■ Alheri da Sharri cikin rubutu
■ Fasali na (1)
■ Dayantacciyar halitta
■ Dabi'ar halin sharri cikin mutum
■ Alheri a luggance da Isdilahi
■ Ayoyin Alheri cikin Kur'ani Mai girma
■ Mafhumin alheri da misdakansa
■ Tafisirin alheri da kashe-kashensa daga kassi da Ammi daga cikin daidaiku da jama'a
■ Kebantaccen alheri daidaiku
■ Gamammen alheri na zamantakewa
■ Sirri cikin alheri da sharri
■ Ma'anonin da alheri yake da shi cikin Kur'ani mai girma
■ Mutane ma'abota alheri
■ Mafi alherin cikin Muminai
■ Alheri daga cikin Kur'ani Mai girma
■ Fasali na biyu
■ Gaggawa zuwa ga ayyukan alheri
■ Fasali na uku
■ Alheri da sharri a wurin Majusawa
■ Alheri daga mahangar malaman Aklak
■ Fasali na hudu
■ Sharri (Kulli tashkiki) wani abune gamamme da yake banbantuwa da juna
■ Alheri da sharri karkashin hasken Nahajul Balaga
■ Alheri shine wazirin hankali sharri wazirin jahilci
- KIBIYOYIN RADDI KAN WUYAN WAHABIYAWA
- CIKIN HALLARAR ALHERI
- HUJJOJIN HALASCIN YIN TAKIYYA A MUSLUNCI DAGA MAHANGAR MANYAN MALAMAI GUDA BIYU
- FARKAR DA MAI BACCI CIKIN TABBATUWAR GANIN IMAM KA'IM A.S
- ALAMOMIN ANNABI CIIKIN KUR'ANI MAI GIRMA
- HAKURI DA FUSHI
- Bada'u tsakanin hakika da kagen makiya
- FALALAR DAREN LAILATUL KADRI
- WAHABIYANCI A TSAKANIN GUDUMA DA
- HASKEN SASANNI CIKIN SANIN ARZIKI
- AQIDUN MUMINAI
- FATIMA TAGAR HASKAYE
- SIRRIKAN AIKIN HAJJI DA ZIYARA
- TARBIYYAR IYALI A MAHANGAR ALKUR'ANI DA AHLULBAITI
Idan muna son sanin alheri karkashin wanda ya rigantu da shi ya kasance daga mutane ma'abota alheri wajibi muyi duba zuw aga wadannan gungu daga nassoshi da suke shiryarwa zuwa ga haka: fadin Allah madaukaki:
1 (وَاذْكُرْ عِبَادَنَا إبْرَاهِيمَ وَإِسْحَقَ وَيَعْقُوبَ أُوْلِي الاَْيْدِي وَالاْبْصَارِ * إِنَّا أَخْلَصْنَاهُم بِخَالِصَةٍ ذِكْرَى الدَّارِ * وَإِنَّهُمْ عِندَنَا لَمِنَ الْمُصْطَفَيْنَ الاْخْيَارِ * وَاذْكُرْ إِسْمَاعِيلَ وَالْيَسَعَ وَذَا الْكِفْلِ وَكُلٌّ مِّنْ الاْخْيَارِ)[1] .
Ka ambaci bayinmu Ibrahim da Is'hak da Yakuba ma'abota karfi da basira* lallai mun kebance su da wata wani tsarkakken abu tunawa da gidan lahira* lallai su a wurinmu suna daga zababbu mafifita* ka ambaci Isma'ila da Yasa'a da Zulkiflu dukkaninsu suna daga mafifita
2 ـ قال رسول الله 6: «إنّ من خير رجالكم : التّقي السمح الكفين ـ كناية عن الجود والسخاء وسماح الخلق ـ التقي الطرفين ـ أي يراعي التقوى في سمعه وبصره ـ البرّ بوالديه ، ولا يُلجىء عباده إلى غيره».
Manzon Allah (s.a.w) ya ce: lallai daga cikin mafifitan mazajen cikinku: akwai ma'abocin takawa mai kyauta mai kiyaye dokokin Allah ta bangaren idanunsa da kunnuwansa, mai biyayya ga iyayensa, baya mayar da bayinsa zuwa ga waninsa.
3 ـ لما قيل لرسول الله: أحبُّ أن أكون خير النّاس : قال : «خير النّاس من ينفع النّاس ، فكن نافعاً لهم».
