■ Alheri da Sharri cikin rubutu
■ Fasali na (1)
■ Dayantacciyar halitta
■ Dabi'ar halin sharri cikin mutum
■ Alheri a luggance da Isdilahi
■ Ayoyin Alheri cikin Kur'ani Mai girma
■ Mafhumin alheri da misdakansa
■ Tafisirin alheri da kashe-kashensa daga kassi da Ammi daga cikin daidaiku da jama'a
■ Kebantaccen alheri daidaiku
■ Gamammen alheri na zamantakewa
■ Sirri cikin alheri da sharri
■ Ma'anonin da alheri yake da shi cikin Kur'ani mai girma
■ Mutane ma'abota alheri
■ Mafi alherin cikin Muminai
■ Alheri daga cikin Kur'ani Mai girma
■ Fasali na biyu
■ Gaggawa zuwa ga ayyukan alheri
■ Fasali na uku
■ Alheri da sharri a wurin Majusawa
■ Alheri daga mahangar malaman Aklak
■ Fasali na hudu
■ Sharri (Kulli tashkiki) wani abune gamamme da yake banbantuwa da juna
■ Alheri da sharri karkashin hasken Nahajul Balaga
■ Alheri shine wazirin hankali sharri wazirin jahilci
- KIBIYOYIN RADDI KAN WUYAN WAHABIYAWA
- CIKIN HALLARAR ALHERI
- HUJJOJIN HALASCIN YIN TAKIYYA A MUSLUNCI DAGA MAHANGAR MANYAN MALAMAI GUDA BIYU
- FARKAR DA MAI BACCI CIKIN TABBATUWAR GANIN IMAM KA'IM A.S
- ALAMOMIN ANNABI CIIKIN KUR'ANI MAI GIRMA
- HAKURI DA FUSHI
- Bada'u tsakanin hakika da kagen makiya
- FALALAR DAREN LAILATUL KADRI
- WAHABIYANCI A TSAKANIN GUDUMA DA
- HASKEN SASANNI CIKIN SANIN ARZIKI
- AQIDUN MUMINAI
- FATIMA TAGAR HASKAYE
- SIRRIKAN AIKIN HAJJI DA ZIYARA
- TARBIYYAR IYALI A MAHANGAR ALKUR'ANI DA AHLULBAITI
Allah matsarkaki madaukaki cikin littafinsa mai hikima ya ce:
1: (إِنَّ الَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ أُوْلَئِکَ هُمْ خَيْرُ الْبَرِيَّةِ * جَزَاؤُهُمْ عِندَ رَبِّهِمْ جَنَّاتُ عَدْنٍ تَجْرِي مِن تَحْتِهَا الاْنْهَارُ خَالِدِينَ فِيهَا أَبَداً رَّضِيَ اللَّهُ عَنْهُمْ وَرَضُوا عَنْهُ ذَلِکَ لِمَنْ خَشِيَ رَبَّهُ)[1] .
Lallai wadanda suka yi imani suka yi ayyuka nagari wadancananka sune mafi alherin cikin mutane* sakamakonsu wurin ubangijinsu gidajen Aljannar zama koramu suna gudana karkashinsu suna masu dawwama cikinsu har abada Allah ya yarda dasu suma sun yarda da shi wannan sakamakon ga wanda yaji tsoran ubangijinsa.
2 ـ (وَأَحْسِنُوَاْ إِنَّ اللّهَ يُحِبُّ الْمُحْسِنِينَ)[2] .
Ku kyatata lallai Allah yana son masu kyautatawa
3 ـ (أُوْلَئِکَ يُؤْتَوْنَ أَجْرَهُم مَّرَّتَيْنِ بِمَا صَبَرُوا وَيَدْرَؤُونَ بِالْحَسَنَةِ السَّيِّئَةَ وَمِمَّا رَزَقْنَاهُمْ يُنفِقُونَ)[3] .
Wadancananka ana basu ladansu karo biyu sakamakon hakurin da suka yi kuma da kyautatawa suna tunkude munanawa kuma daga abin da muka azurtar da su suna ciyarwa.
