Manzo mafi girma (s.a.w) a cikin gidansa

 

121-matayensa uwayen Muminai ne:

 (النَّبِيُّ أَوْلى بِالْمُوْمِنينَ مِنْ أَنْفُسِهِمْ وَأَزْواجُهُ أُمَّهاتُهُمْ )[1] .

 Annabi shi ne mafi cancanta da Muminai daga kawukansu kuma matayensa uwayen Muminai.

122-tsarki da ma'asumancin mutanen cikin bargo:

 (إِنَّما يُريدُ اللهُ لِيُذْهِبَ عَنْكُمُ الرِّجْسَ أَهْلَ الْبَيْتِ وَيُطَهِّرَكُمْ تَطْهيراً)[2] .

Kadai Allah yana nufin tafiyar da dukkanin datti daga barinku Ahlil-bati kuma ya tsarkakeku tsarkakewa.

123- Hususiyar gidan Annabta: 

 (وَإِنْ كُنْتُنَّ تُرِدْنَ اللهَ وَرَسُولَهُ وَالدّارَ الآْخِرَةَ فَإِنَّ اللهَ أَعَدَّ لِلْمُحْسِناتِ مِنْكُنَّ أَجْراً عَظيماً * يا نِساءَ النَّبِيِّ مَنْ يَأْتِ مِنْكُنَّ بِفاحِشَةٍ مُبَيِّنَةٍ يُضاعَفْ لَهَا الْعَذابُ ضِعْفَيْنِ وَكانَ ذلِکَ عَلَى اللهِ يَسيراً * وَمَنْ يَقْنُتْ مِنْكُنَّ للهِ وَرَسُولِهِ وَتَعْمَلْ صالِحاً نُوْتِها أَجْرَها مَرَّتَيْنِ وَأَعْتَدْنا لَها رِزْقاً كَريماً * يا نِساءَ النَّبِيِّ لَسْتُنَّ كَأَحَدٍ مِنَ النِّساءِ إِنِ اتَّقَيْتُنَّ فَلا تَخْضَعْنَ بِالْقَوْلِ فَيَطْمَعَ الَّذي في قَلْبِهِ مَرَضٌ وَقُلْنَ قَوْلاً مَعْرُوفاً * وَقَرْنَ في بُيُوتِكُنَّ وَلا تَبَرَّجْنَ تَبَرُّجَ الْجاهِلِيَّةِ الاْولى وَأَقِمْنَ الصَّلاةَ وَآتينَ الزَّكاةَ وَأَطِعْنَ اللهَ وَرَسُولَهُ إِنَّما يُريدُ اللهُ لِيُذْهِبَ عَنْكُمُ الرِّجْسَ أَهْلَ الْبَيْتِ وَيُطَهِّرَكُمْ تَطْهيراً * وَاذْكُرْنَ ما يُتْلى في بُيُوتِكُنَّ مِنْ آياتِ اللهِ وَالْحِكْمَةِ إِنَّ اللهَ كانَ لَطيفاً خَبيراً)[3] .

 Idan kun kasance kuna nufin Allah da Manzonsa da gidan lahira lallai Allah ya tanadarwa masu kyautatawa daga gareku lada mai girma*yaku matayen Annabi duk wace ta zo da alfasha bayyananniya Allah zai ninka mata azaba ninki biyu kuma yin hakan abu ne mai matukar sauki a wurin Allah*duk wacce tayi tawali'u daga gareku domin Allah da Manzonsa kuma tayi aiki nagari zamu zo mata da ladanta karo biyu kuma mun yi mata tanadin arziki mai karamci* yaku matayen Annabi kufa ba daidai kuke da sauran mataye ba matukar dai kun ji tsoran Allah kada ku lausasa zance ta yanda wanda zuciyar take da tsatsa yayi kwadayi ku fadi magana mai kyawu* kuma ku zauna cikin gidajenku kada ku fito cikin cancade ado irin fitowar jahiliyar farko kuma ku tsayar da salla ku bada zakka ku yiwa Allah da Manzonsa `da'a kadai Allah yana nufin tafiyar da dukkanin datti daga barinku Ahlil-baiti kuma ya tsarkakeku tsarkakewa* ku tuna abin da ake karantawa kanku daga ayoyin Allah da hikima lallai Allah ya kasance Mai ludufi Mai labartawa

124 ـ من خصائص النبي الأكرم  6:

(يا أَيُّهَا النَّبِيُّ إِنّا أَحْلَلْنا لَکَ أَزْواجَکَ اللّاتي آتَيْتَ أُجُورَهُنَّ وَما مَلَكَتْ يَمينُکَ مِمّا أَفاءَ اللهُ عَلَيْکَ وَبَناتِ عَمِّکَ وَبَناتِ عَمّاتِکَ وَبَناتِ خالِکَ وَبَناتِ خالاتِکَ اللّاتي هاجَرْنَ مَعَکَ وَامْرَأَةً مُوْمِنَةً إِنْ وَهَبَتْ نَفْسَها لِلنَّبِيِّ إِنْ أَرادَ النَّبِيُّ أَنْ يَسْتَنْكِحَها خالِصَةً لَکَ مِنْ دُونِ الْمُوْمِنينَ قَدْ عَلِمْنا ما فَرَضْنا عَلَيْهِمْ في أَزْواجِهِمْ وَما مَلَكَتْ أَيْمانُهُمْ لِكَيْلا يَكُونَ عَلَيْکَ حَرَجٌ وَكانَ اللهُ غَفُوراً رَحيماً)[4] .

