b Shin tsoran da yake halasta yin Takiyya tsoro ne na mutum guda ko kuma tsoro irin wanda kowa da kowa yana jinsa - HUJJOJIN HALASCIN YIN TAKIYYA A MUSLUNCI DAGA MAHANGAR MANYAN MALAMAI GUDA BIYU
فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها

Shin tsoran da yake halasta yin Takiyya tsoro ne na mutum guda ko kuma tsoro irin wanda kowa da kowa yana jinsa

Da yawa daga maudu'ai da hukunce-hukuncen shari'a suna jujjuyawa ne da yanayin yanda mutane suke, ba'arin wasu hukunce-hukuncen suna gudana kan nau'in yanda mukallafai suke sai su zama sun game baki dayansu.

Sannan daga cikin rukunan Takiyya akwai jin tsoro, bari zai iya kasance shine jigo cikin rukanan yinta kamar yanda wasu ba'ari daga manyan Malamai suka tafi a kai, saboda haka tambaya anan shine: wanne tsoro ake nufi a cikin Takiyya shin tsoron da mutum guda yake ji ko da kuwa a wurin sauran ba a ganinsa a matsayin tsoro yana wajaba kansa kenan yayi takiyya ko kuma tsoro irin wanda kowa da kowa yake yinsa?

Shaikul Ansari yana cewa: lallai yanda al'amarin yake shine cewa babu shakka cikin tabbatuwar Takiyya cikin kasancewar tsoro daga mutum guda daya wannan shine abinda aka samu yakini kansa- da cewa mutumin ya fuskanci tsoro da barazana kan rayuwarsa ko ta waninsa matukar dai yaki aiki da Takiyya cikin ayyanannen wannan aiki, baya nisanta ya rike tsoro matsayin uzuri cikin barin Takiyya a sauran ayyukansa ko kuma ginin shi'a suke yi kan barin Takiyya cikin kebantaccen aiki ko kuma dukkanin aiki da kowa da kowa yake yinsa cikin garuruwan wadanda ba shi'a ba ko da kuwa shi mutum a kebance babu wani tsoro a gareshi, wannan shine abinda ake fahimta daga idlakin da umarni kan yin Takiyya ya zo da shi da abinda ya zo daga himmatuwa a kanta.

Shaikul Ansari yayi riko da idlakin da ya zo cikin dalilai kan cewa abin nufi daga tsoro shine tsoro na mutum guda da kuma na kowa da kowa cikin fadinsa amincin Allah ya tabbata a gareshi:

(ليس منّا مَن لم يجعل التقيّة شعاره ودثاره مع من يأمنه لتكون سجيّته مع مَن يحذره )[1] .

 Baya daga garemu duk wanda bai sanya Takiyya a matsayin takensa ba malullubinsa mayafin da yake lulluba da shi tareda wanda yake amintar da shi domin ta zama dabi'arsa tareda wanda yake taka tsantsan daga gareshi.

Na'am ya zo cikin hadisin Imamul Rida amincin Allah ya kara tabbata a gareshi:

أبي الحسن الرضاصلوات اللّه عليه معاتبآ لبعض أصحابه الذين صحبهم : (إنّكم تتّقون حيث لا تجب التقيّة وتتركون حيث لا بدّ من التقيّة )[2] .

An karbo daga Baban Hassan Rida amincin Allah ya tabbata a gareshi: lallai ku kun kasance kuna yin Takiyya a wurin yinta ba wajibi bane kuma kuna barin yinta a wurin da ya zama wajibi a yi ta.

Za a iya dora wannan hadisi a ba'arin wurin baya cin karo da ka'idar usul hada tsakanin hadisai masu karo da juna da sama musu mafita.

Sannan Assayidul Komaini (ks) ya tafi kan ra'ayin da Shaikul Ansari ya tafi kansa bari ma dai yayi kari kansa cikin Takiyya mudariyya (takiyyar bi sannu-sannu) da cewa abin nufi Takiyya bawai domin tsoro daga mutum ko dukkanin mutane kadai ba, bari dai hatta har lokacin ma da babu barazanar tsoro takiyya tana wajabta hakan yana faruwa a lokacin kiyaye maslahohi da suka shafi kowa da kowa, cikin Risalarsa yana cewa: sannan yanda al'amarin yake shine cewa halascin yin takiyya da wajabcinta bai tsayu kan jin tsoran kan rayuwarka ba ko ta sauran mutane, bari dai zahirin abinda yake cikin riwayoyi cikin wannan babi –lallai su gamammun maslahohi sun kasance sababi kan wajabta yin takiyya daga wadanda ba shi'a ba, saboda haka takiyya tana wajaba ko da kuwa mutum baya fuskanta barazana kan rayuwarsa da waninsa.