■ Alheri da Sharri cikin rubutu
■ Fasali na (1)
■ Dayantacciyar halitta
■ Dabi'ar halin sharri cikin mutum
■ Alheri a luggance da Isdilahi
■ Ayoyin Alheri cikin Kur'ani Mai girma
■ Mafhumin alheri da misdakansa
■ Tafisirin alheri da kashe-kashensa daga kassi da Ammi daga cikin daidaiku da jama'a
■ Kebantaccen alheri daidaiku
■ Gamammen alheri na zamantakewa
■ Sirri cikin alheri da sharri
■ Ma'anonin da alheri yake da shi cikin Kur'ani mai girma
■ Mutane ma'abota alheri
■ Mafi alherin cikin Muminai
■ Alheri daga cikin Kur'ani Mai girma
■ Fasali na biyu
■ Gaggawa zuwa ga ayyukan alheri
■ Fasali na uku
■ Alheri da sharri a wurin Majusawa
■ Alheri daga mahangar malaman Aklak
■ Fasali na hudu
■ Sharri (Kulli tashkiki) wani abune gamamme da yake banbantuwa da juna
■ Alheri da sharri karkashin hasken Nahajul Balaga
■ Alheri shine wazirin hankali sharri wazirin jahilci
- KIBIYOYIN RADDI KAN WUYAN WAHABIYAWA
- CIKIN HALLARAR ALHERI
- HUJJOJIN HALASCIN YIN TAKIYYA A MUSLUNCI DAGA MAHANGAR MANYAN MALAMAI GUDA BIYU
- FARKAR DA MAI BACCI CIKIN TABBATUWAR GANIN IMAM KA'IM A.S
- ALAMOMIN ANNABI CIIKIN KUR'ANI MAI GIRMA
- HAKURI DA FUSHI
- Bada'u tsakanin hakika da kagen makiya
- FALALAR DAREN LAILATUL KADRI
- WAHABIYANCI A TSAKANIN GUDUMA DA
- HASKEN SASANNI CIKIN SANIN ARZIKI
- AQIDUN MUMINAI
- FATIMA TAGAR HASKAYE
- SIRRIKAN AIKIN HAJJI DA ZIYARA
- TARBIYYAR IYALI A MAHANGAR ALKUR'ANI DA AHLULBAITI
Yayinda na daidaita halittarsa nay i busa cikinsa daga ruhina, na biyu kuma daga Alamul Sufli ta kasa ((ya halicce shi daga turbaya) kowanne guda daga biyun yana da abubuwa da suke lazimtarsa da abubuwa d ayake amsawa da haifarwa, haka lamarin yake daga wanda ya rakkabau daga dayantacciyar halitta –kamar yanda muka yi bayani a baya daga nafsul ammara bisu'i d aaka halitta a kan sharri sai kaga tana karuwa tana fajirci tana ketare iyakoki da dokoki da dagawa da zalunci, sai ta zabi sharri ta karkata zuwa gare shi, cikin wannan ma'ana ce ake cewa (mutum ya dabi'antu kan sharri) kamar yanda wannan ma'ana ta zo cikin riwaya mai daraja:
1 ـ قال أمير المؤمنين علي 7: «الشرّ كامن في طبيعة كلّ أحد، فان غلبه صاحبه بطن ، وإن لم يغلبه ظهر».
Sarkin Muminai Ali (a.s) ya ce: shi sharri yana nan boye cikin dabi'ar kowanne mutum, idan mutum yayi galaba kansa sai ya buya, idan kuma bai samu galaba kansa sai ya bbayana.
Ma'ana dai dole ne a zage dantse da kokari kan galaba kan sharri cikin gida daga biyewa son rai da sha'awe-sha'awe da tande-tande da karkace-karkace daga bari madaidaiciyar hanya tsakatsaki da kyawawan halaye, sai ka same shi yana karkata zuwa ga wuce gona da iri da takaitawa, idan ya samu nasara da galaba kan sharri sai sharri ya wanzu daure cikin badininsa ba zai iya komai ba, idna kuma bai yi galaba kansa ba bari dai shi sharrin ne ya samu galaba a kansa to a wannan lokaci zaka samu ya bayyana kan gabbansa sai mutum ya zama masharranci mutane su dinga jin tsorsana su nemi a nesanta shi daga cikinsu hukuma ta koreshi
2 ـ قال 7: أكره نفسک على الفضائل ، فان الرذائل أنت مطبوع عليها.
Amincin Allah ya tabbata a gare shi ya ce: ka tilastawa zuciyarka kan falaloli, hakika mugunyun dabi'u an dabi'antar da kai kansu.
3 ـ قال رسول الله 6: تكلّفوا فعل الخير ـ أي فيه كُلفة ومشقّة وليس من الأمر السهل والهيّن ـ وجاهدوا نفوسكم عليه ، فان الشرّ مطبوع عليه الإنسان .
Manzon Allah (s.a.w) ya ce: ku kallafama kawukanku yin ayyukan alheri (ma'ana cikinsa akwai tsanani da wahala bai da sauki)- ku yaki zukatanku kan yin aikin alheri, lallai an dabi'antar da mutum kan sharri.
وقال أمير المؤمنين 7: النفس مجبولة على سوء الأدب ، والعبد مأمور بملازمة حسن الأدب .
Sarkin Muminai Ali (a.s) ya ce: an halicci raio kan munana ladabi, shi bawa an umarce shi kan kyawunta ladabi.
A dabi'ar rai yana biyewa sabo, shi kuma bawa yana bakin iyawarsa kan dawo da rai daga munana ladabi, duk sanda ya sakar masa ragama da linzamito lallai yayi tarayya cikin batata da gurbatarta, duk wanda ya taimakawa ransa cikin batanta lallai yayi tarayya cikin halaka kansa, wajibi mu san mecece wannan halitta ina fagenta dole mu san rai da mahallinsa da kufaifayinsa da natijojinsa, tana iya ita wannan halitta fagenta da mahalinta ya kasance imani da akida, ita kuma rai fagenta ya kasance aiki da furuci.