Yakai wannan Annabi hakika mu mun halasta maka matayenka wadanda ka basu sadakokinsu da abin da damanka ta mallaka daga abin da Allah yayi kyautarsa kanka da `ya`yan baffanenka da `ya`yan gwaggwanenka da `ya`yan `yan uwan mahaifiyarka wadanda suka yi hijira tare da kai da mace Mumina idan ta yi  kyautar kanta zuwa ga Annabi idan Annabin ya nufi aurenta kebance gareka koma bayan sauran Muminai hakika mun san abin da muka farlanta kansu cikin mazajensu da abin da damammakinsu ta mallaka domin kada kunci ya kasance a kanka kuma Allah ya kasance Mai gafara da jin kai.

                                                                          

(لا يَحِلُّ لَکَ النِّساءُ مِنْ بَعْدُ وَلا أَنْ تَبَدَّلَ بِهِنَّ مِنْ أَزْواجٍ وَلَوْ أَعْجَبَکَ حُسْنُهُنَّ إِلّا ما مَلَكَتْ يَمينُکَ وَكانَ اللهُ عَلى كُلِّ شَيْءٍ رَقيباً)[5] .

 Wasu Matayen basa halasta gareka daga bayan haka kuma ba zaka canja su da matan aure ba ko da kuwa kyawunsu ya kayatar da kai face dai abin da damanka ta mallaka kuma Allah ya kasance Mai sanya ido kan komai.

(يا أَيُّهَا النَّبِيُّ قُلْ لاِزْواجِکَ إِنْ كُنْتُنَّ تُرِدْنَ الْحَياةَ الدُّنْيا وَزينَتَها فَتَعالَيْنَ أُمَتِّعْكُنَّ وَأُسَرِّحْكُنَّ سَراحاً جَميلاً * وَإِنْ كُنْتُنَّ تُرِدْنَ اللهَ وَرَسُولَهُ وَالدّارَ الآْخِرَةَ فَإِنَّ اللهَ أَعَدَّ لِلْمُحْسِناتِ مِنْكُنَّ أَجْراً عَظيماً)[6] .

 Yakai Annabi ka cewa matayenka idan kun kasance kuna nufin duniya da adonta to ko zo in jiyar da ku dadi in sallameku sallama mai kyawu* idan kuma kun kasance kuna nufin Allah da Manzonsa da gidan lahira to lallai Allah yayi tanadi ga masu kyautatawa cikin su da lada mai girma.

125- sirrin da aka yada da bayanin ayoyin haramtawa:

 (يا أَيُّهَا النَّبِيُّ لِمَ تُحَرِّمُ ما أَحَلَّ اللهُ لَکَ تَبْتَغي مَرْضاتَ أَزْواجِکَ وَاللهُ غَفُورٌ رَحيمٌ * قَدْ فَرَضَ اللهُ لَكُمْ تَحِلَّةَ أَيْمانِكُمْ وَاللهُ مَوْلاكُمْ وَهُوَ الْعَليمُ الْحَكيمُ * وَإِذْ أَسَرَّ النَّبِيُّ إِلى بَعْضِ أَزْواجِهِ حَديثاً فَلَمّا نَبَّأَتْ بِهِ وَأَظْهَرَهُ اللهُ عَلَيْهِ عَرَّفَ بَعْضَهُ وَأَعْرَضَ عَنْ بَعْضٍ فَلَمّا نَبَّأَها بِهِ قالَتْ مَنْ أَنْبَأَکَ هذا قالَ نَبَّأَنِيَ الْعَليمُ الْخَبيرُ * إِنْ تَتُوبا إِلَى اللهِ فَقَدْ صَغَتْ قُلُوبُكُما وَإِنْ تَظاهَرا عَلَيْهِ فَإِنَّ اللهَ هُوَ مَوْلاهُ وَجِبْريلُ وَصالِحُ الْمُوْمِنينَ وَالْمَلائِكَةُ بَعْدَ ذلِکَ ظَهيرٌ * عَسى رَبُّهُ إِنْ طَلَّقَكُنَّ أَنْ يُبْدِلَهُ أَزْواجاً خَيْراً مِنْكُنَّ مُسْلِماتٍ مُوْمِناتٍ قانِتاتٍ تائِباتٍ عابِداتٍ سائِحاتٍ ثَيِّباتٍ وَأَبْكاراً)[7] .

