■ Alheri da Sharri cikin rubutu
■ Fasali na (1)
■ Dayantacciyar halitta
■ Dabi'ar halin sharri cikin mutum
■ Alheri a luggance da Isdilahi
■ Ayoyin Alheri cikin Kur'ani Mai girma
■ Mafhumin alheri da misdakansa
■ Tafisirin alheri da kashe-kashensa daga kassi da Ammi daga cikin daidaiku da jama'a
■ Kebantaccen alheri daidaiku
■ Gamammen alheri na zamantakewa
■ Sirri cikin alheri da sharri
■ Ma'anonin da alheri yake da shi cikin Kur'ani mai girma
■ Mutane ma'abota alheri
■ Mafi alherin cikin Muminai
■ Alheri daga cikin Kur'ani Mai girma
■ Fasali na biyu
■ Gaggawa zuwa ga ayyukan alheri
■ Fasali na uku
■ Alheri da sharri a wurin Majusawa
■ Alheri daga mahangar malaman Aklak
■ Fasali na hudu
■ Sharri (Kulli tashkiki) wani abune gamamme da yake banbantuwa da juna
■ Alheri da sharri karkashin hasken Nahajul Balaga
■ Alheri shine wazirin hankali sharri wazirin jahilci
- KIBIYOYIN RADDI KAN WUYAN WAHABIYAWA
- CIKIN HALLARAR ALHERI
- HUJJOJIN HALASCIN YIN TAKIYYA A MUSLUNCI DAGA MAHANGAR MANYAN MALAMAI GUDA BIYU
- FARKAR DA MAI BACCI CIKIN TABBATUWAR GANIN IMAM KA'IM A.S
- ALAMOMIN ANNABI CIIKIN KUR'ANI MAI GIRMA
- HAKURI DA FUSHI
- Bada'u tsakanin hakika da kagen makiya
- FALALAR DAREN LAILATUL KADRI
- WAHABIYANCI A TSAKANIN GUDUMA DA
- HASKEN SASANNI CIKIN SANIN ARZIKI
- AQIDUN MUMINAI
- FATIMA TAGAR HASKAYE
- SIRRIKAN AIKIN HAJJI DA ZIYARA
- TARBIYYAR IYALI A MAHANGAR ALKUR'ANI DA AHLULBAITI
Yaku yan'uwa masu tace soyayya abokai masu cika hakkin abota ku taho zuwa ga ayyukan alheri, kuyi gaggawa zuwa ga neman gafara da neman aljanna wacce fadinta ya kai fadin sama da kasa, da farko mu kasance daga masu aikata alheri, sannan mu kirayi mutane zuwa gare shi lallai yanda lamarin yake Manzon (s.a.w) Allah ya ce: mai shiryarwa zuwa ga alheri daidai yake da mai aikata shi, a wani wajen ya ce: duk wanda ya shiryar zuwa ga aikin alheri to yana da ladan misalin wanda ya aikata.
Kad aka raina aikin alheri komai kankantarsa kamar yanda Imamanmu tsarkaka suka ladabtar da mu kan haka
قال أمير المؤمنين على 7: «افعلوا الخير، ولا تحقّروا منه شيئاً، فان صغيره كبير، وقليله كثير».
Sarkin Muminai Ali (a.s) ya ce: ku aikata ayyukan alheri kada ku raina komai daga alheri, lallai karaminsa babbane, kadan dinsa mai yawa.
Wannan yana daga abin yayi daidai da hankali da amfani da shi, duk wanda yake tunani irin wannan da sannu zai ga farin ciki a rayuwarsa domin a kowanne lokaci zai askance daga ma'abota alheri kamar yanda dukkanin wadanda suke kewaye da shi suma zasu ga farin ciki, kuma zai kasance daga Muminai a hakika yana dauke da siffofin Sarkin Muminai wadanda daga cikinsu akwai: (an aminta daga sharrinsa kuma alherinsa abin fata ne) dukkanin mutane suna fatan alherinsa suna nufinsa, lallai bukatun mutane zuwa gareka suna daga ni'imomin Allah a kanku kada ku kosa daga ni'imomin Allah, mafi alherin mutane shi ne wanda ya amfanar da mutane ko da kuwa da kofin ruwa ne ko kuma ta hanyar dauke dutse daga kan hanyar musulmai.
قال الإمام الصادق 7: «لا تصغّر شيئاً من الخير، فإنّک تراه غداً حيث يسرّک».
Imam Assadik (a.s) ya ce: kada ka raina wani abu daga alheri, lallai gobe zaka ganshi a inda zai faranta maka.
Lallai duk wanda yayi aiki gwargwadon kwayar zarra daga alheri zai ga sakamakonsa, ta iya yiwuwa wannan kankanin aiki shi ne wanda zai nauyaya masa mizanin kyawawan ayyukansa, sai ya kasance daga `yan gidan Aljanna daga ma'abota farin ciki, haka lamarin yake dangane da aikin sharri komai kankantarsa, tana iya yiwuwa kwayar zarra daga sharri ya kasance sababin dawwama cikin tsiyata, dominzai rinjayi awon ayyukansa na sharri kan ayyukansa nagari cikin mizani da za ayi awo da shi ranar lahira, ka lura sosai kada ka gafala.
Daga cikin siffofin Muminai shi ne suna yiwa juna wasicci da gaskiya, babu shakka cewa aikin alheri yana daga abubuwan da suke amsa sunan gaskiya, ya zama dole mu yiwa juna wasicci da ayyukan alheri da gaggawa zuwa garesu kamar yanda Allah ya umarce mu da haka cikin fadinsa madaukaki: (ku yi tsere zuwa ga ayyukan alheri) wannan yana daga mafi bayyanar abubuwan da suke amsa suna alheri mai gamewa.
