■ Alheri da Sharri cikin rubutu
■ Fasali na (1)
■ Dayantacciyar halitta
■ Dabi'ar halin sharri cikin mutum
■ Alheri a luggance da Isdilahi
■ Ayoyin Alheri cikin Kur'ani Mai girma
■ Mafhumin alheri da misdakansa
■ Tafisirin alheri da kashe-kashensa daga kassi da Ammi daga cikin daidaiku da jama'a
■ Kebantaccen alheri daidaiku
■ Gamammen alheri na zamantakewa
■ Sirri cikin alheri da sharri
■ Ma'anonin da alheri yake da shi cikin Kur'ani mai girma
■ Mutane ma'abota alheri
■ Mafi alherin cikin Muminai
■ Alheri daga cikin Kur'ani Mai girma
■ Fasali na biyu
■ Gaggawa zuwa ga ayyukan alheri
■ Fasali na uku
■ Alheri da sharri a wurin Majusawa
■ Alheri daga mahangar malaman Aklak
■ Fasali na hudu
■ Sharri (Kulli tashkiki) wani abune gamamme da yake banbantuwa da juna
■ Alheri da sharri karkashin hasken Nahajul Balaga
■ Alheri shine wazirin hankali sharri wazirin jahilci
- KIBIYOYIN RADDI KAN WUYAN WAHABIYAWA
- CIKIN HALLARAR ALHERI
- HUJJOJIN HALASCIN YIN TAKIYYA A MUSLUNCI DAGA MAHANGAR MANYAN MALAMAI GUDA BIYU
- FARKAR DA MAI BACCI CIKIN TABBATUWAR GANIN IMAM KA'IM A.S
- ALAMOMIN ANNABI CIIKIN KUR'ANI MAI GIRMA
- HAKURI DA FUSHI
- Bada'u tsakanin hakika da kagen makiya
- FALALAR DAREN LAILATUL KADRI
- WAHABIYANCI A TSAKANIN GUDUMA DA
- HASKEN SASANNI CIKIN SANIN ARZIKI
- AQIDUN MUMINAI
- FATIMA TAGAR HASKAYE
- SIRRIKAN AIKIN HAJJI DA ZIYARA
- TARBIYYAR IYALI A MAHANGAR ALKUR'ANI DA AHLULBAITI
Alheri da Sharri daga mahangar ilimin Kalam da Falsafa
Hakika matsalolin alheri da sharri suna daga mafi muhimmancin mas'alolin cikin ilimin Kalam da Falsafa tare da sassabawar mashayarsu da madogaransu, masana Falsafa daga Masha'iyun da Ishrakiyunda Rawwakiyun, haka zalika daga tsofaffin masana Falsafa kamar misalin Sakarad da Afladon da Arasto da wadanda suka zo daga bayansu da ma na wannan zamani dukkaninsu sun himmatu da wannan mas'ala himmatuwa mai girma, tsawon zamunnuka da suka gabata sun bada gudummawa ga al'umma ta hanyat gabatar da kyawawan fikirori da tunani, sun sassaba cikin bayanin menene alheri da sharri kamar yanda zaka samu hakan cikin Kamus din Falsafa, sai dai cewa ta'arifi na farko-farko yake nuni da ishara cikin zawiyyar Falsafa shi ne ta'arifin Shaikul Ra'is Ibn Sina.
Hakika Ibn SIna yayi ishara zuwa ga cewa alheri shi ne maksudi da zati shi kuma sharri bijirowa yake, kamar yanda dukkanin abin da yake cikin wannan duniyar ya samu ne sabida alheri sabida wata manufa shi ne abin da ake kira da (Illa Ga'iyya).
