Deprecated: __autoload() is deprecated, use spl_autoload_register() instead in /home/net25304/al-alawy.net/req_files/model/htmlpurifier-4.4.0/HTMLPurifier.autoload.php on line 17
Dayantacciyar halitta - CIKIN HALLARAR ALHERI
فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها

Dayantacciyar halitta

Sannan ubangiji matsarkaki ya sanya halittar mutum dayantacciya tana imani da Allah matsarkaki tana kuma karkata gare shi ta nufeshi, wannan duka cikin ma'anar halitta ta fidira kaga shi ne makagin sammai da kassai, kuma dukkanin abin haihuwa ana haifarsa a kan fidira (shiriya) shiriyar Allah da ya halicci mutane kanta wancananka shi ne addini na daidai, ya sanya halittarsa dayantacciya jijiyoyi guda uku da suke samun karfinsu da asalinsu daga Allah matsarkaki, shi ne son kyawu da kamala da son alheri, kowanne mutum tare da lafiyayyar halittarsa yana son yana yana samun kamala yana kammala yana son yaga ya kasance kyakkyawa tsaftatacce a zahirinsa da badininsa, kamar yanda yake son alheri ga kansa da waninsa, babu wanda aka haifa a `Dagutu Mujrimi a kankin kansa ko kan jama'a, babu wanda aka haifa Kafiri ko Mushriki, bari dai ana haifar kowa kan shiriyar Allah ta tauhidi (babu abin bautawa sai Allah) sai dai cewa iyayensa ne su Yahudantar da shi suna ce masa (Uzairu `dan Allah ne) ko kuma su mayar da shi Banasare kirista suce akwai Alloli uku (Uba da `da da tsarkakakken ruhi) ko kuma su mayar da shi Bamajuse usce akwai ubangijin alheri da ubangijin sharri, ko kuma ubangiji haske da duhu.

Ita halitta tare da lafiyarta da kuma rashin gurbatarta da gurbataccen mahalli tana karkata ta nufi ubangiji da ma'asumin dalilinta, lallai dalilin halitta dalili ne ma'asumi daga kuskure kuma tana son alheri da kyawu da kamala