b GABATARWA - CIKIN HALLARAR ALHERI
فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها

GABATARWA

Da sunan Allah Mai rahama mai jin kai

Cikin hallarar Alheri

Budaddiyar Wasika

Dukkanin godiya ta tabbatata ga Allah kamar yanda dama ya kasance Ahalin a gode masa da yaba masa adadin dukkanin abin da iliminsa ya kewaya kansa, tsira da amincin Allah su kara tabbata ga Muhammad mafificin halittu shugaban Annabawa da Manzanni Abu Kasim da iyalansa tsarkaka musammam ma Bakiyatullahi kan doran kasarsa Allah ya gaggauta bayyanarsa mai daraja.

Dan'uwa mai daraja aboki abin kauna bawan Allah nagari rabautaccen Mumini Ustaz mai daraja mai fahimta Kamili, mutumin Kirki Alhaji Kamalu Alwanu Allah ya dawwamar da girmansa ya azurta rabonsa, Allah ya sanya masa albarka cikin iyalansa a duniya da lahira.

Ina mika gaisuwa gareka gaisuwar muslunci da mutanen Aljanna (Fasalamun Alaikum) amincin Allah kammalalle ya tabbata a gareka da dukkanin wanda yake fakewa jikinka musammam ma danginka masu daraja tare da rahamarsa da albarkokinsa, Allah ya dawwamar daku cikin lafiya da aminci cikin kulawarsa da falalar Manzon Allah (s.a.w) da kulawar Ahlil-Baiti tsarkaka cikin inuwar shugabanmu shugaban zamaninmu Alhujjatul Muntazar (a.s) Allah ya gaggauta bayyanarsa mai daraja.

Masoyi ya kai wanda mahaifanka suka sanya maka suna (Kamalu) lallai sunaye tabbas suna saukowa ne daga sama hakika ka amsa sunan da aka sanya maka, ka kasance shekaru masu yawan da suka shude kana neman kamala da hakika, baka gushe ba tunda ka rigaya ka san cewa hadafin baki dayan hallita shi ne Kamala, bari dai domin mutum ya samu kammaluwa domin ya kai ga kamalarsa da yake nema yake cigiya wacce aka ajiyeta cikin dayantacciyar halitarsa, lallai shi mutum yana son alheri yana begensa yana kuma kaunar kyawu da kamala, kadai hakan na tabbatuwa ta hanyar bautar Allah da neman saninsa, kana bincike cikin ilimi da sanin Ahlil-baiti nima tare da kai ban gushe ba ina ta bincike, lallai su suna geffana kasa, sune waliyyan Allah cikin kasan kubbarsa, duk wanda ya neme su zai samesu , duk wanda ya kwankwasa kofa ya nace da kwankwasa zai shiga cikin gida, dole ne a zage dantse da mujahada mara yankewa, da tsananta bincike  mara yankewa har sai gashinka yayi furfura, duk wanda yake neman daukaka da madaukakatofa dole ya `bata dare ido bude, dole y adage da naci cikin neman ilimi da kwankwasa kofarsa, har ya samu damar shiga gidan aminci, ya shiga ni'ima da Aljanna  da Aljannar kyawawan sunaye da rai mai nutsuwa mai yarda yardadda, ya shiga  cikin bauta irinta rabautattu da makusanta cikin matsugunin gaskiya wurin Sarki Mai iko, domin ubangijinsa ya shayar da shi tsarkakakken abin sh, me yafi kyawu daga wannan haduwa da ubangiji a mukamin fana'I da wanzuwa, fana'I cikin Allah da wanzuwa tare da shi_ lallai Sarki Mai iko Masani yana shayar da abokin zamansa da Kofin kudura da hasken ma'arifa abin sha tsarkakke, ai tsarkakakke a kankin kansa kuma mai tsarkake waninsa, me zai kasance bayan wannan abin sha daga maye da fana'i da haukacewa cikin soyayya da dimauta da maraici da kaunar ubangiji?!

Masoyi Alhaji Kamalu: kai dama al'adarka fiye da shekaru 20 da suka shude cikin duniyar abota da yan'uwantaka ka kasance Aboki mai tace soyayya `dan'uwa mai daraja Abokin shawara Mai bada nasiha da tausayawa, kana tsara zamani da kaifin basirarka, ka tserewa tsaraiku da basirarka, baka kasance kana bata lokacinka mai daraja da rayuwarka cikin abin da bai da amfani ba.

