■ Alheri da Sharri cikin rubutu
■ Fasali na (1)
■ Dayantacciyar halitta
■ Dabi'ar halin sharri cikin mutum
■ Alheri a luggance da Isdilahi
■ Ayoyin Alheri cikin Kur'ani Mai girma
■ Mafhumin alheri da misdakansa
■ Tafisirin alheri da kashe-kashensa daga kassi da Ammi daga cikin daidaiku da jama'a
■ Kebantaccen alheri daidaiku
■ Gamammen alheri na zamantakewa
■ Sirri cikin alheri da sharri
■ Ma'anonin da alheri yake da shi cikin Kur'ani mai girma
■ Mutane ma'abota alheri
■ Mafi alherin cikin Muminai
■ Alheri daga cikin Kur'ani Mai girma
■ Fasali na biyu
■ Gaggawa zuwa ga ayyukan alheri
■ Fasali na uku
■ Alheri da sharri a wurin Majusawa
■ Alheri daga mahangar malaman Aklak
■ Fasali na hudu
■ Sharri (Kulli tashkiki) wani abune gamamme da yake banbantuwa da juna
■ Alheri da sharri karkashin hasken Nahajul Balaga
■ Alheri shine wazirin hankali sharri wazirin jahilci
- KIBIYOYIN RADDI KAN WUYAN WAHABIYAWA
- CIKIN HALLARAR ALHERI
- HUJJOJIN HALASCIN YIN TAKIYYA A MUSLUNCI DAGA MAHANGAR MANYAN MALAMAI GUDA BIYU
- FARKAR DA MAI BACCI CIKIN TABBATUWAR GANIN IMAM KA'IM A.S
- ALAMOMIN ANNABI CIIKIN KUR'ANI MAI GIRMA
- HAKURI DA FUSHI
- Bada'u tsakanin hakika da kagen makiya
- FALALAR DAREN LAILATUL KADRI
- WAHABIYANCI A TSAKANIN GUDUMA DA
- HASKEN SASANNI CIKIN SANIN ARZIKI
- AQIDUN MUMINAI
- FATIMA TAGAR HASKAYE
- SIRRIKAN AIKIN HAJJI DA ZIYARA
- TARBIYYAR IYALI A MAHANGAR ALKUR'ANI DA AHLULBAITI
A bayanne yake alheri daga Allah shi ne wanda Allah ya nufe shi ga bawansa, na nakasceka wasu curi daga riwayoyi da suke nuni kan idan Allah ya nufi bawansa da alheri me yaek yi masa yaya yake ilmintar da shi da tarbiyantar da shi, lallai shi ne mai tarbiyar talikai, yana sanar da mutum abin da mai sani ba.
1 ـ قال الإمام الصادق 7: «إذا أراد الله بعبد خيراً زهده في الدنيا، وفقهه في الدين ، وبصّره عيوبها، ومن أُوتين فقد أوتي خير الدنيا والآخرة .
Imam Assadik (a.s) ya ce: idan Allah ya nufi bawansa da alheri yana nesantar da shi daga duniya, ya fahimtar bashi fahimta cikin addini, ya nuna masa aibobin duniya, lallai duk wanda aka bashi wadannan abubuwa hakika an bashi alherin cikin duniya da lahira.
