Al'ummar Jahiliya gabanin aiko da Annabtar cikamaki

ababen zargi:

1-inkarin aiko da Annabi da imani da lahira, ma'ana inkarin makoma da da'awar baki dayan Annabawan Allah (a.s) da'awarsu ta kasance kan tabbatar da asalai guda biyu na tushe cikin rayuwar mutane, sune mafara wanda shi ne imani da Allah da `dayanta shi da kuma imani da ranar lahira:

 (وَقالُوا إِنْ هِيَ إِلّا حَياتُنَا الدُّنْيا وَما نَحْنُ بِمَبْعُوثينَ )[1] .

Kuma suka ce ba komai bace face wannan rayuwar tamu a duniya mu ba za a tashemu ba.

(بَلْ قالُوا مِثْلَ ما قالَ الاْوَّلُونَ * قالُوا أَإِذا مِتْنا وَكُنّا تُراباً وَعِظاماً أَإِنّا لَمَبْعُوثُونَ * لَقَدْ وُعِدْنا نَحْنُ وَآباوُنا هذا مِنْ قَبْلُ إِنْ هذا إِلّا أَساطيرُ الاْوَّلينَ )[2] .

 Bari dai sun fadi misalin abin da na farko suka fadi* yanzu idan mun mutu mu ka zama turbaya da kasusuwa za a tashemu*hakika a gabani ammana alkawarn haka mu da iyayenmu ba komai bace face tatsuniyoyin mutanen farko.

2-Bautar gumaka:

 (أَ فَرَأَيْتُمُ اللّاتَ وَالْعُزّى وَمَناةَ الثّالِثَةَ الاْخْرى * أَلَكُمُ الذَّكَرُ وَلَهُ الاْنْثى * تِلْکَ إِذاً قِسْمَةٌ ضيزى * إِنْ هِيَ إِلّا أَسْماءٌ سَمَّيْتُمُوها أَنْتُمْ وَآباوُكُمْ ما أَنْزَلَ اللهُ بِها مِنْ سُلْطانٍ )[3] .

Shin kun ga Lata da Uzza da Manata ta ukunsu* shin kuna da `da namiji shi kuma da `diya mace* wannan rabo ne tauyayya* ba komai bace face sunaye da kuka kira su da su ku da iayayenku Allah bai saukar da dalili a kansu.\

3-alfahari da yawa gayya da wadata da ta'assubanci:

 (وَقالُوا لَنْ نُوْمِنَ لَکَ حَتّى تَفْجُرَ لَنا مِنَ الاْرْضِ يَنْبُوعاً * أَوْتَكُونَ لَکَ جَنَّةٌ مِنْ نَخيüلٍ وَعِنَبٍ فَتُفَجِّرَ الاْنْهارَ خِلالَها تَفْجيراً * أَوْتُسْقِطَ السَّماءَ كَما زَعَمْتَ عَلَيْنا كِسَفاً أَوْ تَأْتِيَ بِاللهِ وَالْمَلائِكَةِ قَبيلاً * أَوْيَكُونَ لَکَ بَيْتٌ مِنْ زُخْرُفٍ )[4] .

 Suka ce ba zamu taba imani da kai har sai ka bubbugar da idaniyar ruwa daga kasa* ko kuma wata gona daga Inibi da Dabino ta kasance gareka ka bubbugar da koramu karkashinta bubbugarwa* ko kuma ka fado mana da sama a kanmu kabukka kamar yanda kake rayawa ko kuma ka zo da Allah da Mala'iku banga-banga* ko kuma wani gida daga zinariya ya kasance gareka.

(وَقالُوا ما لِهذَا الرَّسُولِ يَأْكُلُ الطَّعامَ وَيَمْشي فِي الاْسْواقِ لَوْ لا أُنْزِلَ إِلَيْهِ مَلَکٌ فَيَكُونَ مَعَهُ نَذيراً * أَوْيُلْقى إِلَيْهِ كَنْزٌ أَوْ تَكُونُ لَهُ جَنَّةٌ يَأْكُلُ مِنْها)[5] .