4 ـ (لِّلَّذِينَ أَحْسَنُواْ الْحُسْنَى وَزِيَادَةٌ وَلاَ يَرْهَقُ وُجُوهَهُمْ قَتَرٌ وَلاَ ذِلَّةٌ أُوْلَئِکَ أَصْحَابُ الْجَنَّةِ هُمْ فِيهَا خَالِدُونَ)[4] .
Ga wandada suka kyawunta suna da abu mai kyawu kuma da kari wata kura da kaskanci ba zasu rufe fuskokinsu wadancananka suna ma'abota Aljanna suna masu dawwama cikinta.
5 ـ (وَمَا يَفْعَلُواْ مِنْ خَيْرٍ فَلَن يُكْفَرُوْهُ وَاللّهُ عَلِيمٌ بِالْمُتَّقِينَ)[5] .
Abin da suka aikata daga alheri ba za a taba I musu inkarinsa ba lallai Allah masanin masu takawa ne.
(وَلِكُلٍّ
وِجْهَةٌ هُوَ مُوَلِّيهَا فَاسْتَبِقُواْ الْخَيْرَاتِ أَيْنَ مَا تَكُونُواْ
يَأْتِ بِكُمُ اللّهُ جَمِيعاً إِنَّ اللّهَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ)[6] .
Kuma ga kowacce kusurwa yana da Alkibla wanda yake shi mai fuskantar shi ne sai kuyi tsre zuwa ga ayyukan alheri duk inda kuka kasance Allah zai zo daku baki daya lallai Allah Mai iko ne kan komai.
6 ـ (وَقِيلَ لِلَّذِينَ اتَّقَوْاْ مَاذَا أَنزَلَ رَبُّكُمْ قَالُواْ خَيْراً لِّلَّذِينَ أَحْسَنُواْ فِي هَذِهِ الدُّنْيَا حَسَنَةٌ وَلَدَارُ الآخِرَةِ خَيْرٌ وَلَنِعْمَ دَارُ الْمُتَّقِينَ)[7] .
Aka cewa wadanda sukayi takawa me uabngijinku ya saukar suka ce alheri ga wadanda suka kyawunta aiki cijin wannan duniya kyawuntawa lallai tabbas gidan lahira shi ne mafi alheri madalla da gidan masu takawa.
7 ـ (وَالْبَلَدُ الطَّيِّبُ يَخْرُجُ نَبَاتُهُ بِإِذْنِ رَبِّهِ وَالَّذِي خَبُثَ لاَ يَخْرُجُ إِلاَّ نَكِداً كَذَلِکَ نُصَرِّفُ الآيَاتِ لِقَوْمٍ يَشْكُرُونَ)[8] .
Kuma gari mai kyawu tsirinsa yana fita da izinin Allah kuma wanda ya munana shi tsirinsa baya fita sai wahala kamar wannan ne muke jujjuya ayoyi ga mutanen da suke godiya.
Bai buya ba cewa shi Kur'ani baki dayansa littafi ne na alheri da farin ciki, kuma abin da muka ambata daga ayoyi masu daraja wadanda suke ishara zuwa ga ba'arin misdakan alheri duka samfuri da misali ga alheri, kada ka gafala, domin cika fa'ida na duba maka littafin Mu'ujamu Mufahrisul Alfazul Kur'ani sannan na fito maka da wadannan ayoyi da suke ishara zuwa ga alheri.
8 ـ (ذَلِكُمْ خَيْرٌ لَّكُمْ عِندَ بَارِئِكُمْ فَتَابَ عَلَيْكُمْ إِنَّهُ هُوَ التَّوَّابُ الرَّحِيمُ)[9] .
Wadancananka alheri ne gareku a wurin ubangijinku sai ya karbi tubanku lallai shi mai yawan karbar tuba ne da jin kai.
9 ـ (قَالَ أَتَسْتَبْدِلُونَ الَّذِي هُوَ أَدْنَى بِالَّذِي هُوَ خَيْرٌ)[10] .
Ya ce yanzu kuna neman canji da mafi kaskanci daga wanda yake shi ne alheri.