Matsalolin sharri da alheri ana la'akari da su matsaloli na farko-farko cikin hankali mutum, bahasi kansu bai tsaya kan wani ayyanannen zamani ba ko wasu al'umma ko wata ayyananniyar Falsafa ba ko kuma hatta addini da mazhaba, lallai wannan bahasin bai ta'allaka da ilimin bayan dabi'a ba (metaphysics) bari da bahasi ne da yake da alaka da rayuwa ta halittun zahiri da dabi'a, kowa da kowa a kowanne zamani yana neman alheri yana kuma nesantar sharri.
Rayuwarmu ta yau tare da dukkanin matsalolinta da yake-yake da rashin doka da oda da tozartar kyawawan dabi'u da abin da mutumin wannan zamani yake shan radadinsa daga matsalolin ruhi da na zahiri mafi cikin dukkanin na cikin komawa zuwa ga dayantacciyar halittar Allah da riko da koyarwar adddini da aiki da shari'ar Allah a doran kasa, hakika makarantun zamani sun shelanta gazawarsu cikin samarwa da mutum farin ciki da kwanciyar hankali da amintar da shi daga sharri.
Hakika wannan duniyar da muke rayuwa cikinta wurine mai kyau da daukar hankali, lallai ya gangaro daga Allah ubangijin kyawu wanda yake kunar kyawu, shi kyawu ne cikin kowanne abu babu abin da yake gangarowa daga gare shi sai kyawu, kowanne abu cikin samuwa an tsara su cikin surori da shakalai, cikinsu akwai alheri da kamala da suke kebantarsa, cikinsu akwai darajoji da suka dace da samuwarsa da kamalarsa.
Wannan baya nufin rashin samuwar sahrri cikin duniya, bari dai Malam Farabi yana cewa: (dukkanin al'amuran cikin duniya da halayen mutum masu yawa cikinsa su mabanbanta ne, daga cikinsu akwai alheri da sharri)
Ibn Sina ya ce: ana kiran sharri da wannan tawaya wacce take misalin jahilci da rauni da jirkita cikin dabi'a, ana cewa sharri misalin radadi ne da bakin ciki, haka ana kiran miyagun ayyuka da sharri, haka ana kiransa da sharri sakamakon bubbugowarsa daga dabi'a da wasunsu.
Cikin ta'arifin menene alheri yana cewa: alheri shi ne abin da kowa yake shaukinsa, samuwarsa take cika da shi, shi alheri shi ne kamalar samuwa cikin kowacce halitta wani yanki daga samuwa tana tabbatuwa cikinsa yanki ne da yake daidai da yankin da yake d ashi cikin kamala da alheri, kowacce halitta da take da samuwa alheri ce, tan sassabawa da sabawar mikdarin samuwarta da riskarta ga wannan samuwa.
Ba a boye yake ba lallai daga siffofin Allah matsarkaki madaukaki akwai siffar (alheri) kamar yanda ya zo cikin littafin Tajridul I'tikad) na Allama Kajo Nasiriddini Dusi.
Allama Hilli cikin sharhinnsa ya ce: wajabcin samuwa yana shiryarwa kan tabbatuwar siffar alheri ga Allah ta'ala, sabida shi alheri magana ce kan samuwa shi kuma sharri magana ce kan rashin kamalar abu daga fuskar abin da ya cancance shi, shi ko wajibul wujud ba zai taba yiwuwa ya tawaya daga wani abu daga kamala ba, kwata sharri baya bijira zuwa gare shi ba ta kowacce irin fuska, shi ubangiji tsantsar alheri ne, maganar Allama ta kare.
Ina cewa: hakika masana Falsafa da malaman Kalam sun gangara kan bahasin alheri da sharri a wasu `yan wurare, daga cikinsu akwai abin da ya ta'allaka da siffofin ubangiji –kamar yanda bayani ya gabata lallai shi Allah shi alheri ne tsantsa babu sharri cikinsa babu cikin zatinsa babu cikin siffofinsa da ayyukansa, baya aikata sharri baya aikata mummuna duk da cewa yanada cikakken iko kansa.
