b Tafisirin alheri da kashe-kashensa daga kassi da Ammi daga cikin daidaiku da jama'a - CIKIN HALLARAR ALHERI
فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها

Tafisirin alheri da kashe-kashensa daga kassi da Ammi daga cikin daidaiku da jama'a

Ba dukkanin abin da mutane suke fada ne alheri ba , ya zama dole bayan ta'arifinsa ya zama ya samo asali daga ubangiji daga wahayi da hankali, da mutanen gida wadanda sune mafi sani daga abin da yake cikin gida, na nakasceka tafsiri daga shugabannin Ahlil-baiti:

قال أمير المؤمنين علي  7ليس الخير أن يكثر مالک وولدک ، ولكن الخير ان يكثر علمک ، وان يعظم حلمک ، وان تُباهي النّاس بعبادة ربّك ، فانّ أحسنت حمدت الله، وان أسأت استغفرت الله[1] .

 Sarkin Muminai Aliyu (a.s) ya ce: alheri ba shi ne dukiyarka da `ya`yanka su zamana sun yawaita ba, alheri shi ne iliminka ya yawaita hakurinka ya girmama, ka yiwa mutane kwarjini da bautawa ubangijinka, idan ka kyawunta ka godewa Allah, idan kuma ka munana sai ka nemi gafararsa.

Sau da yawa mutane suna tunanin cewa alheri kadai yana tare da wanda dukiyarsa da `ya`yansa suka yawaita, sai dai cewa alheri na hakika yana tare da wanda ya mallaki wadannan abubuwa na badini: hakuri da ilimi, lallai shi hakuri wazirin ilimi ne da shi yake maidawa Jahili jahilcinsa, da shi kuma yake bautawa Allah ta'ala, mutum cikin zantukansa da ayyukansa baya wofinta daga kasancewa mai kyautatawa, wannan ni'imace mai girma da yake godiya ga Allah kanta, ko kuma dai ya kasance mai munana aiki, sai ya nemi gafarar Allah ya tuba zuwa gare shi, lallai shi yana tsakankanin neman gafara da godiya.

وقال  7«فعل الخير ذخيرة باقية وثمرة زاكية».


amincin Allah ya tabbata a gare shi ya ce: aikin alheri wanzazziyar taskace tsarkakakkiyar riba ce.

قال الإمام الحسن  7«الخير الذي لا شرّ فيه : الشكر مع النعمة ، والصبر على النازلة»

Imam Hassan (a.s) ya ce: alherin da babu sharri cikinsa: shi ne godiya tare da ni'ima, hakuri kan musiba mai sauka.

وقال  7«العلم رأس الخير كلّه ، والجهل رأس الشرّ كلّه» «من يزرع خیراً يوشک أن يحصد خيراً».

Amincin Allah ya tabbata a gare shi ya ce: shi ilimi shi ne jagaban dukkanin alheri, jahilci shi ne jagaban dukkanin sharri, dukkanin wanda ya shuka alheri ya kusa ya girbi alheri.

قال أمر المؤمنين علي  7«ما خير بخير بعده النّار، وما شر شر بعده الجنّة ، وكلّ نعيم دون الجنّة فهو محقور. وكلّ بلاء دون النّار عافية».

Sarkin Muminai Aliyu (a.s) ya ce: dukkanin alherin da wuta take biyo bayansa to wannan ba alheri bane, kuma dukkanin sharrin da Aljanna ke biyo bayansa wannan ba sharri bane, dukkanin ma'abocin ni'ima da bata kaishi zuwa ga Aljanna lallai shi Wulakantacce ne, duk wani bala'I koma bayan wuta Afuwa ne.

Tana iya yiwu ka samu mutum da tarin `ya`ya da tarin dukiya  sai dai cewa tare da haka fitina ce gare shi kunace zuwa ga wuta, ba zasu kasance alheri gare shi zai kasance Wulakance, haka lamarin yake cikin kishiyar haka, ma'auni da Sikeli cikin sanin alheri da sharri shi ne Aljanna da wuta, wannan na nuna cewa tsakanin duniya da lahir akwai dangantaka mai karfi.

Ya ubangiji muna rokonka ka bamu kyakkyawa a duniya da lahira ka tseratar damu daga azabar wuta da Ashararai da sharrukansu, muna neman tsarinka daga sharrin kawukanmu.