Sanannen lamari kuma
bayananne cewa Allah matsarkaki ya baiwa Annabawansa da Waliyansa da A'imma
tsarkaka matattarar zantuka ma'ana takaitaccen zance da yake kunshe da taskokin
ilimi da ma'arifa, bayananne lamari mai tajalli kan hadisan Ahlil-baiti: shi ne
cewa zantukansu suna daga dunkulallun zantuka da suka tattaro hikimomi idna
Allah ya so bawansa da alheri cikin misalin wannan makamin lallai Allah daga
ludufinsa ya hsiryar da mutane baki daya da shiriyar ta halitta da shari'a, duk
wanda ya karbi shriyarsa ta fari lallai zai kara masa haske kan haske, idan ya
kasance daga ma'bota alheri sai Allah ya kara masa alheri, Allah ya nufi
rahamarsa da jinkansa ga Muminai a kebance da masu kyautata aiki yana kara musu
alheri da ilimi da hikima, lallai yand al'amarin yake shi ne duk wanda Allah ya
bashi hikima hakika ya bashi alheri mai tarin yawa, ya kama yayi taka tsantsan
da zuhudu cikin duniya kana ya rudu da ita, kada yayi kwadayi cikinta, bari da
ya dauke wurin da zai shuka domin lahirarsa, (lallai duniya wurin shuka ce
domin lahira kasuwar Waliyan Allah ce) sai yayi zuhudu cikinta a kankin kanta,
sannan shi zuhudu bashi ne wai kada ka mallako komai ba, zuhudu shi ne kada ka
bari duniya da abin da yake cikinta su mallakeka, sannan bayan zuhudu Allah ya
fahimtar da mutum addininsa, hakika Kalmar fikhu a luggance tana da ma'anar
fahimta kuma ya zamana mutum yayi aiki karkashin hasken fahimta da ilimi,
sannan Allah ya haska masa aibobin duniya da na kankin kansa, a dabi'ance yake
cewa lafiyayyen hankali da halitta basu kaunar aibu mai aibu, sannan dukkanin
aka bashi wadannan abubuwa guda uku hakika an bashi alherin duniya da lahira,
ma'ana wadannan abubuwa da ma ire-irensu suna amfanarwa duniya da lahira suna
samarwa mutum da farin ciki a duniyarsa da lahirarsa.
2 ـ قال رسول الله 6: «إذا
أراد الله بعبد خيراً فقهه في الدين وألهمه رشده».
Manzon Allah (s.a.w) ya ce: idan Allah ya nufi bawansa da alheri sai ya fahimtar da shi addini da kimsa masa shiriyarsa.
Wannan yana daga mafi kyawun hadisai masu bushara da shiriyarwa kan ilimin ilhama, kamar yanda Allah matsarkaki yake wahayi ya zuwa ga Kudan Zuma yake kimsa masa shiriyarsa cikin samarwa kansa rayuwa da tafiyar da ita cikin kebantaccen tsari, haka zalika yake kimsawa bawansa da ya nufeshi da alheri da gyara sai ya ajiye abubuwa a muhallanssu, ya kasance ma'abocin hankali da hikima da adalci cikin rayuwarsa, sannan alherinsa ketare daga kansa zuwa waninsa, ya gyara masa abokin rayuwarsa, sannan daga cikin mafimuhimmancin rukunan rayuwar mutum shi ne sulhu da kauna da rahama da jin kai su kasance cikin danginsa da iyalansa, sannan ubangiji ya azurta shi da wadatar zuciya.
3 ـ قال أمير المؤمنين علي 7: «إذا أراد الله بعبدٍ خيراً ألهمه القناعة ـ فيقنع بما رزقه الله سبحانه ـ وأصلح له زوجه .
Sarkin Muminai Aliyu (a.s) ya ce: idan Allah ya nufi bawansa da alheri yana kimsa masa wadatar zuciya, sai ya wadatu da abin da Allah ya azurta shi, ya sulhunta masa matarsa.
4 ـ وقال 7: «إذا أراد بعبد خيراً فقهه في الدّين وألهمه اليقين».
Amincin Allah ya tabbata a gare shi ya ce: idan Allah ya nufi bawansa da alheri yana fahimtar da shi addini kuma ya kimsa masa yakini.
Yakini me kasani dangane da yakini lallai shi yana daga abu mai tsada da daraja daga ni'imomin ubangiji, me yafi yawa daga nassoshin Kur'ani da riwayoyi da suke shiryar kan daraja da falala da girman yakini, idan Allah ya so bawansa da alheri yana kimsa masa yakini, sai ya dinga kawo komai kan bayyana da haske da imani da yakini ba tare da shakka ko kokwanto ba.