10 ـ (مَّا يَوَدُّ الَّذِينَ كَفَرُواْ مِنْ أَهْلِ الْكِتَابِ وَلاَ الْمُشْرِكِينَ أَن يُنَزَّلَ عَلَيْكُم مِّنْ خَيْرٍ مِّن رَّبِّكُمْ)[11]
Wadanda suka kafirce daga ma'abota littafi da mushrikai basu kaunar a saukar muku da alheri daga ubangijinku.
11 ـ (مَا نَنسَخْ
مِنْ آيَةٍ أَوْ نُنسِهَا نَأْتِ بِخَيْرٍ مِّنْهَا أَوْ مِثْلِهَا)[12] .
Bamu goge daga wata ay aba ko mantar da ita face mun zo da mafi alheri daga gareta ko dai misalinta.
12 ـ (وَمَا تُقَدِّمُواْ لأَنفُسِكُم مِّنْ خَيْرٍ تَجِدُوهُ عِندَ اللّهِ)[13] .
Abin da ku ka gabatarwa kanku daga alheri zaku same shi a wurin Allah.
13 ـ (فَمَن تَطَوَّعَ خَيْراً فَهُوَ خَيْرٌ)[14] .
Duk wanda yayi tadawwu'i da wani alheri shi alheri ne
14 ـ (وَتَزَوَّدُواْ فَإِنَّ خَيْرَ الزَّادِ التَّقْوَى)[15] .
Kuyi guzuri lallai mafi alherin guzuri shi ne guzurin tsoran Allah
15 ـ (وَمَا تَفْعَلُواْ مِنْ خَيْرٍ يَعْلَمْهُ اللّهُ)[16] .
Abin da kuka aikata daga alheri Allah yana sane da shi.
16 ـ (قُلْ مَا أَنفَقْتُم مِّنْ خَيْرٍ فَلِلْوَالِدَيْنِ وَالأَقْرَبِينَ)[17] .
Kace abin da kuka ciyar daga alheri ga iyaye yake da makusanta
17 ـ (وَمَا تَفْعَلُواْ مِنْ خَيْرٍ فَإِنَّ اللّهَ بِهِ عَلِيمٌ)[18] .
Abin da kuka aikata daga alheri lallai Allah yana sane da shi.
18 ـ (وَيَسْأَلُونَکَ عَنِ الْيَتَامَى قُلْ إِصْلاَحٌ لَّهُمْ خَيْرٌ)[19] .
Kuma suna tambayarka dangane da Marayu kace gyara garesu alheri ne.
19 ـ (وَمَا تُنفِقُواْ مِنْ خَيْرٍ فَلأنفُسِكُمْ)[20] .
Abin da kuka ciyar daga alheri ga kawukanku yake.
20 ـ (وَمَا تُنفِقُواْ مِنْ خَيْرٍ يُوَفَّ إِلَيْكُمْ وَأَنتُمْ لاَ تُظْلَمُونَ)[21] .
Abin da kuke ciyarwa daga alheri za a cika muku ba za a zalunceku ba.
21 ـ (بِيَدِکَ الْخَيْرُ إِنَّکَ عَلَىَ كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ)[22] .
A hannunka dukkanin alheri yake lallai kai Mai iko kan komai.
22 ـ (كُنتُمْ خَيْرَ أُمَّةٍ أُخْرِجَتْ لِلنَّاسِ)[23] .
Kun kasance mafi alherin al'umma da aka fitar domin mutane.
23 ـ (وَلاَ يَحْسَبَنَّ الَّذِينَ كَفَرُواْ أَنَّمَا نُمْلِي لَهُمْ خَيْرٌ لاَِنفُسِهِمْ)[24] .
Kada wadanda suka kafirce suyi zaton cewa kau da kan da muka yi daga garesu alheri ne ga kawukanku.
24 ـ (وَمَا عِندَ اللّهِ خَيْرٌ لِّلأَبْرَارِ)[25] .
Abin da yake wurin Allah shi ne mafi alheri ga rabautattu
25 ـ (قُلْ مَتَاعُ الدَّنْيَا قَلِيلٌ وَالآخِرَةُ خَيْرٌ لِّمَنِ اتَّقَى وَلاَ تُظْلَمُونَ فَتِيلا)[26] .