 Suka ce wannan wanne irin Manzo yana cin abinci yana yawo a kasuwa da dai an saukar masa da wani Mala'ika sai ya kasance mai gargadi tare da shi* ko kuma ajefo masa taska ko kuma wata gona ta kasance gare shi da zai dinga ci daga gareta.

(وَقالُوا نَحْنُ أَكْثَرُ أَمْوالاً وَأَوْلاداً وَما نَحْنُ بِمُعَذَّبينَ * قُلْ إِنَّ رَبِّي يَبْسُطُ الرِّزْقَ لِمَنْ يَشاءُ وَيَقْدِرُ وَلكِنَّ أَكْثَرَ النّاسِ لا يَعْلَمُونَ * وَما أَمْوالُكُمْ وَلا أَوْلادُكُمْ بِالَّتي تُقَرِّبُكُمْ عِنْدَنا زُلْفى )[6] .

Suka ce mune mafi yawan dukiya da `ya`ya mu ba za ai mana azaba ba* ka ce ubangijina yana shimfida arziki ga wanda ya so yana kuma kuntatawa sai dia cewa mafi yawan mutane basa sani* dukiyoyinku da `ya`yan basu sune zasu baku kusanci a wurinmu ba.

4-babbar jarrabawa mai tsanani ga mata 

 (وَإِذا بُشِّرَ أَحَدُهُمْ بِالاْنْثى ظَلَّ وَجْهُهُ مُسْوَدًّا وَهُوَ كَظيمٌ * يَتَوارى مِنَ الْقَوْمِ مِنْ سُوءِ ما بُشِّرَ بِهِ أَيُمْسِكُهُ عَلى هُونٍ أَمْ يَدُسُّهُ فِي التُّرابِ أَلا ساءَ ما يَحْكُمُونَ )[7] .

 Idan aka yi wa dayansu albishir da samun `ya mace sai fuskarsa ta turbune bakir kirin yana dannewa* yana buya cikin mutane sakamakon mugunyar abin da akai masa abishir da shi sun yanzu zai rike cikin wulakanta ko kuma zai binne cikin turbaya abin da suke hukuntawa ya munana.

(وَإِذَا الْمَوْوُدَةُ سُئِلَتْ * بِأَيِّ ذَنْبٍ قُتِلَتْ )[8] .       

 Idan wacce aka binneta da ranta akai tambaya kanta* da wanne laifi ne aka kasheta.

5-jama'ar da kasuwanci da dukiya sune madogararsu:

 (وَإِذا رَأَوْا تِجارَةً أَوْ لَهْواً انْفَضُّوا إِلَيْها وَتَرَكُوکَ قائِماً)[9] .

Idan suka ga kasuwa ko wargi sai su watse su barka kai kadai a tsaye.

(لاِيلافِ قُرَيْشٍ * إيلافِهِمْ رِحْلَةَ الشِّتاءِ وَالصَّيْفِ )[10] .

 Al'adar Kuraishawa *al'adarsu kan tafiya lokacin hunturu da bazara.

6-riba tana ninnikawa cikin sa:

 (الَّذينَ يَأْكُلُونَ الرِّبا لا يَقُومُونَ إِلّا كَما يَقُومُ الَّذي يَتَخَبَّطُهُ الشَّيْطانُ مِنَ الْمَسِّ )[11] .

 Wadanda suke cin riba basa mikewa face yanda wanda Shaidan ya dimauta shi daga shafa.

(لا تَأْكُلُوا الرِّبَوا أَضْعافاً مُضاعَفَةً )[12] .

Kada kuci riba ninkin ba ninki.

7-giya da caca suna yaduwa cikin sa:

 (يَسْئَلُونَکَ عَنِ الْخَمْرِ وَالْمَيْسِرِ قُلْ فيهِما إِثْمٌ كَبيرٌ وَمَنافِعُ لِلنّاسِ وَإِثْمُهُما أَكْبَرُ مِنْ نَفْعِهِما)[13] .

Suna tambayarka dangane da giya da caca ka ce musu cikin su akwai babban laifi da kuma amfani ga kuma amma laifin da yake cikin su yafi girmama daga amfaninsu. 

