ka ci abin da ka fara kacibus  da shi na biyu kuma ka boye shi na uku kada ka debe masa tsammaninsa, na biyar ka guje masa.

Ya ce sai ya wayi gari sai bakin dutse ya tarbe shi sai ya tsaya ya ce: ubangijina Azza wa Jalla ya umarce ni da in ci wannan, sai ya tsaya gigice sai ya dawo cikin nutsuwarsa ya ce: hakika ubangijina girmansa ya girmama ba zai taba umarta ta ba face da abin da nake da iko kansa sai ya tunkari wannan dutse domin ya cinye shi, yayin da ya kusanto shi sai nya kankan ce lokacin da ya tuke gaban dutsen sai ya ashe lomar tuwo ce sai ya cinye ta, ya sameta maf dadin abu da ya ci, sannan yayi gaba ya tafi sai ya ga wani kwano daga kirar zinariya, sai ya ce: ubangijina Azza wa Jalla ya umarceni in boye wannan, sai ya tona kasa binne shi ciki, sannan yayi gaba ya waiwayo sai ya ga wannan kwano ya fito, sai ya ce ni dai na rigaya na aikata abin da ubangijina Azza wa Jalla ya umarceni, sai ya tafi sai ya gag a wani tsuntsu bayan tsuntsu shaho na biye da shi sai ya dinga kewaya shi, sai ya ce: ubangijina Azza wa Jalla ya umarceni in fuskanci wannan, sai ya bude aljihun hannun rigarsa sai tsuntsun ya shiga sai Shaho ya ce ka dauke mini abin farauta ta alhalin tsahon kwanaki ina farautar kama shi, sai ya ce: ubangijina Azza wa Jalla ya umarceni da kada in debe tsammani daga wannan, sai ya dan gutsiro wani gutsire daga cinyarsa ya wurga masa, sannan ya tafi, yayin da ya tafi sai kawai ga wani mushen nama yana wari tsutsa duk ta baibaye shi-sai ya ce ubangijina Azza wa Jalla ya umarceni in gujewa wannan, sai ya gudu daga gare shi.

Sai ya dawo sai cikin mafarki ya ga kamar an ce masa: lallai kai ka aikata abin da aka umarceka, shin ko kasan menene ya kasance?

Sai ya ce: a a, sai aka ce masa: amma wannan dutse lallai shi ne fushi, lallai idan bawa yayi fushi baya ganin kansa ya jahilci matsayinsa daga girmamar fushi, idna ya kiyaye kansa ya san darajar kansa, fushinsa ya tausasa, karshensa zai kasance kamar daddadar loma wacce ya cinye ta.

Aka ce masa amma wannan kwano shi ne aiki nagari idan bawa ya binne shi ya boye shi Allah sai yaki har sai ya bayyanar da shi domin yayi masa ado da shi, tare da abin da yayi masa tanadi daga ladan lahira.

Amma wannan tsuntsu shi ne mutumin da yake zo maka da nasiha saboda haka ka karbe shi ka kuma karbi nasiharsa.

Amma wannan Shaho shi ne mutumin da yake zuwa wajenka da bukata kada ka debe masa tsammani.

Amma wannan nama mai wari to shi gulma ce ka guje daga gareta.

Ku fadaka yaku ma'abota hankula da basira, kuyi taka tsantsan daga fushi da mai yawan ruguzawa, lallai shi daga wuta yake, sai dia cewa tare da kwankwade shi danne shi da kallafawa kai yin hakuri da hakuri da juriya da afuwa da kau da kai mai kyawu yana kasance mafi da`din da`da`da loma mai saukin hadiya abin sha daga dada`dan ruwa ma'ana ce da bata kafewa, wurin Allah muke neman taimako, babu tsimi babu dabara sai da Allah madaukaki mai girma.

46ـ قال الإمام الصادق ×: الحلم سراج الله يستضيء به صاحبه إلى جواره، ولا يكون حليماً الا المؤيد بأنوار الله، وبأنوار المعرفة والتوحيد.

Imam Sadik (a.s) ya ce: hakuri fitila ce da ma'abocinta ke haskaka makocinsa da ita, babu mai kasancewa ma'abocin hakuri face wanda Allah ya karfafe shi da haskensa, da hasken ma'arifa da tauhidi.

Shi hakuri na kewayawa kan fuskoki biyar:

1-da ya kasance mabuwayi sai ya kaskantu.

2-ko kuma yayi kira zuwa gaskiya sai shi a zalunce shi cikinta.

3- ko kuma ya kasance mai gaskiya sai a tuhume shi.

4-ko kuma a cutar da shi ba tare da ya aikata wani laifi ba.

5-ko kuma ya nemi gaskiya amma su sai su saba masa.

Idan ka baiwa dukkaninsu hakkinsu to lallai ka dace da dai, ka kishiyanci wawa da kau da kai daga gare shi da kin bashi amsa, mutane zasu kasance mataimakanka, sabida duk wanda ya kula wawa ya bashi amsa to lallai ya bawata kansa lokaci ne kawai.

قال رسول الله’ : (مثل المؤمن مثل الأرض، منافعهم منها وأذاهم عليها، ومن لا يصبر على جفاء الخلق لا يصل إلى رضا الله تعالى، لأن رضى الله مشوب بجفاء الخلق)، وحكي أن رجلاً قال لأحنف بن قيس: إياك أعني قال: وعنك أعرض.

Manzon Allah (s.a.w) ya ce: (misalin mumini misalin kasa ce, amfaninsu daga gareta yake cutarwarsu kanta yake, duk wanda baya hakuri kan jafa'in mutane ba zai cimma yardar Allah ta'ala ba, saboda ita yardar Allah haustine take da jafa'in mutane).

An hakaito cewa wani mutum ya cewa Ahnaf Ibn Kaisu: da kai nake magana, shi kuma ya ce masa kai na kau da kai kanka.


[1] Biharul-Anwar:68:404

[2] Biharul-Anwar:68 sh 415

[3] Biharul-Anwar:68 sh420

[4]-Biharul-Anwar:68 sh408

[5] -Biharul-Anwar:68 sh408

[6] -Biharul-Anwar:68 sh 408