b Mafhumin alheri da misdakansa - CIKIN HALLARAR ALHERI
فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها

Mafhumin alheri da misdakansa

Idan muka sao fadadawa cikin ma'anar alheri da mafhuminsa da misdakansa daga mahangar muslunci, zamu ga lallai yana da ma'anoni masu tarin yawa cikin fagage daban-daban, ga wasu yanki daga cikinsu karkashin abin da ya zo daga riwayoyi masu daraja:

قال أمير المؤمنين علي 7 :

1 ـ خير إخوانک من واساک وخير منه من كفاک .

Sarkin Muminai Aliyu (a.s) ya ce: mafi alherin `yan'uwanka shi ne wanda ya taimakeka mafi alherinsu wanda ya wadaceka.

2 ـ خير مالک ما أعانک على حاجتک .

Mafi alherin dukiyarka ita wacce ta taimakeka kan bukatarka.

3-Mafi alherin wanda ka yi hakuri kansa shi ne wanda ya zame maka dole.

4-Mafi alherin makullai wasu al'amura ne: gaskiya, mafi alherin hatimanta cika alkawali, ya zama dole kayi bakin iyawarka ka kasance cikin masu gaskiya cikin farawar kowanne aiki kamar yanda muke kasance masu cikawa a karshensa.

5-mafi alheri milla shi ne addini Ibrahim (a.s) ita milla itace al'umma da take da addini, magi alherin al'umma.

6-mafi alheri sunna ita ce sunnar Muhammad (s.a.w) lallai cikin alherin duniya da lahira yake.

7-mafi alherin guzuri zuwa lahira guzurin tsoran Allah.

8-mafi alherin ilimi shi ne ilimin da ya amfanar-ya Allah ni ina neman tsarinka daga ilimin da baya amfanarwa domin shi ne mafi girman hijabi daga sharri mai kisa.

9-mafi alherin ayyuka shi ne aikin da ya amfanar, amma aiki mara amfani tabbas zai gushe amma aiki mai amafanar da mutane shi wannan yana wanzuwa a doran kasa.

10-mafi alherin shiriya itace wacce akayiwa biyayya, amincin ya tabbata ga wadanda suka bi shiriya.

11-mafi alherin wadata itace wadatuwar zuciya-sau da yawa zaka samu mai wadata cikin kudade da dukiya sai dai cewa zaka sameshi kaskantacce matalauci cikin kyawawan halaye, misalin wannan mutumi yana rayuwa cikin talauci tsawon rayuwarsa ko da kuwa ya mallaki dukiyar Karuna.

12-mafi alheri abin da aka wurga cikin zuciya shi ne yakini.

13- mafi alherin hannuwa shi ne amfanuwa

14-mafi alherin garuruwa shi ne garin da ya karbeka-sai ka nemi gafara cikinsa ka samu nustuwa ka rayu cikinsa cikin karamci da izza cikin yalwar arziki daga yanci addini da ra'ayi da fadin albarkacin baki.

Tafisirin alheri da kashe-kashensa daga kassi da Ammi daga cikin daidaiku da jama'a

Ba dukkanin abin da mutane suke fada ne alheri ba , ya zama dole bayan ta'arifinsa ya zama ya samo asali daga ubangiji daga wahayi da hankali, da mutanen gida wadanda sune mafi sani daga abin da yake cikin gida, na nakasceka tafsiri daga shugabannin Ahlil-baiti:

قال أمير المؤمنين علي  7ليس الخير أن يكثر مالک وولدک ، ولكن الخير ان يكثر علمک ، وان يعظم حلمک ، وان تُباهي النّاس بعبادة ربّك ، فانّ أحسنت حمدت الله، وان أسأت استغفرت الله[1] .

 Sarkin Muminai Aliyu (a.s) ya ce: alheri ba shi ne dukiyarka da `ya`yanka su zamana sun yawaita ba, alheri shi ne iliminka ya yawaita hakurinka ya girmama, ka yiwa mutane kwarjini da bautawa ubangijinka, idan ka kyawunta ka godewa Allah, idan kuma ka munana sai ka nemi gafararsa.

Sau da yawa mutane suna tunanin cewa alheri kadai yana tare da wanda dukiyarsa da `ya`yansa suka yawaita, sai dai cewa alheri na hakika yana tare da wanda ya mallaki wadannan abubuwa na badini: hakuri da ilimi, lallai shi hakuri wazirin ilimi ne da shi yake maidawa Jahili jahilcinsa, da shi kuma yake bautawa Allah ta'ala, mutum cikin zantukansa da ayyukansa baya wofinta daga kasancewa mai kyautatawa, wannan ni'imace mai girma da yake godiya ga Allah kanta, ko kuma dai ya kasance mai munana aiki, sai ya nemi gafarar Allah ya tuba zuwa gare shi, lallai shi yana tsakankanin neman gafara da godiya.

وقال  7«فعل الخير ذخيرة باقية وثمرة زاكية».


amincin Allah ya tabbata a gare shi ya ce: aikin alheri wanzazziyar taskace tsarkakakkiyar riba ce.

قال الإمام الحسن  7«الخير الذي لا شرّ فيه : الشكر مع النعمة ، والصبر على النازلة»

Imam Hassan (a.s) ya ce: alherin da babu sharri cikinsa: shi ne godiya tare da ni'ima, hakuri kan musiba mai sauka.

وقال  7«العلم رأس الخير كلّه ، والجهل رأس الشرّ كلّه» «من يزرع خیراً يوشک أن يحصد خيراً».

Amincin Allah ya tabbata a gare shi ya ce: shi ilimi shi ne jagaban dukkanin alheri, jahilci shi ne jagaban dukkanin sharri, dukkanin wanda ya shuka alheri ya kusa ya girbi alheri.

قال أمر المؤمنين علي  7«ما خير بخير بعده النّار، وما شر شر بعده الجنّة ، وكلّ نعيم دون الجنّة فهو محقور. وكلّ بلاء دون النّار عافية».

Sarkin Muminai Aliyu (a.s) ya ce: dukkanin alherin da wuta take biyo bayansa to wannan ba alheri bane, kuma dukkanin sharrin da Aljanna ke biyo bayansa wannan ba sharri bane, dukkanin ma'abocin ni'ima da bata kaishi zuwa ga Aljanna lallai shi Wulakantacce ne, duk wani bala'I koma bayan wuta Afuwa ne.

Tana iya yiwu ka samu mutum da tarin `ya`ya da tarin dukiya  sai dai cewa tare da haka fitina ce gare shi kunace zuwa ga wuta, ba zasu kasance alheri gare shi zai kasance Wulakance, haka lamarin yake cikin kishiyar haka, ma'auni da Sikeli cikin sanin alheri da sharri shi ne Aljanna da wuta, wannan na nuna cewa tsakanin duniya da lahir akwai dangantaka mai karfi.

Ya ubangiji muna rokonka ka bamu kyakkyawa a duniya da lahira ka tseratar damu daga azabar wuta da Ashararai da sharrukansu, muna neman tsarinka daga sharrin kawukanmu.