(يا أَيُّهَا الَّذينَ آمَنُوا إِنَّمَا الْخَمْرُ وَالْمَيْسِرُ وَالاْنْصابُ وَالاْزْلامُ رِجْسٌ مِنْ عَمَلِ الشَّيْطانِ فَاجْتَنِبُوهُ )[14] .

 Yaku wadanda kuka yi imani kadai dai giya da caca da refu da kiban kuri'u kazanta ne daga aikin Shaidan ku kaurace mata.

Misalin wannan jama'a ta Jahiliya da ta ginu kan Kabilanci da ta'assubanci da bin sawun iyaye makauniyar bin sawu, lallai sun kasance masu bautar gumaka da inkarin ranar lahira sannan kuma alfahari ya shagaltar da su, suna kuma binne `ya`ya mata cikin turbaya, son dukiya da fifita da cin riba ya mamaye su, ayyukan fasadi daga zina da caca da refu sai suka bi sawun tattakin Shaidan ma'auni ya juya a wurinsu, ya zama mummunan abu shi ne kyakkyawa gare su kyakkyawa kuma shi ne mummuna, sai Allah ya aiko Annabi Muhammad (s.a.w) zuwa gare su hakika Ibrahim Kalilul Rahman da Isa `dan Maraym sun yi busharar zuwansa , ya zamanto cikamakin Annabawa da Manzanni ma'abocin tafkin Kausara ranar lahira:

Shi ne addu'ar da Annabi Ibrahim Kalilul Rahman (a.s) kamar ya fada:-1

(رَبَّنا وَابْعَثْ فيüهِمْ رَسُولاً مِنْهُمْ يَتْلُوا عَلَيْهِمْ آياتِکَ وَيُعَلِّمُهُمُ الْكِتابَ وَالْحِكْمَةَ وَيُزَكِّيهِمْ )[15] ».

Ya ubangijinmu ka aiko da Manzo cikin su daga gare su da zai karanta musu ayoyin ka ya koya musu littafi da hikima ya tsarkake su.

2-Busharar Isa Almasihu (a.s)

 (وَإِذْ قالَ عيسَى ابْنُ مَرْيَمَ يا بَني إِسْرائيüلَ إِنِّي رَسُولُ اللهِ إِلَيْكُمْ مُصَدِّقاً لِما بَيْنَ يَدَيَّ مِنَ التَّوْراةِ وَمُبَشِّراً بِرَسُولٍ يَأْتي مِنْ بَعْدِي اسْمُهُ أَحْمَدُ فَلَمّا جاءَهُمْ بِالْبَيِّناتِ قالُوا هذا سِحْرٌ مُبينٌ )[16].

 Yayin da Isa `dan Maryam ya ce ya `ya`yan Isra'ilu hakika ni Manzo ne gareku mai gasgata abin da yake gabanku daga Attaura mai bushara da wani Manzo da zai bayyana sunansa Ahmad yayinda ya zo da hujjoji sai suka ce sihiri mabayyani.

3-hakika shi ne cikamakin Annabawa da Manzanni:

 (ما كانَ مُحَمَّدٌ أَبا أَحَدٍ مِنْ رِجالِكُمْ وَلكِنْ رَسُولَ اللهِ وَخاتَمَ النَّبِيِّينَ )[17] .

 Muhammad bai kasance baban kowa daga mazajenku ba sai dai cewa shi Manzo kuma cikamakin Annabawa.

(الْيَوْمَ أَكْمَلْتُ لَكُمْ دينَكُمْ وَأَتْمَمْتُ عَلَيْكُمْ نِعْمَتي وَرَضيتُ لَكُمُ الاْسْلامَ ديناً)[18] .

 .Yau ne na kammala muku addininku na cika ni'imata kanku na yardar muku da muslunci addini

Muslunci a Kur'ani a wani lokacin ya kan zuwa da gamammiyar ma'ana, wanda shi ne sallamawa ga Allah matsarkaki shi ne abin da baki dayan Annabawa suka zo da shi tun daga

Adamu har zuwa cikamakin Annabawa kamar yanda ya zo cikin fadin sa madaukaki:

(إِنَّ الدِّينَ عِنْدَ اللهِ الاْسْلامُ )[19]  

Muslunci ne kadai addini a wurin Allah.