Yayinda wani ya gayawa Manzon Allah (s.a.w) cewa ina so in zama mafi alherin cikin mutane: sai ya ce: mafio alherin mutane shi ne wanda yake amfanar da su, ka zama mai amfani ga mutane.
4 ـ وقال 6: «خير النّاس منزلة رجل على متن فرسه يخيف العدو ويخيفونه ـ أي بطل في الإسلام مهاب مغوار».
tsira da
amincin Allah su kara tabbata a gare shi da iyalansa ya ce: mafi alherin mutane
cikin matsayi shi ne mutumin da ya kasance a kan Dokinsa yana tsorata Makiya
suma suna tsorata shi-ma'ana Jarumin mutum a muslunci mai cike da kwarjini.
5 ـ «خير الرجال من كان بطيء الغضب سريع الرّضا ـ وهذه من الصفات الإلهيّة سبحانه وتعالى».
Mafi alherin mazaje shi ne wanda ya kasance Mai jinkirin fushi da Mai saurin yarda-wannan na daga siffofin ubangiji mastarkaki madaukaki.
6 ـ قال أمير المؤمنين 7: «خير النّاس من نفع النّاس».
Sarkin Muminai (a.s) ya ce: mafi alherin mutane shi ne wanda ya amfanar da mutane.
7 ـ «خير النّاس من زهدت نفسه ، وقلت رغبته ، وماتت شهوته ـ فيأكل بشهوة أهله لا بشهوة نفسه ـ وخلص إيمانه ، وصدق إيقانه».
Mafi alherin mutane shi ne wanda ransa tayi zuhudu, kwadayinsa ya karanta, sha'awarsa ta mutu, yana cin abinci domin sha'awar iyalinsa bawai don tasa ba, imaninsa ya tace ya tsarkaku, yakininsa ya gasgatu.
8 ـ «خير النّاس من كان في يسره سخيّاً شكوراً، خير النّاس من كان في عسره موثراً صبوراً» (وَيُؤْثِرُونَ عَلَى أَنفُسِهِمْ وَلَوْ كَانَ بِهِمْ خَصَاصَةٌ).
Mafi alherin mutane shi ne wanda ya kasance mai kyauta da godiya a lokacin yalwata, mafi alherin mutane shi ne wanda ya kasance cikin kuntatarsa mai fifita waninsa kansa mai hakuri, (suna fifita wasunsu a kan kawukansu ko da kuwa suna da wata larura).
9 ـ «خير النّاس من أخرج الحرص من قلبه ، وعصى هواه في طاعة ربّه ـ كما في مراجع التقليد: مطيعاً لمولاه مخالفاً لهواه» ـ.
Mafi alherin cikin mutane shi ne mutum da ya cire kwadayi daga cikin zuciyarsa, ya sabawa son ransa cikin biyayyar ubangijinsa- kamar yanda yake cikin Maraji'an Taklidi mai biyayya ga ubangijinsa mai sabawa son ransa.
10 ـ «خير النّاس من طهّر من الشهوات نفسه ، وقمع غضبه ، وأرضى ربّه».
Mafi alherin mutane shi ne wanda ya tsarkaka daga sha'awe-sha'awen ransa, ya yiwa fushinsa takunkumi, ya yardarm da ubangijinsa.
11 ـ «خير النّاس من إن غضب حلم ، وان ظُلم غَفر، وان أُسيء إليه أحسن».
Mafi alherin mutane shi ne wanda idan yayi fushi sai ya danne fushinsa, idan aka zalunce shi sai ya yafe, idan aka munana masa shi sai ya kyautata.
12 ـ «خير النّاس من تحمّل مؤونة النّاس».
Mafi alherin mutane shi ne wanda ya dauki nauyin mutane.
13 ـ قال الإمام الصادق 7: «خياركم سمحاؤكم ، وشراركم بُخلاؤكم».
Imam Assadik (a.s) ya ce: mafi alherinku masu kyautar cikinku, mafi sharrin cikinku sune Marowantan cikinku.
14 ـ وقال 7: «إن خير العباد من يجتمع فيه خمس خصال : إذا أحسن استبشر، وإذا أساء أستغفر، وإذا أعطى شكر، وإذا ابتلي صبر، وإذا ظُلم غفر».
Amincin Allah ya tabbata a gare shi ya ce: hakika mafi alherin cikin bayi shi ne mutumin da abubuwa biyar suka tattaru cikinsa: idan ya kyautata sai yayi bushara, idan ya munana sai ya nemi gafara, idan akayi masa kyauta sai yayi godiya, idan aka jarrabeshi sai yayi hakuri, idan aka zalunce shi sai ya yafe.