b Alheri da Sharri cikin rubutu - CIKIN HALLARAR ALHERI
فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها

Alheri da Sharri cikin rubutu

Allah ya karfafeka duniya da lahira yayi maka rahama da wanda ya fake dakai da yalwatacciyar rahamarsa, ka sani shi alheri da sharri a luggance kalmomi ne da suke maimaituwa cikin sakafar addini da Irfani da Falsafa da ilimin sanin taurari da Adabi, sun dogara ne da mahangar da mutum ya ginu a kai, mahanga kansu na sassabawa da sassabawar mahangarsa da mashayarsa da makarantar da ya ginu kanta, sai dai cewa shi Alheri cikin gamammiyar ma'anarsa ana dora shi kan dukkkanin kyakkyawan abu kammalalle cikakke dukkanin abin da yake tattare da amfanoni da mutum cikin rayuwarsa ta hankali da shari'a.

Shi kuma Sharri kishiyar Alheri ne ma'anance ana dora Kalmar kan dukkanin mummunan abu gurbatacce tawayayye da dukkanin abin da dabi'a take gudunsa.

Wadannan kalmomi biyu suna da samuwa tsawon lokaci cikin makarantun falsafar kasashen Girka da Italiya da Indiya da Farisa da ma wasunsu, tarihinsu yana komawa zuwa dubunnan shekaru da daruruwan karnoni.

Sannnan asalin alheri ana kirga shi daga asali guda daya wanda dukkanin makarantun Falsafa da Kalam suka yi tarayya cikinsa kai hatta addinan da suka zo daga ubangiji tun zamanin farko har zuwa wannan zamani da muke ciki.

Kai hatta makarantar Sadrul Muta'allihin Mulla Shirazi yana kirga alheri matsayin abin da yake tsugunawa matsgunar samuwa shi kuma sharri shi babu ce tsantsan bai da samuwa yana cikin jerin abubuwa da basu da samuwa.

Alheri da sharri su bayyana cikin wasu unwanai na daban kamar misalin umarnin ubangiji lallai suna daga alheri sakamakon abin da ya tare da su daga masalahohi na wajibi da lazim, hani daga aikata mummuna ya daga sharri sakamakon abin da ya tattare da shi daga barna, haka zalika ya zo da taken `da'a da sabo, ni'ima da azaba, kwanciyar hankali da bala'i, lada da ukuba, farin ciki da tsiyata, da dai makamancin haka.

Hakika kalmomin alheri da sharri sun zo cikin Kur'ani mai girma cikin maudu'ai daban daban da ma'anoni daban daban koma yafi kamata muce cikin misdak masu banbanta da juna, Allah ya so Muminai su gaggauta suyi sauri da tserereniya zuwa ga alherai zuwa ga kyawawan halaye da ayyuka nagari, da kauracewa miyagun halaye da sharri komai kankantarsa ko da kuwa wurin mutane basa ganinsa a sharri sakamakon kankantarsa da kallonsa ba a bakin komai sai dai cewa wurin abu mai muni kuma da sannu mutum zai tsince shi cikin mizaninsa 

 (فَمَن يَعْمَلْ مِثْقَالَ ذَرَّةٍ خَيْراً يَرَهُ وَمَن يَعْمَلْ مِثْقَالَ ذَرَّةٍ شَرّاً يَرَهُ)[1] .

 Duk wanda ya yi wani aiki gwargwadon kwayar zarra daga alheri zai ganshi*duk wanda yayi aiki daga sharri gwargwadon kwayar zarra zai gan shi

Lallai zai ganshi a gidan duniya ko a lahira banbanci tsakanin gidajen biyu a bayyane yake gam asana, duk wanda ya shuka Alkama ba zai yiwu ya girba Sha'iri ba bari dai Alkamar da ya shuka zai girba, zai hadu da sakamakon aikin sharri matukar dai bai tuba ba bai gyara halinsa ba bai canja mummuna da kyakkyawa ba.