A wani lokacin kuma ya kan zuwa da kebantacciyar ma'ana wacce yake kishiyar Yahudanci da Nasaranci daga addinan sama bayan shafe su da zuwan addinin muslunci

(وَمَنْ يَبْتَغِ غَيْرَ الاْسْلامِ ديناً فَلَنْ يُقْبَلَ مِنْهُ )[20] .

 .Duk wanda ya nemi wani addini komabayan muslunci ba a karba daga gare shi ba

4-lallai shi ne ma'abocin tafkin nan da za a gangara gare shi:

(إِنّا أَعْطَيْناکَ الْكَوْثَرَ * فَصَلِّ لِرَبِّکَ وَانْحَرْ)[21] .

 Lallai mun baka alheri mai tarin yawa*kayi salla domin ubangijinka ka kuma soke abin yanka.

Kalmar Kausar tana dauka wasu ma'anoni daban-daban daga cikin akwai Fatima Azzahra shugabar mata (a.s) kamar yanda ya zo daga hadisan bangarori biyu Sunna da Shi'a

5-ambatonsa (s.a.w) a cikin litattafan sama da suka gabata 

 (وَلَمّا جاءَهُمْ رَسُولٌ مِنْ عِنْدِ اللهِ مُصَدِّقٌ لِما مَعَهُمْ نَبَذَ فَريقٌ مِنَ الَّذينَ أُوتُوا الْكِتابَ كِتابَ اللهِ وَراءَ ظُهُورِهِمْ كَأَنَّهُمْ لا يَعْلَمُونَ )[22] .

Yayin da Manzo ya zo musu daga wurin Allah yana mai gasgata abin da yake gare su sai wani bangare daga wadanda aka baiwa littafi suka yi wurgi da littafin Allah bayansu kai ka ce basu sani ba. 

(الَّذينَ يَتَّبِعُونَ الرَّسُولَ النَّبِيَّ الاْمِّيَّ الَّذي يَجِدُونَهُ مَكْتُوباً عِنْدَهُمْ فِي التَّوْراةِ وَالاْنْجيلِ يَأْمُرُهُمْ بِالْمَعْرُوفِ وَيَنْهاهُمْ عَنِ الْمُنْكَرِ وَيُحِلُّ لَهُمُ الطَّيِّباتِ وَيُحَرِّمُ عَلَيْهِمُ الْخَبائِثَ وَيَضَعُ عَنْهُمْ إِصْرَهُمْ وَالاْغْلالَ الَّتي كانَتْ عَلَيْهِمْ فَالَّذينَ آمَنُوا بِهِ وَعَزَّرُوهُ وَنَصَرُوهُ وَاتَّبَعُوا النُّورَ الَّذي أُنْزِلَ مَعَهُ أُولئِکَ هُمُ الْمُفْلِحُونَ )[23] .

Sune wadanda suke bin Manzo Ummiyu wanda suke samunsa rubuce wurinsu cikin Attaura da Linjila yana umartarsu da kyakkyawa yana hana su munkari yana halasta musu tsarkaka yana haramta musu munana yana kuma dauke nauyi da barin su da sasarin da ya kasance kansu wadanda suka yi imani da shi suka taimake shi da tallafa masa suka kuma bi hasken da aka saukar tare da shi sune rabautattu.

A bayyane yake lallai Kalmar Risala (sako) tana daga ma'ana da take jingina da ta dogara da surantata da hankalta kan wasu ma'anonin daban ma'ana (Mursil) mai aike da (Rasul)  `dan aike, shi sakon muslunci saukakakke da ya kasance daga Allah ta hannun Manzo mafi girma Muhammad (s.a.w)  ya zuwa baki dayan mutane har zuwa ranar lahira, Allah ya aiko shi da shiriya da addinin gaskiya domin ya bayyana baki dayan addini ko da kuwa Mushrikai basa so, akwai karfaffar dangantaka da alaka tsakanin girmamar Sakon da girmamar `dan sakon, kamar misalin mai `daga karfe nauyi cikin duniyar gasar wasannin motsa jiki, kamar yanda mai `daga nauyayyan karfe ya kasance Jarumin duk duniya  da ya tarbiyantar da jikin sa don `daukar nauyayyan karfe , lallai na nufin cewa shi yana `daukar Kilo mai tarin yawa da nauyi fiye da waninsa, babu kwantankwacinsa  a fadin duniya.