5 ـ وقال 7: «إذا أراد الله بعبد خيراً ألهمه الاقتصاد وحسن التدبير، وجنبه سوء التدبير والإسراف».
Amincin Allah ya tabbata gare shi ya ce: idan Allah yaso bawa da alheri yana kimsa masa tattali da kyawunta tafiyarwa, ya nesanci almubazzaranci da munana gudanarwa.
Wannan yana nuni kan yi tsakatsaki da tattali cikin rayuwa, sai mutum ya san yaya zai juya kudinsa da kyawunta gudanarwa zuwa yanzu mun san wasu adadin abubuwan alheri da Allah yake baiwa bawansa, sune kamar haka: 1zuhudu cikin duniya 2 fikhu da fahimtar addini 3 fadaka kan aibobin duniya da kankin kai 4 kimsawa mutum shiriyarsa 5 kimsa masa wadatar zuciya 6gyaran rayuwarsa ta aure 7 kimsa masa yakini 8 tsakatsaki da tattali da kyawunta gudanar da rayuwa 9 kauracewa Almubazzaranci.
Sannan akwai wasu wuraren da zan fito maka da su daga nassoshin addini karkashin koyarwar makarantar Ahlil-baiti amincin Allah ya tabbata a garesu, wadannan lamurra sune: 10 kame kiyaye ciki da Farji daga haramun 11 daidaitaccen hankali da mikakken aiki 12 samar da mai wa'azi daga gare shi da zai dinga umartarsa da hana shi 13 yana mai bude masa aiki na nagari gabanin mutuwarsa sannan Allah ya karbi ransa ya koma zuwa gare shi 14 yana bude masa aiki nagari lokacin mutuwarsa har sai wanda suke kewaye da shi sun gamsu da shi 15 yan zarginsa cikin barcinsa 16 ya tsarkake shi da aikin nagari da yake kimsa masa gabanin mutuwarsa har ya karbi ransa kansa 17 ya bude masa kullewar zuciyarsa ya sanya yakini da gaskiya cikinta 18 ya sanya zuciyarsa ta kasance mai kira zuwa ga abin da ya mallaka cikinta 19 ya sanya zuciyarsa ta kasance lafiyayya 20 ya sanya harshensa ya kasance mai fadin gaskiya 21 ya sanya halayensa su kasance daidaitattu 22 ya sanya kunnuwansa su kasance masu ji 23 ya sanya idanunsa su kasance masu gani yana ganin gaskiya ranar lahira ba za a tashe shi Makaho ba 24 ya sanya zuciyarsa ta kasance mai neman gaskiya 25 Allah ya shiryar da shi zuwa ga imani 26 ya kyautata dabi'unsa 27 Allah bai jarrabeshi da rowa 28 Allah ya haskaka zuciyarsa daga haske 29 ya bude kofofin kunnensa 30 ya sanya masa Mala'ika da zai dinga daidaita shi
(فَمَن يُرِدِ اللّهُ أَن يَهْدِيَهُ يَشْرَحْ صَدْرَهُ لِلإِسْلاَمِ)
Duk wanda Allah yayi nufi shiriyarsa yana fadada kirjinsa da muslunci.
31ya fadada kirjinsa da muslunci sai harshensa ya dinga furuci da gaskiya 32 ya kulle zuciyarsa da muslunci 33 ya tattara baki dayan alheri cikin abubuwa guda uku: kallo, shiru, magana, dukkanin kallon da lura cikinsa wannan kallo rafkana ne, dukkanin shirun da cikinsa babu zurfafa tunani gafala ne, dukkanin maganar da cikinta babu tunawa da Allah to wannan magana surutu banza ce, farin ciki gag a wanda kallonsa ya kasance fadaka, shirunsa zurfafa tunani, maganarsa ambaton Allah, yayi kuka kan kuskuran da ya aikata, mutane suka amintu daga sharrinsa.