Kace dadin duniya kadan ne kuma lahira itace mafi alheri ga wanda yaji tsoron Allah ba za a zalunceku ba koda kuwa zaren gurtsin dabino ba.
26 ـ (وَالصُّلْحُ خَيْرٌ)[27] .
Sulhu alheri ne
27 ـ (وَإِن يَمْسَسْکَ بِخَيْرٍ فَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدُيرٌ)[28] .
Idan Allah ya shafeka da alheri to fa shi Mai iko ne kan komai.
28 ـ (وَالدَّارُ الآخِرَةُ خَيْرٌ لِّلَّذِينَ يَتَّقُونَ أَفَلاَ تَعْقِلُونَ)[29] .
Kuma gidna lahira shi ne mafio alheri ga wadanda suke tsoran Allah yanzu ba zaku sanya hankali ba.
29 ـ (وَلَوْ كُنتُ أَعْلَمُ الْغَيْبَ لاَسْتَكْثَرْتُ مِنَ الْخَيْرِ وَمَا مَسَّنِيَ السُّوءُ)[30] .
Da na kasance ina sanin gaibu da na yawaita ayyukan alheri kuma da wata cuta shafeni ba.
30 ـ (فَإِن تُبْتُمْ فَهُوَ خَيْرٌ لَّكُمْ)[31] .
Idan kuka tuba shi alheri ne gareku.
31 ـ (وَإِن يُرِدْکَ بِخَيْرٍ فَلاَ رَآدَّ لِفَضْلِهِ)[32] .
Idan Allah ya nufeka da alheri tofa babu mai mayar da falalarsa.
32 ـ (بَقِيَّةُ اللّهِ خَيْرٌ لَّكُمْ إِن كُنتُم مُّؤْمِنِينَ)[33] .
Falalar Allah mai wanzuwa itace mafi alheri gareku idan kun kasance Muminai.
33 ـ (وَلاَجْرُ الآخِرَةِ خَيْرٌ)[34] .
Ladan gidan lahira shi ne mafi alheri.
34 ـ (وَيَدْعُ الإِنسَانُ بِالشَّرِّ دُعَاءهُ بِالْخَيْرِ وَكَانَ الإِنسَانُ عَجُولا)[35] .
Kuma mutum yana addu'a da sharri misalin addu'arsa da alheri kuma mutum ya kasance mai gaggawa.
35 ـ (وَالْبَاقِيَاتُ الصَّالِحَاتُ خَيْرٌ عِندَ رَبِّکَ ثَوَاباً وَخَيْرٌ أَمَلاً)[36] .
Falalolin Allah masu wanzuwa sune mafi alheri wurin ubangijinka matsayin lada kuma mafi alherin fata.
36 ـ (كُلُّ نَفْسٍ ذَائِقَةُ الْمَوْتِ وَنَبْلُوكُم بِالشَّرِّ وَالْخَيْرِ فِتْنَةً)[37] .
Dukkanin Rai mai dandanar mutuwa ce kuma zamu jarrabeku da alheri da sharri domin fitina.
37 ـ (وَمِنَ النَّاسِ مَن يَعْبُدُ اللَّهَ عَلَى حَرْفٍ فَإِنْ أَصَابَهُ خَيْرٌ اطْمَأَنَّ بِهِ)[38] .
Daga cikin mutane akwai wanda yake bautawa Allah kan wani gefe idan alheri ya same shi sai ya samu nutsuwa da shi
38 ـ (ذَلِکَ وَمَن يُعَظِّمْ حُرُمَاتِ اللَّهِ فَهُوَ خَيْرٌ لَّهُ عِندَ رَبِّهِ)[39] .
Wancan kuma duk wanda ya girmama hukunce-hukuncen Allah lallai shi mafi alheri ne gare shi a wurin ubangijinsa.
39 ـ (ارْكَعُوا وَاسْجُدُوا وَاعْبُدُوا رَبَّكُمْ وَافْعَلُوا الْخَيْرَ)[40] .