Haka zalika Manzo mafi girma (s.a.w) shima babu kwatankwacinsa cikin ilimin Allah tsakankanin halittu, domin ya `daukin wannan sako mai girma da ta wadatar da dukkanin sakwannin da suka daga sama da dukkanin litattafai da Suhufai takardun ubangiji wadanda aka saukarwa da Annabawa da Manzanni tun daga Adamu har zuwa Cikamakin su, lallai kamar yanda ya zo cikin hadisi mai daraja:

لله سبحانه (124 ألف ) نبياً، ولكلّ نبي (12) وصيّاً وخليفةً ووزيراً وإماماً للناس .

Allah yana da Annabawa guda 124000, kuma kowanne Annabi yana da Wasiyyai 12 Halifofi Jagorori ga mutane.

Kasancewa sakon muslunci yana jikkantuwa da bayyana cikin Manzon Allah (s.a.w) kamar yanda lokacin da aka tambayi A'isha dangane da `dabi'un sa wanda Allah ya yabeshi da su cikin fadin sa:

 (وَإِنَّکَ لَعَلى خُلُقٍ عَظيمٍ )[24]  قالت : كان خُلقه القرآن ،

Lallai kana kan `dabi'a mai girma.

Sai tace `dabi'unsa sun kasance Kur'ani.

Lallai wannan misaltuwa da jikkantuwa yana nuni ya zuwa girmamar Manzon Allah (s.a.w) kamar yanda daga girmamarsa ya kasance (ba da ban kai ba da ban halicci Falakai ba) shi Annabi Illa ne ta gaya ga duk wani abu komabayan Allah, haka zalika yana nuni kan girman sakonsa cewa kowannen su yana nuni zuwa ga girmamar dayan sakamakon kasancewa sakon da `dan sakon hakika ce guda daya daga Allah daya rak girman sa ya girmama.

Akwai bayyananniyar dangantaka tsakanin girmamar Manzon Allah (s.a.w) da girmamar sakonsa, dukkaninsu daga tajallin suna mai girma mafi girmama na Allah matsarkaki, tsarki ya tabbata ga ubangijina tare da gode masa.


[1] ()  الأنعام : 29.

[2] ()  المؤمنون : 81 ـ 83. راجع : هود: 7، الاسراء: 49 و98، الجاثية : 24.

[3] ()  النجم : 19 ـ 23. راجع : المائدة : 90، الأنبياء: 51 ـ 54، الشعراء: 71.

[4] ()  الاسراء: 90 ـ 93.

[5] ()  الفرقان : 7 ـ 8.

[6] ()  سبأ: 35 ـ 37. راجع : الزخرف : 31 ـ 32، التكاثر: 1 ـ 2.

[7] ()  النحل : 58 ـ 59.

[8] ()  التكوير: 8 ـ 9. راجع : الزخرف : 17.

[9] ()  الجمعة : 11.

[10] ()  قريش : 1 ـ 2.

[11] ()  البقرة : 275.

[12] ()  آل عمران : 120. راجع : البقرة : 276 و278، الروم : 39.

[13] ()  البقرة : 219.

[14] ()  المائدة : 90.

[15] ()  البقرة : 129.

[16] ()  الصف : 6.

[17] ()  الأحزاب : 4.

[18] ()  المائدة : 3.

[19] ()  آل عمران : 19.

[20] ()  آل عمران : 85.

[21] ()  الكوثر: 1 ـ 2.

[22] ()  البقرة : 101.

[23] ()  الاعراف : 157.

[24] ()  القلم : 4.