■ Alheri da Sharri cikin rubutu
■ Fasali na (1)
■ Dayantacciyar halitta
■ Dabi'ar halin sharri cikin mutum
■ Alheri a luggance da Isdilahi
■ Ayoyin Alheri cikin Kur'ani Mai girma
■ Mafhumin alheri da misdakansa
■ Tafisirin alheri da kashe-kashensa daga kassi da Ammi daga cikin daidaiku da jama'a
■ Kebantaccen alheri daidaiku
■ Gamammen alheri na zamantakewa
■ Sirri cikin alheri da sharri
■ Ma'anonin da alheri yake da shi cikin Kur'ani mai girma
■ Mutane ma'abota alheri
■ Mafi alherin cikin Muminai
■ Alheri daga cikin Kur'ani Mai girma
■ Fasali na biyu
■ Gaggawa zuwa ga ayyukan alheri
■ Fasali na uku
■ Alheri da sharri a wurin Majusawa
■ Alheri daga mahangar malaman Aklak
■ Fasali na hudu
■ Sharri (Kulli tashkiki) wani abune gamamme da yake banbantuwa da juna
■ Alheri da sharri karkashin hasken Nahajul Balaga
■ Alheri shine wazirin hankali sharri wazirin jahilci
- KIBIYOYIN RADDI KAN WUYAN WAHABIYAWA
- CIKIN HALLARAR ALHERI
- HUJJOJIN HALASCIN YIN TAKIYYA A MUSLUNCI DAGA MAHANGAR MANYAN MALAMAI GUDA BIYU
- FARKAR DA MAI BACCI CIKIN TABBATUWAR GANIN IMAM KA'IM A.S
- ALAMOMIN ANNABI CIIKIN KUR'ANI MAI GIRMA
- HAKURI DA FUSHI
- Bada'u tsakanin hakika da kagen makiya
- FALALAR DAREN LAILATUL KADRI
- WAHABIYANCI A TSAKANIN GUDUMA DA
- HASKEN SASANNI CIKIN SANIN ARZIKI
- AQIDUN MUMINAI
- FATIMA TAGAR HASKAYE
- SIRRIKAN AIKIN HAJJI DA ZIYARA
- TARBIYYAR IYALI A MAHANGAR ALKUR'ANI DA AHLULBAITI
Ba a boye yake cewa shiriyar ubangiji ta kasu kashi biyu: wani lokacin ta kan kasancewa daga hidaya ibtida'iyya wacce ta game kowa da kowa daga rahama da jin kai ga Muminai da Kafirai wacce ta ta'allaka da jama'ar mutane kamar yanda yake cikin ayar da ta zo tana magana ga dukkanin mutane kamar misalin fadinsa ta'ala (shiriya ga mutane) sannan a wani karon kuma takan kasance daga hidaya sanawiyya wacce ta kebanta ga Muminai kadai wannan ya ta'allaka da jama'a masu imani kamar yanda yake cikin ayar Kur'ani (yaku wadanda suka yi imani) (shiriya ga masu takawa) sannan zancen kur'ani da yake gangarowa daga Manzon Allah da iyalan gidansa (a.s) wani lokacin yana kasance da kebantaccen harshe_ma'ana ga kebantattun mutane daga Muminai wani lokacin kuma zuwa ga baki dayan mutane, haka lamarin yake cikin mukamin magana kan mafi alherin mutane kamar yanda ya gabata, wani karon mafi alheri daga zababbun cikin Muminai, daga cikin wannan babi akwai abin da ya zo:
1 ـ عن رسول الله 6 قال : «خيركم من أعانه الله على نفسه فملكها».
Daga Manzon Allah (s.a.w) ya ce: mafi alherin cikinku shi ne wanda Allah ya taimake shi a kan zuciyarsa sai ya mallaketa.
2 ـ «خيركم من عرف سرعة رحلته ـ أي الموت الأتي سريعاً ـ فتزود لها ـ بالتقوى والعمل الصالح .
Mafi alherinku shi ne wanda ya san saurin mutuwarsa sai yayi guzuri da takawa da aiki nagari domin mutuwarsa.
3 ـ «خيركم عن يذكركم بالله رؤيته ».
Mafi alherinku shi ne wanda ganinsa yake tunatar da ku Allah
4 ـ أي الجلساء خير؟ قال : «من ذكركم بالله رؤيته ، وزادكم في علمكم منطقه».
Su wanene abokan zama na alheri? Ya ce: wanda ganinsa ya tunatar daku Allah, furucinsa ya kareku cikin ilimi.
5 ـ «خيركم من دعاكم إلى فعل الخير».
Mafi alherinku shi ne wanda ya kiraku ya zuwa ga aikin alheri.
6 ـ «خيركم المتنزّهون عن المعاصي والذنوب».
Mafi alherinku suna mutane da suka tsarkaku daga aikata sabo da zunubi.
7 ـ «خيركم
من أطعم الطعام ، وأفشى السلام ، وصلّى بالليل والنّاس نيام»
Mafi alherinku shi ne wanda ya ciyar da abinci, ya yada zaman lafiya, yayi sallah da daddare lokacin mutane na halin bacci.