فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها

Sirri cikin alheri da sharri

Daga cikin sirrin hadisai cikin alheri da sharri akwai hadisin da  ya zo cikin littafin Alkafi da isnadinsa daga Imam Sadik (a.s)  

الإمام الصادق  7 قال : «إن أوحى الله إلى موسى  7 وأنزل عليه في التوراة : إنّي أنا الله لا إله إلّا أنا، خلقت الخلق وخلقت الخير، وأجريته على يدي من أحب ، فطوبى لمن أجريته على يديه .

وأنا الله لا إله إلّا أنا خلقت الخلق وخلقت الشّر، وأجريته على يدي من أُريده ، فويل لمن أجريته على يديه»[1] .

 Imam Assadik (a.s) ya ce: hakika Allah yayi wahayi zuw aga Musa (a.s) ya saukar masa cikin Attaura: lallai ni ne Allah babu abin da bautawa sai ni, na halicci dukkanin halittu na halicci alheri na gudanar da shi kan hannun wanda na ke so, farin ciki ya tabbata kan hannayensa.

Kuma ni Allah babu abin bautawa sai ni na halicci sharri na gudanar da shi kan hannun wanda na nufa, azaba ta tabbata kan wanda na zartar da shi kan hannunsa.

Ina cewa: duk wanda ya kasance abin so cikin ilimin Allah sakamakon azurtarsa cikin yunbun halittarsa da ruhinsa zababb, lallai zai samu dacewa da taufikin Allah zuwa ga ayyukan alheri, sai Alllah ya zartar da alherai ta hannunsa, tofa ya kamata ya kauracewa gori da cutar da wanda ya taimakawa, kamar yanda ya zo cikin Du'a'u Makarimul Aklak

«واجر على يدي الخير ولا تمحقه بالمنّ والأذى».

Kuma ka gudanar da alheri a hannuna ka kuma ka goge shi da gori da cutarwa.

Dukw wanda ya kasance daga tsiyatattu cikin yunbun halittarsa da ruhinsa ma'abociyar sharri sakamakon zabar sabawa Allah da aikata zunubai da shirka da kafirci ba tare da ya tuba ba, lallai Allah zai gudanar da sharri kan hannuwansa.

Ya zo cikin littafin (Ilmul Yakini) wallafar Maula Faizul Kashani: amma banbanci rayuka cikin haka, da rashin daidaituwarsu cikin alheri da sharri da sassabawarsu cikin farin cikin da tsiyat, ya kasance sakamakon sassabawar tanadi da shiri da nau'antakar tabbatattun abubuwa, hakika sinadaran kaskantattu sun kasance biye da tsarin halittar hakika, da take banbantuwa cikin taushi da kauri, sannan dandanonsu mabanbanta ne cikin kusanci da nesanci daga daidato na hakika da ruhin mutane mabanbanta biye da halitta ta farko cikin tacewa da daudantuwa da karfi da rauni, suna jere cikin darajojin kusanci da nesanci ga Allah ta'ala, kasantuwat tabbatuwa kan kishiyar kowanne daya daga cikin sinadari akwai abin da yake dacewa da shi daga farko , saboda haka mafi kyawun kamaloli suna tare da mafi cikar tanadi da shiri , haka zalika mafi munin tanadi da shiri yana tare da mafi tawayarsu, kamar yanda yayi ishara zuwa gare shi da fadinsa (a.s)

«النّاس معادن كمعادن الذهب والفضّة ، خيارهم في الجاهلية خيارهم في الإسلام»[2] .

 Su mutane ma'adanai ne kamar ma'adanan zinariya da azurfa, mafi alherinsu a zamanin Jahiliya sune mafi alheri dai a zamanin muslunci.

Ina cewa: wannan baya cin karo tare da asalin (al'amari tsakanin al'amura biyu) cikin mas'alar Jabar da tafwizi kamar yanda ya tabbata a muhallinsa, nayi bayani dalla-dalla cikin littafin (Alhakku wal hakika baina Jabar wat tafwizi) an buga shi cikin risalar (Lum'atul Afkar fil Kairi wal Iktiyari) an buga su cikin Mausu'ar (Risalatul Islamiyya) sai aduba can.