Al'adarka ka kasance mutum mai fafutikar aiki da nema jarumin mutum da yake kutsawa fagen fama da dauka babu dadi a rayuwa mutum mai son alheri ga waninsa gabanin kansa, shi zargin Mai zargi bai damunsa cikin al'amarin Allah matukar dai ya san yana kan gaskiya da daidai yana kan iliminsa da yakini.

Al'adarka kai Hazikin mutum ne mai zurfin tunani, Mumini mai riko da addini kana magana da kowa na kusa da na nesa yaro da babba mace da namiji Malami da Jahili Talaka da Mawadaci domin alherin ya isa zuwa garesu, kullum tunaninsa yaya zai samu nasara da rabauta cikin rayuwarsa, kuma yana masu alheri bai jiran yabo ko godiya, bari dai kai kana kira zuwa ga alheri da neman gafara hatta ga wadanda suke maka hassada kan ni'imar da Allah yayi maka daga falalarsa.

Kai al'adarka ka kasance abin buga misali mutum mai tsarkin niyya `dankasuwa kuma `dan shi'a mai gudun duniya, kai ko mai kake da shi da ta kai ga ana buga misali da kai, lallai ni daga kusa-kusa naga zuhudu da idona daga gareka, lallai shi bashi da kudi bashi mukami, bari dai duk wani suna da take da lukubba sun fadi gareka basu da kima haka yabon masu yabo, bari dai na sameka kana godiya ga dukkanin wanda ya nuna maka aibinka musammam ma cikin girmamawa, na sameka kana karbar suka tare da dukkanin fadada kirji domin ka kasance yanda kake ka samu daukaka da kaiwa ga matattakalar kamala da kyawu, inama ace dukkanin `yan kasuwar shi'a da farko su samu nasara cikin kasuwancinsu sannann su kwaikwayi mutane ire-irenka cikin tsoran Allah da kiyaye hakkokin Allah da mutane.

Da dukkanin samuwata ina fata kuma ina nema dare da rana tare da dukkanin nacina da kafewata da Allah ya sa mu mabiya Ahlil-Baiti mu samu Kalmar falala da faifaye bayani cikin dukkanin fagen rayuwa daga tattalin arziki a fadin duniya haka ma cikin siyasa da sakafa da wasunsu, sabida addininmu addinin muslunci shi ne cikamakin addinai da shari'a da ta zo daga Allah, lallai shi ne mafi falala mafi kamala:  

 (الْيَوْمَ أَكْمَلْتُ لَكُمْ دِينَكُمْ وَأَتْمَمْتُ عَلَيْكُمْ نِعْمَتِي وَرَضِيتُ لَكُمُ الإِسْلاَمَ دِيناً)[2]  (وَمَن يَبْتَغِ غَيْرَ الإِسْلاَمِ دِيناً فَلَن يُقْبَلَ مِنْهُ)[3] .

 A yau na kammala muku addininku da cika ni'imata a kanku na yardar muku da muslunci addini.

Duk wanda ya nemi wani addini koma bayan muslunci ba za karba daga gare shi ba.

Mazhbarmu itace mafi cikar Mazhaba mafi falala mafi kamala daga dukkanin Mazhabobi da makarantun tunani da Akidu da suluki, lallai muna imani da Allah da Manzonsa cikamakin Annabawa da Manzanni Muhammad (s.a.w) kuma munyi imani da samuwar Imami Ma'asumi Rayayye Waliyin Allah mafi girma babbar hujjarsa, albarkacinsa aka azurtamu, kuma da samuwarsa kasa da sama suka tabbata, hakika kofar ijtihadi bude take cikin fakuwarsa, dukkanin wannan na nuni zuwa ga rayuwa Mazhaba da dawwamarta da wanzuwarta, bawai misalin sauran matattun Mazhabobi wadanda suka suka kullewa kawukansu kofar ijtihadi.