Cikin ta'arifin alheri a mahangar Falsafa: shi alheri
yana daga samuwa, shi ko sharri yana daga abubuwan da basu da samuwa, bayanin
haka na cikin buga misali: da ace Zaidu zai kashe Amru da Takobi, zai zamana ya
aikata laifi da sharri idan ya kashe shi bisa zalunci, sabida haka menene
sharri cikin kashe Amru.
lallai samuwar Zaidu a kankin kanta
alheri ne, iko da karfinsa duk daga alheri suke, samuwar Amru alheri ne haka
samuwa tausassan wuyansa alheri ne, duka alheri ne, to ina sharri?
Shi alheri yana lazimtar samuwa, idan Allah ya kasance wajibul wujud ga zatinsa sabida zatinsa to lallai shi tsantsar alheri ne kuma alheri tsantsa, shi ne manufar dukkanin haduffa sababin dukkanin sabubba haske dukkanin haske, shi ne alheri mafi girma mafi cika mafi kammala wanda kowa ke nufinsa, babu wani abu face yana tasbihi da godewa ubangijinsa, yana tasbihi a duniyar samuwa domin koma ga ubangijinsa , dukkanin halittu suna da wani mikdari daga alheri, dukkanin kasantattu suna shaukinsa, ita samuwa na nufion alheri alheri na nufi samuwa, dukkanin halittu ko da cewa samuwarsu a kankin kansu sharri ne sai dai cewa tare da la'akari da nizamul Ammi da gamammen alheri suna kasancewa alheri, dukkanin samamme wanda shi ne zatin da samuwa ta tabbata a gaershi-yana motsi da shaukin halittarsa domin samun kamalar sauwarsa.
Ya zo cikin littafin (Jami'ul Ashrarar wa Manba'il Anwari) wallafar Assayidul Haidari Amuli sh 603 cikin bahasin Yakini da kasashi zuwa kashi uku: Ilmul yakini, Ainul yakini, Hakkul Yakini, ya ce: shi ilimul yakin shi ne abin da ya kasance da sharadin dalili, shi kuma ainul yakini shi ne wanda ya kasance da hukuncin bayani, shi ko hakkul yakin shi ne wanda yake daga siffatawar idanuwa, ilmul yakin ya kebanci ma'abota manyan hankula ma'ana hankula da suka samu goyon baya daga Allah, misalin fadin ma'abota hikima ta ubangiji masu tsinkaya kan hakikanin abububwa a yanda suke kansa wadanda Allah ya kebance su da alheri mai tarin yawa cikin fadinsa madaukaki:
(يُؤتِي الْحِكْمَةَ مَن يَشَاءوَمَن يُؤْتَ الْحِكْمَةَ فَقَدْ أُوتِيَ خَيْراً كَثِيراً)
Yana bada hikima ga wanda ya so lallai duk wanda aka baiwa hikima tabbas an bashi alheri mai tarin yawa.
Alheri mai yawa shie ilimummuka da tsinkaye kan sirri kaddara da ta so daga hikimar ubangiji kebantacciya ga ma'bota hikima na ubangiji bawai masana falsafa da suke nesa daga barinta ba.
Ainul yakin ya kebantu da Malamai masana ilimummukan hakika ta gado daga ubangiji wacce bayaninta ya gabata daga ilimin Annabawa da Manzanni da ta zo musu daga wahayi da ilhama da kashafi, wacce ta isa hannun wadanda suke bayansu ta hanyar gado sakamakon fadinsa (s.a.w) Malamai sune magada Annabawa)
Hakkul yakin ya kebantu da ma'abota ma'arifa ma'ana Annabawa da Waliyyai da kammalallu wadanda suka samu sanin Allah da sauran abubuwa kamar yanda suke ta hanyar kashafi da musahada da zauki da fana'i da makamantansu, maganarsa ta zo karshe.
Wannan duka yar takaitacciyar ishara cikin sanin alheri da sharri daga mahangar masana falsafa da hikima Arifai. Sai ka lura.