Ya zo cikin littafin Attauhid na shaik Saduk:

باسناده عن معاذ بن جبل قال : قال رسول الله 6«سبق العلم وجفّ القلم» ومعنى القَدَر بتحقيق الكتاب وتصديق الرسل ، وبالسعادة من الله عزّ وجلّ لمن آمن وأتّقى ، وبالشقاء لمن كذب وكفر ـ وهذا يدل على ان الإيمان والكفر من العبد وينسبان إليه ـ وبولاية الله للمؤمنين وببرائته من المشركين

Da isnadinsa daga Mu'azu Ibn Jabal ya ce: Manzon Allah (s.a.w) ya ce: ilimi ya rigaya ya gabata kuma Alkalami ya bushe. Ma'ana kaddara da tabbatuwar littafi da gasgata Manzanni da farin ciuki daga Allah Azza wa Jalla ga wanda yayi imani yaji tsoran Allah, da kuma tsiyata da wanda ya karyata su ya kafirce-wannan na nuni kan cewa Imani da kafirci daga bawa suke gangarowa sannan ake danganta su zuwa gare shi-da wilayar Allah ga Muminai da barrantarsa daga Mushrikai

ثمّ قال رسول الله 6: عن الله أروي حديثي : ان الله تبارک وتعالى يقول : يا ابن آدم بمشيّتي كنت أنت الذي تشاء لنفسک ما تشاء، وبإرادتي كنت أنت الذي تريد لنفسک ما تريد، وبفضل نعمتي عليک قويت على معصيتي ، وبعصمتي وعوني وعافيتي أدّيت إليّ فراضي ، فأنا أولى بحسناتک منک ، وأنت أولى بسيئاتک منّي ، فالخير مني إليک بما أوليت بداء ـ أي ابتداءً ـ والشرّ منّي إليک بما جنيت جزاءً، وبإحساني إليک قويت على طاعتي ، وبسوء ظنّک بي قنطت من رحمتي ، فلي الحمد والحجّة عليک بالبيان ، ولي السبيل عليک بالعصيان ، ولک جزاء الخير عندي بالإحسان ، لم أدع تدبيرک ، ولم آخذک عند عزمک ، ولم اكلّفک فوق طاقتک (طاعتک) ولم أُحمّلک من الأمانة إلّا بما قدرت (ما أقررت) به على نفسک ، رضيت لنفسي منک ما رضيت لنفسک منّي[3] .

 Sannan Manzon Allah (s.a.w) ya ce: daga Allah nake rawaito hadisina: hakika Allah arbarkoki da daukaka su tabbata a gare shi yana cewa: ya kai `dan Adam da mashi'ata ne kai kasance kai ne kake so ga kanka abin da kake so, kuma da iradata ka zama kai ne kake nufarwa kanka abin da duk kake nufi, da taimakona da afuwata ka sauke farillaina zuwa gareni, lallai ni mafi cancantuwa da kyawawanka kai kuma kai ne mafi cancanta da munanan ayyukanka daga gareni, alheri daga gareni zuwa gareka daga abin da ka jibantar da farko , sharri daga gareni zuwa gareka daga abin da ka aikata yana matsayin sakamako,da ihsanina gareka ka samu karfafa kan `da ata, sakamakon munana zatonka gareni ka debe tsammani daga samun rahamata , gareni godiya da hujja suke kanka da bayani, ni ina dama kanka sakamakon sabon da kayi, kana da sakamakon alherinka a wurina da ihsani, ban taba barin kula da kai ba, ban bata tuhumarka lokacin azamarka ba, ban taba dora maka abin da ba zaka iya b, ban taba dora maka amanar da ba zaka iya ban a yardarwa kaina daga gareka abin da ka yardarwa kanka.

Faizul Kashani ya ce: da isnadinsa daga Ibn Abi Umairu daga abin da yake kusanta daga gare shi daga Ahlil-baiti: abin da yake kusanta daga garesu su biyun: ma'ana mutanen gida da ubangiji.