Hakika Allah yayi mana alkawari kuma shi baya taba saba alkawarinsa da cewa lallai wannan kasar bayinsa nagargaru zasu gajeta, sune wadanda zasu yi shimfida da share fagen tsayuwar babbar Daular muslunci domin ya bayyanar da shi kan addini baki dayansa cikin dukkanin sasannin duniya da jagorancin Mai kawo gyara na duniya baki daya Almahadi daga iyalan Muhammad (s.a.w) daga tsatson Fatima Azzahara (a.s) zai cika kasa da adalci da daidaito bayan ta cika da zalunci da danniya, hakan ba zai taba tabbatuwa ba face cikin kammalalliyar wayewa da daukar mas'uliya mai girma wacce aka dorata kan wuyanmu, hakika muna rayuwa cikin dauki ba dadin tunani da habbakar sana'a da fasahar zamani cikin sauri da gudu kamar haske, muna cirata daga wannan mataki zuwa wani matakin daban cikin gini da canje-canje da raya kasa da tanade-tanade da adadi, sai dai cewa kada mu manta hakika gine na hakika ga kowacce irin al'ummaya kamata ne ya fara daga gina mutum da yi masa tanadin kammaluwa ta hakika wayayya domin samun cigaba zuwa gaba, mafificin misali cikin haka shi ne fadin Allah madaukaki:

 (إِنَّ اللّهَ لاَ يُغَيِّرُ مَا بِقَوْمٍ حَتَّى يُغَيِّرُواْ مَا بِأَنْفُسِهِمْ)[4] .

 Allah baya canja mutane har sai sun canja da kansu.

Daga wannan tushe na Kur'ani zamu fara tattaki na farko daga gina zati da daidaiku, sannan mu tsallaka zuwa ga gina dangi wadanda sune tubali na farko cikin gina al'umma (ku tseratar da kanku da iyalansu daga wuta) domin kaiwa ga gina wayayyar jama'a masu riko da sakon muslunci da Akidunsa na asali, da gadonsa na cigaba mai daraja, hakika addininmu shi ne mafi alherin addini kuma Annabinmu shi ne shugaban Annabawa da Manzanni Muhammad (s.a.w) littafinsa shi ne Kur'ani mai daraja dawwamammiyar mu'ujizarsa, cikin tsatsonsa fitilun shiriya Jiragen tsira duniya da lahira.

Domin nade tafiyar mil dubu a mil daya wajibi kanmu mu fara tsarkake kawukanmu mu yi musu ado da sakafar musluncida bubbugar daga greshi ina nufin Kur'ani da Ahli-Baiti (a.s) karkashinta mu dasa yaren soyayya da fuskantar juna, lallai mafi alherin cikin mutane shi ne wanda ya amfanar da mutane, mu sowa dukkanin mutane abin da muke sowa kawukanmu, bari dai su mutane masu son alheri suna fifita mabukata a kawukansu ko da kuwa suna cikin matsananciyar bukata, ta wannan hanya mu yi tanadi ga al'ummar da za su zo a bayanmu su kasance mutane tsarkaka Muminai masu son alheri wayayyu da suke daukar ma kawukansu nauyin yada adalci da zaman lafiya a fadin duniya, kowa ya kasance yana gina kasarsa cikin aminci da zaman lafiya kowa da kowa ya samu damar rayuwa tare da su shi cikin aminci da soyayya.

Wajibi ga dukkanin dan shi'a daga maza da mata yara da manya na birni da mazauna kauyuka su tsaya su yi tunani madaukakin tunani su share fage ga zuwan wannan babbar Daula ta adalci da karamci da mutumtaka cikin dukkanin duniya gabas da yamma kudu da arewa.

Dole ne magudanan lamurra da makullansu daga siyasa da tattalin arziki da sakafa da dukkanin abin da yake rassantuwa daga garesu misalin harkokin jarida da labarai da dukkanin kashe-kashensa dole su zamana a hannun `dan shi'a mai zurfin tunani wayayye mai riko da sakon akidun muslunci bayan ya rigaya ya cika da makaman ilimi da ma'arifa da tsoran Allah da adalci da karamci da falala.

