فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها

Fasali na biyu

tambayoyi da amsa cikin alheri

kasantuwar mutum yana da buri da kwadayi sannan yana tare da halittar sha'awa ta dabbanci da ta mutum, lallai daga halittar sha'awa da kwadayi da burinsa akwai: neman sani da tsinka kan duk abin da bai sani ba, zaka same shi yana kokarin tsinkaya yana karanta abubuwa da dukkanin geffansu, hakan ya sa muka ganin kwakwalwarsa na motsi na kai kawo cikin tunani, yana wurgo da tambaya domin ya samu fahimtar komai, wani lokacin yana tambaya kan mafi alherin mutane, awani karon kuma mafifitan Muminai, daga cikin tambayoyin da aka bijiro a wannan fage akwai tambaya akn menene amfi alherin al'amura? Menene mafi alherin dabi'u, wacce sifface siffar ma'abota alheri? Menene ma'auni cikin banbacewa tsakanin sharri da alheri? Wanne kofofi ne kofofin alheri?menene mafi falala daga alheri? Da dai makamantan haka daga bahasosi da maudu'ai da suka ta'allaka da mafhumin alheri da misdakansa.

Domin bayar da tunani da fikira da farko-farko ga dukkanin wadannan tambayoyi da wasunsu, kasantuwar muna magana ne dangane d aalheri daga zwiyyar muslunci da ka'idodjinsa sannan kuma tushen wayewarsa ya bubbugo daga Kur'ani da sunna mai daraja, zamu kawo jumla daga riwayoyi cikin wannan fage ba tare da mun tsawaita sharhi da ta'aliki ba, bari dai zamu mika su zuwa ga mai Karatu yayi amfani da wayewarsa ta ilimi da karatunsa.

Wadanne al'amura ne mafi alherin lamurra:  

1 ـ قال رسول الله 6«خير الأُمور عاقبةً» أي تكون عاقبة الأمر على خير.

Manzon Allah (s.a.w) ya ce nafi alherin al'amura karshensu, ma'ana karshe ya kasance karshe na alheri.

2 ـ «خير الأُمور عزائمها، وشرّ الأُمور محدثاتها».

Mafi alherin lamurra masu girma da nauyinsu, mafi sharrin al'amura kagaggunsu.

3 ـ قال أمير المؤمنين  7«خير الأُمور ما عُري عن الطمع».

Sarkin Muminai (a.s) ya ce: mafi alherin lamurra shien wanda ya tsira daga kwadayi.

4 ـ «خير الأُمور ما أسفر عن اليقين».

Mafi alherin lamurra wanda ya samu daga yakini.

5 ـ «ما سهلت مبادئه ، وحسنت خواتمه ، وحمدت عواقبه».

Mafi alherin cikin lamurra sune wanda mafaransa suka saukaka, hattamashi ya kyawunta, karshe ya zama abin yabawa.

6 ـ «خير الأُمور: النمط الأوسط ـ أي الوسادة التي يتكأ عليها من طرفين ـ إليه يرجع الغالي وبه يلحق التالي».

Mafi alherin al'amura shi ne matashin tsakiya, ma'ana matashin da ake jingina da shi daga geffansa biyu-gare shi mai zurfafa yake komawa kuma da shi ake riskar da wanda zai zo daga baya

7 ـ «أوصيكم عباد الله بتقوى الله، فإنّها خير ما تواصي العباد به ، وخير عواقب الأُمور».

Ina muku wasiyya yaku bayin Allah da ku kiyaye tsoran Allah, lallai tsoran Allah shi ne mafi alherin abin da ake yiwa juna wasiyya da shi, kuma mafi alherin karshen lamurra.

 

 -Menene mafi alherin dabi'a?2

1 ـ قال رسول الله 6«ألا أدلّكم على خير أخلاق الدنيا والآخرة؟ قالوا: بلى يا رسول الله قال : من وصل من قطعه ، وأعطى من حرمه ، وعفا عمّن ظلمه».