Ku yi ruku'u kuyi sujjada ku bautawa ubangijinku ku aikata ayyukan alheri.
40 ـ (لاَ تَحْسَبُوهُ شَرّاً لَّكُم بَلْ هُوَ خَيْرٌ لَّكُمْ)[41] .
Kada ku yi zaton cewa sharri ne gareku bari dai alheri ne gareku
41 ـ (فَقَالَ رَبِّ إِنِّي لِمَا أَنزَلْتَ إِلَيَّ مِنْ خَيْرٍ فَقِيرٌ)[42] .
Sai ya ce ya ubangiji lallai ni mabukaci daga abin da ka saukar mini daga alheri. (abinci)
42 ـ (وَيْلَكُمْ ثَوَابُ اللَّهِ خَيْرٌ لِّمَنْ آمَنَ وَعَمِلَ صَالِحاً)[43] .
Kaiconku ladan Allah shi ne mafi alheri ga wanda yayi takawa ya aikata aiki na kwarai.
43 ـ (مَن جَاء بِالْحَسَنَةِ فَلَهُ خَيْرٌ مِّنْهَا)[44] .
Wanda ya zo da kyakkyawan aiki lallai yana da mafi alheri daga gare shi.
44 ـ (لاَ يَسْأَمُ الاِْنسَانُ مِن دُعَاء الْخَيْرِ)[45] .
Mutum baya kosawa daga addu'ar alheri.
45 ـ (وَمَا عِندَ اللَّهِ خَيْرٌ وَأَبْقَى لِلَّذِينَ آمَنُوا وَعَلَى رَبِّهِمْ يَتَوَكَّلُونَ)[46] .
Abin da yake wurin Allah shi ne mafi alheri da wanzuwa ga wadanda suka yi imani suna dogara kan ubangijinsu.
46 ـ (وَرَحْمَتُ رَبِّکَ خَيْرٌ مِّمَّا يَجْمَعُونَ)[47] .
Rahamar ubangijinka itace mafi alheri daga abin da suke tarawa.
47 ـ (أَلْقِيَا فِي جَهَنَّمَ كُلَّ كَفَّارٍ عَنِيدٍ * مَّنَّاعٍ لِّلْخَيْرِ مُعْتَدٍ مُّرِيبٍ)[48] .
Ku jefa dukkanin Kafiri mai tsaurin kai cikin Jahannama* mai yawan hana alheri mai ketare iyaka mai shakka.
48 ـ (مَا عِندَ اللَّهِ خَيْرٌ مِّنَ اللَّهْوِ وَمِنَ التِّجَارَةِ وَاللَّهُ خَيْرُ الرَّازِقِينَ)[49] .
Abin da yake wurin ubangijinka shi ne mafi alheri daga wargi da kasuwanci Allah shi ne mafi alherin masu azurtawa.
49 ـ (وَمَا تُقَدِّمُوا لاَِنفُسِكُم مِّنْ خَيْرٍ تَجِدُوهُ عِندَ اللَّهِ هُوَ خَيْراً وَأَعْظَمَ أَجْراً)[50] .
Abin da kuka gabatar ga kawukanku daga alheri zaka same shi wurin Allah shi ne mafi alheri da girman lada.
50 ـ (يَا أَيُّهَا النَّاسُ قَدْ جَاءكُمُ الرَّسُولُ بِالْحَقِّ مِن رَّبِّكُمْ فَآمِنُواْ خَيْراً لَّكُمْ)[51] .
Yaku wadanda kuka yi imani hakika Manzo ya zo muku da gaskiya daga ubangijinku ku yi imani shi ne mafi alheri gareku.
51 ـ (وَقِيلَ لِلَّذِينَ اتَّقَوْاْ مَاذَا أَنزَلَ رَبُّكُمْ قَالُواْ خَيْراً)[52] .
Kuma aka cewa wadanda suka yi takawa me ubangijinku ya saukar suka ce alheri.
52 ـ (فَمَن يَعْمَلْ مِثْقَالَ ذَرَّةٍ خَيْراً يَرَهُ)[53] .
Duk wanda yayi aiki mikdarin kwayar zarra daga alheri zai gan shi.