 Yakai wannan Annabi me ya sanya kake haramta abin da Allah ya halasta maka kana Mai neman yardarm matayenka kuma Allah Mai gafara da jin kai ne* hakika Allah ya farlanta muku warware rantsuwowinku kuma Allah shi ne Majibanci al'amarinku kuma shi ne Masani Mai hikima*lokacin Annabi ya sirranta wani labari zuwa ga ba'arin matayensa yayin da ta labartar da shi kuma Allah ya tsinkayar da shi kan labarin ya bayyana wani ba'ari ya kau da kai daga wani ba'ari yayin ya bata labari sai tace wane ne ya gaya maka wannan labari sai ya ce Masani Mai labartarwa ne ya gaya mini* idan ma kun tuba zuwa ga Allah hakika zukatan sun rigaya sun karkata idan kuka yi taimakekeniyar junanku a kansa to lallai Allah shi ne majibanci al'amarinsa da Jibrilu da Salihan Muminai kuma Mala'iku a bayan wancan mataimaka ne* ta yiwu Allah ubangijinsa idan ya sake ku ya canja masa da mafi alherinku Musulmai Muminai masu tawali'u masu tuba masu ibada masu azumi zawarori da `yan mata.

126-aurensa da Zainab da bayani kan hikimar yin hakan:

 (وَإِذْ تَقُولُ لِلَّذي أَنْعَمَ اللهُ عَلَيْهِ وَأَنْعَمْتَ عَلَيْهِ أَمْسِکْ عَلَيْکَ زَوْجَکَ وَاتَّقِ اللهَ وَتُخْفي في نَفْسِکَ مَا اللهُ مُبْديهِ وَتَخْشَى النّاسَ وَاللهُ أَحَقُّ أَنْ تَخْشاهُ فَلَمّا قَضى زَيْدٌ مِنْها وَطَراً زَوَّجْناكَها لِكَيْ لا يَكُونَ عَلَى الْمُوْمِنينَ حَرَجٌ في أَزْواجِ أَدْعِيائِهِمْ إِذا قَضَوْا مِنْهُنَّ وَطَراً وَكانَ أَمْرُ اللهِ مَفْعُولاً * ما كانَ عَلَى النَّبِيِّ مِنْ حَرَجٍ فيما فَرَضَ اللهُ لَهُ سُنَّةَ اللهِ فِي الَّذيüنَ خَلَوْا مِنْ قَبْلُ وَكانَ أَمْرُ اللهِ قَدَراً مَقْدُوراً)[8] .

 Yayin da kake cewa wanda Allah yayi ni'ima kansa ka rike matarka kanka kaji tsoran kuma kana boyewa cikin ranka abin da Allah yake bayyanar da shi kana tsoran mutane alhalin Allah ne mafi cancanta kaji tsoransa yayin da Zaidu ya gama biyan bukatarsa daga gareta sai muka aura maka ita.

127-kiyaye ladabi tare da Manzon Allah (s.a.w)

 (يا أَيُّهَا الَّذينَ آمَنُوا لا تَدْخُلُوا بُيُوتَ النَّبِيِّ إِلّا أَنْ يُوْذَنَ لَكُمْ إِلى طَعامٍ غَيْرَ ناظِرينَ إِناهُ وَلكِنْ إِذا دُعيتُمْ فَادْخُلُوا فَإِذا طَعِمْتُمْ فَانْتَشِرُوا وَلا مُسْتَأْنِسينَ لِحَديثٍ إِنَّ ذلِكُمْ كانَ يُوْذِي النَّبِيَّ فَيَسْتَحْيي مِنْكُمْ وَاللهُ لا يَسْتَحْيي مِنَ الْحَقِّ وَإِذا سَأَلْتمُوهُنَّ مَتاعاً فَسْئَلُوهُنَّ مِنْ وَراءِ حِجابٍ ذلِكُمْ أَطْهَرُ لِقُلُوبِكُمْ وَقُلُوبِهِنَّ وَما كانَ لَكُمْ أَنْ تُوْذُوا رَسُولَ اللهِ)[9] .

Yaku wadanda kuka yi imani kada ku shiga gidan Annabi sai bayan yi muku izini zuwa ga abinci ba da ku kasance masu kallon kwaryarsa sai dai cewa idan an kiraku ku shiga idna kuma kun ci ku fita daga gidan ba da ku kasance masu debe haso ga wani labari lallai hakan yana cutar da Annabi shi kuma yana jin kunyarku kuma shi Allah baya jin kunya daga gaskiya  idan zaku tambaye sui wani kaya ku tambaye daga bayan hijabi wannan shi ne mafi tsarki ga zukatanku da zukatansu bai kamata gareku ku cutar da Manzon Allah ba.

[1] ()  الأحزاب : 6.

[2] ()  الأحزاب : 33.

[3] ()  الأحزاب : 29 ـ 34.

[4] ()  الأحزاب : 51.

[5] ()  الأحزاب : 52.

[6] ()  الأحزاب : 28 ـ 29.

[7] ()  التحريم : 1 ـ 5.

[8] ()  الأحزاب : 37 ـ 38.

[9] ()  الأحزاب : 53