34 naga dukkanin alheri ya tattaru cikin yanke kwadayi daga abin da yake hannun mutane.
35 daga cikin hadisai masu kayatarwa da suka tattaro dukkanin alheri akwai hadisin da aka karbo daga Imam Bakir (a.s)
الإمام الباقر 7: أوحى الله إلى آدم 7: «يا آدم ، إنّي أجمع لک الخير كلّه في أربع كلمات : واحدة منهن لي ، وواحدة لک ، وواحدة فيما بيني وبينک ، وواحدة فيما بينک وبين النّاس ، فأمّا التي لي فتعبدني ولا تشرک بي شيئاً، وأمّا التي لک فأجازيک بعملک أحوج ما تكون إليه ، وأمّا التي بيني وبينک : فعليک الدعاء وعليّ الإجابة ، وأمّا التي فيما بينک وبين النّاس ، فترضى للنّاس ما ترضى لنفسک».
Allah yayi wahayi ga Adamu (a.s) ya Adamu lallai ni zan tattaro maka alheri baki dayansa cikin kalmomi hudu: daga daga cikinsu gareni take, daya kuma taka ce, daya tsakanina da kai, daya kuma tsakaninka da mutane, amma wacce take taw ace shi ne ka bauta mini kada kai mini tarayya da komai, amma wacce take gareka shi ne zan maka sakayya da aikinka da kafi bukatuwa zuwa gare shi, amma wacce take tsakaninka dani na nakasceka da riko da yin addu'a nayi maka alkawarin amsawa, amma wacce take tsakaninka da mutane ka yardarwa da mutane abin da kake yardarwa ga kanka.
35 dukkanin alheri yana cikin kiyaye harshe, Allah ya tattare alheri cikin mutum yak are harshensa da kansa daga aibobi da miyagun ayyuka da alfasha da munana ladabi.
36ـ عن الإمام الصادق 7: «ما على أحدكم أن ينال الخير كلّه باليسير»؟ قال الراوي : قلت : بماذا جعلت فداک؟ قال : «يسّرنا بادخال السرور على المؤمنين من شيعتنا».
An karbo daga Imam Assadik (a.s): me ya hana dayanku ya ribace baki dayan alheri da kankanin abu? Sai mai riwaya ya ce: nace masa: da menene Allah ya sanya raina fansarka? Sai ya ce: ya faranta mana ta hanyar shigar da farin cikin kan Muminai daga `yan shi'armu.
37 abubuwa uku sun tattaro alheri: ni'imta waninka, kiyaye alfarma, sadar da zumunci.
38 matattarar alheri yana cikin yin aiki da abin da zai wanzu da ku da kai daga abin da yake karewa.
39 matattarar alheri yan cikin wilaya domin Allah, kiyayya domin Allah, soyayya domin Allah, da yin gaba domin Allah.
40 Allah ya sanya baki dayan sharri cikin wani gida ya sanya makullin gidan cikin son duniya-son duniya shi ne jagaban dukkanin laifi-sannan ya sanya baki dayan alheri cikin wani gida ya sanya makullin gidan cikin gudun duniya.
41 duk mutumin da aka haramta masa tausayi an haramta masa dukkanin alheri 42 kadai ana riskar baki dayan alheri da hankali, babu addini ga wanda baya da hankali –wannan yana nuni kan girman hankali da aiki da shi cikin rayuwar Mumini 43 ilimi shi ne jagaban dukkanin alheri, Jahilci shi ne jagaban dukkanin sharri 44 dukkanin alheri yana cikin wanda ya san mutuncin kansa –farin ciki ya tabbata ga wanda ya san darajar kansa baya mikar da kafarsa fiye inda ya halasta ta mika kuma shi baya wulakantar da kansa sabida tarkacen duniya da kayan dadinta 45 dukkanin alheri ya tattaru cikin tsoran Allah da girmama shi.