Wannan takaitaccen kirana da na ciroshi daga nassoshin addini zuwa ga `yan kasuwa yan shi'a hakama zuwa ga `yan siyasa masu yunkurin kawo gyara d ama dukkanin dabakokin al'umma tare da dukkanin yake tattare da su daga mas'uliya da alkawarori da sana'o'i da ayyuka ina kira da kasance mafifita mafi cika da kammala cikin dukkanin zamani a kowanne waje suke.
lallai su ma'abota alheri ne da kyautatawa ma'abota daraja da imani, hakika Imamansu tsarkaka sune Asalin alheri da reshensa ma'adaninsa matsuganarsa, duk wanda yayi imani da su ya kasance dauke da akidunsu da dokokinsu da madaukakan dabi'unsu ya kasance dauke da iliminsu da ma'arifofinsu da halayensu to dole ne ya kasance cikin matsayi da mustawar danganewa garesu da ya kasance shi ne mafi falala da fifiko a duk inda ya sauka da inda ya bari, kamar yanda ya zo daga garesu tsarkaka:

كونوا لن ازينآ ولا تكونوا شينآ، كونوا بين الناس بنحو إذا قصد أفضل الناس في حفظ الامانات والوفاء بالعهود والمواثيق واداء الوظائف والمسؤوليات ، فانه يشار اليكم أولا، وقالوا: رحم الله الإمام جعفر بن محمد الصادق  7 كيف أدّب أصحابه .

Ku kasance ado a garemu ka da ku kasance aibu garemu, ku kasance tsakankanin mutane da yanayin da idan ana neman mutum mafi falala a fifiko cikin kiyaye amana da cika alkawari da yarjejeniya da sauka wazifa da mas'uliya lallai daku za a fara yin ishara, suce: Allah yayi rahama ga Imam Jafar Ibn Muhammad Assadik (a.s) mamakin yanda ya tarbiyantar da mutanensa tarbiyya!

Hakane: wajibi ne mu kasance tozan daukaka da girma cikin kyawawan dabi'u da ladubba da kiyaye hakkokin ubangiji da na mutane, da sauke wazifa gwargwadon mas'uliya da kiyaye dokokin hankali da na shari'a

Ya zama dole mu kasance mafi alherin mutane hakan zai kasance yayi da muka kasance misalin rana da take kyautar haske da kyawu da kamala ga dukkanin mutane, lallai ita rana tan kyauta amfanonita ga kowa da kowa wannan cikin yini kenan sannan da daddare ya zama wajibi mu kasance kamar misalin wata mai haskaka kowa da kowa na birni da kauye na daji da sahara dukkaninsu zasu shiriya damu zasu bukaci haskenmu su nemi sanin hanya da tafarki, mu kasance daga mafi tsarkakar niyyar masu kira da da'awa zuwa ga Allah matsarkaki da ilimi mai amfani da aiki nagari.

Wajibi kanmu mu tsarkake kawukanmu mu kasance ababen koyi nagari ga waninmu, kamar yanda Kur'ani mai girma ya kowa mana:

«واجعلني للمتقين إمامآ»

Ka sanya ni jagora ga masu tsoranka.

Sai mu kasance jagororin alheri ababen koyi cikin imani da aiki nagari ga masu takawa ballantana ma ga waninsu.

Hakika magana cikin wannan fage yana rassana da sasanni saboda haka in takaice maudu'in in tsunduma cikinsa kai tsaye sai dai cewa yayin da na ga wannan tambaya karbabbe ce a hankalce, lallai al'ummar wannan zamani suna bukatuwa zuwa gareta matuka sai na nemi uzuri daga gareku daku bani dama in rubuta amsa cikin taken `dan takaitaccen littafi tare da bayani filla-filla cikin Risala da na samata suna (Fi Rihabil Kairi) saraina nan gaba za a dabba'ata a yada ta duniya ta kasance daga takardun da mutane zasu amfana da karanta su bayan mutuwa ta sai na samu kusanci zuwa ga ubangiji da wannan risala, in tanadinta ga lahirata ranar da dukiya da `ya`ya basa amfanar da komai sai mutumin da ya je wa ubangiji da lafiyayyar zuciya, ya hadu da shi babu kowa cikinsa sai ubangiji da kuma abin da ya kasance kansa daga sunansa da rininsa.

 (اللّهم أرزقني حبّک وحبّ من يحبّک وحبّ كل عمل يوصلني إلى قربک)

Ya ubangiji ka azurtani da sonka da son wanda yake sonka da son duk wani aiki da zai sadar da ni zuwa ga kusancinka

Amin amin.

Dan'uwanku masoyi bawan Allah Adil-Alawi

24/1/1430 hijiri