Manzon Allah (s.a.w) ya ce: yanzu bana shiryar daku kan mafi alherin kyawawan dabi'u a duniya da lahira ba?sai suka ce ka bamu labari ya Manzon Allah ya ce: shi ne wanda ya sadar da zumunci daga wanda ya yanke shi daga gare shi, ya bada kyauta ga wanda ya haramta masa, ya yafewa wanda ya zalunce shi.

2 ـ «ألا أخبركم بخير أخلاق أهل الدنيا والآخرة؟ قالوا: بلى يا رسول الله فقال : إفشاء السلام في العالم»

Bana baku labari ba da mafi alherin kyawawan dabi'I duniya da lahira? Suka ka bamu labari ya Manzon Allah sai ya ce: yada zaman lafiya cikin duniya.

3- menene siffofin ma'abota alheri?

1 ـ في حديث المعراج قال سبحانه وتعالى : «يا أحمد ان أهل الخير وأهل الآخرة رقيقة وجوههم كثير حياؤهم ، قليل حمقهم ، كثير نفعهم ، قليل مكرهم ، النّاس منهم في راحة ، وأنفسهم منهم في تعب ، كلامهم مرزون ، محاسبين لأنفسهم ، متعبين لها، تنام أعينهم ولا تنام قلوبهم ، أعينهم باكية ، وقلوبهم ذاكرة ، إذا كتب النّاس من الغافلين كُتبوا من الذاكرين ... لا يشغلهم عن الله شيء طرفة عين ولا يريدون كثرة الطعام ، ولا كثرة الكلام ، ولا كثرة اللباس ، النّاس عندهم موتى ، والله عندهم حيّ قيوم ».

Ya zo cikin hadisin Mi'iraji Allah matsarkaki ya ce: ya Ahmad hakika ma'abota alheri da mutanen lahira fuskokinsu tausasa ne, masu kunyar da yawa, wautarsu ta karanta, amfaninsu ya yawaita, makircinsu yana da karanci, mutane suna cikin hutu daga sharrinsu, zukatansu na cikin gajiya daga garesu, zantukansu kyawawa, suan yiwa kawukansu hisabi, idanuwansu na kuka, zukatansu suna tunawa da Allah, idna an rubuta mutane daga masu gafala su za a rubuta su daga masu tunawa da Allah…babu abin da yake shagaltar da su daga barin Allah ko da kuwa mikdarin kiftawar idanu ne, basu sun yawan cin abinci da yawan magana, da yawan tufafi, su a wajensu dukkanin mutane matattu ne, Allah ne kadai yake a raye a tsaye kan kula da halittunsa, ma'ana suna aiki da iklasi ba tare da damuwa da me mutane zasu ce ba, lallai shi matacce baya sanin abin da kake aikatawa.

2 ـ قال أمير المؤمنين علي  7«سنّة الأخيار: لين الكلام وإفشاء السلام».

Sarkin Muminai Ali (a.s) ya ce: sunnar mutane ma'abota alheri shi ne tausasa harshe da yada zaman lafiya.

3 ـ «ألا وان الله سبحانه قد جعل للخير أهلاً، وللحق دعائم ، وللطاعة عصماً».

Ku saurara hakika Allah matsarkaki ya sanyawa alheri Ahalinsa, haka ya sanyawa gaskiya makarai da majinginai, haka ya sanyawa `da'a shinge.

4-menene ma'auni tsakanin alheri da sharri

Hakika Allah ya sanya mizani domin mutane su tsayu da adalci sai ya sanyawa komai alama da shaida da mizani da ma'auni domin sanin kyakkyawa da mara kyau, banbance alheri daga sharri, gaskiya daga karya, menene mizani da sikeli da zamu iya sanin alheri da sharri?

قال أمير المؤمنين  7«ان الخير والشرّ لا يُعرفان إلّا بالنّاس ، فإذا أردت أن تعرف الخير فاعمل الخير تعرف أهله ، وإذا أردت أن تعرف الشرّ فإعمل الشرّ تعرف أهله».