Bayan doga bayani filla-filla cikin gubatar akidar Jabar da Tafwizi da ingancin al'amari tsakanin al'amura biyu sai ya ce: duk wanda yayi kallo zuwa ga sabubba na kusa-kusa ga aiki ya ganshi mai cin gashin kansa ya fadi akidar kaddara da tafwizi: akidar Mu'utazilawa da cewa dukkanin ayyukanmu daga garemu suke da ikonmu tsantsa.

Allah ya karemu daga wannan akida, hakika Allah ya daukaka daga ya kyale bawansa ya barshi da kansa, ya buwaya daga haka.

Wanda ya kalli sabubban farko yaki kallon sabubba na kusa-kusa ya tafi kan akidar Jabar da larura (Jabariya kamar misalin Ash'arawa) basu banbance tsakanin ayyukan mutum da ayyukan daskararrun halittu, lallai Allah shi ne mafi adalci daga daga tilasta halittunsa sannan yayi musu azaba, lallai shi ne mafi karamci daga ya kallafawa mutane abin da ba za su iya ba.

Dukkanin akidun biyu akidu ne na mai ido daya da baya gani da idanunsa biyu-biyu.

Su Kadariyya: suna masu kallo da idonsu na gefan dama, da mai karfin gani, wanda da shi ne ake riskar abubuwa da sabubba mafi nisan zango, kamar misalin mai ido gud adaya da yake cewa: (ni ne ubangijinku mafi daukaka)

Amma Jabariyya: su suna kallo da ido na gefan hagu, mafi rauni, wanda yake riskar abubuwa na zahiri da sabubba na kusa-kusa kamar misalin Iblis inda yake cewa: ya ubangiji na rantse da abin da ka halakar dani da shi) sai ya danganta halaka ga Allah, Iblis shi ne `dan Jabariyya na farko, Ash'arawa sawunsa suke bi.

Amma wanda yayi kallo da kallo na gaskiya zaka zuciyarsa tana idanu guda biyu-kammalalliyar basira, yana kallon gaskiya da idanun dama sai ya danganta dukkanin ayyuka zuwa ga Allah matsarkaki

 (قُلْ كُلًّ مِّنْ عِندِ اللّهِ)[6] .

 Kace dukkaninsu daga wurin Allah suke.

Zai ga halittu da idanunsa na hagu sai tabbatar da tasirinsu cikin ayyuka: hakan ya faru sakamakon abin da hannunka ya tsiwirta, sai dai cewa da horewar Allah bawai cikin cin gashin kai ba (babu tsimi babu dabara sai da Allah) da haka ne maganar Imam Assadik (a.s) take tabbata cikin fadinsa:

«لا جبر ولا تفويض بل أمر بين الأمرين»

Babu maganar Jabaru babu maganar tafwizi sai dai cewa wani al'amari tsakanin al'amuran biyu.

Sai kayi riko da shi matsayin Mazhaba gare shi kamar dai misalin `yan shi'a Imamiyya mabiya makarantar Ahlil-baiti (a.s) wannan shi ne abin da ake kira da babban rabo ne.

Sakamakon tadabuki tsakanin akidar jabaru da tafwizi, da dacewa tsakanin wajabci da yiwuwa, Allah acikin Kur'ani sai ya danganta ayyuka zuwa ga kansa, a wani lokacin kuma zuwa ga Mala'iku, wani karon kuma zuwa ga bayinsa, kamar yanda ya zo cikin karbar rai 

 (اللَّهُ يَتَوَفَّى الاْنفُسَ حِينَ مَوْتِهَا)[8]  (قُلْ يَتَوَفَّاكُم مَّلَکُ الْمَوْتِ الَّذِي وُكِّلَ بِكُمْ)[9] (قَاتِلُوهُمْ يُعَذِّبْهُمُ اللّهُ بِأَيْدِيكُمْ وَيُخْزِهِمْ)

Allah yake cikawa rayuka kwanakinsu lokacin mutuwarsu. Kace yana cika muku kwanakinku Mala'ikan mutuwa wanda aka wakilta shi kanku.

Ku yake su Allah zai azabtar da su da hannunku ya kunyata su.

Sai ya danganta kisa da yaki zuwa ga bayi ya danganta azaba zuwa ga kansa, ka lura sosai.