MIHWARI NA (2)

 

MANZO MAFI GIRMA (S.A.W) CIKIN MOTSIN AL'UMMA

Hakika Manzo mafi girma (s.a.w) ya sha wahalhalu kala-kala daga jahiltar matsayin da mukaminsa madaukaki cikin dukkanin marhalolin rayuwarsa wacce ya yi gogayya da su cikin harkar motsin al'ummar musulmi da muslunci, babu banbanci cikin kasancewa gabanin muslunci ko bayan aiko shi ne, bayan hijira ne ko gabaninta cikin rayuwarsa ne ko bayan wafatinsa (s.a.w) lallai daga duddugar wannan fakuwa ko kuma muce fakantuwa da gangan kan rashin saninsa wanda ya haifar da jahiltar girman matsayin Annabin rahama da mutumtaka da hakikanin saninsa kamar yanda yake a hakika shi ne ya haifar musu da ci baya da watsi da girmamarsu da girmansu mai tushe da cigabansu wanda ya mamaye duniya baki daya da falala da karamci da fannoni, su dawo su koma suna yakar junansu da rigimar Mazhabanci da Kabilanci wacce suka gado ta daga jahiliya farko, sai ya zama karfinsu yana tafiya suna fadawa cikin rashin nasara cikin fagagen cigaba da habbaka har lamarin ya kai ga baki barai daga waje suna mallakarsu wuyayensu suna mulkarsu suna zuwa suna kwashe dukiyarsu da arzikinsu suna shanye musu jini, suna kwashe ribar wahalhalun da suka sha, suna yin mulkin mallaka a garuruwansu suna rikarsu matsayin taguwar da zasu taka su hau ta kais u ga cimma burinsu da maslahohinsu da samun ikon yin mulki kan raunana a duniya baki dayada ko kowanne yanayi ne ya kasance raunana sun.

Al'umma ba ta samu dagawa da cigaba cikin kowacce marhala daga marhalolinta a tsahon zamanunnuka  ya zuwa ga fahimtar girman matsayin Manzo mafi girma (s.a.w) ballantana kwaikwayonsa da jikkantuwa da halayensa a zahiri cikin jama'a da bangarrorin al'umma da dabakokinta.

Wajibi kan kowanne musulmi ya san tarihin rayuwar Annabinsa da sunnoninsa da sirarsa mai haskaka da ayoyin rahama da tausayi da soyayya da nuna kauna, ya kuma san mu'ujizarsa madawwamiya wato Kur'ani mai girma, kai wajibi ma ya san wadannan Sahabbai wadanda suka abokance shi cikin gari da tafiye-tafiyensa, cikin dukkanin daurorin rayuwarsa sun kasance kamar inuwarsa, bari dai cikin kowanne hali da yanayi ya kasance kunne mai sauraronsa ba kowa bane sai Sarkin Muminai Ali (a.s) shi kamar yanda suke fada (aya ne daga ayoyin annabtarsa) kuma mu'uhijza ta biyu da take shiryarwa zuwa ga gaskiyar Annabtarsa da girman sakonsa, ta yanda wannan mu'ujiza ta yi rainnon mutum mai kima kamar Sarkin Muminai Ali (a.s).

Mai karatu cikin rayuwar Manzon Allah (s.a.w) zai hangi wasu mutane na kusa-kusa ya zuwa gare shi (s.a.w) bari dai zuwa ga Allah matsarkaki kamar misalin Ali (a.s) da Salmanul muhammadi wanda gameda shi Manzon Allah (s.a.w) yana cewa:   

 (سلمان منّا أهل البيت )

Salmanu daga garemu yake Ahlil-Baiti.

Da misalin su Abu Zar da Mikdadu da Yasir har ta kai gay a zo cikin hadisi mai daraja

ان الله ليشتاق إليهم ، وإن الجنّة لتشتاق إليهم[1] .

 Allah yana shauki zuwa gare su, lallai aljanna tana shaukinsu.

Kadai sun samu wannan matsayi da daraja sakamakon saninsu ga Manzon Allah (s.a.w) da ma'arifa jamaliya da kamaliya, basu taba bijire mas aba, kamar yanda ya kasance ba'arin abubuwan da ya tabbata da matakan da ya dauka, sakamakon imani da suke da shi kansa cewa shi (baya furuci da son rai sai abin da akai masa wahayi) dayansu bai fadi irin Kalmar wancan mutumin ba da a lokacin hallarar wafatin Annabi (s.a.w) yayin da Annabi ya nemi wadanda suka hallara a wurinsa da su nemo masa tawada da da alkalami da takardar da zai rubutu domin ya rubuta musu wani al'amari da idan sukai riko da shi ba zasu taba bata ba a bayans, sai wancan mutumi ya gano kudurin Manzon Allah (s.a.w) da cewa fa yana ishara ne zuwa hadisul Assaklaini: littafin Allah da tsarkakakkun tsatso Ahlil-baiti shugabansu Sarkin Muminai (a.s) lallai Manzon Allah(s.a.w) ya furta wannan hadisi a wurare masu tarin yawa

 (إني تارک فيكم الثقلين كتاب الله وعترتي أهل بيتي ما ان تمسّكتم بهما لن تضلّوا بعدي أبداً وانهما لن يفترقا حتّى يردا عليّ الحوض )

Lallai ni ian bar muku nauyaya guda biyu littafin Allah da tsatsona Ahlin gidana matukar koka yi riko da su ba zaku taba bat aba a bayana har abada kuma su biyu basu taba rabuwa da juna har sai sun gangaro gareni a tafki.

Wannan hadisi ne mutawatiri da bangarori biyu suka yi ittifaki kansa ma'ana Shi'a da Sunna, a wannan lokaci sai wancan mutumi ya ce: wai Annabi ya zautu yana cikin sururi wai ya tabu da zautuwa sakamakon zafin ciwo kamar gamagarin sauran mutane-wal ayazubillahi, ina zaka hada irin wannan mutumi da Salmanu da misalsalansa daga Sahabbai masu girma zababbu da Allah ya yarda da su?!

Babu shakka da kokwanto cewa kusanci da nesanci daga mutumtakar Manzon mafi girma (s.a.w) suna da tasiri mabayyani kan mutanen da suka fahimci Manzo a kebance, haka suna tasiri gamamme ga al'umma musulma, duk wanda ya kasance mai yn adalci bai cudanyu da jarrabuwa da makauniyar biyayyar iyaye ba bashi da ta'assubanci kuma kan lamarin Allah zargin mai zargi baya damunsa zai fahimci wadannan uzurai da dalilai na maudu'I zai kuma tafi tare da su kafada da kafada a mustawan nauyi da yah au wuyansa, zaka samu natijoji da nasarori suna sassabawa gurinsa da sassabawar ka'idodji da akidun da aka tabbatar da ingancinsu kan hasken Kur'ani da kuma makarantar Ahlil-Baiti amincin Allah ya tabbata gare su.