فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها

Alheri da sharri a wurin Majusawa

Daga cikin sanannun addinai wanda har yanzu akwai sauarn mabiyansa akwai addini Majusawa wadanda suka bautawa wuta, tsakanin Majusawa da Sa'ibawa masu bautar taurari akwai kamanceceniya da juna ta fuskanin akidarsu kan haske da duhu, addinin Majusawa yana komawa zuwa ga imani da biyuntar da ubangiji, ubangiji haske da ubangijin duhu.

A wurinsu dukkanin alheri yana bubbugowa ne daga haske, sannan dukkanin sharri yana gangarowa na daga duhu.

Kairn bayani kan haka: lallai shi duhu tsiyata ne da rashin albarka cikin wannan duniya da muke rayuwa akwai alheri da sharri da amfani da mutuwa da rayuwa da talauci duka cikinta, babu ko kwanto kan cewa talauci da jahilci da sabo dukkaninsu daga sharri suka gangaro, sannan ilimi da rayuwa da wadata dukkaninsu sun bubbugo daga alheri , kuma kamar yanda muke ganin haske haka muke haduwa da duhu, shi haske alheri shiko duhu sharri ne, kamar aynda dare yake unwanin sharri sakamakon afkuwar sharruka cikinsa daga barayi da aikata laifuka da yada barna daga barayin kan hanya da yaduwar cututtuka da sauransu, duhu sharri ne haske alheri ne, muslunci ya zo da littafi mai tsarki Kur'ani mai girma yana bayanin hakika kan cewa shi haske da duhu da dare da rana dukkaninsu daga halittun Allah suke kamar yanda hakan ya zo cikin farko suratu An'am tare da abind ata kunsa daga kissar Annabi Ibrahim masoyin Allah daga labarin ruguza gumaka da kore bautar taurari.

Allah ya cancanci yabo ya halicci haske da duhu, hakika tushen alheri shi ne wanda ya aikata shi, amma sharri yana nan a ruhin mutum, babu wata magana cewa wai alheri yana da ubangiji wai sharri yana da ubangiji mai cin gashin kansa kuma wai tsakaninsu akwai gaba da kiyayya, kuma wai ibada taba karkata zuwa ga ubangijin alheri domin ta taimaka masa kan ubangijin sharri, duk zancen banza ne, Allah ne ya halicci rayuwa da mutuwa domin ya jarrabaku wanene yafi kyautata aiki cikinku, ya sanya duhu da haske sakamakon kasancewa abubuwa na larura domin kamalar mutum da farin cikinsa, lallai kamar yanda ya cancanci yabo kan lafiya da radadi da ciwo, idan ya zama tilas aji radadin ciwon hakori, sai dai cewa bayansa akwai wasu ni'imomi masu tarin yaw cikin gwanance halittar jijiyoyi mikakku daga kwakwalwa zuwa farfajiyar da take tsakanin dadashi da hakori, hakama cikin sauran cututtuka lallai Allah yana da sojoji a sama da kasa, hakika misalin cutar zazzabi ni'ima ce ba azaba ba, domin an halicceta ne domin lafiyar jikinmu.

Baki dayan duhu da haske da sharri da alheri suna taimakawa cikin rayuwarmu da kamalarmu, radadinmu ya kasance ne domin faranta mana bawai don tsiyatamu ba, mutumin wannan zamani yana iya fahimtar ni'imar da take cikin radadi da sharri  da duhu da haske, kamar yanda yake iya fahima da gane dadi da alheri da haske, maganar ubangiji biyu ta samo asali ne daga jahiltar hakikanin abubuwa.