■ MUKAMI NA FARKO: CIKIN ZARGIN FUSHI DAGA LITTAFIN ALLAH DA SUNNA
■ FUSHI MABUDIN DUKKANIN SHARRI
■ MUKAMI NA BIYU
■ CIKIN HAKIKANIN FUSHI
■ KASHE-KASHEN MUTANE CIKIN FUSHI
■ MUKAMI NA UKU: SABUBBAN FUSHI A WURIN MUTUM
■ MUKAMI NA HUDU: ALAMOMIN FUSHI
■ MUKAMI NA BIYAR: TA YAYA ZAMU MAGAN CE MATSALAR FUSATA
■ MAGAN CE MATSALAR FUSHI A ILIMAN CE DA
■ AIKACE
■ HAKURI DA DANNE FUSHI DA YIN AFUWA DAGA CIKIN KUR’ANI MAI GIRMA
■ MUKAMI NA SHIDA CIKIN HAKURI DA DAURIYA
■ MUKAMI NA BAKWAI CIKIN DANNE FUSHI
■ MUKAMI NA TAKWAS: FALALAR HAKURI CIKIN DAUSAYIN RIWAYOYI
■ MUKAMI NA GOMA: NASIHOHI DA KISSOSHI KAN DANNE FUSHI DA KUMA YIN HAKURI
■ KOMAWA KAN BAYANIN FARKO
■ MUKAMI NA GOMA SHA BIYU: CIKIN BANGARORIN ILIMI NA DABAN CIKIN MAGAN CE MATSALAR FUSHI
■ MUKAMI NA GOMA SHA UKU:
■ MUKAMI NA GOMA SHA HUDU: CIKIN BAYANIN MIKDARIN DA YA HALASTA A YI FUSHI DA HUCE HAUSHI CIKINSA CIKIN BAYANI SINFOFIN MUTANE A CIKIN FUSHI
- KIBIYOYIN RADDI KAN WUYAN WAHABIYAWA
- CIKIN HALLARAR ALHERI
- HUJJOJIN HALASCIN YIN TAKIYYA A MUSLUNCI DAGA MAHANGAR MANYAN MALAMAI GUDA BIYU
- FARKAR DA MAI BACCI CIKIN TABBATUWAR GANIN IMAM KA'IM A.S
- ALAMOMIN ANNABI CIIKIN KUR'ANI MAI GIRMA
- HAKURI DA FUSHI
- Bada'u tsakanin hakika da kagen makiya
- FALALAR DAREN LAILATUL KADRI
- WAHABIYANCI A TSAKANIN GUDUMA DA
- HASKEN SASANNI CIKIN SANIN ARZIKI
- AQIDUN MUMINAI
- FATIMA TAGAR HASKAYE
- SIRRIKAN AIKIN HAJJI DA ZIYARA
- TARBIYYAR IYALI A MAHANGAR ALKUR'ANI DA AHLULBAITI
Daga cikin Karin maganar larabawa:
ka zama me hakuri sai ka kasance shugaba.
Ahnaf ya ce: na haneku da biyewa ra'ayin gabaye wawaye, sai suka ce: menene ra'ayin gabaye? Sai ya ce: wadanda suke ganin kau da kai da yin afuwa matsayin aibu da abin kunya.
An cewa Mi'anu Ibn Za'idatu: tuhuma da zunubi yana daga shugabanci? Sai ya ce: a a sai dai cewa mafi kyawun abin da yake kasance shi ne yin afuwa daga yayi laifi, macetansa suka karanta, bai samu mai taimako ba.
An rawaito cikin ba'arin labarurruka cewa wani Sarki daga Sarakuna yayi umarni da a dafa masa abinci, sannan ya gayyaci wasu mutane daga `yan fadarsa yayinda aka mikar da shimfidar abinci sai hadiminsa ya taho yana rike ta tiren abinci, yayin da ya kusanto kusa da Sarki sai kwarjinin Sarki ya dimauta shi har ta kai da yayi tuntube sai miyar ta dank an tufafin Sarki, sai Sarki ya bada umarni a sare kan wannan hadimi nasa don ya kasance diyyar kan gangancin da yayi na zuba miya kan Sarki.
Sai aka ce masa: kaiconka menene haka kuma?
Sai ya ce: ya kai wannan Sarki kadai na aikata haka saboda kare mutuncinka a cikin tarihi don gudun kada mutane idan sun ji labarin laifina da akansa ka kasheni suce ya kashe kan karamin laifin da bai kai ya kawo ba kuma bai cutar da shi ba sannan shi wannan bawa kuskure ne ya aikata, kuma ba da niyya ya aikata wannan laifi ba, sai ya zama an zargeka da aikata mummunan zalunci da danniya, sai ka aikata wannan babban laifi domin ka samu uzuri cikin laifi ka daukewa kanka zargi.
Ya ce: sai Sarki ya dan sunkuyar da kansa kadan sannan ya dago ya kalleshi ya ce: ya mai mummunan aiki ya mai kyawun uzuri, hakika mun yafe mummunan aikinka da laifinka mai girma sakamakon kyawunta uzurinka, ta fi ka `yantu don neman yardar Allah ta'ala.
An hakaito cewa wani mutum ya kera jabun takarda da take dauke da rubutun Fadalu Ibn Rabi'u, da ta kunshi cewa yab bashi dinare dubu, sannan ya zo da ita wajen wakilin Fadalu, yayinda wakilin ya duba ta bai samu shakku kan cewa lallai rubutun Fadalu bane, sai ya fara tattaro masa dinare dubu, kwatsam sai ga Fadalu ya zo domin ya tattauna da wakilinsa kan wani al'amari mai muhimmanci, yayinda ya zauna sai wakilin ya bashi labarin batun wannan mutum da ya kawo takardar karbar kudade ya mika mishi wannan takarda, sai Fadalu ya duba ta sannan ya kalli fuskar wakilinsa, sannan ya ce masa: shin kasan menene ya sanya ni zuwa wurinka a wannan lokaci? Sai ya ce: ban sani ba, sai ya ce masa: domin ina tasheka domin ka gaggauta baiwa wannan wanda ya zo da takardar kudaden da aka rubuta cikin wannan takarda.
Da jin haka sai ya gaggauta tattaro kudaden ya mikawa wannan mutumi shiko ya karba yana mai mamaki, sai Fadalu ya kalle shi ya ce masa: ka kwantar da hankalinka ka tafi sha'aninka cikin aminci kan ranka, sai wannan mutumi ya sunbaci hannunsa, ya ce ka suturta ni kaima Allah ya suturta ka a duniya da lahira, ya juya yayi tafiyarsa.