1 ـ قال رسول الله 6: «من فتح له باب خير فلينتهزه ، فإنّه لا يدري متى يغلق عنه».
Manzon Allah (s.a.w) ya ce: duk wanda aka budewa kofar alheri to yayi gaggawar amfanarta, lallai shi bai san lokacin da za a kulleta ba.
2 ـ «ان الله يحب من الخير ما يعجّل».
Allah yana son alheri da aka gaggauta yinsa.
3 ـ قال أمير المؤمنين علي 7: «بادروا بعمل الخير قبل ان تشغلوا عنه بغيره».
Sarkin Muminai Ali (a.s) ya ce: kuyi gaggawa da yin aikin alheri gabanin ku shagaltu da waninsa
4 ـ «بادر الخير تُرشد».
Ku gaggauta aikin alheri zaka shiriyu.
5 ـ قال الإمام الباقر 7: «من همّ بشيء من الخير فليعجّله ، فإنّ كلّ شيء فيه تأخير، فانّ للشيطان فيه نظرة».
Imam Bakir (a.s) ya ce: duk wanda ya himmatu da aikata wani abu daga alheri to ya gaggauta yinsa dukkanin abin da yake da jinkiri to lallai Shaidani na da wani kallon cikinsa.
Da wannan mafarar ne ake cewa: fikira ta farko fikira ce ta ubangijin rahama, amma fikira ta biyu fikira ce ta Shaidan, alal misali da za a ce maka kayi wani aiki daga ayyukan jin kai da alheri kamar misalin kula da marayu ko gina masallaci da dai misalin haka, lallai da farko zaka ji cewa kayi niyyar bada gudummawar dala 100 wannan fikira da fara zuwar maka fikira ce ta jin kai tsantsa, to ka gaggauta bayarwa, idanb ka yi jinkiri daga zaka iya canja ra'ayi ka bada dala 50 zaka ji cewa bada dala 100 kudi mai yawa bara dai kawai na bada dala 50, lallai wannan fikira ta biyu ta cudanya da wasiwasin Shaidan tunani mara kyau, idna ka jinkirta tsawon awa daya sai kace kai gaskiya dala 50 tana da yawa bara na bada dala 10, idan awa biyu sai kace kai ni nama fasa b azan basu ko sisi ba ai wasu sun basu gudummawar kudade masu tarin yawa, idan ka jinkirta tsawon kwanda daya baka bayar sai kace wanene zai gasgata wadannan muatne masu neman gudammawa ta iya yiwuwa `yan damfara ne suna son tara kudade ne kawai ta wannnan hanya, basu tsarkakakkra niyya zasu yi amfani da wadannan kudade a wuraren da basu da ce ba, haka dai Shaidan zai ta wasa da kai yana jefa maka wasiwasi da kokwanto , daga niyyar bada dala 100 ka gangara zuwa ga munanawa bayin Allah zato (lallai ba'arin zato laifi ne)
6 ـ قال الإمام الصادق 7: «إذا هممت بخير فلا تؤخّره ، فانّ الله تبارک وتعالى ربّما اطّلع على عبده وهو على الشيء من طاعته فيقول : وعزّتي وجلالي لا أُعذّبک بعدها».
Imam Sadik (a.s) ya ce: idan ka himmatu da wani alheri to kada ka jinkirta shi, lallai Allah mai albarkoki da daukaka ta iya yiwuwa ya tsinkaya kan bawansa yana halin wani abu daga da'arsa sai ya ce: na rantse da izzata da girmana ba zan azabtar da kai ba bayan wannan aiki.
7-Babana ya kasance yana cewa: idan ka himmatu da wani alheri to ka gaggauta shi lallai kai baka san abin da zai faru ba.
8-idan dayanku ya himmatu da alheri ko sadar da zumunci, lallai ya sani a damansa da hagunsa akwai Shaidanu, saboda haka ya gaggauta shi kada su hana shi.
9 ـ قال أمير المؤمنين علي 7: «لا خير في الدنيا إلّا لرجلين : رجل أذنب ذنوباً فهو يتداولها بالتوبة ، ورجل يُسارع في الخيرات».
Sarkin Muminai Ali (a.s) ya ce: babu alheri cikin duniya sai ga mutane biyu: mutumin da ya aikata zunubi yana riskar da shi da tuba, da kuma mutumin da yake gaggauta ayyukan alheri.
10 ـ «وفي خبر آخر : «رجل يزداد كل يوم إحساناً، ورجل يتدارک سيئته بالتوبة».
ya zo cikin wani hadisi: mutumin da
yake karuwa da yin ihsani a kowacce rana, da kuma mutumin da yajke riskar
laifinsa da tuba.
Ba a boye yake ba kyawawan fikirori da tunani na taka gudammawa cikin nishadin mutum da farin cikinsa, suna bashi galaba kan matsaloli da tsanance-tsanance da debe tsammani da kasala da ragwanci da kosawa, daga nan kuma zaka same shi yana gaggauta ayyukan alheri da ayyuka nagargaru masu bada nasara, haka kishiyarsu suke, hakika duk wanda fikirori mara kyawu sukayi galaba kansa lallai take zaka samu ya fadi ya samu rashin nasara a rayuwarsa zai kamu da nau'ukan cututtukan ruhi da gangar jiki da hankali, kamar yanda haka yake tabbace a ilimin sanin halayyar `dan Adam na zamani, ka sabunta rayuwarka da tunani da fikira mai kyau tare da dukufa da yin aiki har ta kai g aka samu nasara da rabauta, Allah ne mai taimako.