Sarkin Muminai Ali (a.s) ya ce: hakika alheri da sharri ba a iya saninsu sai ta hanyar mutane, idan kana son sanin alheri to ka aikata alheri zaka san Ahalinsa, idan kana son sanin sharri ka aikata sharri zajka san Ahalinsa.

Wannan yana daga dokokin sinkiya sababi da musabbabi illa da ma'aluli, su ma'abota sharri sashensu yana jawo sashe sakamakn samuwar sinkiya tsakaninsu da kamanceceniya, haka lamarin yake dangane ga ma'abota alheri, jinsi tare da jinsinsa yake karkata, tsuntsu da dan'uwansa tsuntsu yake tashi sama.

-Menene kofofin alheri?5

1 ـ قال رسول الله 6 لمعاذ بن جبل: «ان شئت أنبأتک عن أبواب الخير؟» قال : أجل يا رسول الله قال : الصوم جُنّة ـ أي حصن حصين من عذاب الله وسخطه ومن النّار، والصدقة تكفّر الخطيئة ، وقيام الرجل في جوف الليل يبتغي وجه الله، ثم قرأ هذه الآية : (تَتَجَافَى جُنُوبُهُمْ ...).

Manzon Allah (s.a.w) ya cewa Mu'azu Ibn Jabal: idan kana so zan gaya maka kofofin alheri? Ya ce: na'am ina so ya Manzon Allah ya ce: Azumi Katanga ne-ma'ana karfaffan shinge ne daga AzabarAllah da fushinsa da wuta, ita kuma sadaka tanba kankare kura-kurai da tsayuwar dare domin neman yardar Allah, sannan ya karanta wannan ayar (geffansu suna bushewa)

2 ـ «الخير كثير فاعله قليل».

Alheri abu ne mai yawa da masu aikata shi suke da karanci gaske.

3 ـ قال الإمام الباقر 7 لسليمان بن خالد: «ان شئت أخبرتک بأبواب الخير؟ قال : نعم جُعلت فداک قال : الصوم جُنّة من النّار، والصدقة تذهب الخطيئة ، وقيام الرجل في جوف الليل بذكر الله».

Imam Bakir (a.s) ya cewa Sulaimanu Ibn Khalid: idan kana so zan gaya maka kofofin alheri? Ya ce ina so raina fansarka, ya ce: Azumi garkuwa ne daga wuta, sadaka tana tafiyar da kuskure, da tsayuwar mutum tsakiyar dare domin ambaton Allah

Misalin wannan riwaya riwaya daga Imam Sadik (a.s) da ya gayawa Aliyu Ibn Abdul-Aziz.

6-menene mafificin alheri?

1 ـ قال رسول الله 6«خير من الخير معطيه».

Manzon Allah (s.a.w) ya ce: mafi alheri daga alheri shi ne mai bada alherin.

2 ـ قال أمير المؤمنين  7«فاعل الخير خير منه وفاعل الشرّ شرّ منه».

Sarkin Muminai Ali (a.s) ya ce: mai aikata alheri ya fi zama alheri daga kankin kan alherin, mai aikata alheri shi ne mafi zama sharri daga sharrin.

3 ـ «أفعلوا الخير إن استطعتم ، فخير من الخير فاعله».

Ku aikata alheri idan kun samu dama, mafi alheri daga alheri shi ne mai aikata alherin.

4 ـ «ليس بخير من الخير إلّا ثوابه».

Babu wani abu da yafi alheri daga alheri face ladansa.

5 ـ قال الإمام الهادى  7«خير من الخير فاعله ، وأجمل من الجميل قائله ، وأرجح من العلم حامله».

Imam Hadi (a.s) ya ce: mafi alheri daga alheri shi ne mai aikata shi, mafi kyau da kyawu shi ne mai fadar alheri.