b Ma'anonin da alheri yake da shi cikin Kur'ani mai girma - CIKIN HALLARAR ALHERI
فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها

Ma'anonin da alheri yake da shi cikin Kur'ani mai girma

Kur'ani mai girma yayi ishara zuwa ga alheri a wurare takwas:

1- alheri: yazo da ma'anar dukiya daga cikin fadinsa madaukaki:

 (إِن تَرَکَ خَيْراً الْوَصِيَّةُ)

Idan ya bar wata dukiyya wasiyya.

2- alheri ya zo da ma'anar imani daga cikin fadinsa madaukaki:

 (وَلَوْ عَلِمَ اللّهُ فِيهِمْ خَيْراً)

Da Allah ya san wani alheri cikinsu.

Ma'ana imani, wannan aya ta sauka a lokacin yakin Badar, misalinsa fadinsa madaukaki:

 (إِن يَعْلَمِ اللّهُ فِي قُلُوبِكُمْ خَيْراً)

Idan Allah ya san wani alheri cikin zukatanku. Ma'ana imani.

3-alheri da ma'anar mafi falala daga cikin fadinsa madaukaki:

 (وَأَنتَ خَيْرُ الرَّازِقِينَ)

Kuma kaine mafi alherin masu azurtawa.

  (خَيْرُ الْحَاكِمِينَ) و (خَيْرُ الرَّاحِمِينَ).

Kai ne mafi alherin masu hukunci.

 kai ne mafi alherin masu jin kai.

4-alheri da ma'anar lafiya: daga cikin fadinsa madaukaki:

 (وَإِن يُرِدْکَ بِخَيْرٍ)

Idan Allah ya nufeku da alheri. Ma'ana lafiya

5-alheri da ma'anar lada da sakamako daga ciki akwai fadinsa:

 (جَعَلْنَاهَا لَكُم مِّن شَعَائِرِ اللَّهِ لَكُمْ فِيهَا خَيْرٌ)

Yayinda muka sanyata gareku daga abubuwan bautar Allah kuna da alheri cikinta. Ma'ana kuna da lada a ciki.

6-alheri da ma'anar abinci daga ciki akwai fadinsa madaukaki:

 (رَبِّ إِنِّي لِمَا أَنزَلْتَ إِلَيَّ مِنْ خَيْرٍ فَقِيرٌ)

Ya ubangiji lallai ni mabukaci ne daga abin da ka saukar gareni daga alheri. Ma'ana daga abinci

7-alheri da ma'anar nasara da ganima daga cikin fadinsa ta'ala:

 (وَرَدَّ اللَّهُ الَّذِينَ كَفَرُوا بِغَيْظِهِمْ لَمْ يَنَالُوا خَيْراً)

Kuma Allah ya mayar da wadanda suka kafirta da fushinsu basu samu wani alheri ba. Ma'ana basu samu ganima ba

8-alheri da ma'anar Dawakai: daga cikin fadinsa madaukaki:

 أي ظفراً وغنيمة .


 (إِنِّي أَحْبَبْتُ حُبَّ الْخَيْرِ عَن ذِكْرِ رَبِّي)

Lallai ni na fifita son alheri daga tunatarwar ubangijina. Ma'ana son Doki.

Wannan sune jumla daga ma'anonin alheri da misdakansa cikin Kur'ani mai girma.