b Alheri daga mahangar malaman Aklak - CIKIN HALLARAR ALHERI
فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها

Alheri daga mahangar malaman Aklak

Hakika nafsul din mutum da tsarkake ta ne da yi mata ado da kyawawan dabi'u da kuma taceta da siffofin masu kyawu hakikanin maudu'i cikin ilimin Aklak.

Sannan ita nafsul din mutum tana da karfi daban daban da suke kokawa da juna, kowanne yana son ya ga yana ruike da ragama da linzami, ya zama dole a dawo da ita zuwa daidaita, shi ne tattare alheri baki dayansa, kamar yanda zalunci da yake kishiyantarsa wanda yake tattare migaun dabi'u da sharri yake.

Adalci: shi ne tattaro dukkanin falaloli baki dayansu ba tare da takaituw akan guda daya ban da daya, bai buya ba cewa abin da ya sanya adalci ya tattare dukkanin alheri sakamakon dukkanin falaloli da miyagun dabi'u haka zalika zantuka da ayyuka akidaice suke cikin mutum daga abubuwa guda uku sune:

1-karfin hankali na furuci.

2-karfin sha'awa na halittar dabbantaka.

3-karfin fushi.

Shi rai yana karkata ne zuwa ga takaita da wuce gona da iri, sai miyagun dabi'u su kasance, lallai cikin wuce iyaka a karfin hankali ana kiransa da (Jarbazatu) sannan takaitawa ana kiransa da (Balhu) wuce iyaka cikin sha'awa ana kiransa (Fujur) takaitawa kuma ana kiransa da (Jumudi) wuce iyaka cikin fushi ana kiransa (Tahawwur) sannan takaitawa ana kiranta da (Jubunan) mataki na tsakiya shi ne Adalci, cikin na farko ana kiransa da (Hikma) na biyu kuma (Iffa) cikin na uku ana kiransa (Shaja'atu), dukkanin rabe-raben guda tara an zuba su cikin karfi guda uku kowanne guda yana kaso uku, falaloli wanda suke na tsakiya suna da kaso uku, daga wannan ne fadin Manzon Allah (s.a.w) ya zo cikin hadisi mai daraja:  

«خير الأُمور أوسطها»[1] .

Mafi alherin al'amura tsakatsakinsu.

Miyagun halaye suna karkatattun geffa daga tsakatsaki, ana kirga wadannan geffa guda shida tsakanin wuce iyaka ga takaitawa daga manyan jagaban dukkanin miyagun dabi'u wanda sune: Fajirci da jayayya, da dimauta da ragwanci wadanda sune jarbaza da balhu, kamar yanda abubuwa uku sune jagaban falaloli: hikima kamewa da jarumta, wanda ya tattaro su kuwa shi ne adalci, dukkanin alheri yanb cikin adalci babu banbanci cikin daidaiku ne ko cikin jama'a, mutum Adali yana kasancewa daga mafifita, kamar yanda jama'a Adala suke kasancewa daga misdakin gamammen alheri da kowa yake nemansa.