■ Alheri da Sharri cikin rubutu
■ Fasali na (1)
■ Dayantacciyar halitta
■ Dabi'ar halin sharri cikin mutum
■ Alheri a luggance da Isdilahi
■ Ayoyin Alheri cikin Kur'ani Mai girma
■ Mafhumin alheri da misdakansa
■ Tafisirin alheri da kashe-kashensa daga kassi da Ammi daga cikin daidaiku da jama'a
■ Kebantaccen alheri daidaiku
■ Gamammen alheri na zamantakewa
■ Sirri cikin alheri da sharri
■ Ma'anonin da alheri yake da shi cikin Kur'ani mai girma
■ Mutane ma'abota alheri
■ Mafi alherin cikin Muminai
■ Alheri daga cikin Kur'ani Mai girma
■ Fasali na biyu
■ Gaggawa zuwa ga ayyukan alheri
■ Fasali na uku
■ Alheri da sharri a wurin Majusawa
■ Alheri daga mahangar malaman Aklak
■ Fasali na hudu
■ Sharri (Kulli tashkiki) wani abune gamamme da yake banbantuwa da juna
■ Alheri da sharri karkashin hasken Nahajul Balaga
■ Alheri shine wazirin hankali sharri wazirin jahilci
- KIBIYOYIN RADDI KAN WUYAN WAHABIYAWA
- CIKIN HALLARAR ALHERI
- HUJJOJIN HALASCIN YIN TAKIYYA A MUSLUNCI DAGA MAHANGAR MANYAN MALAMAI GUDA BIYU
- FARKAR DA MAI BACCI CIKIN TABBATUWAR GANIN IMAM KA'IM A.S
- ALAMOMIN ANNABI CIIKIN KUR'ANI MAI GIRMA
- HAKURI DA FUSHI
- Bada'u tsakanin hakika da kagen makiya
- FALALAR DAREN LAILATUL KADRI
- WAHABIYANCI A TSAKANIN GUDUMA DA
- HASKEN SASANNI CIKIN SANIN ARZIKI
- AQIDUN MUMINAI
- FATIMA TAGAR HASKAYE
- SIRRIKAN AIKIN HAJJI DA ZIYARA
- TARBIYYAR IYALI A MAHANGAR ALKUR'ANI DA AHLULBAITI
Allah ya kiyayeka ya kareka lallai kasani ita wannan duniya gida ne na gogayya da juna da kishiyantar juna, duk inda haske ya kasance to fa zaka samu duhu, idan ka samu gaskiya zaka samu karya, duk inda ka tsinci alheri ya kaga sharri shi alheri sharri ne yake kasancewa kishiya gare shi, kamar yanda Jahilci yake kishiyantar ilimi, kishiyantakar da take tsakaninsu kishiyantace ta warware juna ko kuma kishiyantar malaka da koruwarta ko kuma ta gaba da juna, idan ka san alheri tofa ka san sharri.
Sannan Allah matsarkaki ya halicci nafsi da ran mutum (kuma ina ratsuwa da rai da abin da ya daidaita shi) (sannan ya kimsa masa ya sanar da shi fajircinsa da shiriyarsa) saboda haka shi mutum yana rai da ake kimsa mata abubuwa da fari ta hanyarta yake sanin alheri da sharri, wannan cikin alheri da sharri bayyanannun abubuwa ne, idna al'amari ya rikice a kansa lallai a da ludufinsa kusa-kusa yake ga `da'a kuma nesa yake daga sabo, ya saukar da litattafai, ya aiko da Manzanni, ya turo da Annabawa ya nasabta Wasiyyai sannan ya sanya Salihan Malamai matsayin magadansu, domin shiryar da mutane da nusantar da su da sanar da su alheri da sharri da suka cudanya da juna suka gwamutsu, sannan hadafin halitta da hikima rayuwa shi ne bautar ubangiji wacce ba ta kasance face bayan saninsa, dole ne mai bauta ya san wand ayake bautawa ya kuma san hakikanin ibada:
(وَمَا خَلَقْتُ الْجِنَّ وَالاْنسَ إِلاَّ لِيَعْبُدُونِ)[1]
Ban halicci mutum da Aljani face domin su bauta mini.
Haka na kasance tare da hankali da ya samu karfafa da wahayi, sannan larurar aiko da Annabawa ta kasance, sannan Halifanci da Imamanci da gadon ilimi.
Daga cikin mafi muhimmancin wazifofi da mas'uliya shi ne tsarkake zuciya da ruhi da tarbiyantuwa da tarbiyar ubangiji da sigarsa da launinsa da rininsa tsarkakakke.
(صِبْغَةَ اللّهِ وَمَنْ أَحْسَنُ مِنَ اللّهِ صِبْغَةً)[2]
Rinin Allah wanene yafi kyawunta rini daga Allah.
Da kammalata da falaloli da kyawawan halaye, sannan kololuwar hadafi daga baki dayan wadannan abubuwa shi ne kaiwa zuwa ga alheri da farin ciki na har abada.
Hakika Malaman Falasafa sun sassaba cikin mafhumin alheri da hakikaninsa, sunce: ya kasu zuwa kashi biyu: Mudlaki da Muzafi, shi Mudlaki abin nufi daga gare shi shi ne samar da baki daya, domin shi kowa da kowa yana shauki gare shi shi burin da ake son cimma, shi kuma Muzafi shi ne wanda ta hanyarsa ake kaiwa zuwa ga Mudlaki.
Farin ciki: shi ne kowanne mutum karkashin motsawarsa ta gudanarwa ya kai ga zuwa ga boyayyar kamala da take kunshe cikinsa da halittarsa, da wannan ne ake samun banbanci tsakanin alheri da farin ciki, shi alheri baya banbantuwa dangane d amutane, amma farin ciki yana banbanta garesu.
Yana bayyanar mana daga zantukan Mu'alluml Awwal Arasto: alheri mudlaki shi kamaloli ne na rai, shi kuma alheri muzafi tsani ne na kaiwa ga mudlaki kamar koyon karatu da don samun ilimi, ko kuma mai amfani cikinsa misali dama da dukiya.
Babban Malami Aklak Muhakkikul Naraki cikin littafinsa mai daraja (Jami'ul Sa'adat j 1 sh 70) ya gangara kan bahasin alheri da farin ciki daga karshen bahasinsa yana cewa: wannan kenan kuma hakika ya bayyana daga kalmomin dukkaninsu cewa hakikar alheri da farin ciki bawani abu bane face ma'arifa ta gaskiya da kyawawan dabi'u, idan lamarin ya kasance haka ta yanda yake lallai hakikaninsu shi ne abin da nema ga zatinsa wanzacce tare da rai har abada suma haka,sai dai cewa babu kokwanto kan cewa abind ayake rattabuwa a kansu daga son Allah da nutsuwa da shi da farin ciki na hankali da jin dadin ruhi suna sabawa da su ta fuskanin la'akari idan ma bai rabu da sub a, bukatarsa ga kansa tafi tsananta da karfafa, shi yafi dacewa a kira da sunan alheri da farin ciki duk dacewa baki dayansu alheri da farin ciki.
Da wannan ne muke samu baki daya tsakanin zantukan manyan malamai ma'abota mahanga da dalili, da ma'abota kashafi da ma'abota riko da zahiri daga Malamai, bangare na farko sun tafi kan cewa hakikar farin ciki shi ne hankali da ilimi, bangare na biyu kuma sun tafi kan cewa: soyayya ce da kauna, na uku kuma suka ce: zuhudu da barin duniya.
Maganarsa ta kare Allah ya daukaka mukaminsa.