(وَمَا تَفْعَلُواْ مِنْ خَيْرٍ يَعْلَمْهُ اللّهُ)[

Abin da kuka aikata daga alheri Allah yana sane da shi

2]  (وَلَوْ يُعَجِّلُ اللّهُ لِلنَّاسِ الشَّرَّ اسْتِعْجَالَهُم بِالْخَيْرِ لَقُضِيَ إِلَيْهِمْ أَجَلُهُمْ

 Da Allah zai gaggautawa mutane sharri irin yanda yake gaggauta musu alheri da karshensu ya zo.

   (فِيهِنَّ خَيْرَاتٌ حِسَان

Cikinsu akwai wasu mata masu kyau da kyawun halitta.

Kamar yanda muke magana kan alheri da sharri cikin ilimin dabi'a cikin samuwar sinadaran halittu da duniyar tsirrai da dabbobi da mutane.

Kamar yanda Masana ilimin taurari suke magana dangane da su cikin taurarin farin ciki dana tsiyata.

Kamar yanda ake bijiro da bahasinsu cikin fannoni da sunayen kyawunta da kamala, cikin fannin huduba da zane-zane da fannoni ado da kaya ce-kaya ce da wake-wake da wasan diramar dandamali da Sinima da kafofin yada labarai da dai sauransu.

Hakama zaka samu kalmomin alheri da sharri cikin addinan Majusawa da Zartushawa cikin imaninsu da samuwar ubangijin alheri wanda suke kira da (Yazdan) da ubangijin sharri da suka kira (Abrihaman) na farko shi ne tushen duk wani alheri haka zalika na biyu shi ne tushen dukkanin sharri, sai suka biyunta da ubangiji.

Haka zalika sharri da alheri ya zo cikin bahasin yunbu da tabo kamar yanda ya zo cikin hadisan tabo a muslunci (tabon mutane nagargaru da tabon Ashararan mutane)

Hakama bahasin alheri da sharri ya bijiro cikin bahasin Malaman Falsafar muslunci suna da ra'ayoyi mabanbanta misalin Mu'allimus Sani Alfarabi ya kasa alheri zuwa kashi biyu: Al'iradi da Dabi'i.

A ilimin Kalam makarantun tunani sun sassabawa makarantar Ash'arawa da Mu'utazilawa da magana ta farko daga Ash'arawa shi ne cewa dukkanin alheri da sharri daga Allah matsarkaki suke.

Mu'utazilawa basu yadda cewa sharri daga Allah yake ba.

Falsafar muslunci shi alheri yana matsayin samuwa, Allah yana shi ne wajibul wujud ga zatinsa shi ne ma'abocin alheri shi Mai iko ne a kan komai a kan sharri da sai dai cewa baya aikata sharri domin shi sharri abu ne mai muni, shi dai mai aikata sharri yana aikata shi ne sakamakon jahilci da rashin sani ko kuma gazawa, shi kuma Allah masanin komai ne Mai iko ne kan komaibaya aikata sharri baya aikata duk wani mummuna abu, shi sharri yana daga abind abai da samuwa kuma ba dangantaka rashin samuwa zuwa ga Allah, dukkanin abin da yake zuwa daga gare shi tsantsar alheri ne.

Sannan daga cikin sananniyar gaisuwa da ta shahara cikin garuruwan Larabawa shi ne Sabahul Kairi (barka da Asubahi) da kuma Masa'ul Kairi (barka da yammaci) haka nan fadinsu Sabbahakumullahu bil Kairi (barkanku da Asubahi cikin alheri) wannan duka yana daga fata da addu'a da Allah ya sanya Asubahinku tare da alheri da kyawawa ya kuma nesantu daga sharri, sai safiyarku ta kasance alheri tare da alheri zuwa ga alheri ya kuma shi alheri ya kewayeku da ku, kai kewaye kake wanda Allah shi ne alherin da ya kewayeka, sai ya kewayeka da alherinsa da lafiya, ka kasance daga ma'abota alheri cikin ayyukanka da zantukanka da halayenka a kankin kanka da cikin rayuwarka da jama'a safe da yamma.

Wannan shi ne abin da nake son yin bayani a takaice cikin fasalan da zasu zo a nan gaba, daga Allah muna neman dacewa da taufiki, daga gare shi ingantaciyar magana tajke gangarowa da dukkanin abin da yake kunshe da alheri da lafiya.